Skip to content
Part 32 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Haj na zaune a falo ita da Mama Zulai an cika gabanta da abin karyawa da na yi imani aikin Vicky ne shi Peter idan dai ba lokacin cin abincinsu ba duk bakon da zai zo bai ba shi abinci.

To yaushe ma ya yi da yawa iyakar cin su yake yi.

Na isa gaban Haj na zauna na daidai kafafunta na soma gaishe ta ita ma cikin fara’a mai yawa take amsawa ta faɗa mini jin daɗin ta da yadda ta ga na koma da gani ina cikin kwanciyar hankali.

Na tambaye ta su Su’ada da Aunty Fatahiyya ta ce suna lafiya Su’ada ce dai ta yi zazzaɓi amma ta warware, Mama Zulai ba ta sanya mana baki ba ni ma da suka fara magana da Ahmad Lema shiru na yi ina sauraren su a cikin hirar Haj take shaida mishi wani yaron mahaifinsu da ya girma gaban su Hajiyar ita ta fi kula sha’aninsa yanzu ya zama babban mutum sune a gwamnati ya zo har gida ya yi mata kyautar kujeru biyu na aikin hajji shi ne ta yanke ta ba ni ɗaya sai mu tafi ni da ita.

Bashir Lema ya taya ta godiya sai ya ɗora da cewar ni kam ba zan iya aikin hajji ba saboda cikin jikina wata irin murna Hajiyar ta balle da ita ta yi ta addu’ar Allah ya raba mu lafiya ta ce amma bai yi girman da zan kasa zuwa ba sai mu je sati biyu mu dawo duk da dai na so yin aikin hajji cikakke.

Mama Zulai ta ce “Ta international din ba cikakke ba ne?

Ta girgiza kai “Ban ce ba. Amma dai na so in yi wata guda ina ibada, ko ba za ki iya aikin hajji ba Ummu Radiyya? Na noƙe kaina cike da kunya na fadi zan iya ta ce  “Ma sha Allah.”

Mama Zulai ta ce “Amma ni ya kamata ki ba kujerar nan.”

Haj ta yi mata wani irin kallo”To ba ke na yi niyyar ba ba.” Mama Zulai ta ɓata rai sosai Me zai sa ba za ki ba ni ba?

“Saboda shekara biyu da ta wuce an ba ni na ba ki duk kuma abin da zan samu ke nake fara ba amma har yau kina nan jiya i yau na rasa inda kike kai duk abin da ake ba ki .”

In dai ba ka da shi komai ma yi maka ake.”

Ta faɗi cikin fushi Bashir Lema ya ce  “Ki bar mata Haj, ni zan biya ma Ummun.”

Haj ta girgiza kai “Ba zan bar mata ba, Su’ada zan ba ita Umara kaɗai ta taɓa yi tun tana budurwa. Kuma ma zaman me kike anan kin baro mijinki da yayanki to ki shirya mu koma ban son shashanci.”

Mama Zulai ta yi kamar za ta fashe.

Kwanaki uku Haj ta yi saboda murnar samun labarin cikina tana ta nan nan da ni Amal da Mama Zulai sun cika sun yi fam.

Da za ta tafi suka tafi da Mama Zulai.

Da na shaida ma Vicky tafiyata kuka ta yi ta yi yawan kukan da take ya sa na ce ko za ta tafi gidansu lokacin tafiyar tawa idan na dawo sai ta dawo kai ta girgiza ta ci gaba da kukanta.

Ina ta jin sauƙi don cikina ya yi wata huɗu na warke ras sai kyau da nake ƙarawa cikin ya ɗan fito kaɗan masu son su Dina na ta zuwa har an yi maganar aure an sanya rana Bashir Lema ya ce sai na haihu Nabila ta haihu muna dab da tashi ina kaduna muka sha suna muka ɗaga ƙasa mai tsarki tare da Haj da Su’ada da Rabi’u ƙoƙi da ya biya ma su Haj da iyalansa Bashir Lema London ya ce zai tafi kafin na dawo wurin matarsa na tafi da wani irin kishi da nake jin yana taso mini da na tuna zai kasance da uwargidansa ne .

Mun yi aikin hajji mai daɗi mun tsananta ibada da addu’o’i mun kwaso tsaraba gidan Haj na sauka duk da ya ce na sauka Abuja ban sauka can ɗin ba na ce sai ya dawo.

