Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Tsinin Harshe Ya Fi Na Mashi by Sadik Abubakar

Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

“Na tabbatar da ke Jummai ta yi wa shaƙar da ta yi mini, da yanzu ba wannan maganar muke ba. Wataƙila da kina can gari me arhar gyaɗa.”

“Zainab! Har kullum ina raba ki da irin waɗannan zantuka marasa kangado, za ki ɗaure kanki da kanki fa! Zargin maita da kike gani wuya ne da shi. Ki iya bakinki, ni kin ma kore ni bari na koma gidana da ma cewa na yi bari na zo mu yi hira.”

“Ai ku ba son a faɗi gaskiya kuke ba, amma waye bai san halin Jummai ba. Tani ma da tsohon cikinta haka matsiyaciyar matar nan ta
riƙa wahalar da ita, da kyar ta samu ta rabu da cikin lafiya.”

“Sai an jima kin ji.” Hafsat ta faɗa tare miƙewa ta fice abinta.

“Allah Ya raka taki gona, ki fi ruwa gudu ma. Ke ni fa, ke ma ɗin nan, don dai mun haɗa jini da ke ne da sai na ce ko ‘yar uwar ɗayar ce.”

*****
Zainab kenan da Hafsat ‘yar wan babanta. Tana zargin wata makwabciyarsu da maita. Kuma ta yaɗa zargin har cikin matan unguwar tasu sun fara yarda cewa Jumman mayya ce. Unguwar dai ta kasance ta yaran mata ce, wato mafiya yawan mazauna unguwar ba manya ba ne amare ne da waɗanda ba su haura shekara biyar da aure ba.

Ita dai wannan baiwar Allah da ake wa sharrin cewa mayya ce har ta lashi wasu a unguwar, ta kasance irin mutanen nan ne marasa son magana sannan ba ta da son shiga jama’a, shiru-shiru ce babu ruwanta da jama’a. Wannan dalili da wata sifa tata, wato tana da idanu ƙwala-ƙwala ga su jajir tamkar gautan da ya shekara a rana, su ne suka sa mutanen unguwar tasu ke yi mata wannan ƙazafin.

Sun jima suna mata wannan zargi, tun ba ta sani har ta sani; tun ba ta kulawa har ta fara jin haushin abin. Yanzu har ta kai ta kawo waɗanda ba ‘yan unguwar ba ma sun sani.

Watarana a gidan wani suna da aka yi a nan unguwar tasu, mata sun taru an cika gidan fal ana ta shagali, masu kai da kawon raba abinci na yi, masu zaman gulma na yi. Babu irin nau’in gungu na mata da babu a gidan, Zainab da ‘yar uwarta Hafsat da wasu kawayensu na zaune suna cin abinci sai ga Jummai nan ta leƙo ta taya mai jego murna haɗe da yi mata barka. Ɗago kan da Zainab za ta yi ta hangi Jummai na shigowa, daidai lokacin ta zuba lomar shinkafa a bakinta, ai ko kamar an saka injin buga iska an huro shinkafar nan, fesh, ta feshe abokan cin abincin, ta kama wani tari na munafurci tana dafe ƙirji.

“Kai Zainab mene ne haka kuma? Kamar ƙaramar yarinya ana cin abinci ki yi wannan ɗanyen aiki?”
Hafsat ce ta faɗi wannan maganar.

Yayin da Zainab ta riƙa kakarin amai na ƙarya ta ce, “Ku yi mini uzuri don Allah ba yin kaina ba ne, masu ciki biyu ne suka iso ku ma ku yi ta kanku.”

“Ba mu gane masu ciki biyu ba? Wacece mayya kuma da ta shigo har ta kama ki haka?”

Da wutsiyar ido Zainab ta nuna Jummai, wacce ta sha alwashin yau dai sai ta tanka wa Zainab ɗin dangane da jakar tsabar da take ƙoƙarin rataya mata, kaji su bi ta suna tsattsaga. Gabaɗaya mutanen da ke wajen suka jiyo da kallon mamaki ga Jummai, ƙarasawa ta yi tana cewa, “Yau sai kin nuna mini maitar da kike zargina ko kuma ki fito da wanda na taɓa ci. Na gaji da wannan renin wayon naki, ni ba shiga sabgarki nake ba. Ke ba ke ba shashasha ma, waɗanda suka fi ki nutsuwa ma ba shigar harkarsu nake ba. Don haka wallahi yau ɗin kin yi na farko kin yi na ƙarshe, ba sharrin maita ba kowanne irin sharri ne kin daina yin sa, za a koya miki yadda rayuwar duniya take.”

