Skip to content
Part 29 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Ƙarfe goma na safe na farka daga barci ba wanda ya fado mini sai Vicky yarinyar da aka kawo domi na dole na duba halin da take ciki.

Na sauka gadon a hankali na shiga toilet bayan fitowa ta wardrobe na buɗe na zaro zane na ɗaura saman rigar barcina kaina akwai hula na fita ɗakin.

Yan zaman falon ba su fito ba na wuce dakin da na sauki Vicky tana zaune bisa katifar da ke yashe a tsakar dakin tana gani na ta zaburo tana gaishe ni na amsa na ce ta biyo ni kitchen muka shiga na nuna mata duk nau’in kayan abincin da muke da su na tambaye ta irin abincin da ta iya murmushi kawai ta yi mini tare da ba ni tabbacin ta iya kalolin abinci da dama.

Na rama mata murmushin na kuma ba ta umarnin ta yi mana abin break past ina tsaye ta fara sannan na ce mata zan je in yi wanka kafin ta kammala na fita ina mamakin rashin ganin Peter a kitchen ɗin.

Na fito Bashir Lema da Amal idona ya gane mini kuka mai tsanani Amal ke yi tana faɗin maganganu a kaina na dake ta bai yi mini komai ba sai ya kore ni.

Tsaye ta miƙe tana dire-dire daga inda nake tsaye na taka na isa inda yake zaune yana lallashin ta ta yi shiru, kaina na kwantar a hannun kujerar da yake cikin siririyar murya na ce kaina da kulawa ya ce me ya sami kan na zubo da hawaye sai na miƙe na kama hanya ya kira ni ban tsaya ba sai takunsa na ji ya bar Amal da ta sauya kukanta daga na iya shege zuwa na baƙin ciki da takaici.

Ina shiga yana shigowa kama ni ya yi ya sanya ni jikinsa yana tambaya ta me ya same ni na narke mishi muka zauna bakin gado salo kala-kala na yi ta masa na mantar da shi wata Amal muka sha soyayyar mu, daga bisani muka yi wanka ko da muka shirya fita ya ce zai yi na ce zan bi shi bai musa ba ya ce in sa takalmi na sa muka fita.

Suna zaune a falo ya isa wurin su Amal ce kaɗai ke fushi da shi ya gama magana da su Suhaima ta ce ina za shi ya ce yanzu zai dawo sai da ta dube ni ta ce mishi tana zuwa kafaɗarta ya riƙo ya ba ta haƙuri ya ce ba zai daɗe ba da yamma sai su fita ta bata rai ƙwarai ya biyo ni muka fita bayan na yi sallama da Vicky.

Bai je wurin mutumin da ya so gani ba ta waya ya kira shi ya ce sai gobe wuraren shakatawa ya kai ni na ci abinci ya kai ni na sayi abin da raina ke so ƙwarai na ji sanyi da tuƙuƙin baƙin cikin da na daɗe da shi na su Amal.

Washegari da safe na fita wurin Vicky ina faɗa mata abin da za ta dafa ban daɗe ba na koma na samu ya fito daga wanka na zauna ina gaishe shi ina ta kallon sa a yayin da yake shiryawa wani baƙin yadi ya sanya da ya bi farar fatarsa ya yi wani irin kyau ya manna farin Glass ya murza hula sai sannan na tashi na dauko mishi agogo sai da ya daura ya sumbaci laɓɓana tare da yi mini godiya, ya kama ni zuwa kan kujera sannan ya labarta mini Kaduna za su tafi shi da su Dina tun wancan satin yake so su tafi rashin samun mai aiki da zan ji motsinta ya hana shi tafiya na ji ba daɗi na ce “Ni fa? Ya shafa cikina ban san ki yi doguwar tafiya kin ga ba wata lafiya ce da ke ba.”

Shiru na yi ba don na gamsu ba ni dai ba na ciwon komai kasala ce dai ke damu na.

Na ce “Abinci fa?  Ya ce sai sun je can za su karya ya miƙe muka fita.

