Skip to content
Part 34 of 39 in the Series Ummu Hani by Fadimafayau

Ran Ayatullah ya baci sosai kawai ya ki magana ne dan mutumin tamkar uba yake gunsa amma in ba haka ba da tuni ya magantu yarinyar ta ci mutuncin sa sannan ace shi ya yi, shirun da Ayatullah ya yi ya bawa kawu haushi cikin faɗa yake faɗin “Wato ina mana kamin shiru sabida ga dan iska ko.” A kufule Ayatullah ya ce to mai zaka ce tunda ita Aisha din baza tai ka karya ba aishike nan.

Ah lallai koda yake ba laifin ka bane laifina ne da na nace sai anyi auren nan na kuma san mai yasa baka so sabida kawai ni talaka ne amma ka sani ni din daka raina haka da Uban naka yake Ayatullah bai kuma tankawa ba Kawu ya gama banbamin sa ya ce ya tashi ya tafi ya kuma tabbatar cewar biki ba fashi nan da wata uku za’a a daura aure.

Ayatullah ya jima a mota ransa ba dadi yanzu sam bama auren Aishar ya dame shi ba face yadda zai naimo Ummu dinsa tsoron sa shine to inma ya nemo ta to ya yi yaya da auren ta, yadda yake jin son yarin yar yanzu shikam ya kudiri aniyar ko rokar mijin ta ya sake ta ne zaiyi abu daya ne bazai iya ba shine kisan kai anma zai iya komai dan samun ta matsayin matar sa.

Kusan daga nan ma yawon neman ko zaiga Ummu ya tafi sai dai wayam tun yana tunanin ganin har ran sa ya fara raya masa kodai bats dawo kano din bane dan ko mai kama da ita bai gani ba tunda ya dawo.

A gida ma Abban sa kiran sa ya yi ya haushi da faɗan dan mene zaije ya ma kawu rashin kunya yasan in ya faɗi cewa baiyi ba nan ma Abba kuma cewa zai yi ya karyata kawu dole ya daure ya yi ta bawa Abba hakuri jiki ba kwari.

*****

Salati Umma suka sa lokacin da suka tabbatar jariran gaske ne. Hajiya ce ta fita ta kira Ummu wadda yanzu zuciyar ta ke adake dan yanzu ta kudiri niyar koma mene ya faru kawai.

Umman Salma ce ta ce, “Yanzu Ummu Hani kin mana adalci kenan ko dan mu ba iyaye ki bane, kiyi ciki ki haife duka bazaki iya fada mana ba sam kin ban mamaki wallahi ban taba zaton haka kike ba, ban taɓa tunanin ba iyaye kika daukemu ba.”

Jikin Ummu ne ya yi sanyi kwarin gwiwar da takejin tana dashi duk sai ta neme shi ta rasa cikin shessheƙa kuke take fadin “Wallahi ba haka bane har cikin raina kudin iyaye nane kawai ina tsoron mai zakuce ta zaku kallen bansan ta yadda zan gansar da ku cewar ciki ne dani ba kuma cikin na halak ne bansani ba shi yasa na kasa fade nayi zaton zaku gane sai sai yaddar da kukai dani yasa kuka kasa yadda ciki ne dani wannan ya kuma ban tsoro na kasa fada muku ina tsoron bazaku yadda na sunna ba ne.”

Ruko hannunta Umman su salma ta yi, “ki dena kuka ko duniya sunki yadda dake mu masu yadda ne munsan da auren ki ai ko watannin cikin da haihuwar aka duba watannin auren naki kenan yanzu ki shirya zamu je gidan su Faruk din ko ba komai suga jinin su a kuma gyara rabon gadon da a kai.”

Amshe hannun ta ta yi ta hau girgiza kai gami da durkusawa ta hau rokar su dan Allah ku min gata ku dubi darajar Annabi karku kai batun yaran nan gun dangin babban su nasan in sun aminta nasu ne kwace ce su zawuyi, ni kuma bazan basu ba banson ko kadan Shari’a ta haɗa mu dasu tunda ko kin aminta sukai na halak ne bazan amin ta ba dan Allah ku barmin abuna kaddara ta ce nida su.”