A fusace Zainab ta miƙe tsaye tare da hayayyaƙo wa Jummai tamkar za ta haɗiye ta tana faɗin, “Ke dalla garafara can mayyar banza mayyar wofi, yo waye bai san wannan mugun halin naki ba. Ke nan har kina da bakin magana, lallai rashin kunyar taki ta gawurta. To bari ki ji, da dai kin wahalar da ni, amma yanzu ba ki isa ba kurwata ɗaci gare ta.”

“Kada ki ƙara kira na da mayya.”

A zafafe Zainab ta dangwale wa Jummai hancin tare da cewa, “An kira ki mayyar, me za ki yi, ƙarya ake yi ne?”

Kafin ka ce me ita ma jumman ta mayar mata da martanin dangwale hancin, nan fa kokawa ta kaure tsakaninsu duk da cewa sauran mutanen da ke wajen sun yi ta ba su baki akan su bari amma sun ƙi. Nan da nan gidan ya yamutse hayaniya kawai ke tashi wani baya gane abin da wani yake cewa. Jummai ta riƙe Zainab gam sai jibga take kamar Allah Ya aiko ta; da kyar mutane suka raba su. Haki kawai Zainab take, ta gaza magana ta daku sosai.

Gidan suna ya hargitse, kafin kiftawar ido masu ƙaramar zuciya har sun fara halin nasu. Cigiyar wayoyi aka fara, daga wannan ta ce ina wayata? Sai ka ji wata ma ta yi makamancin wannan tambayar. Me jego ta fito ba da haƙuri kafin ta koma an ɗauke jakar da take tara kuɗin gudummawar da abokan arziki ke kawo mata, mutum biyar aka sacewa waya a ɗan taƙin da bai wuce mintuna biyar ɗin ba.

Nan fa kiɗa ya sauya, waɗanda aka yi wa sata suka yi tsalle suka dire suka ce, Allah Ya kashe su ya rufe ba za su ɗauki ƙaddara ba, Zainab ce ta haddasa fitinar da aka yi musu satar don haka sai an fito musu da wayoyinsu. Komawar da Me jego za ta yi ɗaki ta ɗauko wayarta domin a kira wayoyin da ba a gani ba, jaka ta ce, “Ɗauke ni inda kika aje.”

A tsakar gida kuma mata ne suka yi ram da Zainab wasu na cewa, “Da haɗin bakinta aka yi musu satar, ita ta zo da ɓarayin don haka lallai ta fito musu da wayoyinsu.”

“Ke wallahi ba ki isa ba ki raina mana hankali kin ji, idan kina son hukuma ta raba mu to kada ku fito mana da wayoyinmu.”

Wata ke nan cikin waɗanda aka sha basilla. kafin ka ce kwabo, zufa ta karyo wa Zainab ta rasa wa za ta saurara bare har ta iya cewa wani abin, daga wannan ta rufe bakinta sai wata ta ɗora, haka dai ake ta yi mata gayyar haƙori.

“Tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa kan doka.”

Hafsat ta faɗa daidai lokacin da Me jego ta fito daga ɗakin tana sallallami, “Me ya faru Fatima?”

Wata cikin matan ta tambaya a kiɗeme, yayin da sauran jama’a suka watso hajjar mujiyarsu kan Fatima, wato Me jego.

“Ku taku satar me sauƙi ce, ni gabaɗaya an ɗauke mini jakar, wayata da kuɗin Abban Ilham dubu ɗari biyar (₦500,000) a ciki da ya ba ni na ajiye masa ranar Litinin zai karɓa.”

“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!”

Mafi yawan matan suka furta cikin sigar razani haɗe da zaro idanu, wata ta ɗora da cewa, “A garƙame gidan nan kawai babu wacce za ta fita sai an caje ta tsaf har ɗan kanfai.”

