Koda Ummu suka dawo Aisha ta riga ta tashi, harma ta yi shirin islamiya ta magariba dan haka kawai cewa Ummu tai Basira tazo tace Abbansu yace ta cewa Faruk ya ɗan jira su.
To kawai Ummu tace ta hau warkajamin ta.
******
Zaune take tana bawa Muhammad Mama, Hajiya ta fito ya dan tago kansa ya yaɗa mata hannu yana murmushi, Hajita tace ohni Rakiya, wato Ummu kindai ƙi yaye yaron nan, kinajin abinda Umman Walid tace miki ki yaye shi ba sai bikin yazo ba kinƙi yaro yai wayo.
Murmushi Ummu ta yi, fadin haka da Hajiya ta yi sai ya tuna mata da iyayan ta lokacin tana goyon ƴan biyu harma da Khairi, haka Abbansu zaita mita yara sun zama barden goyo taki yaye su, ta ce ita sai yaranta sun shekara biyu.
Azahiri kuwa murmushi Ummu ta yi, kafin tace khai Hajiya shima fa Faruk ɗin yasan ina shayarwa, kuma munyi da shi sai Muhammad ya shekara biyu zan yaye shi ta faɗa a shagwaɓance tana shafa kan Muhd ɗin.
Salati Hajiya ta saka eyye to baki isa ba, sati mai zuwa dole ki yaye shi, ba inda zaki da yaro rabe rabe azo ganin amarya aga tana zaune tana shayarwa to me za’a ce ya auro.
Dariya Ummu ta yi kafin tace basai a ɗaga auren ba zuwa ya isa yaye.
Ah lallai yaro na gudu da kafar sa ki ce bai isa yaye ba, Hajiya ta faɗa ba alamun wasa.
Watansa fa tara kwata kwata, Ummu ta faɗa tana kallon yaron.
Girgiza kai Hajiya ta yi kafin ta ce sai kuma kiyi, batun yaye dole ne, ni zan fita.
To a dawo lafiya tace tana ƙoƙarin gyara rigarta bayan ta dire Muhammad dan ganin ya ƙoshi.
Hajiya na fita ita kuma ta ɗauki abincinta taci, kafin tayi soro dan karɓar Khairiyya, maza na gama shiri ki tafi kar Ya Sheikh yai fishi dan ma munyi sa’a yana muku uziri yanzu.
Bari kawai yaya har fa mamaki nake ya zane wasu mu ya barmu bacin yasan anan muke zama ba wani abin muke ba inji Khairiyya.
Murmushi tayi Ummu, kafin tace, “tausayi ne yasan nan ce kawai hanyar samunmu, ya kuma san indai kun zauna ɗin lalura ce tasa na barku.”
Hakane Khairiyya ta faɗa kafin ta yi ciki agaggauce, dan shiryawa su Su Aisha sun jima da tafiya, kusan kullum haka suke wani zai zauna kafin Ummu ta gama komai sauran su tafi in ta gama sai ta amshi mai zaman.
Muhammad na naniƙe da Ummu, Khairiyya ta fito ta miƙa masa hannu alamar tawo mu tafi, ya maƙe kai jikin Ummu alamar ba zai je ba Khairiyya ta ɗan masa dukan wasa ta ce karkazo ɗin ta fita tana dariya Ummu tace “Lala kika dakeshi sai na rama masa.”
Sai yanma lis Hajiya ta dawo kamar shekaran jiya yauma kasuwa taje haka akai ta shigo da kayan da ta siyo a kasuwa, wanda duk kayan bikin Ummu ne da amarya ke buƙata na gida.
Ummu tayi tayi ta amshi wani abin agunsu na cinikin su taƙi filin ta guda ta siyar dan yiwa Ummu kayan ɗaku.
Yauma saida Ummu ta yi kuka gami da godewa Allah ya amshi tasu mahaifiyar ya basu wata.
*****
Kusan kwana uku tsakani Kawu ya aikawa yace ummu ta Faɗawa Faruk in sun shirya shida iyayen nasa sa su zo ranar Lahadi.
Daɗi cika Ummu yayi, dan tanason Faruk sosai ji take tamkar ta janyo gobe tazo ta faɗa masa danma yanzu kunyar kiransa awaya take da tuni ta kira ta faɗa masa.
Ko da daddare kasa faɗa masa tayi, amma shi kansa yadda take hirar yasan tabbas tana cikin farin ciki.
