Kuka sosai Ummu take harda shessheƙa ganin da gaske yaran nata basu da rai sunƙi kuka, samun kanta ta yi da kasa miƙewa bare ta yi yunƙurin fita dan kiran wani yazo ya tallafa mata. Kursum da tun sanda Yayar tata tayo cikin gida jikin ta ya bata akwai wani abu ita ce ta mike ta biyo bayan Ummun bayan da ranta yayi ta azazzalar ta tazo taga ko lafiya ganin ta jima bata fito ba.
Shiru Falon lokacin da Kursum ɗin ta shigo a hankali ta karasa uwar ɗakin bata son Ummu din ta ganta dan kar taga kamar tana mata labene sai dai shesshekar kukan tasa ta daga labulen da sauri ganin yaran da tayi cikin jini da kuma yayar ta su na kuka yasa ta yi saurin karasawa tana fadin, “Lafiya dai yaya?” Nuna mata su Ummu tayi sai a lokacin ta kula sosai yaran masu riga ne cikin azama ta sa hannu ta yaga rigar duka biyun kasan cewar ta mai zafin nama.
Ɗayan ne ya tsanyara ihu yayin da dayan kuma ya hau wutsul wutsul cak Ummu ta tsaya da kukan ta hau kallon su tamkar ta ce da Kursum ta miƙo mata su sai dai tana jin kunya duda yarin yar kanwar ta ce.
Kursum mutun ce mai kwazo da fasaha ga lura sosai kusan tun Umman su na raye tana faɗa in basuyi wasa ba ita zata zama yayar su a hankali gashi kuwa ita ta tsaya tana kuka kanwar ta, ta biyu ta fita hankali ko da yake ita Kursum harkar jinya take karanta dole tasan abubuwan da basu sani ba game da lafiya.
Tas Kursum ta goge gun da yaran sa shinfide su biss gado kafin ta dauki zannuwan ta shifa toilet din da ke uwar dakin ta hau wanke su bayan ta jona ruwan zafi, sai da ta haɗa ruwan zafin ta sanya kayan jikin shawar tolet din dan bata son fita da su tukunna ta fito ta ce Ummu ta shiga tayi wanka, kafin Ummu ta fito ta ma yaran wanka ta amsowa Ummun abinci ta haɗa mata da tea mai zafi.
Ummu ta fito yaran sau wutsul wutsul suke kamar ance kar suyi kuka tun sanda dayan ya koka duk su biyun ba su kuma ba, sai da ta ci abincin tukunna Kursum ta miƙa mata ɗaya cikin yaran ta ce kamar su daya anma wannan yafi kyau dariya Ummu ta yi ta karɓe shi ta leka dayan haske kawai na hannun ta ya fi anma kamar su da farin har mamaki ta yi dan batasan ana iya ganin kama in yaro na jariri ba.
Kursum ce ta miƙe bari inje kar su ya Salma su biyo ni gyada kai kawai Ummu ta yi yayin da Kursum din ta bar ɗakin, koda Ummu ta ci abinci kwanciya ta yi ta lulluba dan bata jin kwarin jikin ta so tayi tunda yaran sun yi bacci ta fito amma ta kasa.
Washegari da wurwuri Ummu ta yi wanka tama yaranta kafin ta fito tsakar gida kwana biyu Muhammad a gun Hajiya yake kwana wannan yasa sam ba wanda yasan da jariran tun jiya sam ita tasa ba wanda zata fadawa ta haihu kamar yadda tasan indai ba ita ta faɗa ba Kursum bazata faɗa ba sai dai kamar Ummu ta manta hakan ba mai yiwuwa bane tunda baka isa ka hana jariri kuka ba.
Hasana ce ta fito daga ɗakin Ummu ɗin da gudu tana fadin naga anbebi biyu Usaina ta shiga dakin da gudu dan hango mai yar uwar tata ta gani aiko ilai yara biyu ta gani ɗaya na kuka ta fito da gudu tana murna Hajiya ganin haka ta shiga ɗakin dan ta ɗauka da farko shirmen Hasana ne.
Salati ta sa ta shiga dakin Umman su Salma ta faɗa mata abibda ta gani suka duru ɗakin sallallami kawai suke cike da tsoro sai dai kamanin yaran da Faruk ya tabbatar musu yaran Ummu ne to anma yaushe ta haifesu har basu sani ba.
Hajiya ce ta leƙa shago ta kwalawa Ummu kira Ummun ta fito ta shiga cikin gida gabanta ya hau faduwa gani su a dakin ta anma kwarin gwiwar ta na yanzu kusan yafi na lokacin suna ciki tana jin a yanzu zata iya fuskantar koma waye kan yayan ta.
Hankalin Ayatullah ya tashi sosai a razane ya ke kallon Babansa kafin ya ce anma Abba. kafin ya karasa Abban ya ce “Kar kace mun baka sonta ko ba zabin ka ba ce na riga na amsa masa kai din mijin mace hudu ne kawai ka daure inma da wadda kake so to ka tunkare ra da batun su biyu zaka aura ni inkaga na janye batun A’isha to ubanta ya ce ya fasa umarni na baka in har na isa da kai.”
Gyaɗa kai kawai Ayatullah ya yi kafin ya ce, “shikenan Allah yasa hakan ya zama alkairi” “amin” Abba ya ce shikenan zaka iya tafiya anma kaje ka same ta, tom kawai Ayatullah ya iya cewa dan shikam ji yake an kware shi kwata kwata tsarin sa ba farar mace ya fison mai duhu doguwa irin Ummu Hanin sa shi da ace Aisha dinma doguwa ce da to da ɗan sauki sauki watakila in ya daurewa rabsa ya iya zama da ita duda yasan da wuya ya so ta, Ummu kawai ita ke a ransa.
Kwana uku tsakani Abba ya takura masa sai yaje ya samu A’isha dole yau babu daɗi ya nufi gidan Kawun nasa wato gidan su Aisha ɗin, hannu bibiyu aka amshe shi mutan gidan sai wani nan nan suke dashi banda ita yarinyar dab kuwa sai wani yanutsa take har ji yayi kamar ya make ta dan haushi.
“Sannu ko” ta faɗa lokacin da suka ware a zauren gidan shima din a ya mutse ya amsa tasa dariya “oh ashe kaima auren dolen za’a ma ka ce komai dai dai kenan, kallon ta yayi ya watsar itama ta ja tsaki kafin ta miƙe ni kaga bazaka zo kana min isa ba in kaga bakayi ka fada musu zai fi dan ni ba masoya na rasa ba.”
Ransa me ya baci yanzu da wannan maras tarbiyya din akeso ya rayu ina da sake wallahi ya faɗa bai Bata amsa ba ya fi ce daga gidan.
Har ya kai babban titi Kawu Bashir din ya kirawo shi a kofar gida ya tadda shi aiko yasha faɗa ta inda mutumin ya shiga bata nan ya ke fita ba wai shi Ayatullah zai wulakanta ko dan yaga baida arziki shi ne zai ce baya son diyar sa. Tsuru kawai Ayatullah ya yi ya kasa magana.