“E, haka za a yi, haka za a yi.” Suka faɗa a tare, sai dai kash! Kafin tunanin hakan ya zo, tuni wasu mata biyu da ba me iya tantace su suka yi layar zana daga gida n. Wata cikin matan ta ce, “Babu wani caje da za mu tsaya yi mu ɓata wa kanmu lokaci, ga wacce ta zo da ɓarayin nan.” Ta nuna Zainab haɗe da wani irin mugun kallo tamkar ta kashe ta, sannan ta ci gaba da cewa, “Ni caji ofis kawai zan je ɗauko mata Ɗansanda, wallahi sai an biya ni wayata. Ko wata guda ba ta yi ba, Abban Islam ya sayo mini kuma ya gargaɗe ni akan ko gilashin ne ya fashe sai raina ya ɓaci, bare kuma na ce masa an sace. Sam ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa.”

Tana faɗa ta fice, ta nufi wani ɗan ƙaramin caji ofis da ke kusa da gidan sunan, ta shiga kai tsaye ta nufi kan kanta ta yi ƙorafin cewa ta kawo ƙarar zargin wata mata ta yi sanadin sace mata waya, ba ita kaɗai ba har da wasu. Nan take aka hada ta da ‘Yansanda biyu, mace da namiji. Suna zuwa, sauran matan suka ce “Kin yi daidai wallahi gara da kika kawo hukuma, domin an caje kowa ba a ga koda waya ɗaya ba. Su hukuma sun san yadda za su ɓullo wa lamarin.”

“Ya isa haka, ya isa.” Jami’ar ‘yarsandar ta faɗa tare da duban wacce ta kai ƙarar ta ce, “Wace ce ake zargi da tayar da hatsaniyar?”

Ta nuna Zainab, tare da cewa, “Ga ta nan ranki yadaɗe.”

Zainab tuni ido ya raina fata,  ta yi tsuru-tsuru da ita, yau fa ake yin ta, lallai baki shi ke yanka wuya. Allura ta tono garma. “Baiwar Allah ɗauki mayafinki mu je.”

‘Yarsanda ta faɗa, sai yanzu ne zai ta buɗa baki ta ce, “Don Allah ki yi haƙuri, ni wallahi babu ruwana, da wannan muke rigima ne.”

Zainab ta faɗa tare da nuna Jummai, ‘yarsandar ta ce, “Idan mun je can za ki yi bayanin komai.”

Nan dai aka tisa ƙeyar Zainab zuwa ofishin ‘yansandan, sauran waɗanda aka yi wa satar da me jegon su ma suka rankaya gabaɗaya domin neman hakkinsu. Suna isa aka rubuta jawabi duk yadda aka yi. Dayake ƙaramin ofishin ‘yansanda ne, me mukamin DCO ne ke shugabantar wajen, shi ne kuma ya karɓi ƙorafin. Bayan ya ji ta bakin masu korafin sai ya dubi Zainab ya ce, “Garin ya haka ta faru? Ina kayan da ake zarginki da su?”

“Yallaɓai, ni wallahi ban san komai ba game da wayoyinsu, hasalima ma ni a gefe guda nake. Cacar ba ki muka yi da wata kawai shi ne suka fara cigiyar wayoyin.”

“Da ma ba su ce ke kika dauka da hannunki ba amma suna zargin kin haɗa baki da wasu, yayin da kika tada hatsaniyar ke da waccan matar, su kuma suka yi hauzi da wayoyin.”

Me jego ta ce, “Ranka yadaɗe, ba fa wayoyi kawai aka sace ba, har da jakata akwai kuɗin megidana dubu dari biyar (₦500,000) a ciki da wayata duka an yi gaba da su.”

Yallaɓai ya jinjina kai alamar al’amarin babba ne, nisawa ya yi sannan ya ce, “Za mu tsare wacce ake zargi mu faɗaɗa bincike domin a yi wa kowa adalci, kafin nan kowacce ta zo da megidanta ke ma wacce ake zargi za ki kira megidanki ko mahaifinki ko yayanki.”

