Shimfida
Ummu hani ta nisa kamin ta ce, yawwa daman na ga yau bakwai, shi ne na ce ko wazai ɗauki Muhammad ta nuna jaririn da ke hannunta, wanda tunda aka haifeshi babu wanda yai tunanin saka masa suna cikin dangin umman su da na Abbansu.
Kawu Bala ya numfasa, sannan yace toni dai kinsan mata ta tayi tsufan da ba zata iya rainon yaro…
Kamin ya rufe baki, Inna Abu yayar ummansu ce data rasu, ta ce bare kuma ni, ga tsufa, ga masifaffen miji, innaje masa da jariri ai sai ya koren ya ce na kawo masa nauyi.
Haka kowa yai ta bada uzirin sa.
Ummu Hani ta share hawaye, gami da saɓa Muhammad dake kuka a kafaɗa, ta ce to shikenan, mu yanzu ya zakuyi ɗaukan namu, ɗai ɗai zaku rarrabamu, ko bibiyu, nidai duk wanda zai ɗauken sai ya haɗa da Muhammad ni zan kula dashi.
Kamar ɗazun, haka sukai ta bada uziri naƙin ɗaukan su, ji take tamkar ta fashe da kuka, sai dai tanajin ita dinfa jaruma ce, intai kuka kannenta fa.
To shikenan, yanzu shinkafar da Alhaji Badamasi da wadda Alhaji Bashir ya kawo, naga kun rarraba a tsakanin ku, nai muku shiru ne, dan nayi zaton ku zaku riƙe mu, yanzu sai ku aje mana, fatan kunsan marayu suka bawa ba dangin marayu ba.
Nan guri ya ɗauka, ka gamin mara kunya mu ba iyayanki bane.
Bata ce komai ba, ta mikawa Aisha Muhammad, ta hau shigar da shinkafar ɗaki inda sauran ƙannenta suka fara taya ta.
Kawu Bala ne ya rike tasa, tasa hannu zata amsa yaƙi bayarwa, tace ka saki ko Wallahi tallahi in kaika ƙara gun hukuma, Ba shiri ya saki yayin da kowa ya watse.
Ko da suka watse, toilet ta shiga tasha kukanta yanzu ita yaza tai da Muhammad, wanda ita tasa masa sunan, bayan haka sauran ƙannenta biyar ya za tai dasu, wato babu wanda yafi danginsu zalunci suna nufin kenan su kaɗai zasu rayu ko me.
Yaya taji Aisha kira ta, wanke fuskar ta tai sannan ta fito, kinga Muhammad na kuka, ta amsheshi ta goya ta zari mayafi, ba inje in dawo, nan yan biyu suka sa kuka, ta rike musu hannu, sannan ta dubi Aisha, ki kula da su khairi, zan je in nemo abinda zamu dinga bawa Muhammad, A’isha tace to yaya sai kin dawo, ta ja su Hasana suka fice.
Rimi ta wuce da yan kudin da suka rage mata, ta haɗo saiwar magunguna, wanda zasu sa ruwan mama yazo, dan ta yanke shawarar ita zata shayar dashi kawai, tunda basu da kuɗin madara.
*****
Ummu Hani kenan yarinya yar kimanin sheka goma sha shida, da rayuwa ta sauya mata ko ya zata kaya ku biyo ni.
Babi Na Daya
Kuka kawai take tana girgiza Ummansu da ke ta faman murkususu,
“Umma dan Allah karki mutu, in kema kika mutu kamar Baba ina zamu sa kanmu, ta yaya zamu rayu?”
Yayin da Ummu hani ke wannan batun, kannen ta ke gefe suna kuka, ita kuwa umma bama tasan inda kanta yake ba.
Ummu hani ce ta miƙe da sauri, ta dubi A’isha ƙanwar ta, ta ce,
“Ki kula da umma zanje in samo mai kaita asibiti.”
“To yaya, Anman dare fa yayi.” Aisha ta bata amsa.
Ummu hani bata kula da batun ƙanwar tata ba, tai hanyar soro kwata kwata zuciyarta ta bushe, tsoro ya barta burin ta kawai taga ummansu ta samu lafiya.
Cike da karfin hali ta buɗe sakatar gidan nasu, tayo waje, duhu ya mamaye ko ina, sabida rashin wutar da ake fama da shi, yayin da bakajin komai sai ihun karnuka. Anman duk da haka Ummu Hani bata tsorata ba, duk da kasan cewarta yarinya mai tsoro amman yau ɗin wata jarumta ta musanman ce ta ziyarce ta.
Sai alokacin tama fara tunanin cikin tsakiyar daren nan ina zata, ta ga mai adai daita sahu ga shi duk area ɗin nasu babu wani mai mota da ta sani.
Durkushe tai a ƙofar gidan nasu tana kuka, ko me ta tuna oho ta miƙe zunbur ta hau tafiya.
Tayi tafiya mai ɗan nisa zuwa bayan layinsu, kamin ta tsaya a ƙofar wani ɗan ƙaramin gida, koda yake kusan unguwar duk haka gidajen su yake, bugawa ta hauyi aranta tana fatan suzo su buɗe.
