Kukan da Ummu tasa ne yasa dukkan su kallon bakin kofa ba wanda ya tsanmaci ganin ta ba ɗakin ta shiga kai tsaye gun Faruk ta nufa tama mance cewar iyayan sa fa sirikan ta ne hannun sa ta kamo tana kuka,
“Dan Allah Faruk ka jikaina karka sake ni wallahi bazan iya rayuwa ba auren ka ba, sakin da zaka min shi ne zai zamto cutarwa a gare ni bawai zama da kai ba dan Allah ka dubi rayuwa ta in har ba son gina kiyayya maras yankewa tsakani na da kai ba kar kayi sakin nan bazan ta. . .