Shiru Umma ta yi “Shikenan Allah ya raya su ya bamu ikon kula da su,” “Amin” duk suka ce banda Ummu da ta Fada a ranta kafin ta shige toilet ta kuma sa kuka duk wannan lefin mutuwa ne da Faruk ɗin ta na raye da shikenan tasan sai sunfi kowa farin ciki zuwa yanzu da ta haifa masa yara ya zama.

Su Aisha sunfi kowa mamakin ganin yaran sai dai kuma ba wanda ya tambayi ya akai ko ke yasa hasali ma rungumar yaran sukai tamkar nasu kowa cikin gidan son yaran yake wannan ya ragewa Ummu damuwar ta sosai.

Sannu a hankali Ummu sunyi wata biyu kenak da haihuwa sai dai ko da wasa ko sai daya bata taɓa fita da yaran ba anma abinka da mutun ake kiwo yanzu ba dabba ba kan kace me tuni unguwar tasu ta dauka an haifi shegu har biyu duda cewar ba wanda ya taba ganin yaran.

Kasancewar su sabbi a unguwar da kuma basu wani shiga jama’a sosai ba yasa mutane suka kasa shigowa gidan dan ganin yaran sai dai wanda bai taba zuwa shagon Ummu ba da sunan cin abinci cikin yan kwanakin nan zaka ganshi duk cikin burin mutane na son kashe kwakwatar idanun su.

Tun Ummu na nuna rashin damuwa na abinda ake mata da dan kiran da mutane ke mata har ta fara tun tana tausayin yaran nata har ta dawo tausayin kanta.

Yau ita kaɗai ta nufi kasuwa dan sayo kayan abinci kamar kullum takawa take ta nufi titi hijab ne a jikin ta har gwiwa ranta babu daɗi kwana biyun nan ji take ina ma da ita ta mutu. Motar har ta wuce ta dawo ta tsaya gaban ta, zuge glass din motar akai matashin saurayi ne kusan zata iya cewa Faruk ya girme masa sosai.

Murmushi ya mata yan mata ina zuwa ya faɗa daga cikin motar fuskar ta a haɗe ta ce ka tare mu hanya ina son samun babur din hawa ne, murmushi ya yi sorry dear ya faɗa sanda ya danyi baya da motar ya fito ya bi bayan ta. Kusan kan ya karaso ta shiga dan sahu dafe kai ya yi har ya nufi motar sa ya canja shawara ya karasa gun matasan da ke zaune. Sallama ya musu suka amsa ya tambaye su ko sun san ta.

Ɗaya cikin su ne ya masa kwatancen inda shagon nata yake wato gidan nasu godiya ya masu kafin ya koma motar sa ya tayar yabar gun. Washe gari da rana a gun Ummu Hani ya sauka aiko da ita ya fara arba sam bata gane shi ba tayi tsanmanin customer ne Aisha ce ta zuba masa abinda ya buƙata. Sai da ya cinye ya dubi Kairi dan da ita yaga suna kama da Ummu ya ce kanwata ya sunan yayar taku. Kallon sa Kairi ta yi kafin ta nuna Salma ta ce waccan.

Girgiza kai ya yi a’a bakar mai kama da ke, murmushi ta yi Oh Ummu Hani sunan gyada kai yayi ya biya kudin kafin ya kairi godiya yabar gun. A ranar ya dawo da daddare yana son ganin Ummu kin fita ta yi da kyar Hajiya ta rakura mata ta fita ranta ba dadi dan kam ita bata shirya soyayya ba bare aure.

Baki gane ni ba ko, jiya mun haɗu kina titi Allah sarki ta ce kawai, to gaskiya tun jiyan naga nayi mata na ba inzo inji ya za’ayi, dariya ya bata wai ya yi mata karfin halin sa na daban ne, nisawa ta yi kafin ta ce daga ganin ka baka taba aure ba amma kaganni nan na taba aure a dan tsorace ya kalleta ransa cike da mamaki wane marar sa’ar ne shikam zai gangancin sakin wannan ya faɗa aransa.

