Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Tun A Duniya by Nana Aicha Hamissou

Alhaji Garba Nera tare da matansa zaune saman luntsuma-luntsuman kujerun da suke jere a tanfatsestsen falon gidansa. Kallo ɗaya za a yi masu a fahimci suna cikin yanayi maras daɗi saboda shimfiɗaɗɗar damuwar da take saman fuskokinsu, sannan babu mai cewa da ɗan’uwansa kala, sakamakon tashin hankali da suke cikin a dalilin iftila’in da ya faɗa wa Alhaji Garba a daren shekaranjiya na ƙonewar supermarket ɗinsa, don babban attajiri ne wanda sunansa ya zagaye sako da lungu na garinsu. Kafin wannan iftila’in ma ba a fi wata guda ba ‘yan fashi suka shigo gidan haɗe da ɗauke masu duk wata kaddara da suka mallaka, sai ga shi kuma sun wayi gari da labarin gobarar supermarket ɗin Alhaji Garba wanda ta ƙone kurmus kasancewar gobarar tsakar dare ne, kuma tana da alaƙa da wutar lantarki, dalilin da ya sa aka ɗau lokaci mai tsayi kafin wutar ta mutu. Wannan iftila’in ya yi matuƙar girgiza su, ba su kaɗai ba hatta mutanen gari sun girgiza matuƙa har ma wasu suka fara zargin ko da sa hannun wasu mutane cikin lamarin duba da abin da ya faru kwanakin baya.

“Assalamu alaikum! Assalamu alaikum! Assalamu alaikum!”

Muryar Jidda mai aikinsu ta ratsa massarafar sautinsu haɗe da katse masu zaman shirun da suke yi.

Maimakon amsa sallamar, sai wata razananniyar tsawa mai matuƙar firgitawa Hajiya Binta ta daka wa Jidda tana faɗin,

“Wacce irin jaka kidimahuwa ce ke? Me ya sa ba kya fahimtar yanayin mutane? Kin yi sallama fiye da ɗaya an maki banza, me ya sa ba za ki shafa wa mutane lafiya ba? Ki ɓace mana da gani ko na ci ubanki a gidan nan banza shashasha kawai!”

“Ki bi ta sannu mana, zagi ba namu ba ne mu da muke cikin wannan yanayin.”

Cewar Hajiya Salima kasancewarta mace mai sanyi sosai, saɓanin Hajiya Binta mace masifaffiya kuma halin da suke ciki ya dame ta matuƙa, saboda auren Alhaji ma da ta yi yana da alaƙa da dukiyarshi.

“Ke na jima da sanin ba ki damu da annobar da ta faɗa mana ba, tun da…”

“Ya isa haka!”

Alhaji Garba ya yi saurin katse su a ɗan tsawace, zuciyarshi tana tafarfasa, don haka bai fatan sun ƙara masa wani abu a kan wanda yake ciki.

“Alhaji Ahmad yana jira na ɗakin baƙi tun ɗazu sai na dawo.”

Ya faɗa yana mikewa tsaye

*****

“Na rasa gane me yake faruwa da ni abokina, duba ka gani asarar da na tafka cikin watannin nan.”
Alhaji Garba ya faɗa cikin rawar murya tamkar zai fashe da kuka.

Cikin kwantar da murya Alhaji Ahmad ya ce,

“Ka yi haƙuri abokina! Kowanne bawa da tasa kaddarar. Lokuta da dama Allah Yakan jarabce mu da kaddara don a gwada imaninmu, saboda haka ina so ka ɗauki wannan jarabawar a matsayin kaddara.”

“Ni fa gani nake kamar da sa hannu a wannan lamarin!”

Alhaji Garba ya faɗa hawaye suna cika mashi idanuwana kiris yake rage ya fashe da kuka.

“Haba abokina! Ya kamata ka fid da zargi a ranka, ka yi imani da Allah, sannan ka yarda da kaddara mai kyau ko akasin haka.”

Alhaji Ahmad ya faɗa yana ƙafe shi da ido. Kafin ya bar gidan sai da ya yi mashi wa’azi sosai. Amma sam Alhaji Garba bai ɗauki ko kalma guda a ciki ba, kodayake ba ma fahimtar abin da ya faɗa yake yi ba don hankalinshi yana wani waje daban.