BAYAN MAGARIBA

A ɗan taƙin da ke tsakanin Magariba da Isha dukkan mazajen waɗannan mata suka dawo daga wajen neman na Masara, ita kuwa Zainab da ma tun tuni mahaifiyarta ta je ofishin ‘yansandan bayan da ‘yar uwarta Hafsat ta sanar da labarin. To sai dai duk da zuwan mahaifiyar tata ba a sake ta ba sakamakon masu ƙorafin suna gida, don haka ita ma sai DCOn ya ce ta koma sai lokacin da sauran masu ƙorafin suka dawo za a ci gaba da sauraren ƙarar.

To mutum biyu daga cikin mazajen matan ƙin zuwa ofishin ‘yansandan suka yi, guda ya ce, ba zai je ko’ina ba kuma ba sake saya wa matar waya ba, da ma ba wannan ne karo na farko ba da ta saba yin wasarairai da wayar ana sacewa. Don haka ta saya da kuɗinta. Gudan kuwa cewa ya yi, shi kenan ya yafe wa duk ma wacce ta ɗauka, indai waya ce zai saya wa matar wata.

Mijin me jego da aka fi targaɗawa da sauran mazan da ba za su haƙura ba, su suka halarci ofishin ‘yansandan, bayan an sake bayanin yadda abin ya kasance, Zainab ba ta musa ba, a nan mahaifiyarta ta rufe ta da faɗa, babban yayanta ma sai fadan yake mata. Yallaɓan ya ce, “A iya abin da bincike ya nuna, ba a samu fara cigiyar wayoyin ba sai da Zainab ta tayar da hatsaniya tsakaninta da wacce take wa zargin maita, don haka a nan dole ta ɗauki alhakin biyan mutane dukiyoyinsu idan ba su yafe ba.”

“Zargin maita?” Mahaifiyar Zainab ta fada cikin sigar mamaki hade da zaro idanu, kafin ta ci gaba da magana mijin Zainab ɗin ya karɓe zancen da cewa, “Wallahi Umma na yi fama da ita akan ta iya bakinta, abin duk da ba ka da hujja akansa to wuyar sha’anin ne da shi, amma ba ta ji.”

A fusace Umman ta dubi Zainab da wata harara me cike da tuhuma ta ce, “Uban wa kike wa sharrin maita? Allah wadaranki Zainab!”

DCOn ya katse ta da cewa, “Ya isa Baba, ki daina furta mata irin waɗannan kalamai, tabbas za su yi tasiri a jikinta, addu’a za ku ci gaba da yi mata. Yaran zamani sai haƙuri idan muka ce za mu biye ta halinsu sai su sa mu yi musu abin da ko ƙuda ma ba zai raɓe su ba. Allah Ya shirya mana su kawai.”

Gabaɗaya suka amsa da, “Amin.”

Ya sake juyawa ga masu ƙorafi, ya ce, “To kun ga abin da ya kasance.”

Mutum ɗaya ya ce shi ya yafe Allah Ya kiyaye gaba, saura mutum biyu da kuma mijin me jego. Babban yayan Zainab ya ce zai biya naira dubu ɗari biyar ɗin da ke cikin jakar me jego da wayarta iPhone4S. Haka mijin nata shi ma ba yadda ya iya ya ɗauki gabaran biyan kuɗin wayoyi biyu. Daga karshe DCO ya yi wa Zainab cikakken gargaɗi da jan kunnen akan matuƙar aka sake kawo ƙarar ta da irin wannan ƙorafi na sata, to sai ya tura ta kotu kuma daga can gidan gyaran hali za a tisa ƙeyarta.

Kwana daya tak! Da faruwar wannan abu, Jummai ta yankowa Zainab sammaci a kotu. Ta yi ƙarar ta ne akan tana laƙa mata sharrin maita. Bayan da mijinta ya dawo ya samu labarin hakan, nan take ya yi mata saki ɗaya sannan ya ce, shi babu ruwansa ba zai iya da ita ba. Ya yi bakin ƙoƙarinsa ya ga ji.

