Skip to content
Part 12 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Umar na tsaye yana kalle kalle ta fito riƙe da Muhd, yana hangota ya saki fuska itama daurewa tayi ta ɗan murmusa kamin ta ƙarasa ta gaidashi.

Cikin sakin fuska ya amsa gami da cewa sai kuma kika ganni ko, murmushi ta yi, “Eh wallahi.”

Shiru suka ɗanyi kamin ya ce, “Eh to daman batun Faruk ne.” Sai da gabanta ya faɗi jin sunan Faruk ta daure bata ce komai ba.

“Ɗazu ya zo ya samen ya faɗan komai da ya faru, banji daɗi ba sai dai abu ɗaya yamin daɗi.”

Ɗagowa ta yi ta kalle shi, ya ce, “yes, abu ɗaya yamin daɗi a ƙalla cewar yau Faruk ne da bakin sa yake faɗamin cewa ya shirya barin abinda nai nai in hana shi ya ƙi hanuwa.”

Ɗagowa ta yi ta kalleshi kamin ta ce, “In har kai da kuke tare ka hana shi yaƙi hanuwa ta yaya zan samu tabbacin zai dena?”

Ɗan sosa kansa yayi kamin ya ce, “Wannan dalilin da yasani farin ciki shine Faruk mutun ne da baya furta abin da ba zai aiwatar ba, ina da tabbacin tunda har ya ce zai bari na tabbatar ya bari ɗin.”

“Ki yadda dani bazan taɓa yadda a cuceki ba, dan yana abokina bazan kareshi ba inda ace banda tabbacin cewar sa ya dena ɗin gaske ne wallahi bazan zo in tare ki da batun sa ba.

Ki daure ki masa uziri ki daure ki ci gaba da sauraron sa, nasan da sannu zaki gyara shi zuwa yadda kike son miji kuma uba ga ƙannen ki da yaran ki ya zama.”

Ɗan numfasawa ta yi kamin ta ce, “Shikenan naji Allah ya gafar ta mana baki ɗaya, amma wallahi duk sanda na gano bai sauya ba tabbas zan barshi.”

“Shikenan mun gode Amaryarmu.” Murmushi ta yi “kayya bari faɗin amaryar mu har yanzu ban gama tunani ba.”

“A’a dai kiyi haƙuri ki daure ki amshi sunan nan.” Ya faɗa yana murmushi itama murmusawa ta yi kamin ta ce shikenan na amsa dan kai, to godiya muke ya faɗa yana rissinawar wasa su kai murmushi tare.

Sallama ya mata ta amshi Muhd dake hannunsa ta yi cikin gida, yayin da shi kuma ya tsaya neman yaro.

Kaya ya bawa yaron niƙi niƙi da naira ɗari sabuwa ta yaron ya ce ya miƙawa Ummu Hani cikin gida yako amsa cike da murna.

Ummu na zama yaro ya shigo da kaya ta zubawa kayan ido wato dai da gaske ne sai hali yazo ɗaya ake abota shima Faruk haka yake haya taɓa cewa ta tsaya ta amsa bare ta samu damar godiya ko cewa ya basshi sai ta shigo yake aiko yaro dasu ko da ta je ya tafiyar sa.

Abin ka da zuciya cikin ruwan sanyi Faruk ya lallaɓa Ummu Hani ta haƙura dan babbar wayarsa ma ita ya bawa ta aje masa ya sai mai madannai sai da kuma yasa ta kira gidansu ta tambaye su in yanzu suna ganin sa da waya.

Ya takura mata sosai kan ta amince ya turo a ɗaura musu aure tun tana zillewa har ta fara tunanin to ma ita yanzu waye zai ɗaura mata aure sai yanzu ta kuma yadda bafa ta da gata.

Shiko Faruk ya damu burin sa kawai aɗaura musu aure kwana da yinin da yake baya ganin ta da ƙyar yake iya kaiwa.

Damun da Faruk yake mata ya fara yawa wanda har ya fara bayyana a fuskarta tanason sa sai dai bata son faɗa masa itafa bata da inda zata kai shina ɗaura mata aure.

Yau suna zaune ita da Hajiya su A’isha duk basa gida Hajiya ta dube ta, “Ummu wai meke damun ki ko kun kuma samun matsala da Farukun ne?”