Yake ta yi bawai na taba auren bane kawai a’a inada yara har biyar kanne kuwa ba adadi in mutun zai aureni to tare da su za’a haɗa, murmushi ya yi inma ku dari ne karku damu indai wannan ne sharudan ki na aminta kallon sa ta yi da sauri ya sakar mata murmushi ta yi saurin juyar da kanta nasan sunan ki ni sunana Ahmad ya kuma fada bayan dan shirun da su kai.

Kusan tin daga ranar ba ranar ba ranar da Ahmad baya zuwa gun Ummu Hani. Tun tana dar dar dashi har tadan saki jiki duda cewa ko kaɗan ta kasa jin son sa araanta anma yana mugun ɗebe mata kewa dan shi din mutun ne mai barkwanci gami da zaulaya duk kannen ta sun saba dashi da sun hangi motar sa zaka ga kaf dinsu farin ciki ya bayyana a fuskar su wannan yasa taji hankalun ta ya kuma ɗan kwantawa dashi.

Watan su guda tare ya takura yana son ya turo iyayen sa ita sam ba aure a rayuwar ta yanzu sai dai tana son aƙalla ya zama akwai wani namiji a gidan nasu ko yaya ke ya sama musu daraja ita da kannen ta a dena musu kallon zaman kansu suke su da iyaye mata.

Bata wani yi dogon tunani ba ta bashi dama ya tura bayan take ta saku kawun ta ya bata lokacin da suke nan lokacin da ta sanar da shi sai da tayi kukan tunawa da Faruk ji tayi sam bata masa adalci ba musan man yadda taga Ahmad na murna tasan cewar shi bawai auren ta zaiyi dan ya kalle ta ba bane.

Ranar da kawu yasa iyayen Ahmad suka isa gidan wurin goma na safe cikin mutunci da girmama wa aka gaggaisa kafin kawun Ahmad ya ce dama yaron su ya turo su yana buƙatar auren diyar su Ummu Hani. Murmushi kawu Bala ya yi ya ce “hakika munji dadi sosai da zuwanki sannan indai har diyar nan tamu ce karkuji komai mun baku,” kawun Ahmad yayi murmushi “hakika munji dadin wannan kyauta dan haka ina ganin sai a sa lokacin da ya kamata ayi bikin shidai yaron namu baiso asa da tsayi.”

Kawu Musa ne wannan karan ya ce ah ai muma basai ansa lokaci mai tsayi ba tun dama yarin tamu bazawara ce ai kunsan ba’a wani fi’ilce fi’ilce a bikin bazawara.”

“Bazawara kuma?” Kawunnan Ahmad suka ce, gaban kawu Musa ne ya faɗi kaddai basu sani ba towo kar yarin yar nan ta yi tunanin zai kashe mata aure ne daurewa ya yi cikin murmushin karfin hali ya ce, “Eh to Bazawa za’a ce gaskiya danma kar mu boye muku shi yasa na faɗa muku anma ko tarewa bata yi ba mijin Allah ya masa rasuwa ya yi hadari ne.”

Tun lokacin kawunnan Ahmad suka sauya fuska jiki ba kwari sukai sallama kowa ya watse, ayayin da shi kuwa zunudin ango Ahmad ya karu ji yake tamkar yafi kowa sa’a in tashi ne kawai a daura musu auren su daga baya ayi komai anma dole ya hakura.

Yau Ummu bata fita Shago ba Salma na makaranta Aisha ce kawai ta fita sai Kairi da take taya ta mika abinci kowa yana daki Ummu na wanki ta jiyo hayaniya daga shagon kamar karta fita ta saɓa mayafi ta fita.

Wasu mata ta gani nata surfa masifa inda Aisha ta biye musu suna bala’i da hanzari ta karasa tana fadin ke Aisha mene hakan sanin halin Aisha da rashin hakuri yasa aranta taji ita ce kawai mara gaskiya sai dai tana karasa daya ciki ta ce shegiya wannan ce Umnu Hanin tsai Ummu ta tsaya tana mamakin mai ta musu suke zagin ta haka.