A falon na tsaya ya shiga wurin su Dina kamar na leƙa Vicky kafin ya fito sai dai na fasa Shi ne gaba sai Dina Amal da Suhaima ne karshe Dina ta ce mini Sannu suka wuce ya zo inda nake muka jera sai da ya gama magana da su Peter da Sam muka isa jikin motar kamar zan yi kuka na ce sai yaushe sati guda da ya faɗa mini ya sa hawayena da ke kusa zubowa sai da ya gama rarrashina ya shiga motar, Dina ce gaba shi da su Amal a baya.

Sai da motar ta fita gidan na koma ciki ina jin rashin ƙarfin jikina na daɗa ninkuwa.

Kitchen na wuce na iske Vicky ko’ina ya ɗauki ƙamshi ta yi mini murmushi na mayar mata tare da yi mata sannu da aiki ta ce in yi haƙuri in ba ta minti goma za ta kammala na ce na ba ta ma ashirin na fita na koma ɗaki wanka na yi na shirya na fito ta shirya dinning na zauna na ci kamar kunnena zai yi motsi na yaba ma iya girki irin nata, da na kammala kujerun falon na koma na zauna na kira ta bayani na yi mata kan aikin da za ta yi mini Khalil ya fito yana miƙa da alama bai daɗe da tashi ba mu duka biyun yake ƙare ma kallo sai na ga Vicky duk ta muzanta don wata doguwar riga ce ta wani yadi mai santsi jikinta da ta kama ta ga ta tana da jiki baƙa ce mai matsakaicin tsawo ko dai za ka ce ita ɗin ba ta da kyawun fuska to ta mori ƙirar jiki hannuwanta ta sa ta kame jikinta ya zauna yana tambaya ta sun wuce na ɗaga mishi kai ganin ta ƙi sakewa na ce ta tashi mu tafi.

Toilet ta fara wankewa sai ta gyara gado ta yi mopping ta ce mini me za a dafa?

Na ce ta je ta huta tukuna da ta fita rufe ƙofa na yi na kama barcina da ban gajiya da shi.

Sai biyu saura na farka saurin yin alwala na yi na yi sallah sai na fita ɗakin Vicky na leƙa da sai da na ranƙwashi ƙofar ta buɗe don ta datse sallaya da na gani a shimfiɗe ta ba ni tabbacin ita ɗin musulma ce ta gaishe ni da tambayan me za ta dafa na ce ta yi komai na koma falon Khalil ya shigo da alama baya gidan wuri na ya taho yana faɗi mini yarinyar nan ta yi girki da shi dama bisa lalura yake cin girkin ƙaton nan.

Na ce mishi to.

Yana ta ja na da zance ina amsa mishi da E ko a’a ko to har ta zo ta ce mini ta kammala, sanin idan na hau dinning shi ma biyo ni zai yi na ce ta kai mini ɗaki da ta dawo na sa ta haɗa mishi tana gamawa ta kama hanyar ɗakinta na ce ba ta ɗauki abincin ba ta ce ba yanzu ba.

Ban jima ba ni ma na tashi na tafi na bar shi lambar Bashir Lema na laluba ya tabbatar mini da isar su tuni har ya ba Haj muka gaisa.

Ban ƙara fita ba sai washegari na samu kuma ta kammala abin karyawa Peter ya tafi ganin gida daga mu sai Easter.

A kwanakin da su Amal ba su nan sai na ji gidan ya yi mini daɗi ina fitowa na sha iska har wurin hutawa a harabar gidan na kan fita na daɗe, sosai nake samun nishaɗi har na yi ta jin haushin kaina da ban gano fitowar ba tun da, Vicky na fitowa idan ba ta aiki ta zauna ɗan nesa da ni Khalid a gida yake wuni sai yamma yake fita watarana ya raba dare ya dawo wataranar kuma sai dai mu haɗu da safe.

Ranar da suka kwana biyar ya shaida mini za su dawo na cika da mamakin dawowar tasu kafin cikar mako daya da ya ce za su yi ya ce mini saurayin Suhaima ne zai dawo daga Turai ‘ita ta hana su kai wa satin ta ce su dawo.

Na ji mamakin jin saurayin Suhaima ba ma Amal ba ko Dina, na dai yi musu fatan dawowa lafiya na sanya Vicky ta yi abinci masu daɗi aka ajiye masu.