Yaƙe ta yi, “A’a Hajiya ba komai kawai yanayin rayuwa ne.”

Murmushi Hajiya ta yi “kin ga Ummu ki faɗan gaskiya ko da ace ban haifeku ba ni ƴaƴa na m, na ɗaukeku hakan yada duk na karance ku duk wanda ya sauya a cikin ku nasani ki faɗan meke damun ki.”

Kuka ummu tasa kamin ta faɗi meke damun ta. Shiru Hajiya ta yi ku ai ba shegu bane kuna da dangi koda basu riƙeku ba haƙƙinku na su aurar da ku na kansu kije ki same su ki faɗa musu kin samu miji kuma danginsa zasu zo gun su.

Shiru Ummu ta yi tana tunani ina ma ace Muhd dinsu shine Babba kai ita inama ace yakai kamar Aisha da wallahi shi zata bawa wakilcin su dukansu ya dinga ɗaura musu aure.

Kinji dai ko me na nace miki, Hajiya ta katse mata tunani to kawai ta ce ranta fal tunanin yadda sukai da su kawu ran bakwan ummansu anman ba komai haka zata daure ta je.

Washe gari taja Kairi su kai gidan Kawunsu yana Kofar gida suka gai dashi Ummu ta ce gunsa tazo yako haɗe rai zaton sa ko kuɗi tazo amsa.

Ganin haka yasa daman ba batun kuɗi bane kallon ta ya yi da mamaki yarin yar akwai raini ya faɗa aransa a fili ya ce ina jinki.

“Eh to daman akwai wanda mukai batun aure shine yake son turowa na ce ba inzo in fada ma ka fadi ranar da zasu zo din.”

A fusace kawu ya kalleta “Eyye kince ba batun kuɗi bane yanzu batun ubanki ne, wato sai yanzu muke da amfani nan nan kan shinkafa kika ci mana mutunci yanzu da yake kinsan shinkafa bazata miki kayan ɗaki ba, shine kika lallaɓo kika tawo kin manta me kika ce ni ba ubanki bane haka kika faɗamin ku tashi ku bani waje ya faɗa a fusace.
Miƙewa ummu ta yi gami da share hawayenta, har tayi ɗan taku biyu zuwa uku sai kuma ta dawo, a fusace kawu yace me kuma kika dawo yi.

Kallon sa ta yi cike da takaici, tace “ni ba kuɗi nazo nema gunka ba, domin inda shine zan gwammace inje in bara in ci da ƴan uwana, har abada bana fatan randa zata zo inzo neman kuɗi gun ku, haƙƙin kune ku ci damu kun ƙi, ba zan takura muku ba don bani nace ku ci damu ba, kamar yadda aure ma da badan haƙƙinku ne ku aurar damu ba da wallahi bazaka ganni agunka ba, haƙƙin Allah na sauke tunda kun kasa ɗauka karkayi mamakin jin cewar naje gidan radiyo neman maɗaurin aure na.”

A tsorace ya kalle ta, ita kuwa cigaba ta yi, “ba batun kayan ɗaki ya kawo ni ba, ba kuma inason ku tallafa min bane, domin mafi ƙarfi da iko wato Allah ya jima da agaza mana, kawai yanzun ma dan na zamo mace ce, mai cewa ya bada aurena sai iyaye ko wani nawa, anma tunda ku kun kasa akwai Shari’a ba ƙarar ku zan kai ba, kawai zanje ta ɗauran aure ne,” ta juya tabar gun tana cigaba da share hawaye yayin da wannan abin na baƙin ciki da ya tsaya mata a wuya tun mutuwar ummansu da sai ɗan kwanakin nan ta samu yai ɗan ƙasa, duda ba tafiya yai ba ya kuma zuwa ya tokare mata numfashi.

Ita kanta tana mamakin yadda take iya jarumtar faɗawa kawunnan nata magana, sai tayi tazo tanajin haushin kanta ai ko ba komai su ɗin matsayin iyayen ta suke.

Sai da suka bar lokon sannan Khairiyya ta dubi yayar tata tace, amma yaya kafin muje gidan radiyo ɗin da kamata ya yi mu gwada zuwa dikan gidajen yayyen Abba in munyi sa’a ko ɗaya ne cikin su in yai tunani me kyau zai saurare mu.