Washe gari kuwa tun kan ta faɗa masa yace “wai Matar ya ne, naga yau annashuwar ta daban ce kusan ma zance tun jiya.”
Murmushi kawai ta yi ta rasa me yasa bakin ta ya yi mata nauyi, duk kuwa da yadda take son faɗa masa.
Dubanta ya yi tsaya ya ce, kafin yaɗan tsai da idonsa kanta na wani lokaci, Ance, “in zo ne?” Kome tambayar ta mata bazata sai duk taji kunya ta kuma lulluɓe ta.
Dariya ta yi, Nasani yaushe aka faɗa ya tambaya cike da ɗoki.
Dariya tai jiya ne ta ce ahankula.
“What!, lallai ma yarin yar nan wato shine kika min baƙin cikin kwana cikin farin cikin da kika kwan ko.”
Shiru tai taɗan kama kunnenta tana dariya alamar ayi haƙuri.
“Ya zanyi, ai ke amarya ce bakya laifi yanzu yaushe suka ce aje?” Ya faɗa murya asanyaye yana wani langaɓar da kai.
Dariya ta yi kafin ta ce, “to mene hakan kuma?” Shima murmushi ya yi “baki faɗan ba yaushe ne?” “eh jibi suka ce in kun shirya.”
“Wayyo Allah inama yau ne, ni wallahi ji nake kamar in munje kawai in tubure sai an ɗaura auren kawai inzo in tafi da matata.”
Dariya tasa jibeka kamar gaske wai kasa aɗaura.
Kallon ta yai eyye wato kina nufin bazan iya ba ko lallai naki wasa.
Nifa bance ba zaka iya ba kawai dai kawai dai ta faɗa gami da fashewa da dariya.
Au kawai dai kawai dai kuwa zan baki mamaki wallahi ya faɗa da alamun dafa gaske nake.
“Ni dai ayi haƙuri pls Dear” ta faɗa gami da kashe murya.
Da sauri ya kalleta “me kika ce Please dan Allah ki maimaita” ya faɗa a marairai ce.
Kanne kai ta yi gami da yin cikin gida.
Girgiza kai yayi yana murmushi kafin yasa yara su miƙa mata kayan da yazo dasu, yaja motarsa ransa fes yai gida.
Ganin kayan kawai girgiza kai ummu tayi Faruk bazai canja ba har abada tayi tayi ya dena mata wahala yaƙi.
******
Koda Faruk ya koma gida mum ɗin su ya fara sanarwa, tai ta murna dan ita da kanta ta ƙagu taga Faruk ya auri Ummu hanin nan tasa yadda ya damu da ita da yadda yake son Ummu hani itama sai taji duniya tana son yarinyar.
Kusan kowa na gidan nason ummu hani, Musamman da ya kasance da aure Faruk din kesonta, gashi tun haɗuwar su da yarin yar nutsuwa ta kuma saukar masa duk da cewar ya canja ada anma bai kuma nutsuwa kamar yanzu ba.
Ranar Lahadi kuwa kamar yadda aka sa Abban Faruk da shi da Amininsa da ƙannensa guda uku sukai gidan kawun su Ummu Hani, Aminin Abban Faruk yayi yayi ya bari su suje yaƙi yace shi yaci burin ya ga auren faruk dole sai yaje anyi komai a idonsa, sukai ta masa dariya.
Anyi sa’a kaf kawunnan Ummu sun hallara, dan duk sun tsorata mutun ɗaya ne bai zoba shima ya ce a bada uzirinsa.
Sun sha mamakin iya mamaki da wanda Ummu ɗin zata aura, dan su zaton su wani ne kawai cikin ƴan unguwa ganin mahaifin Faruk da kansa ya kuma basu mamaki.
Tun kan ayi batun ƙannen ummu Mahaifin Faruk ya ce sunyi da wajewa kan cewar zasu riƙe mata su.
Kusan abinda yafi yiwa kawunnan Ummu daɗi kenan, dan kam su basa son ace za’a kawo musu su.
Aminin Abban Faruk Alhaji Sulaiman ya ce Anmma ya kuke gani?, kune a haƙƙu da ku kula da su in kun bamu dama sai mu ɗauka ɗin ba musu suka ce sun bada.
Nisawa ya kumayi kafin ya ce sai kuma batun bin cike, zaku faɗa mana tsawon lokacin da zamu dawo dan muji matsayar ku dan mu tuni mun gama namu binciken.