Masifu goma da ashirin sun kewaye Zainab, ita kanta ta yi nadamar furta wa Jummai kalmar maita, idonta ya raina fata, cikin ‘yan kwanaki ƙalilan ta rame ta yi baƙi. Ta rasa farinciki da walwala, ita kanta yanzu haushin kanta take ji. Ga aurenta ya mutu ga sammacin kotu wanda ba ta da kalma ɗaya da za ta iya kare kanta da ita.

“Na shiga uku! Wai mene ne yake samu na haka? Allah na tuba ka yafe mini kurakuraina.”

Ta furta cikin sassanyar murya, wasu hawayen nadama na tsere bisa kuncinta. Hafsat da ke kusa da ita ta ce, “AlhamduLillah! Tunda har kin gano kin yi kuskure kina roƙon Ubangiji Ya yafe miki, haka ake so dama. Lokacin da idonki ya rufe babu irin hakaito miki da wannan yanayi da kika jefa kanki a ciki da ban yi ba, amma sai kika biye wa ruɗin shaiɗan da son zuciyarki, kika saka auduga kika toshe kunnenki.  Don haka yanzu shawarar da zan ba ki idan an je kotu gobe, ki amsa laifinki da wuri, ki ce sharrin shaiɗan ne kina neman afuwar kotu.”

“To shi kenan na gode sosai, kuma don Allah ke ma ki yafe mini duk rashin kunyar da na yi miki, wallahi ba a hayyacina na yi ba.”

“Ki daina kuka, ba komai Allah Ya yafe mana gabaɗaya.”

“Anty Hafsat, yanzu Auwal haka zai yi mini don ya ga ina son sa?” Ta furta tana sake fashewa da kuka, rungume ta Hafsat ɗin ta yi tana cewa, “Gaskiya Auwal ya yi haƙuri da ke, ba kowanne namiji ba ne zai iya haƙuri da irin halinki, kina yawan janyo fitintunu, ba wannan ne karon farko ba. Don haka ki yi haƙuri har ya huce, ransa ne ya ɓaci amma shi ma yana son ki sosai, rashin nutsuwarki ce dai ta ja miki. Ki bari ya sakko tukunna ni zan yi masa magana.”

Washegari aka shiga kotu, bayan magatakarda ya karanto ƙarar da Jummai ta shigar bisa sharrin da Zainab take mata na maita, sai Maishari’a ya buƙaci mai ƙara da wacce ake ƙara da su fito su tsaya a ɗan kawayen da ake tsayawa yayin kare kai ko ba da hujja.

Maishari’a ya dubi Zainab ya ce, “Malama Zainabu, Malama Jummai na ƙarar ki bisa zargin kina yi mata sharrin maita, shin ko za ki iya yi wa kotu bayanin abin da kike da’awa tare da kawo gamsassun hujjoji?”

Cikin rawar murya Zainab ta ce, “Allah Ya gafarta Malam, wallahi sharrin shaiɗan ne, ni ba ma sosai muke mu’amala da ita ba. Ina roƙon wannan kotu me adalci da ta yi mini afuwa ba zan sake kwatanta irin wannan maganar ga kowa ba.”

Maishari’a ya ɗan yi shiru yana nazarin korafin da zantukan da Zainab ta yi, wato neman fitina ne kawai irin na wasu matan, ƙage ne da ƙazafi kawai. Ya ɗan gyara zaman tabaransa ya dubi Zainab ya ce, “Suka irin na harshe yana shiga da zurfi kuma yana da tasiri matsananci da ke tsayawa a zuciya. Suka irin na mashi yana iya warkewa, amma suka irin na harshe ba ya warkewa.
Harshe na’ura ne na sarrafa magana da fasaha kuma shi  ke fassara abin da ke zuciya, siffarsa ɗan ƙarami ne amma sukarsa na da girman biyayya gare shi. Abu ne mai girma da laifinsa, da shi ne kafurci ke bayyana ko imani. Wanda kuma su ɗin nan su ne maƙura na ɗa’a da saɓo, yana da fage mai faɗi a alheri, kamar yadda yake da da makamancinsa wurin girma na sharri. Da shi ne ake yaɗa tuhume-tuhume ake kuma ƙazafi ga mata katangaggu muminai, da harshe ne fitintinu da rikece-rikece ke aukuwa. Haka nan da shi ne ɓoyayyun abubuwa ke bayyana. Kuma da shi ne ake halatta abubuwa masu alfarma, kuma ake shuka fitintinu da gaba da baƙin ciki da hasara cikin zukata. Har ila yau da shi ne kuma ake zagi kuma ake yafuce ake annamimanci, kuma da zunɗe, da yaɗa jita-jita kuma da tsinuwa da cin nama da alfasha da kuma maganar banza, da batsa da suka. Harshe ba ya gajiya da motsi, kuma ba ya raguwa saboda magana, amma kuma duk da haka abu ne kiyayayye, adananne, kuma za a yi wa mutum hisabi game da shi ranan da za a yi narkon azaba.

