Baban Nawwara! Baban nawwara! a firgice ya dago kai ya Kalli mai kiransa, matar sa ce maman nawwara. ” Shin yau ba aikine? ya dago Kai ya Kalli bangaren da agogo yake a rataye, karfe 7:45 na safe.
Subhanallahi! duk na shagaltu har lokaci ya ja haka? ya mike cikin gaggawa ya nufi bandaki don yin wanka,bai dau Lokaci ba,yafito ya wuce uwar daki don shiri.ya fito sanye da jallabiya ruwan madara,da hula wacce ta dace da kayan, tare da bakin takalmin sau ciki, ya nufo teburin cin abincin rataye da jakar laptop.kamshin turarensa ne yasa ta dago da kanta ta kalle shi,ya nufo tare da zama a daya daga kujerun ya dauki kofin shayi
na’a na’a yayi kurba uku ya mike “to ni zan tafi sai na dawo” Allah ya kiyaye hanya, ya dawo da kai lafiya! “Ameen” ya amsa tare da dauko mukullin babur dinsa dake kan tebur ya fice.
Tanimu sambo wato baban nawwara dan kimani shekara talatin da biyar, dogo, fari, Mai yalwar kasumba wadda ta qarawa fuskar kwarjini da kyau,kumatunsa Mai madaidaicin jiki kamili.
Yana koyarwa a makarantan mata wato FGC, shi ne malamin lissafinsu. ya dau shekaru aqqala biyar yana koyarwa a makarantar,yana da ‘ya daya wato nawwara yar shekara uku da haihuwa, yana masifan sonta, sobada sunan mahaifiyarsa ce da ita. Amma tana fama da cutar sankarar bargo (leukemia).
Cutar ‘yar tasa na jefa shi duniyar tunani indai ya kadaita.
isar sa makaranta ke da wuya ya nufi ofishin malamai (staff room) daidai baranda, ya hadu da shugaban makarantar,”malam Tanimu ya fada cikin Sakin fuskar “Ina fatan dai lafiya ka shigo makaranta warhaka?”Lafiya yallabai ya fada tare da russunawa,wata ‘yar matsala aka samu,amma komai ya daidaita,to Allah ya taimaka, kira min malamai, ofishina don tattaunawa game da jarrabawar karshe wato(WAEC)”to ya fada tare da wucewa da gaggawa.
Zulfa wacce akafi sani da (chapcisco)matashiyar yarinya ce mai ji da kanta,ga rawar kai, uwa uba ga rashin kunya ga malamai,bata tsoron ta mutu balle ta yi rai, kowa shakkar ta yake a makarantar.
Wata rana da maraice malamin turanci ya fitar da ita waje dan batayi aikin gida da ya bayar. Tana waje a tsugune malam tanimu ya tambayeta laifinta, ta zayyana mai komai. Me neman kuka aka jefe shi da kashin akuya! dama yana cike da ita ya kalleta a fusace,ta inda yake shiga ba tana yake fita ba, yayi mata tas.
Daga baya ya fara mata nasiha me ratsa zuciya cikin lallashi da tausasa murya” Kinga rayuwar nan ta wuce wasa da shashanci, balle ke ‘ya mace wacce rayuwar ta kamar tumatir, mai gajeriyar rayuwa kuma uwa wata rana.
Me zai hana kiyi amfanin da kuruciyar ki ta hanya madaidaiciya, yi nayi bari na bari.
Wannan Karatun ba kowa kike yiwa ba face kanki, in ki ka maida hankalin sannan kika bar rashin kunya da kike yi wa malamai zaki ci ribar rayuwarki nan gaba.
Zaki ga alfanun karatunki, sannan zaki taimaki kanki da alumma baki daya. kar inji kar in gani a sake kokawa da ke.tashi mu tafi”ya fada tare da wuce wa gaba.Tamike jiki a sanyaye tabi bayansa zuwa aji.”Assalamu alaikum barka da warhaka” inji malam tanimu
” Yauwa malam” inji malamin turanci
“Dan Allah wanna yarinyar ya kalleta tare da nunata,ayi mata afuwa insha Allahu gobe zata kawo aikin”inji malam tanimu.
“Ba matsala ya fadi cikin daure fuskar Allah ya kaimu, ta ci darajar ka, da ta yabawa aya zakinta, wuce ki shiga aji cikin fada yake magana.
Tun daga ranan zulfa ta canza ta zama nutsatstsiya,ga kwazo da ladabi da biyayya.
“Assalamu alaikum barka da warhaka” inji malam tanimu
” Yauwa malam” inji malamin turanci
“Dan Allah wanna yarinyar ya kalleta tare da nunata,ayi mata afuwa insha Allahu gobe zata kawo aikin”inji malam tanimu.
“Ba matsala ya fadi cikin daure fuskar Allah ya kaimu, ta ci darajar ka, da ta yabawa aya zakinta, wuce ki shiga aji cikin fada yake magana.
Tun daga ranan zulfa ta canza ta zama nutsatstsiya,ga kwazo da ladabi da biyayya.
Kowa ya hallara ofisin principal aka bude taro da addua, ya fara jawabi kamar haka,
” na tara ku ne ba don komai ba sai don jarrabawar yaran nan na shedar kammala babbar sakandare (WAEC). Kun San yadda akeyi a makaranta yanzu, dalibai tara kudi suke a basu amsa. Yanzu kamar nawa zamu karba awajen dalibai
“mu karbi dubu biyar a kowace jarrabawa inji daya daga cikin malaman
“Hakan yayi yallabai” sauran malaman suka hada baki.
“Excuse sir” inji malam tanimu.
“Kana da karin bayani ne malam tanimu” inji shugaban makaranta.
