Skip to content
Part 20 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Fatima ce zaune a gaban dadinta dan amsa kiran da ya yi mata, Fatima ya kira sunan ta wannan yasa gaban ta faɗuwa dan ta jima bata ji ya an baci sunan ta ba sai dai ya ce Baby na.

A nutse ya ce alfarma nake son kimin jiya munyi waya da Abban ku wato yana nufin mahaifin su Faruk, gaban Fatiman ne ya cigaba da faɗuwa tsoron ta kar Dady ɗin yace alfarmar ta janye daga auren Faruk yake nema wanda ta sa ni bazata iya wannan alfarmar ba.

Jiya munyi waya da shi yake faɗamin ya miki miji yana son nan da abinda baifi wata ba zaki tare.

A hankula tayi ajiyar zuciya dan taga alamar Dad bai san waye aka bata ba, a nutse ta ce shikenan Dady insha Allahu zaka same ni mai biyayya.

Daɗi ne ya cika Dady yasan halin Fatima da rikici bai tsammanin zata amince ba, albarka yasa mata kafin ya ce yanzu dai kimin lissafin duk abin da kike so zan ce masa ya turo angon ku gana, zan kuma yiwa antin ku magana kan abinda ya da ce a siyo.

Godiya Fatiman ta yi ta zubawa gami da ƙoƙarin ɓoye murnar ta tasan tunda Abban yaƙi faɗawa Dady ko wa ya bata baya son ya sa ni ne se an ɗaura aure wannan yasa itama bata nuna tasan zancen ba.

Koda ta koma ɗakin ta gado ta faɗa cike da farin ciki, wayar ta da ke ruri yasa ta ɗauka ba tare da ta duba me kiran ba ranta tas take jin sa.

Sallamar da yayi cikin muryar sa mai cike da kwarjini yasa ta amsawa rai a bace, mun tashi Lafiya Nasir ya tambaya.

Lau kawai ta iya cewa kafin ta ce irin wannan kira da sassafe haka lafiya dai, yaji babu daɗi ya dai daure kafin ya ce daman faɗa miki zan yau zan tawo, to se ka dawo ta faɗa a hasale.

Har ta kashe wayar ta kuma kiran sa, Ko aje wayar baiyi ba, idanun sa na kan wayar baima san mai yake tunani ba kiran ya shigo sanin masifar ta yasa da hanzari ya ɗaga.

Yawwa murna zaka tayani nanda wata guda zan zama matar wani ta faɗa cike da murna.

Ransa ya sosu gabansa ya faɗi a hankula ya ce “to Allah yasa albarka” ya kashe wayar.

Hawayen da ya zubo idanun sa yasa Ayatullah da ke gefen da sa dariya, wallahi mutumin nan kana ruwa wai mace kakewa kuka macen ma ragowar wani.

Yaushe na yi kukan inji Nasir yo ai gwanda ni mutun nake so, kai kuwa baka san yarinya ba karshan ta ma a mafarki kuka haɗu, inaga ma aljana ce amma ka bi ka ɗorawa kanka masifa.

Murmushi Ayatullah ya yi yo ni yaushe na faɗa ma ina sonta kawai na kasa mantawa da ita ba kuma so bane ina mamaki ne yadda yarinya karama irin ta ta iya haihuwa.

Dariya Nasir ya yi kaji dashi shi yasa ai harda zana ta, ko baka yadda ba son ta kake, ni kaga bari in wuce ai mun gaisa kar jirgin da zan shiga ya tashi.

Aikam dai ban gode ba yau kwanan ka nawa anan sai yau zaka wani zo shima agaggauce.

*****
Shiko Faruk bayan barin sa gidan su Ummu Hani da takardun Salma washe gari da wuri ya shirya cikin shaddar sa sky blue, yasan a lokacin da ya shirya Umman su lazimi take Abba kuma yana masallacin cikin gida wannan yada kawai ya fi ce yana son yin abubuwa da yawa a safen nan.

Kai tsaye Buk new site ya wuce, senate building ya nufa, inda aka tanada dan parker motoci ya aje motar sa inda ya yi office din professor Bashir Umar wanda shine matsayin Registerer wato mahaifin su Umar aminin sa.