A gidanmu nake wuni na zaga yan’uwa cikina ya ƙara fitowa don yanzu kana gani na za ka gane me kenan bayan kyan da ake zuzuta na yi na kuma yi ƙiba ba kamar da ba da nake siririya ƙwarai.

Share duwawu na yi na yi zama na Kaduna sai da na kwana goma ya dawo, duk yadda yake ririta ni sai da na gane na bata mishi komawar da ya yi ban koma ba zai shigo Kaduna ya ce ma Haj na ce to idan ya shigo sai mu tafi tare ya ce sam in dawo.

Na yi sallama da mama da yan’uwa ta jirgi na koma don haka ba ɓata lokaci muka isa .

Ganin motarsa a harabar gidan ta sa na gane yana nan bai fita ba, na fita direban da ya dauko ni ya kwaso mini kayana dukkan su suna zaune a falo har shi, Vicky ta sheƙo da fara’a duk da ita din ba maabociyar ta ba ce tana mini oyoyo murmushi na yi ta yi tuna hawayen da ta yi ta sharewa ranar da na shaida mata zan tafi

Miƙewa Bashir Lema ya yi daga inda yake ya buɗe mini hannayensa kamar na isa na faɗa ko dan ba su Amal haushi

Nauyin yin hakan dai ya kama ni na kasa, da na isa hannu na miƙa masa ya kama zai sanya ni jikinsa na yi saurin yin gaba ya biyo ni ba wanda ya ƙara jin motsin mu ko Vicky da ta kira sanin zancen abinci za ta yi shi ya kashe wayar gabaɗaya wata irin kiɗima ya yi a kaina da ta ba ni mamaki kamar ba wurin matarsa ya je ba sai da na fara masa kukan shagwaɓa ya tsahirta mini na ce yunwa nake ji.

Mun fita na samu Vicky ta kasa ta tsare abincina da ta shirya a falon da nake Khalil da ya shigo lokacin ya shaida mishi fitar su Dina ni kuma ya matso kusa da ni ya yi mini barka da dawowa da tambayar tsaraba na ce idan na koma ɗaki zan ciro mishi.

Ina zaune a kasan Carpet ina cin abincina Bashir Lema na saman kujera saitina yana duba jarida na ci na yi ƙat don yanzu ci nake sosai na juya wurin sa na ce za ni na yi sallah masallaci ya fita na koma ɗaki na idar da sallar ya shigo na yi addu’o’ina na shafa sai na mike akwatunan da na dawo da su na buɗe yana duba jaridarsa lokaci-lokaci yana ɗagowa ya dube ni riguna masu matuƙar kyau da tsada kowa bi-biyu na sawo ma su Dina ba don ina da tabbacin za su ansa ba ko su sanya ni dai na sawo saboda mahaifinsu kuma shi zan ba ya ba su idan ba su ansa ba ruwansu.

Jallabiyas masu ɗan karen kyau da tsada na cire mishi da agogo na Khalil da Vicky na cire daban zan ba su da kaina.

Na isa inda yake na ajiye mishi tare da bayanin na kowa wani ƙayataccen murmushi ya sakar mini sai ya janyo ni ya sa a ƙirjinsa ya kuma yi godiya murmushi na yi na jin daɗin farin cikin da na sanya shi da na san kayan da na saya ma ya’yansa ne suka fi faranta masa na tada kaina daga ƙirjinsa zai kuma mayar da ni na ce zan kai ma Khalil da Vicky nasu ne, ya bar ni na tafi.

Khalil jallabiya biyu sai pray mat da agogo, Vicky jallabiya biyar da hijabs sai pray mat.

Tana zuba masa abinci na same su na ajiye mishi nashi kusa da shi da fara’a ya ce thanks na matsa na miƙa mata makimanciyar jakar da na zuba mata na ta, ta ƙanƙame jakar sai ta fara zubo da hawaye na yi murmushi na ce “Ke kuka ba ya yi miki wahala ne Vicky?

Khalil ya yi murmushi mai sauti da har na juyo na dube shi kallon da yake mata ya sa na ji gabana ya buga na wuce ina ji na cikin wasu-wasi.

Washegari muna karya kumallo daga ni sai shi don ba mu fito da wuri ba Amal ta fito ɗauke da kaya a hannu, kallo ɗaya na yi mata jin tana ƙwala ma Vicky kira na gane kayan da na ba su ne Vicky na isowa ta watsa mata kayan, na dube su sai na ci gaba da cin dankalin da nake, Bashir Lema ko tari bai ba har ta gama maganganun rashin ɗa’a kan kayan da na gane nata ne da na Suhaima.

