Satin su Ummu ɗaya da dawowa Dady ya dawo sai dai ba gawar Faruk lokacin da suka iso da Umar yan uwa kowa na zuba idanun yaga an shigo da gawar sai dai ba ita ba dalilin ta da yawa sun share hawayen da suke ta zubarwa dan tunanin da ya ziyarci ransu na tabbas Faruk bai mutu ba, sai dai ita Mami harma da Ummu Hani wannan tunanin kwata kwata basu yi shi ba dan ransu ya basu Dady ba fa zai bar Faruk ya tawo ba in har yana da ran.
Wankan da Dady ya shiga kafin Mami tazo da yadda ake ta magana da san barka na rashin mutuwar Faruk ɗin yasa Mami da Ummu fara wasi wasi har suka fara tunanin da sauran Jama’a suke.
Ganin Mamin zata fara shakku yasa ta fitowa harabar gidan dan tambayar Umar ko sunyi maganar gawar da Dady, Umar ɗin na tsaye jikin mota duk ya faɗa bazaka ce shi dinnan ne mai garun jiki ba, a nutse ya gaishe da Mami ta amsa a hanzar ce kafin ta ce “Ni kuwa ya kuka yi da Alhajin ya yi maka maganar Faruk ɗin kuwa?”
Girgiza kai yayi a’a tunda muka dawo ya shiga motar ya riƙe kansa da na masa sannu ma da kyar ya amsa shi yasa ban tambaye shi anma gaskiya banga alamun yazo da gawar nan ba sai dai in daga baya zata zo, jin ya ce Dady din baya jin daɗi yasa ta saurin komawa ɗakin bai fito ɗin ba kuwa da hanzari ta tura toilet ɗin a kas ta ganshi a zube salati tasa ta hau kwala kira waje.
Kai tsaye asibiti suka wuce da shi hankali tashe yayin da Ummu tama rasa mai zatai tunani tanason yadda da batun mutane tana tsoron sawa zuciyar ta hope ya zama ba haka ba sai dai ganin jikin Dady yasa ta kuma ruɗewa sosai.
A asibiti an bawa Dady taimakon gaggawa bai farka ba sai washe gari wayar sa na hannun mami tunanin ta za’a kira ace gawa tazo sai dai shiru jin jinin Dady ne ya hau yasa suka kasa tambayar sa game da Faruk ɗin.
*****
Shiko Ayatullah kusan kwana huɗu kenan yana jelen neman Ummu Hani babu ita ba dalilin ta tama dena zuwa inda suka saba zama tun yana tunanin hidindumu suka mata yawa har hankalin sa ya kawo kodai an sallame su sun ba ƙasar sosai hankalin sa ya tashi bayan binciken da yayi na amma mijin nata transfer sai dai ba wanda ya san inda aka mai dashi.
Cikin yan kwanakin duk Ayatullah ya bi ya damu abu biyu ke damun sa in rashin ganin Ummu da kuma inya tuna waifa duk damuwarsa kan matar wani ne tsoro kan cika na in ya mutu a wannan halin ya ce ma Allah mai to.
Kusan tun yana gudarwa tunanin yarin yar har takai ta kawo ya kasa yakar zuciyar sa da ya zauna indai ba Patient yake dubawa ɗan lokacin da sukai tare shike dawo masa kwata kwata ma ya tattaro kayan sa daga gidan sa ya dawo asibitin indai ba lokacin duty din sa ba ne to yana bakin bishiyar da suke zama yana son ɗora mata laifi na tafiya bata masa Sallama ba sai dai wani gun na zucuyar sa na tunanin to mai ne alakar su da zata masa sallama shifa a gunta ba komai ba ne.
Yanzu karatun ma ba sosai yake ba duk da kuwa sun kusa komawa sch inda zasuyi final paper duk ya zaƙu ya dawo Nigeria ko zai ganta duk bashi da tabbas ɗin inda aka maida mijin nata.
Ganin gidan ya yoye lokacin da aka fito da Dady yasa Ummu Hani bin kannenta suka tawo tare duk da tana som sanin ya ake ciki game da Faruk ɗin sai dai tasan maganar bazata yuwu a ranat ba dole sai Dady ya farfaɗo ita kuma tasam in aka barta ita ɗaya a gidan tunanin ranar da ta fara zuwa gidan ita da Faruk ne zai dame ta da yadda ya kullum maganar sa ita ce yadda zasu rayi a gidan ita dashi da kannenta da abinda zasu haifa ne.
Tunda suka hawo a adai dai ta Sahu babu mai maga dai dai da Muhammad tunda suka dawo duk jikin sa ya yi sanyi tamkar yasan mai ke wakana. Adaidai bakin lokacin su aka sauke su har lokacin motar Faruk na gun sai a lokacin Salma ta tuna dana sanin biyowa ta nan tayi aiko dik yadda suka so ɗauke hankalin Ummu sai da idon ta ya faɗa kan motar duk dauriyar su kukan Ummu sai da ta sasu kuka dan Faruk ɗin ne ya dawo musu a rai da kyar suka lallashe ta suka jata zuwa Lonkon su.
Tafe suke tana binsu a baya tun tana binsu har ta ja ta tsaya ta dubi Aisha ta ce, “Aisha ina gidan namu ne karku cemin dai na haukace koda yake nasan rashin Faruk zai iya sani komai.” Ta faɗa tana duba lokon indai har hankalin ta dai dai yake to tabbas babu gidan su a Lonkon sabon gida ta gani a inda take tunanin nan gidan nasu yake sai dai kuma sun wuce shi sosai bare tai tubanin rashin hankalin nata ne yasa take ganin sabon gida a gun.
Riƙo hannun ta Salma ta yi “Ki bari muje gidan mu zamu miki bayanin komai.” Kwace hannun ta ta yi “Kumin bayani yanzu inji in na haukace ɗin in ƙara gaba basai na zo na ɗora muku nauyi ba.”
Cikin kuka Aisha ke magana, “Tun bayan tafiyar ku wasu suka zo suka ce mana gidan namu na gado ne su suka ci shi suka nuna mana komai suna son mu tashi.” Zaro ido Ummu ta yi to ina shi Kawun tana nufin Alhajjin da ya basu gida.
“Eh ya mutu ashe wata uku da suka wuce sun nuna mana takardun wasiyyarsa kan ma abamu daki daya kyauta shi ne suka ce su shago zasu bamu naga bazamu iya kwana a shago ba muka koma gidan gadon su Hajiya to bamufi kwana uku ba a kai ta rikici itama sai tare muka bar gidan muka koma gidan su Salma.”
Kuka Ummu tasa sosao ta ji mutuwar mutumin shine mutun na Farko da ya fara jin ƙan su tun bayan mutuwar Iyayen su shine wanda ya fiye mu dangin su alokacin da basu da kowa sai Allah shine gatan su da Allah ya turo musu sai gashi lokaci guda Allah ya ɗauki abinda kuka take tana musu addu’a shida Faruk su ɗin jigo ne cikin rayuwar su, dakyar aka jata zuwa gidan su Salma din, yan biyu na ganin ta suka yo gunta suna murna ga Umman mu ta dawo…
An dai kusa zuwa karshe da yardar Allah, shin ya kuke gani Faruk ya mutun kuwa? Kamar dai da walakin. Shin Ayatullah zai gano masoyiyar tasa kuwa? Sai na ji ra’ayoyin ku zan ɗora insha Allahu.