Sectary din sa ne ya masa iso zuwa cikin office ɗin. Mutumin na zaune yana tulawar Alqur’ani kusan ya zame masa ɗabi’a in babu komai a gaban sa babu kuma baƙi yana bitar karatun Alkur’ani ne.

Sai da ya kai aya sannan ya ce, “A’a Faruku kaine a office din fatan dai lafiya?” Ya faɗa lokaci guda cike da kulawa fuskar sa sanye da murmushi.

Murmushi Faruk yayi ya ɗan rissina ya gaidashi mutumin ya miƙo masa hanu “a’a salamun Alaikum” suka gaisa.

Faruk ne ya miƙo masa takaddun Salman yana faɗin daman alfarma nazo nema, Admission ne ta ci jamb din ta sosai sannan post utme ma haka, to first list ya fito bata samu ba na ce bari inzo kafin a fidda second list.

Karɓa dattijon yayi yana dubawa, hakkun kam ta ci, to abinne da yawa kasan masu neman Buk da suka cancanci adauke su sun ninka adadin da makaranta ke buƙata.

Bari in ma deputy register magana, ko da shike bari in duba list ɗin da ya kawon jiya jibi muke sa ran fidda sauran list ɗin.

Jamb number din ta da post utme Number ya dauka yana sawa cikin list din da zasu fitar sai ga sunanta.

Kaga ikon Allah anma bata admission tana cikin second list, an bata optometry godiya Faruk ya hau yi, Dattijon yace No karka damu ta cancan ta ne ko baka zo ba sunan ta zai fito.

Murmushi Faruk ya yi kafin ya ce “kuma zuwa yaushe zasu fara registration?”

Eh to gaskiya bamu tsayar ba se an fidda calendar anma dai ba zai kai February ba.

“Oh anma kusa,” inji Faruk eh to gaskiya an kusa prof. Ya bashi amsa.

Ko ita ce sirikar tamu prof ya tambaya murmushi Faruk yayi a’a ba ita ba ce, sai ta tare nake son ta fara karatun ita wannan yar uwar ta ce

To Allah ya taimaka, bari in ma printing admission letter din kawai nan Faruk yahau godiya.

Yana tafe a mota akan hanyar sa ta zuwa gidan su Ummu Abba ya kirashi.

Na zo ɗakin ka har ka fita na ɗauka sai 9 kake fita, eh Abba naje BUK ne ok yanzu kazo inason ganin ka tun shekaran jiya nake son muyi maganar muke sabani tom ya ce ya juya motar zuwa gida.

*****

Ita kuwa Gwaggo ko da taje gidan Kawu Musa ta tura Ibrahim ɗan gidan kawun kan ya kira sauran kawunnan nasu.

Anyi sa’a mutun guda ne baya nan cikin su. Tana fara bayanin abinda ya kawota Kawu Bala ya hau faɗa “ku me yasa baza ku mata ba, ai kuma yar ku ce.”

Cikin hasala Gwaggo ta ce, “Eh yar mu ce anma ku Allah ya ɗorawa hakkin kuyi mata tunda ku dangin ubanta ne.
“Wallahi inhar bakuyiwa yarinyar nan kayan ɗaki ba wallahi sai na kaiku ƙara sai duniya taji abinda kukayi kuka bar yara ƙanana cikin wani yanayi suke ciyar da kansu suna rayuwa su kaɗai.

Ko ita babbar koda namiji ce bai ci ace tana kula da wasu ba bare kuma mace ce.

Nan da aka kawo kuɗin Aure da kayan aure nunawa kukayi kune iyayen ta ku ke iko da ita yanzu kuma da aka zo batun kaya wato mune iyayen ta to wallahi baku isa ba.”

Sai da suka hau sama suka faɗo, faɗa kariris tukunna suka yadda zasu haɗa kuɗi suyi mata kayan ɗaki nanda wata guda.

Koda gwaggo ta tafi su Kawu sukai faɗa su kam Sule ya cuce su wato suna nufin Mahaifin su Ummu Hani, Kawi idris ya ce shi yasa ai lokacin auren akai akai kar ya auro zurriyar gidan Malam Abdullahi tunda shi baida ɗa namiji ko ɗaya yaƙi.

