Ko da rana Ummu Hani bata rasa abin bawa ƙannen nata ba, dan maƙota nata kawo abin sadaka har baƙi masu zuwa gaisuwa ta samu na basu.
Kwana biyun duk a tsorace tayi su, yadda da rana gidan da mutane irin masu zuwa gaisuwa, sai dai dare na yi da kowa ya watse zata nemi nutsuwarta ta rasa, musamman in lokacin rufe gida yayi taje rufe ƙofa, sosai take kuka dan a lokacin mutuwar iyayan nasu sabuwa take dawo mata.
Zaune take tana yiwa Muhammad wanka, tun tana gogeshi da tsumma hartai ƙundun balar fara yi masa wanka, Aisha ta shigo riƙe da fidarsa da ta dafa masa madara, tace yaya gashi an gama.
“Kinsa aruwan sanyi ta huce?” Ummu ta tambaya, “Eh,” Aisha ta Bata amsa, “Yawwa to bara in ga masa wanka, sai ki amshe shi zan wa su Husaina wanka.” Ummu ta ce.
“Ai tun ɗazu nai musu” Inji Aisha.
“Kai anman kin samu lada, na na gode.” Ummu ta faɗa, dariya A’isha tai, “Cewa zaki yi Allah ya yi albarka,” inji Aisha, Ummu tai dariya “T o Allah yayi albarka.” Aisha ta ce “amin.”
Shiru sukai na ɗan wani lokaci, kamin Aisha ta ce, “Yanzu yaya ya zamuyi da Muhammad, kinga dai yanzu darajar kuɗin sadaka muke samun kuɗin siya masa madara.”
Shiru Ummu Hani ta yi, kamin ta ɗan nisa, “Waye ya ce miki mu zamu riƙe shi, gobe nasan insha Allah su kawu zasu yi batun rarrabamu, nasan sunƙi yin maganar ne zuwa suyi shawara.”
“Hakane kuma” Inji Aisha, “Ni wallahi duk raina babu daɗi yanzu shikenan haka zamu rarrabu.”
Ummu Hani ce ta dafata, “Haƙuri zamuyi Aisha haka tamu ƙaddarar take kinajin akwai wanda zai iya ɗaukanmu dukkanmu lokaci guda, abin da kawai nake so daku koma ya ake muke a inda kukaje ku daure kuyi haƙuri, ku jure wataran sai labari yanzu kiramin Khairiyya da Sajida.”
Tana nan zaune ta gama yiwa Muhammad wanka ta shafeshi da mai tana bashi madara, su Khairiyya suka shigo agefenta suka zauna sai da ta kwantar da Muhammad sannan ta fara magana.
“Yawwa nasan dai kunsan gobe insha Allah zamu bar gidan nan, shine nace ko waccenku ta tabbatar ta haɗa komai nata guri ɗaya na gama haɗa nasu Hasana.”
“Nasan kunsan rayuwa shekara 12 da 10 aƙallah kunsan me ake ciki, zaman gidan wasu gun iyayan da ba naka ba bashi da daɗi, musanman ace mutun yana kamarku zai je zaiga canji iri iri, ku daure ku zamto yara na kwarai kunji.” Ko to yaya suka ce.
Aisha dake bakin kofa ta shige ɗaki tasa kuka, ita tana mamakin jarumta ta yayar tasu da har take iya komai bata kuka, ita yanzu ko su Hasana da Muhammad ta kalla sai tayi kuka ya tawo mata, ita kuwa yayar tasu har zama take tai ta tayasu Hasana shirmensu dik da kana kallon fuskarta kasan daurewa take, anman duk da haka tana ƙoƙari.
*****
Washe gari yake bakwai kamar ranar daya, yauma an samu masu kawo buhun hunan shinkafa wanda sun samu aƙalla buhu uku.
Ummu Hani da kanta ta ɗebo kwano biyar ta ce adafa dan kar yauma akwashe ta kulle ɗakin da aka ajiye.
Duk wanda yazo yakan bada hamsin ɗari ayiwa mai mutuwa sadaka Ummu Hani ba ta taɓa komai take bawa gwaggo ta ajiye, wato yayar Ummansu mai rasuwa.
Kusan ƙarfe biyu ne ummu hani tace gwaggo ta bata ɗari cikin kuɗin nan gwaggo ta hau masifa me zatai da har ɗari biyu.
Cikin sanyin murya Ummu Hani tace daman Muhammad zan siyowa madara tun safe baici komai ba.
“Yau kajimin yarinya da kini bibi, shi jaririn ne zai sha madara har ta ɗari biyu? Tsayama tukun duk ina kokon gidannan? Me yasa baza ku bashi ba?” Shiru Ummu Hani ta yi ranta babu daɗi, ita dai tasan kuɗin nan bana gwaggo bane bare tace, anman ɗari biyu ko a kuɗin tane ai tana ganin ita me badawa ce.
Barin gurin kawai Ummu Hani ta yi inda ta yi waje kai tsaye ta yi gidan maƙotansu.
“Umma Bilki dan Allah madara zaki sanmin zan bawa Muhd.”
Aikam kinzo a sa’a yanzu Ummi ke haɗawa walid, ce ta haɗa da ku, to Umma mun gode Allah yasaka da alkairi Umma ta ce amin.
*****
Da yanma lis kawu Bala ya kira Ummu Hani gabanta sai faɗuwa yake, fatan ta ace wanda zai ɗauke ta shi zai ɗauki Muhd, duk da ta shaƙu da dukka ƙananan ta anman soyayyar jaririn nasu daban take a ranta tana san sa sosai.
Yawwa makullin Ɗakin da kika sanya shinkafa zaki ban babu musu ta ɗauko ta bashi, shida kawu Ummaru suka cicciɓo shinkafar suka fito da ita, Nasir da Faruk suka fito da sauran.
Tas suka rabe shinkafar atsakaninsu Ummu Hani na gefe, gwaggo bata yi batun kuɗin sadaka ba itama Ummu bata yi ba.
Ana kiraye kirayen mangariba maza suka miƙe, to mu zamu wuce sai arba’in mata suka fara to muma dai ɗin da mun idar da sallah zamu watse.
A tsorace Ummu Hani tace to mu ya zakuyi damu, da sauri kawu Bala yace “Yo ai haƙƙinku na kan dangin ubanku.”
To inma ni kake nufi kasan dai bani dashi ban kuma bada ajiyaba, hasalima matata dani munyi tsufan da za’ace muna raino yanzu, kawu Ummmaru ya tari numfashin Kawu Bala.
“Kawu ba gani ba, ga A’isha ga Khairi duk mun wuce raino, hasalima sai dai mu taimaka da aikin gida in yaso sauram sai su Inna su ɗauka.”
“Wa rufan asiri, in kai ina yadda mijina kejin haushi na kawo masa agola, yanzu in kawo masa marayu ai sai ya koren, inna ta tari numfashin ummu hani wannan ya hana kawu bata amsa.”
Share hawayenta ta yi ta saɓa Muhd a kafaɗa tace “To shi kenan yanzu ya zamuyi da jaririn nan?”
“Yo sauran kwanakin baku ke kula dashi ba hakama yanzu zaku cigaba, ni kinga banso in rasa jam’I.” Kawu yasa kai zai fice.
Bakwa voting da comment fa.
This story make me so happy cuz sunana ne ummahani kuma bantaba ganin Anyi labari da sun anan bah Shiyasa abin yabani citta Allah yakara basira
Allah sarki fatan zaki cigaba da biyar labarin har karshe