“Haba bayin Allah kome na muku ai kwa samen cikin gida bawai gun sana’ata ba kuma ni na muku ba kanwata ba hakan ba dai dai bane, dayar ce ta dara ah sannu uwar kisisina da haka take sace zuciyar maza inba haka ba ina Ahmad ina wannan dinbarun fisabilillahi me ya gani jikin ta.”

Sai yanzu Ummu taga kamar dayar gajerar da Ahmad daurewa ta yi ta ce yanzu dai dan Allah ku yi hakuri ku shigo ciki muyi magana, cikin fushi dayar ta ce muce ubanki eyyi to wallahi ki fita sabgar kanin mu tsabar munafirci da mugunta gaki bazawara gaki yayan shege shine zaki zo ki makale masa to a hir dinki.”

Ran Ummu ya ɓaci sosai zagin baban ta da sheganta mata yara da sukai yafi komai bata mata rai cikin takaici ta ce, wai duk kan namiji kuke mun haka badai Ahmad ba ne to ku zuba ruwa s kass ku sha wallahi na hakura koda ace shine autan maza dama shi ya kawo kansa sai ku faɗa masa ya fita sabgata in ba haka ba hukuma zata rabamu kamar yadda kuma wallahi in kuka ci gaba da zargina ko zan yawo tsirira sai naga an hukunta ku.”

Eh ai zaki iya tunda ai kowa yasan ke wa ce suka fada kafin su bar gun ta zube a gub tana kuka. Dakyar su Aisha suka lallashe ta.

Kamar kullum da yanma Ahmad yazo niki niki da kaya ba wanda ya kula shi cikin su yaro ya aiki da kayan Ummu ta dawo masa da abinsa har ciki ya shiga gidan karon farko da ya shiga hankalinsa kuwa duk a tashe suna zaune tamkar gidan mutuwa ya shiga, Salma ce ta mike ta ce Malam me kuma ya kawo ka turo yan uwanka da kayi suka ciman mutunci bai isa ba sai kazo da kanka.

Ummu dake can gefe kwance ta kalla ko kallo bai isheta ba yayin da gabansa ya hau dukan uku uku wato su Yaya Fati sai da suka zo kenan ransa ya baci sosai har ya juya zai fita Ummu ta ce in kaje ka faɗa musu ni bani na kirawoka ba sannan da suke tunanin zan cuce ka shima ka faɗa musu kai ka ce kaji ka gani tun sanda muka fara haduwa na fada ma inada yara inada kane na taba aure.Bai ce komai ba ya juya ya fice ransa na masa suya.

******
Wata guda kenan ya rage auren Ayatullah da Aisha tashin hankali kam yanzu tuni ya zame masa aboki ya kasa gano inda Ummun sa ta ke gashi Abban sa ya sako shi a gaba kan in yanada wata ya fito da ita a haɗa dan shi bazai yadda daga yin biki ya kuma cewa zai kara aure ba.

Hankalin sa bai kuma tashi ba sai yau da Abba ya kirashi ya zageshi tas kan dan mene baya zuwa gun Aisha din dan kusan tun randa ya je bai kuma bi ta kanta ba kasa magana ya yi Abban ya miko masa ledoji ya ce yaje ya kai mata saura yauma in ya je ya yima kawun nasa rashin kunya.

Ransa babu dadi ya shirya cikin farin yadin sa mai kyau ya nufi gidan Kawun nasa ya jima a motar kafin ya aika yaro a kira masa ita yaron ne ya dawo ya ce wai bata nan anma waye murmushin jib dadi yayi ya cewa yaron jeka kawai ya fito niki niki da kayan ya shige gidan.

Mama ce ta ce “au ashe kaine bata nan ta je gidan su ƙawar ta wai zatayi video ɗin Tiktok” a tsorace yace “Tiktok kuma murmushi Umma ta yi “eh kasan ai ta shahara sosai a can tana son Tiktok ɗin”, ƙwafa yayi kawai ya ce “yayi kyau ni bara in koma in tazo a gaidata” kawu ne ya fito kaje ina maza Tijjani rakashi su gaisa nasan zasuyi batun bikin nasu sosai…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ummu Hani 33Ummu Hani 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×