“Eh yallabai Ina ganin wannan shawara bai dace ba, kenan muna son nuna wa daliban nan cewa jajircewa karatu da naci ba amfanin, muna son nuna musu dubu biyar itace komai, ina laifi mu tara yaran nan kowane malamin darasi ya dinga horas da dalibai batun dake cikin darasinsa, sannan mu koya musu yadda ake amsa tambayoyi jarrabawar.”
“Gaskiya ba zai yiwu ba haka kawai nawa ake biyan mu zamu sha wannan wahalar inji daya daga cikin malamai.ya fada cikin fushi.Kafin a ankara.
Wajen ya dau hatsaniya kowa na tofa albarkacin bakinsa.
“Ya Isa! Ya Isa ” inji shugaban makaranta kowa yayi shiru, ya cigaba da karin bayani “Mallam tanimu wanne zamu bi “naka yallabai” inji sauran malamai.”to na sallame ku banda kai malam tanimu”. kowa yafice, sauran malam tanimu da shugaban makaranta ya kalle shi rai a bace, Ina zaton wuta a makera sai gata a masaka! Kana son ka kawo min cikas a wanna lamarin ko, to wallahi baka Isa ba.
“Yallabai me yayi zafi haka daga fadin gaskiya sai Kari yazama ciwon!
Yi mun shiru malam ya fada cikin bacin rai, Wani gaskiya zaka fada min.kawai tashi ka bar min ofis
ya tashi ya bar ofishin jiki ba kwarin.
“Zanyi maganin ka mallam tanimu “inji shugaban makaranta ya fada a cikin ransa bayan malam tanimu ya fita.
Washegari malam tanimu ya tara dalibai masu jarrabawa ya fada musu illar biyan kudin amsan jarrabawa, kar wacce ta yarda ta kawo kudi don abata amsa, don bada da karba kudi duk cin hanci ne da rashawa, haramu ne a addini.
” Na dau alwashin zan horas da ku Kafin lokaci jarrabawarku” amma Ina neman alfarma daya awajen ku” kuyi min alkawari kowaccen ku zata maida hankali”
“Eh malam munyi alkawari sake amsa tare.
Shugaban makaranta na gefe yana kallon abinda ke faruwa,ransa idan ya yi dubu ya baci! amma yayi murmushin mugunta ya wuce abinsa.
Mallam tanimu na zaune kan kujerarsa yana gyaran littattafai dake kan tebur sai yayi Ido biyu da ambulo fara akan teburin ya dauka, budewarsa ke da wuya sai ya ci karo da sakon dakatarwa daga aiki.”innali lahi wa inna ilaihi raji’un” ya fada tare da dafe Kansa. Ya tashi ya nufi ofishin shugaban makaranta.shigarsa ke da wuya,ya taradda shugaban makaranta a gishingide yana waya,cikin dariya yake cewa”ai kawai ka more rayuwarka”malam Tanimu ya bude kofa tare da sallama,wa’aikummus salam ya fada tare da dago Kansa,bani minti biyu zan kiraka,ya ajiye waya ya fuskantaci malam tanimu.malam tanimu ya mika masa farar anbulan dake hannunsa wannan Sakon fa!
“Bani da ikon amsa wannan tambaya,ya fada cikin murmushin mugunta,Sako ne, daga inda ba ni da hurumi akansa” inji shugaban makaranta.
“Nagode” ya ce lokacin da wayarsa ta dauki qara,innalillahi wa inna ilaihi raji’un
“Gani nan tawowa ya juya ya koma inda babur dinsa yake, bai tsaya ko Ina ba sai asibiti.
Duk me rai mamaci ne!
Wasu zazzafan hawaye ne suka zubo me har Wani duhu duhu yake gani.
Na rasa nawwara dakta?
“Hakuri zakayi Mallam tanimu.
Sati na zagayowa ya fara horas da daliban ba qaqqautawa,duk abin da basu gane ba sai yayi masu bayani dalla-dalla yanda za su gane, ya nemi bidiyo masu darussa daban daban su kalla don kara fahimta.
Wata safiyar asabar ya shirya zuwa makaranta, ya dauka babur zai tayar ya ki tashi,dole tasa ya taka har zuwa makaranta don bai ajiye kudi ba,Kuma bai ba kowa ajiya ba.
Kwanci tashi ba wuya har lokacin jarrabawa ya zo,suna zaune a aji shugaban makaranta ya turo malami don karbar kudin da za’a bawa masu kula da jarrabawar,”Ba a bamu kudi a gida ba “inji daliban malam tanimu.
“To zaku gane kuranku har shi mallam tanimu” ya fita ya bar aji.
Amsar da ba’a basu ba har aka gama jarrabawar.
Malam tanimu yana zaune a ofishinsa don wa’ adin da aka daukar masa ya cika, uncle! uncle!” suka fada ofis ba sallama.
“Lafiya irin wanna kira ” inji Malam tanimu
“Jarrabawa ce ta dukkanmu daga me credit takwas sai tara da murnar su”inji daliban.
“Mun gode ,baka nuna gajiya ko gasawa alokacin da kake horas da mu,baka taba nuna gajiya ko kosawa akan mu ba.
Kai ne UBAN da ba namu ba.. , baka nemi ko sisi daga garemu ba, kai malami ne,kuma Uba, abin alfaharinmu gatan dalibai.da taimakonka da tallafawarka ne muka sami nasarar cin wannan jarrabawar,Allah ya biyaka da aljannar Mafi daukaka wato Firdausi
“Masha Allah, na taya ku murna” inji Mallam ya cigaba.
“Kwaliya dai ta biya kudin sabulu” Allah yayi miku albarka ya baku duk abinda kuka sa agaba na alkhairi.
Nagode Nagode
Alhamdulillah!