Haj na zaune a falo ita da Mama Zulai an cika gabanta da abin karyawa da na yi imani aikin Vicky ne shi Peter idan dai ba lokacin cin abincinsu ba duk bakon da zai zo bai ba shi abinci.
To yaushe ma ya yi da yawa iyakar cin su yake yi.
Na isa gaban Haj na zauna na daidai kafafunta na soma gaishe ta ita ma cikin fara'a mai yawa take amsawa ta faɗa mini jin daɗin ta da yadda ta ga na koma da gani ina cikin kwanciyar hankali.
Na tambaye ta su Su'ada. . .