Shiru ummu tai, kamin ta ce yanzu raina aɓace yake in mukaje suka kuma mana irin Abinda kawu Babba yai mana zan iya faɗuwa jiri ma nake yanzu.

To to muƙarasa gidan gwaggo rabi ki ɗan huta, to kawai Ummu ta ce sukai gaba Khairiyya na riƙe da ita kai tsaye gidan gwaggon suka wuce wadda ta kasance yaya ce ga ummansu uwa ɗaya uba ɗaya.

Gwaggo Rabi na zaune tana gurza kuɓewa su Ummu suka shiga, da farin ciki ta taryesu suma sakin fuska sukai kafin su zauna suka gaidata.

Gwaggo kusan tun mutuwar ƙanwar tata, data fuskanci yaran ba kuɗi suke nema ba ba wahala zasu ɗora mata ba, ta saki jiki dasu suka koma kamar da kusan duk adanginsu ita ce ma take zuwa gunsu ada ma abinda yasa ta nuna bazata ɗaukesu ba sabida itama mijin ta ya mutu, ta kuma aure sabon mijin ta kuma ɗan bala’i ne, komai a kafkaf take yinsa dan gudun masifar sa.

Anan gidan gwaggo suka yini ta gama tuwon ta zuba musu sai da suka cinye sannan Khairiyya ta ma gwaggo bayanin yadda sukai da kawu, bayan ummu ta shiga bayi danyi alwala.

Gwaggo taita bawa Ummu baki, tace karta damu gobe zataje ta samu dangin baban nasu inma basu amince ba kar su damu zata roƙi mijinta indan aure tasan zai ɗaura godiya ummu tai mata anjima suka fice.

Sai yanzu Ummu ta ɗanji daɗi, ba tun yau ba ta daɗe da yadda tabbas dangin uwa dangin ne, duk da kuwa cewar dangin uba sunfi iko da mutun, anma tun mutuwar ummansu ta gane dangin ta sun fi sonsu, tunda duk da basa ba su komai aƙalla sukan samu lokaci wani ya leƙo kuma in sunje gunsu basa wulaƙanta su kamar dangin Abbansu.

Suna tafe suna hira har zuwa bakin titi inda suka tari mai adai daita sahu sukai gida.

Shi kuwa kawu su Ummu na barin lokon ya yi cikin gida yana ci gaba da masifa, Matar sa Inna na zaune tana tsintar shinkafa lafiya dai Malam ka ishe mu da hayani haka.

“Mtss” yai tsaki nida wannan mara mutuncin mana, kallon sa ta yi kardai Habu ne ya kuma zuwa? Ta tambaya, tsaki yai in shine ai bazan magana ba tunda kudin sa naci malam ya fada rai aɓace.

“To kai da waye haka?” Inna ta tambaya cike da kulawa.

“Ni da yar gidan Mansur mana,” ya faɗa da alamu faɗin sunan ya kuna ƙona masa rai.

“To kar dai Ummu Hani? Inna ta faɗa cike da Mamaki.

“Wa kuwa in ba ita ba, aikema kinsan a yaransa babu mara mutunci sai ita ni wallahi bai kyautamin ba da ya haifo duk mata tsabar abu kuma ya mutu ya barsu.”

Kallon sa ta yi, “hala dai taimako tazo nema ta tambaya.”

“Yo in taimako tazo nema ai da ba haka ba, da ko ɗari biyu ce zan haɗa ta da ita, ko dan in munje lahiri aƙalla nasan ko sau ɗaya ne na taɓa taimaka mata.”

“To to haka kawai ta zaɓi ta ci maka mutunci ko me?” Inna ta tambaya cike da jimami.

“Wai aure zata yi shine tazo in ɗaura mata.” Malam ya faɗa rai a ɓace.

Dariya inna ta yi, “Anzo wajen, daman na faɗa maka da kanta zata zo ta nemeka, daman dan ubanta ai bazata bada kanta ba, kuɗin dai da ta zaɓi shinkafa sama daku kune gatanta.” Inna ta faɗa cike da cika baki.