(Harshe ba ya furta wata magana face a like da shi akwai mai tsaro halartacce)

(Watarana Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rike harshensa sai ya ce: “Ya Mu’az ka kiyayi wannan! Sai Mu’az ya ce: Wai shin ana kama mu da abin da muke furtawa? sai Annabi ya ce: Mahaifiyarka ta yi wabinka ya kai Mu’az! Shin akwai abin da yake kifar da mutane cikin wuta a bisa fuskokinsu ko hancinsu face abin da harsunansu ke girbe musu.”

Watarana Ibnu Mas’ud ya hau kan Dutsen Safa sai ya rike harshensa sai ya ce: “Ya harshe ka fadi alheri za ka samu riba, ka kame daga fadin sharri za ka kubuta tun kafin ka yi nadama. Sannan ya ce, (Na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: “Mafi yawan kurakuran dan’adam na samuwa ne daga harshensa.””

Wannan wa’azi da jan hankali da Maishari’a ya yi, ba ga iya mai laifin ya amfanar ba, duk wani mahaluki da ya kasance a kotun ya amfana da wannan wa’azi. Sai da jikin kowa ya yi sanyi sannan ya dakata, daga ƙarshe ya umarci Zainab da ta ba wa Jummai haƙuri haɗe da neman yafiyarta, alatilas ta sauke duk wani taurin kai, ta ƙasƙantar da kai ta dube ta cikin yanayin ban tausayi ta ce, “Kin yi haƙuri don Allah, ki yafe mini.”

Zainab ta ce, “Ni na yafe miki duniya da lahira, Allah Ya yafe mana gabaɗaya.”

BAYAN SATI ƊAYA

Bayan sati guda da zuwa kotu ne, sai al’amura suka fara sauya wa Zainab, zaman gidan da take yi ya fara gundurarta tun ba a je ko’ina ba. Tsangwama da tsana ta kowacce fuska, ba ga wajen mahaifinta ba bare kuma mahaifiyarta, hakan ƙananan ƙannenta suka fara raina ta, sukan faɗa mata maganar da ransu ya yi musu daɗi, ba damar ta kama su ta doka. Wannan abu ya ishe ta, rana zafi inuwa ƙuna.

Watarana sai Hafsat ta zo gidan, Zainab take faɗa mata abubuwan da take fuskanta na tsangwama daga iyayen nata. Hafsat ta yi murmushin takaici sannan ta ce, “Ke da ma kina zaton za ki samu sakin fuska kamar yadda kika samu gabanin ki bar gabansu? Ai duk macen da ta bar gaban iyayenta, to ta yi haƙuri da duk abin da ta gani a gidan miji, hakan ya fi mata gaban iyayenta nesa ba kusa, komai wahalar da take sha gidan miji ya fi gidan iyaye, bare kuma ke babu wata wahala da kike sha. Halinki ne ya janyo miki duk abin da kika gani a yau,  idanunki sun makance wa gaskiya, kunnuwanki sun kurumce wa gaskiya. Duk irin jan hankali da hatsarin da ke tattare da yi wa mutum ƙazafi ba wanda ban nuna miki ba amma kika ƙi ji, yanzu kalli yadda kika koma, kin rame kin yi baƙi kin rasa nutsuwarki gabaɗaya.”

“Anty Hafsat, na yi nadama! Don Allah ki taimaka mini, ki yi wa Auwal magana ya yi hakuri na koma gidana.”

Cikin sigar kuka me ban tausayi take maganar, Hafsat ta ce, “Ki daina kuka ki shirya gobe weekend mu je gidan tare da ke, In Sha Allahu zai haƙura.”