Da Hanzari Kawu Musa ya ce ai muma mun gama namu sai dai kawai asa rana.
“To Alhamdulillah” Alhajin sulaiman yace, “daman yaro yace sunyi da yarinya za’a ɗaura aure sai asa ranar da za’ai biki daga baya.”
“Hakan yayi kyau” inji Kawu musa.
Nan aka ɗaura auren Ummu hani da Faruk kan sadakin dubu hamsin da kudin nagani inaso dubu ɗari biyu da hamsin jimilla dubu ɗari uku.
Kawunnan Ummu kam sun ruɗe sukai ta zuba godiya, kai kace sune aka bawa ɗiya basu suka bayar ba.
Bayan an ɗaura ne kawun Faruk yace zuwa jibi za’a kawo lefe sai ku faɗa mana ina ne za’a kai.
Shiru kawu Musa yayi kamin yace “laife kuma na ɗauka cewa kukai za’a ɗaura zuwa wani lokaci ayi biki, in akace biki nan kusa gaskiya kamar an mana tutsu.”
Murmushi Abban Faruk yayi kamin ya ce “kawai kawowa za’ai dan ta ɗinɗinka kafin lokaci da aka sa.
Nan aka watse bayan tsai da matsayar su Kawu zasuyi shawarar lokacin da suke ganin ya dace asa…..
Bayan tafiyar iyayen Faruk kawunnan Ummu hani suka rabe kuɗin a tsakanin su, yayin da Kawu Musa ya ce gobe zai je ya samu ita ummu ɗin, haka suka watse kowa cike da farin ciki.
Shiko Faruk tun bayan tafiyar su Abbansa ya kasa zaune ya kasa tsaye, jira yake kawai su dawo yaji ya sukayi dan tun jiya yake roƙon Abbansa ya yadda aɗaura auren, yace ina shi ai an dena haka.
Aiki suna dawowa tunma kan su firfito, yai gun motar da hanzari Kawu ƙarami ya nufa dan yasan shine kawai zai iya faɗa masa me akayi.
Shima kawun murmushi yai kafin yace wato yaran yanzu ba kunya, to an ɗaura shikenan.
Ɗan tsalle Faruk yayi gami da rungume kawun, nagode sosai kafin ya sake shi ya kamo hannun Dad ɗinsa Dady nagode.
Kwace hannunsa Dad yayi “kaga ni nagaji, me makon ka taren da ruwa, sai ka wani taren da surutu” duk suka sa dariya.
Cikin gida Faruk ya yi da Hanzari yana kiran, “Mum, where are you?”
Fitowa ta yi lafiya dai ake min wannan kira haka sai kace anban ajiya.
Dariya yasa gami da rungume ta, “albishirin kallon sa ta yi goro, Finally, kinyi sirika.” ya faɗa yana dariya.
Ɗan dukansa ta yi na wasa, wato kai Faruk baka da kunya ko.
Ɗan tsuke fuska yayi “kai mum dan Allah shikenan ba zan murna ba,” dariya suka sa baki ɗaya.
Ɗakin sa Faruk ya yi inda ya kira Ummu Hani, tana zaune tana yiwa Usaina wanka inda Sadija ke shafawa Hasana mai, kukan wayar Ummu Hanin yasa Sajida sakin Hasana tai sauri ta miƙo mata wayar bayan ta amsa mata kiran.
Hajiya ce ta taso jeki ki amsa wayar kawo in ɗauraye ta Hajiyar ta faɗa.
Murmushi Ummu tayi, ta ce to kafin tayi ɗaki bayan ta ce Assalamu alaikum.
Shima amsawa yayi kan ya ce wani abu ta gaidashi. Amsawa yayi kafin yace albishirin ki, goro ta ce. “Anfa ɗaura kin zama matata.”
Dariya tasa, wallahi Faruk ka cika wasa sai kace ɗaurin auren film,” Ummu ta Faɗa da alamu bata yadda da batun sa ba.
“Lallai yarinyar nan wato gani sarkin makarya ta ko.”
“No Ba haka bane ayi haƙuri kaji angon Ummu Hani.”
Murmunshin jin daɗi yayi, kafin ya ce “To yanzu yaushe zaki tare.”
Ita har yanzu bata ɗauki batun nasa gaske ba, biye masa kawai tayi tace yo ni ai duk abinda mijina ya ce shi zanyi koma yanzu sai a tare ɗin.