Haushi ne ya kuma kama malam ya ce, “Itama haka ta ce mun, sai dai tace tunda mu da haƙƙin hakan ke kanmu mun gaza zata je radio neman madaurin aure, kinajin zamu iya zaman Kano in har ƴan radiyo suka samu agaba? Banda tsinuwar mutane na kyale yara ƙanana mata suna ci da kansu.”

Shiru Inna ta yi kafin tace, “Kai wannan yarinya kwai tsinanniya.”

“Bari kawai yarinyar nan annoba ce, Ni kinsan Allah ba auren nata ne abin tsoro ba, dan kayan ɗaki nasan zamu iya haɗa mata ko tsoffine nida sauran dangi abin da nake tsoro tai aure ta tattaro ƙannenta ta kawon, dan wallahi bazan iya ɗaukan nauyin rai shida ba koda ace duk sati sau ɗaya zan ci dasu.”

Shiru Inna ta yi kamin tace, “Yo ai malam abu ne mai sauƙi shi yaron da zai aureta zaku kafawa sharuɗa, dole ya zauna anan gidan da suke ta riƙe ƙannenta in yaso sai kuce ya biya rabin kudin haya shida matarsa ku zaku biya rabi na yaran da an kwan biyu ku sanfe in ya gaji ya saketa ta, cigaba da riƙe ƙannenta.”

Dariya kawu ya yi, “Kai Hadiza gaskiya akwai ki da hangen nesa bari yanzu inje in samu su Sani mu tattauna.”
“Tom sai ka dawo.”

Har ya fita ya dawo kinga ko zaki aika Basira taje gidan nasu ta faɗa mata ta faɗawa shi yaron ya jiramu kar in tsaya sanya muji sanmaci dariya inna tai tom sai ka dawo.

Yana fita ta kwalawa Basira kira ta fito tana yatsine.

To dan ubanki ya tsinar me kike min haka Inna ta fada.

Haba dan Allah inna mutun na baccin sa ki wani takura masa Yarinyar ta faɗa rai ɓace.

“Kinga ni ba rashin mutuncin naki na kira kimun ba maza ki shirya kije gidan su Ummu Hani ki ce Babanku yace ta cewa yaron ya jira su.”

Da sauri Basira ta kalli Umman tata Inna karki ce mun aure za tai to da ubanki za tai.

Shiru Basira ta yi, “Oh nikam dai na rasa ina na gado wannan baƙin jinin,” Kallon ta Umma ta yi, “Kema kinsan gun ubanki ne tunda dai ni nasan ban nauyi ba.”

Kallon ta Basira ta yi “Eh shi tasa naga ai…, ko me ta tuna tai ɗaki kawai

Kwafa umma ta yi ,“Yo ai da kin karasa mara mutunci, duk gun kakarku kukai gadon rashin mutunci shi yasa gashi nan wadda tafi kowa kama da ita tafi kowa baƙin hali,” tana nufin Ummu Hani.

Sai da Basira ta yi kwaskwarima kafin ta fita ta yi gidan su Ummu Hani.

Aisha na soro inda suke sai da abinci ta sameta a wani ya tsine take magana yayin da Aisha itama ta maida mata da nata salon rashin mutuncin, dan tafi Ummu iya wulaƙancin ita Ummu kawai bata rike magana ne musanman in tazo iya wuya.

A wulakance ta gaida Basira shima dan Ummu tace musu duk wanda ya girmesu a dangi wajibi ne su girmama shi da wallahi baza ta gaida Basira ba.

Ummun bata nan ne ta tambaya bayan shiru da ta yi na wasu mintina eh kawai Aisha tace ta cigaba da zubawa Usman da zai sai abinci abinci.

Sai da ta zuba masa sannan ta zubowa Basira ta haɗo mata da kunun Aya dan yanzu har shi suke.

Babu kunya Basira ta amshe ta cinye ta shiga ciki ta yi salla ta fito ta wani kalli Aisha shekeke ban kudin mota tace a wulakance.

Kamar Aisha tace bazan bada ba sai kuma ta ciro naira dari ta mika mata, yayin da Basira ta amsa a raine kamin ta ce, “to ki faɗa mata in ta dawo Babana yace ta cewa shi wanda zai aurenta ya ɗan jira su.” Tai ficewar ta…

<< Ummu Hani 11Ummu Hani 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×