Gidan Inna Mai Ɗan Wake kenan, inda yaron ta Habu ke jan adaidaita, tuna hakan yasa Ummu Hani ta yo gidan.
Bugun Ummu Hani shi ya farkar da mutanen gidan, baki ɗaya sukayo zaure suna tambayar waye, cikin rawar murya Ummu Hani ke faɗin “Ni ce.”
Inna ta ɗauki muryar yarinyar, da sauri ta buɗe ƙofar tana faɗin,
“Ummu Hani lafiya, me kike anan, ina umman taku, kinsan kuwa ƙarfe nawa, biyu fa da mintina” Inna Mai Dan Wake ta faɗa atare.
Cikin kuka Ummu Hani tai ma inna bayani, cikin tashin Hankali Inna tace ma Habule yaje maza ya ɗauko mashin ɗin suje asibiti.
Nisawa kaɗan yai kamin yace, kash wallahi yau ban kawo shi gida ba, mai bani hayar ne yace in kai masa yana son zai fita da wuri gobe.
Towo innalillahi wa’inna ilaihirraji’un inna ta faɗa, cikin tashin hankali inda ita kuma Ummu Hani ta kuma fashewa da kuka.
“Karki damu kuje da inna taga jikin Umman taku, ni bara inje tudun gangare gidansu Mahadi shima wataran yana zuwa da mashin.” Habule ya faɗa.
“To dan Allah kayi sauri.” Ummu Hani ta faɗa inda tabi bayan Inna su ka yi gidansu.
Yadda inna taga Ummansu Ummu Hani ya tsorata ta, duk tai male male da jini, cikin ƙarfin hali tace da ummu Hani ta mai da ƙannenta ɗayan ɗakin, sai tazo Ummu Hani tace to, ita ta ɗauki Hasana inda Aisha ta ɗauki usaina da ke bacci suka je suka kwantar dasu, tazo ta tashi Salma da Khairiyya suma ɗakin ta kai su kamin ta fito.
A’isha ce ta biyo ta, ta yi saurin cewa ta zauna ta kula da su Hasana, tasan in suka tashi sukaga duhu ba kowa firgita suke, to kawai Aisha tace ta koma ta zauna ranfa fal da fargaba.
Tambayar Ummu Hani Inna ta fara yi, ko Umman nasu ta aje kayan jariri, girgiza kai ta yi alamar a’a, jiya dai da naje makaranta na siyo wannan, ta nuna mata irin shimi da kanfai na jariri ok tom aje agunki in ta haihu lafiya sai musawa abin da aka samu, to kawai Ummu hani tace ji take tamkar tabi Habule taga me tsaya.
Kusan minti goma sha biyar sai ga Habule anyi sa’a yazo da mashin, nan Inna tace ta ɗebo zannuwa da sauran abubuwan da mai haihuwa zata anfana.
Wayar Habule Ummu Hani ta ara ta haska dan debo kayan, Ummansu bata da wani kaya daga na jikinta sai wasu guda biyu komai ta samu akansu yake.
Nata zannuwan dana A’isha ta ɗebo, sai da ta kai su A’isha gidan Inna Mai Ɗan Wake, sannan tabi su Habule sukai asibiti tanason tai kuka, sai dai tana gudun kar kukanta ya tadawa ummansu hankali, haka ta ƙunshe abinta ranta na mata suya.
Dakyar da taimakon Habule suka samu suka shigar da Umma asibitin, wanda baka ganin komai sai duhuwa, dabadan yar fitilar dake manne jikin wayar Habule ba da banajin zasu fahinci hanyar da zata sada su da shiga asibitin.
Shiru tamkar ba asibiti ba Ummu Hani ta amshi fitilar tana haskawa tana faɗin da wani akusa, har ta karasa inda taga mutun zaune ya kwantar da kansa bisa tebur, sai da ta ƙarasa kusa ta fahinci jami’ar asibitin ce ta saki ajiyar zuciya ta karasa da sauri.
Tattaɓa matar tahau yi, matar ta tashi a tsorace tako hau Ummu Hani da masifa, Ummu kawai kuka tasa tana faɗin Ummanmu dan Allah.
Tsaki matar tayi tace muje ko da suka ƙaraso ta kuma hawa, ta inda ta shiga ba tanan ta nufa ba, tsabar shirme shine zaku barta agida haka, ko dan ba ciwon ne ajikin ku ba, and banda rashin azanci kuna ganin ba wuta kunsan ai bazamu iya komai ba, sannan ba likita, ni primary health care ce, I can’t do anything, it’s beyond my experience gaskiya, zan baku shawara kuyi maza ku kaita asibitin cikin gari.
Fuuu, ta yi ciki tana faɗin kawai ina baccina kunzo kun tashen kunsan zaku damu da kuka barta ciwo ya cinye ta…
Pls comments, rate and share.
Madalla. Fatan alheri. Allah ya ƙara basira.
Amin