Ai kabari kawai gashi abin da ake gudu mu ya bari dashi, daman dan kar ta tara masa yara mata ne ashe mu zata haifawa, yanzu da maza ne ne waye zaizo yana mana fuffukar munƙi kula dasu.

Uhum ni wallahi raina a bace yake kana lallon yarin tar rashin mutuncin da ta mana lokacin mutuwar uwar ta, yanzu ku kalli yadda yar uwar Tata tazo ta ci mana zarafi.

Ita kuwa Gwaggon koda ta koma gida ta kira Ummu Hani ta faɗa mata ta ce musun wata guda da sati biyu.

Farin ciki fal ran Ummu tun daren take son faɗawa Faruk tana jin nauyi wannan yasa ta bari tun da yace zaizo kan batun Admission din Salma ta faɗa masa…

Ɗakin Abba Faruk ya nufa bayan ya aje motar sa, Abban na zaune yana karin safe Faruk ɗin ya shiga, cike da girmamawa ya ce Abba gani bayan ya gaida shi.

Yawwa daman ina son in faɗa maka ne ɓarin Hajiya babba mai rasuwa zan sa a gyara maka shi zaku zauna da Fatima gaban Faruk ne ya faɗi ya dai daure ya ce Abba Fatima kuma Ummun fa Faruk ya faɗa fuskar sa cike da tashin hankali.

Murmushi Abban ya yi kafin ya ce yo banda abin Faruku ai kai mijin Mace huɗu ne Ummu tana nan a matsayin ta na uwar gidan Faruk.

Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, Faruk ya faɗa a ransa kafin ya ce amman Abba…. Ɗaga masa hannu Abban ya yi, kafin ya ce kaga ba shawara na kiraka muyi ba, ba kuma alfarma na ce kamin ba, umarni na baka in kuma umarnin nawa ne bazaka bi ba to ka faɗan inji, kayan lefe nan da Sati zasu kammala zamu kai, sauran inji kayi wani zancen da ba haka ba wallahi sai na saɓa ma.

Sun sun Faruk yasa ƙafa ya bar ɗakin shi kam ƙarshen rashin adalci da za’a masa arayuwa shine a sa ya auri Fatima, kwata kwata bata tsarin matan da yake son zama dasu ko da ace shi yana da burin zama da mata huɗu baya jin zai iya zama da Fatiman.

Ransa ya ɓaci sosai fasa zuwa gidan su Ummun ya yi, ya nufi gidan su Fatima.

Kasan cewar sashen ta daban yasa kai tsaye bangaren ta ya nufa, a baranda ya hangeta tana saman bene kai kawai yasa ya shiga falon yana ƙoƙarin hawa benen ya dora idanun sa kan ta tana ƙoƙarin saukowa.

Da murnarta ta sauko sanye ta ke cikin ƙananan kaya kusan sun zame mata ɗabi’a da wuya ka ganta cikin kayan hausawa, riga ce da dogon wando sun mata kyau sosai dan ita ɗin mai kyau ce ba karya.

Ai na ganka sanda ka shigo sannu da zuwa ta faɗa fuskar ta ɗauke da murmushi, tsaki Faruk yaja kafin ya ce “Ni kinga malama ba sannu da zuwa nazo kimin ba kashedi nazo in miki.

Murmushi ta kuma yi wanda ya kufula Faruk ɗin kafin ta ce koma dai kashe din mene ka dai zauna ko.

Cikin faɗa yake magana, ba zan zauna ba in kuma zaki kamani ki zaunar dani se in gani.

Matsowa ta yi, to mene a ciki ni ba baƙuwae zafi ba ce sai in zaunar da kai ɗin ta fada tana ƙoƙarin kamo hannun sa.

Tankaɗe hannun ya yi “wai ke me yasa Dabba ce baki da tunani,” kallon sa ta yi ranta ya fara ɓaci bata ce komai ba yayin da shi kuma bai damu da damuwar da ta shiga ba ya ce “ki sani ni Faruk nafi karfin zama da mutun irin ki.”

