Ran Ayatullah ya baci sosai kawai ya ki magana ne dan mutumin tamkar uba yake gunsa amma in ba haka ba da tuni ya magantu yarinyar ta ci mutuncin sa sannan ace shi ya yi, shirun da Ayatullah ya yi ya bawa kawu haushi cikin faɗa yake faɗin “Wato ina mana kamin shiru sabida ga dan iska ko.” A kufule Ayatullah ya ce to mai zaka ce tunda ita Aisha din baza tai ka karya ba aishike nan.
Ah lallai koda yake ba laifin ka bane laifina ne da na nace sai anyi auren nan na kuma san. . .