Washegari suka shirya kamar yadda Hafsat ta tsara, suka tafi, cikin sa’a suka iske shi. Bayan sun gaisa, Hafsat ta ɗora da cewa, “Don Allah wata alfarma ɗaya zan nema a wajenka! Auwal don girman Allah ka yi haƙuri, babu shakka ka yi haƙuri da Zainab matuƙa, duk abin da ya faru a baya ya riga ya wuce, Zainab ta yi nadama ta yi alƙawarin ba za ta sake aikata wani abu makamancin na baya ba. Na kawo ta nan ta ba ka haƙuri ne da bakinta.”

“Na ji dukkan bayananki, to AlhamduLillah! Da ma ni ba rabuwa da ita na yi ba, na yi mata hakan ne a matsayin jan kunne na ƙarshe kuma na san har in ba tana da matsalar ƙwaƙwalwa ba ne, to ba shakka za ta hankaltu da wannan jan kunne. Ke shaida ce Hafsat, duk abubuwan da Zainab take ba su cika damu na ba indai ba wani ta taɓa ba, na faɗa mata ba na son tana shiga sabgar da ba ta shafe ta ba. Saboda haka na ce za ta koma makaranta, amma fur sai ta ce ita ba ta so, kada ma na yi asarar kuɗina.”

“Au haka ma aka yi? Lallai Zainab ba ki da gaskiya, to ƙaryarki ta sha ƙarya. Makaranta kamar kin koma ne, ai ni ban san haka aka yi ba. Wato saboda su sauran kawayen naki ba su samu damar yin karatun ba shi ne ke Allah Ya ni’imta ki da wanda zai ɗauki nauyinki shi za ki watsar? Maza ki ba shi haƙuri.”

Allah Sarki! Duk tsiwa da zaƙalƙalar Zainab sun ɓace mata ɓat, ta zama abin tausayi. Rayuwa ta saita mata tunani, duniya makaranta in ji masu iya magana. Nisawa ta yi za ta fara magana, Ya katse ta da cewa, “Shi kenan babu damuwa, ba komai. Zan zo gidan anjima da yammaci.”

“To shi kenan, na gode sosai Auwal, Allah Ya saka da mafificin alkairi, Allah Ya jikan magabata. Zamu koma?”

Duk da cewa unguwar ba nesa ba ne, dubu biyu ya ba su kudin mota, sun ki karɓa amma ya matsa sai da suka karɓa.

Da yammaci kamar yadda ya alkawarta musu zai zo, hakan kuwa ya yi. Ya isa misalin karfe 5:00pm, Bayan sun gaisa da iyayen Zainab ya ce ya zo ne ya mayar da ita. Daga mahaifiyarta har mahaifinta babu wanda ya ji haushin Auwal ɗin lokacin da ta zo da takardar sakin, domin sun san matuƙar haƙuri ya yi haƙuri da Zainab. Don haka sai da suka yi mata faɗa sosai mai ratsa jiki sannan suka yi musu fatan alkairi.

Zainab ta dawo gidanta, cikin ƙanƙanen lokaci jikinta ya dawo ta gyaru sosai ta yi dumurmur da ita. Sannan kuma kamar an yi ruwa an ɗauke, ta manta da duk wasu halayenta na tsokana da rashin son zaman lafiya. Yanzu tsantsar biyayya da ƙauna take nunawa Auwal dinta, jin shi take ya fi yarima ma.

Karshe!

9 thoughts on “Tsinin Harshe Ya Fi Na Mashi”

  1. Ma Sha Allah!
    Zainab maganin masu irin halinki kenan, su dinga ƙirƙirar labarin ƙanzon kurege, suna yaɗawa daga baya kuma abu ya rincaɓe musu su rasa inda za su saka ransu, ga shi dai ita Zainab ta kasa kiyaye harshenta, ga shi nan ɓarin zance ya kai ta ya baro, Allah Ya ba mu ikon kiyaye harshenmu, amin.

    Malam Sadik muna godiya da wannan daddaɗan labari mai ɗauke da ɗumbin darusa, Allah Ya ƙara hasken ƙirji.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×