Daɗi ne ya kuma cika Faruk ya ce karfa daga baya kice bakisan zance ba,.. Haka sukai ta hirar su cike da Farin ciki da ƙaunar juna.
*****
Shi ko Alhaji Sulaiman daga gidan nemawa Ɗan Aminin nasa aure, gida ya wuce kusan tun yarinta suke da Alhajin su Faruk wannan yasa kusan komai suke tare komai kuma ɗaya zaiyi sai ɗaya ya sani.
Wannan yasa duk da cewar Alhaji Sulaiman ɗin ɗiyarsa da yake mutuwar so bata da lafiya, bai fasa zuwa neman auren ba.
Direban sa na parker motar ya fito yayi Ɓangaren ɗiyar tasa. Kamar ɗazu tana kwance yadda ya barta, ƙarasawa yayi ya riƙo hannunta Fatina ya jikin.
A hankula ta ce “Dad ka dawo?” “Eh” ya ce ta kuma cewa “Dad ya kuka yi da su?”
Ɗan kallon ta yayi kafin ya ce, “an dai ɗaura jibi zasu kai lefe asa ranar biki.”
Wani baƙin ciki ne ya daki zuciyar Fatima, wai an ɗaura auren Faruk da wata daban ba ita Fatima ba, shiru kawai tayi kafin ta ce Dad kaje ka huta kaina na ciwo banson magana.
Sai da ya kama mata kan tukunna ya fice. Yana fita ta hau kiran wayar Faruk kusan bugu uku kafin ya ɗaga. “Malama kin fa damen lafiya?” Da abinda ya amsa wayar kenan.
“Eh ai dole kace na dameka, bugowa nai in maka murna kafin in bugo inma jaje, dan wallahi ina tabbatar maka wannan yarinyar baka isa ka aureta ba, ina faɗa maka bama ita ba babu wata mace da ta isa in raba namiji da ita.” Fatima ta faɗa a hasale.
“Sai da ka gama cutata sannan kazo kace wata can zaka aura.” Kan ta ƙarasa yama kashe wayar tako rushe da kuka.
*****
Washe gari kawun Ummu Hani yazo tana zaune tana Fanke, Allah ya taimake ta babu mutane dan fitowarta kenan da sassafe ya zo.
Kuɗi ya miƙa mata, “Ungo nan.” yace bayan sun gaisa sai da gabanta ya faɗi ta amsa jiki na rawa.
“Dubu hamsin ne kuɗin sadakin ki, jiya sunzo an ɗaura muku aure, sai kiyi tunanin lokacin da kike ganin ya dace zamu faɗa musu matsayin lokacin biki ya faɗa bayan ya miƙe, ni zan wuce.”
Kasa magana tayi wato da gaske an ɗaura ɗin, har ya fita ya juyo, “yawwa sun kawo da kuɗin kayan zance nagani inaso, mun ajiye su agunmu zamu cika mu miki abinda ba’a rasa ba.”
“To shikenan kawu na gode.” Kawai ta ce, bayan ta juye kaskon farko na fanken da ta kwashe da bata san ko na nawa bane ta bashi, ya amshe ya yi waje.
Tama rasa me ke damunta, duk da cewar kamata yayi tayi farin ciki sai duk take jin akasin haka.
Duk da batasan yadda ake ba anma tasan kawunnan ta basu kyauta mata ba, ai da sai ko sati ne su nema su yi bincike kan Faruk ɗin.
Wata zuciyar ce ta ce mata karki damu Allah na tare dake insha Allah bazai haɗa ki da mugun mutun ba, sai alokacin ta ɗanji sanyi aranta tuna Allah datayi.
Sai bayan ta tashi sannan ta shiga cikin gida ta bawa Hajiya kuɗin ta faɗa mata yadda sukai da kawu.
Ita kanta Hajiya bataji daɗin abinda kawunnan sukai ba, sai dai ɗiya tasu ce ba yadda ta iya.
******
Kamar yadda suka Faɗa kuwa iyayen Faruk kwana uku tsakani aka kawo lefe, lefe ɗan ubansu, kai zaka rantse da Allah cewar ɗiyar me kuɗi zai aura yadda ya zage ya mata kaya iya kaya.
Su kansu dangin Ummu Hani mamaki iya makaki suka yi, yayin da iyaye mata ke ta fatan inama da ace tata diyar aka kawowa.
Muje zuwa, Wasa farin girki, Yanzu aka fara labarin, don’t forget to follow.