*****

Tashin hankali wanda ba a sa mashi rana! Alhaji Garba ya tafi banki ciro kuɗi don fara wata sana’ar, sai dai abin da ya gani ya girmi tunaninsa. Babu komai cikin akawun ɗinsa, take ya suma sai da aka zuba masa ruwa ya farfaɗo yana ta sambatu rantse-rantsuwa mahaukaci sabon kamu.

Tun daga lokacin rayuwa ta fara yi wa iyalan Alhaji Garba tsanani, babban tashin hankali da suke fuskanta wani lokacin Alhaji Garba ba shi maraba da mahauci saboda magana yake shi kaɗai, sannan har kwanan gobe ya ƙi yarda da kaddara sai fama zargin mutane yake yi.

Ana haka ya ji ciwo a ƙafarsa, likita ya tabbatar da in ba a yi wa kafar aiki nan kusa ba, za ta iya lalacewa har ta taɓa lafiyar jikinsa kasancewar yana da ciwon sukari. Take Hajiya salima ta dawo gida don ta ɗauki takardun gidansa guda a sayar sai dai takardu suka ce ɗauke ni inda kika gan ni. Tara ‘ya’yansu ta yi gabaɗaya su biyar don ta ji ko sun sauya masu wuri ne, amma sai suka tabbatar mata da ba su da makullin ɗakin Alhaji, ita ɗin ma tsabar rikicewa ce irin tata don ta san ba za su yi haka ba saboda duk yara ne babbar cikinsu ma ita ce mai shekara 17. Bayan ta dawo asibiti ta tambayi Hajiya Binta, ita ɗin ma magana ɗaya ce wai ɗan wuta ya yi gulmar kafiri.

*****

Cikin kwana biyu sun nemi kuɗin aikin Alhaji amma ba su samu ba, ga shi Alhaji Ahmad ya yi tafiya zuwa kasar waje, sai Hajiya Salima ta bayar da shawarar a sayar da gidan da suke ciki, ko kaɗan Hajiya Binta ba ta so haka ba, amma babu yadda ta iya suka bazama neman masaya. Ba su sha wiya ba suka samu mai saye kuma sun yi nasarar ganin takardunsa saboda inda aka ɓoye su ɓoyayyan wuri ne.

Ba a saye gidan da daraja ba don an ga mata ne kan gaba, alfarmar sati guda wanda ya saye gidan ya yi masu su tattara su bar masa gidansa. Ba su wani damu ba don burinsu Allah Ya tashi kafaɗun Alhaji. An duba Alhaji Garba cikin ikon Allah kuma ƙafarsa ba ta lalace ba aka ɗora shi a kan magani.

Bayan sati guda kamar daga sama Alhaji Ahmad ya dawo daga tafiya, ya shiga tashin hankali matuƙa akan abin da ya taras, duk yadda ya so ya dawo masu da gidansu abun ya ci tura. Haka suka tattara kayansu suka koma wani gidan Alhaji Ahmad da zama don ranar ne wa’adin da aka ɗibar masu na barin gidan.

Ranar da aka sallamo Alhaji  Garba daga asibiti, daidai haraba inda za su hau motocinsu ya ji an kira sunansa, wata irin sarawa kansa yayi a lokacin da yayi tozali da mata da miji masu kira nasa. Kallon su yake yi babu ko kyaftawa, kafin ya fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya da gangar jiki, yana faɗuwa ƙasa tamkar ƙaramin yaro yana faɗin,

“Sulaiman kai ne? Lubna da ma kina raye? Lubna ki yafe mani abubuwan da na aikata a gare ki. Kalli yadda na koma lokaci guda, ina da yaƙinin alkahinki ne ya fara bibiya ta saboda son zuciya irin nawa, kuma ruɗin zuciya ya sa na manta da mummunan halin da na sanya ki wanda ban san yadda aka yi kika fita daga ciki ba. Don Allah ki gafarta mini kin ji ƙanwata.”

Da kallo sauran mutanen suka bi su, don ba su gane zancen ba. Lubna tana shirin magana sai Sulaiman ya tari numfashinta yana faɗin,

“Bana so ki yi magana don ina kishin muryarki, ba zan so wani ya ji ta ba, bari na ba shi amsa kin ji abar kauna.”

Sai ya ci gaba da cewa,

“Na san gabaɗayanku kuna son sanin ko mu su wane ne ko?”