Cikin zafin rai ta ce “wai Faruk mai ne haka ne, me na maka ka tsane ni haka son ka fa kawai nake.”

“To ni bana son ki kuma bazan zauna da yar iska ba wallahi,” Ya faɗa bayan ya tako daf da ita.

Taɓe baki tayi kafin ta ce, “Kuma dai, wallahi kaji dashi dan inni yar iska ce kaima ɗan iskan ne tunda tare mukai watsewar mu.”

“Ke Malama dakata kema kinsan ni ba ɗan iska ba ne ke kika lalatani.”

Murmushi ta yi “Muka dai lalata juna ko?”

Hannu ya kai zai maketa tayi saurin kaucewa, “kar ka sake.” Ta faɗa alamar kashedi naji zan ɗauki komai banda duka wallahi.

Tsaki ya yi kafin ya ce, “Na faɗa miki koma me kikai wa Abba ya ce in aureki ki je ki faɗa masa ke kin fasa na faɗa miki.”

“Hmm ai in faɗa maka ni ɗuwawu ce zama dani dole, ka shirya kwasar amarci dani kawai malam.”

Ransa ya ɓaci sosai, “Shikenan tunda kinga haka ki ka zabarma kanki ki shirya rayuwa cikin kunci dan wallahi ni bani zaki zauna dashi ba sai dai gangar jikina bazaki taɓa samun jin daɗi ba indai har ni nake matsayin mijin ki, zuciya ta da ni kaina na Ummu ne.”

Dariyar ɓacin rai ta yi, “Eh naji a haka nake sonka zan kuma zauna da jikin naka.”

“Ok, then welcome to the hell dear.” Ya faɗa kafin ya fice daga falon.

Yaraf Fatima ta zube gami da rusa kuka ita kam tanason Faruk sai dai batasan yadda za’ai ta cire masa ƙin ta ba.

Ta rasa me yasa kullum yake kallon ta a matsayin yar iska bacin da ita arayuwar ta bata taɓa mu’amala da wasu mazan ba sai shi, amma shi kullum kallon karuwa yake ma, abin da yafi mata baƙin ciki shine ta sha faɗa masa shi kaɗai ta sani yaƙi yadda.

Kai tsaye motar sa ya nufa a fusace ya ja motar, sai da ya bar area ɗin gidan su Fatiman Sannan ya faka motar a gefen titi ransa suya yake masa idanun sa sun kaɗa sunyi jajur ji yake tamkar yasa kuka, ya rasa wannan wane irin na ci ne na Fatima, yarinyar ta na da matsala in ta sa kulafuci a abu dole saita samu ko ta yaya ne.

Shi babban abinda ke damun sa yarinyar bata da tarbiyyaa banda kuma tsawon rayuwar sa da ita tun yarinta har yau ko sau ɗaya bai taɓa jin son ta ba, ta yaya zai zauna da wanda baya so.

Alamar shigowar saƙo yasa shi ɗaukan wayar sakon Ummu ne na fatan lafiya taga ya ce yana hanya bai karaso ba, kallomin ta na karshe yasa shi murmushi.

“Kasani inata zullumi, fatan dai lafiya, dan Allah kayi sauri kazo duk na ƙagu inganka, Ka iso lafiya masoyina abin sona. Daga matar Faruk”

Aje wayar ya yi kafin yaja motar duk da ransa har yanzu babu daɗi shi ayanzu ma bai san ta yaya zai wani iya faɗawa Ummu wai da Fatima zasu tare ba.

Kai tsaye cikin gidan ya shiga dan ta tashi daga suyar fanke bayan yayi Sallama Hajiya ta amsa daga ɗaki dan Ummun na ban ɗaki, cike da girmamawa ya gaida Hajiyan inda ya shige ɗakin Ummu.

Muhammad na ganinsa ya yo gunsa da gudu ya cafe yaron yana murmushi.

Guri ya samu ya zauna gami da ɗora Muhammad ɗin a cinyar sa yans masa wasa.

Ummu ce ta shigo ɗauke da fara’a a fuskar ta ashe ma kana hanya ta faɗa.