Da hannu ya kira ta ta iso gaban shi Khalil ya tambaye ta ya kwana gidan ta ce ba ta sani ba ya ce ta dubo shi ta tafi. Mamakinsa na ta ƙara rufe ni ban taɓa ganin uban da bai ganin laifin ya’yansa ba irin sa, ba wai kuma bai iya bala’i ba ne ina jin sa a mafi yawancin lokuta shi da uwar su idan ta kawo mishi tsarin ta kan ya’yan, haka ma Khalil bai mishi ta daɗi kan yawon dare  da kwana waje da yake.

Amal ta dawo ta ce ba ta gan shi ba kiran sa ya yi a waya ya dira mishi masifa ina ta kallon sa yana ƙara ba ni mamaki mintuna goma ya ba shi ya iso gida yana neman sa.

Tana cika minti uku kacal ya ƙara ya shigo wani sabon faɗan ya dira masa ni dai ganin wannan abin haushi nama na jan kare na kasa jurewa tashi na yi na yi tafiyata.

Shuɗewar mintoci talatin ya isko ni ya ce na shirya mu je asibiti.

A ranar aka buɗe mini file na fara zuwa Alternative washegari kuma ya tafi Kaduna kan auren su Dina da yake ta matsowa ranar da ya yi kwana biyu da tafiya na wayi gari ban sha’awar komai hakan ya sa na yi ta kwanciya a ɗaki har Vicky da ta ji shirun ya yi yawa ta zo ta yi mini magana na ce lafiyata ƙalau ta adana mini zan fito sai da na gyara ɗakina da jikina na fita lokacin rana ta yi nisa tuni sha biyu ta gota rashin ganin Vicky ya sa ni tafiya ɗakinta don na yi mamakin barin abincina da ta yi idan zan kai yaushe ban fito ba za ta zauna gadinsa.

Na murɗa handle ɗin na sanya kaina Vicky idona ya gane mini ta kai bango Khalil ya tokare ta tana faman kuka saboda tsawon sa ya rufe ta sai bayansa nake gani.

Motsin buɗe kofar ya sa shi wawuyar waiwaya da ta ba ni damar ganin ta, da gudu ta yo inda nake tana kuka ni dai ina tsaye kamar an dasa ni, na rasa takamaimai yadda zan fassara abin da na gani.

Khalil ya tako ya raɓa ni ya fice ni ma na juya jiki a saɓule.

Falo na wuce inda abincina ke ajiye zamana na fara buɗewa Vicky ta iso hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta ta ce mini kar na ci, na dube ta da ɓacin rai ina zabga mata harara na ɗebi abincin zai kai baki ta ƙara fashewa da kuka ta haɗa hannayenta biyu alamar roƙo ta ce kar na ci in bari ta yi mini wani.

Da tsawa na ce “Wai me ya sa kike hana ni cin abinci, wannan ɗin ba ke kika yi ba? Zan faɗa miki gaskiya Vicky sallamarki zan yi ba zai yiwu kina mana saɓo a gida ba.”

Ta tsuguna gabana ta fara rokon kar in ci zuwan Khalil kuma ba abin da nake tunani ba ne in rufa mata asiri.

Banza na yi da ita na ci gaba da cin abincina tana gabana ta dafe kai tana cin uban kuka har na gama ko kallon ta ban yi ba na koma daki kwanciya na yi muna waya da Lema da ya shaida mini ya taso.

Sau biyu Vicky na zuwa tana so na saurare ta na ƙi,  nazari nake a kanta ina son yanke ma kaina shawarar rabuwa da ita sai kuma in ji rauni, ƙarshe na yanke zan bar ta amma har sai ta bayyana mini abin da take ɓoyewa ba ta son faɗa mini.

Ina nan cikin ƙullewar kai Lema ya iso kafin ya shigo wurina su Amal sun tare shi suna son kudi za su gyaran kai don haka yana shigowa inda yake ajiyar kuɗi ya nufa ya buɗe kuɗi suka ce ɗauke mu inda ka ajiye kuka na fara da na gane me kenan kukan kuma ya ƙaru da na ga ɓacin ransa a yau ji na yi duk na tsani kaina a ce daga kai sai mutum a daki ya riƙa neman abin sa babu.

Ya ce zai ɗauki mataki zai gano mai mishi sata ina cikin kukan marata ta murɗa.

<< Ummu Radiyya 31Ummu Radiya 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×