Ya tsahirta haɗe da kai dubanshi gare su, kafin ya ɗora da faɗin,

“Garba ya so Lubna sosai amma a cewarsa, don sai daga baya na gane ba son gaskiya ya yi mata ba, don duk masoyi na gaskiya ba zai kai masoyinsa ga halaka ba duk kuwa girman laifin da zai aikata wa masoyin nashi. Kada na cika ku da surutu saboda ba ni da isashen lokaci, watau duk yadda Garba ya nuna wa Lubna so amma ta ƙi aminta da shi don bai kwanta mata a rai ba, babu yadda bai yi ba amma ta ƙi amsa tayin son shi don ba yi wa so dole. Maimakon ya rabu da ita sai da ya ɓata mata suna a gari har ya kai ta ga zama gidan yari na shekara biyar.”

Ya tsagaita haɗe da duban su, sannan ya ƙara da cewa,

“Duk dukiyar da Garba ya mallaka ba ta hanyar halak aka same ta ba, kuɗin wani babban kamfani da muka yi aiki tare da shi da Lubna ya sace, aka laƙa mata don inda take aiki nan ne aka neme su a rasa. Dayake ba ta da gata, ita ɗin marainiya ce, ba uba ba uwa sai da aka yanke mata hukuncin zaman gidan yari na shekara ashirin. Na sha kuka kamar ba gobe saboda na san halinta ba za ta aikata haka ba sharri ne aka yi mata. Allah da nashi iko tana cika shekara biyar na biya kuɗin aka sallamo ta muka yi aure na so da ƙauna.  Yadda aka yi na san shi ne ya saci kuɗin bayan fitowar Lubna daga kaso mun yi aure na haɗu da babban amininsa ne yake faɗa mini, raina ya ɓace sosai har ma na so na ɗaukaka ƙara amma Lubna ta hana ni. Daga karshe ina so ka sani Garba, zuciyar Lubna kyakyawa ce don tuni ta yafe maka, ce mini ta yi har kuruciya tana damun ka a lokacin, jama’a mun bar ku lafiya don abar ƙauna ba ta iya jimirin tsayuwa.”

Sulaiman yana gama faɗin hana ya bar su a nan tsaye tamkar gumaka, shi kam Alhaji Garba ban da kuka babu abin da yake yi, shaf ya mance da zancen Lubna, lallai TUN A DUNIYA Allah Ya nuna masa ishara, dukiyar da ya tara wacce yake alfahari da ita duk ta tafi lokaci guda. Ga kuma kunyar iyalinsa da yake ji wacce bai taɓa jin irin ta ba.

“Wallahi ba zan ƙara minti ɗaya da aurenka ba sai ka sake ni.”

Tabdijan ! Muryar Hajiya Binta ta ratsa shi, kallon ba ki da tausayi ya yi mata sannan ya buɗi baki da kyar yana faɗin,

“Ku gafarce ni iyalina don Allah, kada ku juya mini baya. Wallahi son zuciya ne da ruɗin shaiɗan ya sa na aikata mata haka, kuma kuruciya tana ɗiba ta a lokacin amma na tuba ku yafe mini.”

“Kun ga mu wuce gida don an fara taruwa a kanmu.”

Hajiya Salima ta faɗa cikin wani irin yanayi, wani irin kallo Hajiya Binta ta yi mata kafin ta mayar da dubanta ga Alhaji Garba da har yanzu yake kuka ta ce,

“Ka sake ni kafin na tara maka mutane a nan! Ba zan iya zama da ɓarawo ba. “
Ta sake faɗa a tsawace

Duk yadda ‘ya’yanta da Hajiya Salima suke ba ta baki amma a banza wai an tura agwagwa a ruwa, sai da Alhaji Garba ya sawwake mata sannan ta rabu da shi, yayin da suka wuce gida jiki a sanyaye. Suna zuwa gida Alhaji Garba ya tari Hajiya Salima da maganar, duk da ta ji haushin abun matuƙa, amma ba ta nuna masa a fili ba don hannunka bai ruɓewa ka yanke ka yar, sai ta ce da shi,

“Ba ni za ka roko ba, ka roki Allah Ya yafe maka.”

“Na gode matata.”

Ya faɗa hawaye suna zubo masa. Tun daga lokacin ya fara istigifari ita kuma Hajiya Salima ta fara sana’a a cikin gida don zama haka ba nasu ba ne.

Ƙarshe

Real Nana Aisha

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×