Ki bari kawai Abbane ya tsaidani, kallon sa tayi cike da alamun tambaya bakajin daɗi ne ta faɗa?

Ah haba lafiya kalau nake me kika gani. Ɗan kar katar da kanta ta yi idon ta akansa cike da tambaya, anya kuwa naga duk kayi zuru zuru, ta faɗa.

Towo ashe nayi zuru zuru duk suka sa dariya. Kuma fa kamar baka karya ba ma, yeh you are right yarin yar nan kin karan ce ni da yawa ina sauri ne ban samu na karya ba.

Girgiza kai ta yi na faɗama bana son kake barmin kanka da yunwa ka ƙi ko bai ce komai ba ya yi murumushi. Ina zuwa ta faɗa Muhammad da ke cinyar Faruk ya taso da hanzari ya bi bayan ta. Tare suka dawo da Muhammad ɗin tana ɗauke da plate da ta ɗoro kwanon tuwo da miya da ɗan likidirin da take dama koko yayin da shi kuma Muhammad ke biye da ita riƙe da kofi.

Dariya Faruk ya yi shine kika samin ɗa aiki ko, ya faɗa yana ƙoƙarin amsar kwanukan hannun ta. Uhum inafa bani na sashi ba ganin kofin sa ne ya ɗauko, ai dole ya ɗauko yaga kin ɗauko masa koko.

Basshi kawai yaron naka ai akwai rowa baya son abaka ne su kai dariya duka.

Buɗe kwanukan ya hau yi ta ce ɗumame ne ka ci kan in gama wanke wanken can ta faɗa bayan ta amshi kofin hannun Muhammad ta tsiyaya masa kokon ya koma gefen Faruk ya hau sha ita kuma ta fi ce daga ɗakin.

Binta da ido Faruk ya yi kwata kwata ba’a kyauta masa ba ya gama tsara rayuwar sa da Ummu Hani anbi an kawo masa wata daban.

Yana cin tuwon lokaci lokaci yana bawa Muhammad a baki ransa babu daɗi sai dai sosai yaji daɗin tuwon Ummu akwai iya girki.

Hajiya ta yi ta yi Ummun ta bata kwanukan ta wanke ta ƙi ta ce ai ba yawa inma ta je ba lallai ya ci a nutse ba zasuyi ta magana ne dole Hajiya ta kyale ta, ta gama da kanta.

Ya kusa cinyewa ta dawo “sarkin jan jani har yanzu baka cinye ba.” Dariya ya yi, “kefa nake jira zo muci.”

“Yo ai ni bance ma inajin yunwa ba nafa karya.

Allah se kin ci ya faɗa matsawa ta yi tasa hannu ta fara ci ba tare da ce komai ba, aransa ji yake inama ace ahaka zasu rayu abun su daga shi sai ita, anma an masa cikas.

Sai da ta fidda kwanukan bayan sun cinye take ce masa “Jiyafa naje gidan Kawu,” murmushi ya yi, “Tom ina jin ki ya ku ka yi?”

“Eh to sunce gaskiya nanda sati shida, mantawa da damuwar da yake ciki ya yi farin ciki ya lulluɓe shi wayyo Allah, Alhamdulillah zan so ganin ranar da zaki kwana a ɗakina wayyo ni.” Dariya da kunya suka rufe ta tasan yanzu sai ya fara wasu zancen da kunnen ta ba zai ɗauka ba da sauri ta ce, “Yawwa admission ɗin ya ku ka yi?”

“Assha kinga inata tunanin mema zan faɗa miki na manta duk ganin ki ya mantar dani.” Dariya ta yi ka cika zaulaya wallahi.

“Ɗazu naje ashe ma gajen haƙuri na yi sunan ta yana second list sati mai kamawa zai fita anma na ma amso mata admission letter.”

Murna tasa ta rungume shi ba tare da ta sani ba tana zuba godiya, daɗi ne ya cika shi kome ta tuna ta hau ƙoƙarin sakin sa sai dai ya riketa sosai ahankula ya ce, “Can we stay like this for a while please…”

<< Ummu Hani 19Ummu Hani 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×