Da wuri suka dawo don jirgi suka biyo kamar yadda suka tafi na cancare kwalliya da ɗaya daga cikin kayana da aka kawo mini ɗinki a yammacin jiya, super ce da ta yi matuƙar karɓa ta na yi ma mijina kyakkyawar tarba don yadda na yi kewar shi.

Da ya nemi na fita a ci abinci ban ƙi ba tun a wurin cin abincin na ji Suhaima da Amal na magana kan zuwan baƙon Suhaima, Suhaima dai da ka gan ta ka san tana cikin farin ciki har take faɗa ma papinsu Dina ta yi saurayi a Kaduna ustaz.

Dina da ke cin abinci tana danna wayarta ta ɗago ta dalla mata harara, Khalil ya ce ma Amal ita fa ta ɗaga hannuwanta ta ce su suka gaji da Papi ita ba yanzu ba .

A raina na ce shegiyar mai rai ai sai ki yi ta zama.

Suhaima ta kwantar da kanta kan kafaɗar uban ta kai masa ƙarar Amal, nan ya lalace wurin yi musu shari’a.

Vicky da ke ta shige da fice ta kawo wannan ta ɗauke wannan da gani a takure take don wata farar riga ta sanya da baƙin skirt sun  kama ta kuma skirt din bai sauka ƙasa ba, a ɗan zaman da na yi da ita na fahimci tana da ƙarancin sutura duk kuma sun matse ta abin da na lura yana jefa ta cikin takura.

Ina son duba mata kayana kasalar da nake fama da ita ke hana ni amma yau in sha Allah na ƙudiri sai na ciro mata ko don kallon Khalil na ƙurulla gare ta.

Ta kawo ma Khalil abinci za ta juya Suhaima ta ce ke ta waiwayo da hannu ta kira ta, ta tako ta isa gaban ta tana kakkama jiki, bayanin abin da za ta dafa da yamma ta yi mata, Amal ta kece da dariya tana faɗin ke wannan ce za ta ba ki abin da za ki ba guess ɗinki?

Ta lumshe ido ta buɗe ta ce ta wuce kawai kamar ƙwai ya fashe mata a ciki ta bar wurin.

Easter Suhaima ta ƙwala ma kira ta iso cikin sauri gyaran falon mahaifiyarsu ta sanya ta, inda za ta sauke baƙon.

Sai da ta sallame ta ta fuskanci mahaifinsu kuɗi ta ce tana buƙata Amal ma ta zaburo ta ce ita ma za ta yi shopping Khalil ma ya ce zai sha mai kuma yana da bikin abokinsa, Dina ma da ba ta magana ta ce ita ma a ba ta Amal ta yi ta mata  shaƙiyanci ya ce in je cikin side drawer in kawo mishi kuɗin ciki na tashi tsam na tafi sai dai na gama buɗe-buɗe na kwabo babu a ciki, na fito da sanyin gwiwa na faɗa mishi ban gani ba mamaki ya bayyana a fuskarsa ya tashi da kansa ya tafi na rufa masa baya shi ma ya duba babu sai dai  Save ɗinsa ya bude ya ciro wasu kuɗin ya fita.

Na hau gado na kwantar da kaina bisa ƙafafuna cikin damuwa da tunanin yadda kuɗin suka yi, tunanin ko Vicky ta ɗauki kuɗin ya yi ta yawo a raina .

A haka ya dawo ya same ni zama ya yi ya miƙo mini hannunsa na kasa zuwa ya tambaye ni damuwa ta ban ɓoye mishi ba ya ajiye kuɗi ya ajiye kuɗi bai gani ba cewa ya yi ƙila ya ɗauka mantawa ya yi na dai ji shi kawai amma ko ni na ga san da ya ajiye, a hankali ya ja hankalina har na warware na ba shi labarin ɗinkunana da aka kawo ya ce Haj Fanna ta faɗa mishi  barci ya yi ni kuma na buɗe kayana na ciro ma Vicky kayana masu babban ɗinki na zuba su a wata jaka na ja ta na fita.

<< Ummu Radiyya 28Ummu Radiyya 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.