Skip to content
Part 34 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Na sunkuyar da kai  “Yes. Ummu ba zan ɓoye miki ba, na  so Lema mun haɗu a jami’ar Amurka mun yi karatu tare shi da Farida. Duk da soyayyar da muka yi Farida ta shiga tsakanin mu.

Bayan ƙare karatuna na dawo Nigeria muna tare ta waya na bi duk hanyar da zan bi Lema ya zama mallakina abin ya gagara duk biye-biyen da na yi an tabbatar mini aure ba zai yiwu tsakanin mu ba na daɗe kafin na dangana na yi aure.

Farida ta tabbatar mini matuƙar tana raye sai dai na ga Lema, shekaru biyar kenan da rasuwar maigidana, Farida ta kuma aiko mini da saƙo sai dai na ga Lema duk kuma ƙwararrun malaman da na nema daga masu cin kuɗina sai masu faɗa mini matarsa ta shiga tsakanin mu zai yi aure amma ba ni ba, na ji daɗi da za a yi ma Farida kishiya ko ba ni ba ina so a yi mata saboda na san ita kaɗai ce mafi ƙololuwar abin da ta fi ƙi ba ta son wata ‘ya mace ta raɓi Lema ba ta kuma son ya’yanta su haɗa uba da wasu ya’yan, Alhamdulillah na ji daɗi da jin aurenki da shi amma na san muddin Farida na raye ba za ta bar ki ki ji dadin auren ba, shi ne na zo miki da wani taimako.”

Ta tsaya ta mayar da numfashi ta zuƙi iska ta fesar

“Ina da malamai da suka san aikinsu in kai ki wurin su ki samu taimakon da za ki mallaki Lema ke kaɗai Farida da shegun ya’yanta da take alfahari su fita a rayuwarsa.’

A zuciyata na soma faɗin A’uzu billahi minash shaiɗanir rajim.

Ta kama hannuna ta sanya cikin nata “Farida ba ta da kyau kar ki ga shiru ta bar ki har kin kai yanzu ko ta bar ki ne wannan haihuwar da za ki yi ita za ta tsokano miki bala’inta.

Ta gama da Lema, mahaifiyarsa sai da ya tashi tsaye ta rabo shi da London tsawon rayuwarsa ta raba shi da kowa nasa sai ita kaɗai da ya’yanta yake ma bauta, yaran sai yadda suke so bai iya ƙwaɓa musu ƙanenta kawai ya zame mishi fitina bai san komai ba sai bin club, a America sun yi ma wata yarinya fyade shi ya sa ya baro ƙasar kafin a fara bincike a bankaɗo shi.

Ya ƙi karatu sai shashanci Lema bai iya komai a kansa. Ummu.” Ta kira sunana na cira kai na dube ta  “Me kika ce? Na ce “Hmm! Ta saki hannuna ta miƙe tsaye “Zan fita ki yi nazarin maganganuna da mafitar da na kawo miki, idan na dawo sai na ji matsayar ki gobe sai mu je wurin wani a nan jere yake.”

Kai na gyaɗa mata da yi mata fatan dawowa lafiya ta fita na bi ta da kallo kafin na yunƙura na sauka gadon gaban mirror na je na tsaya ina kallon kaina,

a zahiri za ka sha cikina da ya yi girma ya fito sosai cikin doguwar rigar da nake sanye da ita nake kallo amma a baɗini tunani ne ya yi awon gaba da ni.

Me hajiya Fannan nan  ta ɗauke ni ki faɗa mini kina son mijina don kina ganin kin haife ni sai ki sa ran zan ci gaba da mu’amala da ke? Na riƙe haɓa ina kakkaɓin yadda ta iya duban ƙwayar idona ta faɗa mini hakan.

Wani ɓacin rai na ji ya sauko mini na juya inda aka miƙo mini kayana da mai wanki ya wanke ya goge, na ɗauko jakar da na zo da ita na sanya su nata kayan da ta ba ni na haɗa su wuri guda na rufe jikina na fito ɗakin.

Da mai aikinta na fara cin karo ta gaishe ni cikin girmamawa na wuce a jikina na ji ta bi ni da kallo ban waiwaya ba har na isa Gate ficewa na yi na yi ta takawa tafiya mai nisa na yi ba tare da na san inda nake dosa ba kafin na samu abin hawa na faɗi inda zai kai ni.

Ina ta tunani har muka kai transfer na yi masa ta kuɗinsa na isa Gate na ƙwanƙwasa Sam ya leƙo ta wata yar kafa ganin ni ce ya buɗe yana gaishe ni, na wuce ciki rashin ganin motar Bashir Lema ta sa na fara tunanin ina zan shiga idan ya fita ?

Na dai ƙarasa ciki ba kowa a falon da suka fi mu’amala da shi na nufi ɗakin Vicky muka yi kaciɓis fuskarta ta washe da fara’a Barka da dawowa ta shiga yi mini cikin farin ciki da ya kasa barin fuskar ta ta na juya ina cewa  “Dama dubo ki zan yi .”

Tana biye da ni har falon da na fi zama don na yi hanyar dakina ta ce oga ya fita .

Na zauna ta tafi kitchen ruwa  ta kawo mini ta zauna daga gefena a ƙasa tausayinta na ji ya lulluɓe ni tuna abin da ya faru da ita a rayuwa ta rasa iyayenta saboda ta amshi addinin gaskiya in sha Allah zan zame mata yar’uwa.

Labari na yi ta jan ta da shi har na tambaye ta Lema ya yi ma Amal hukunci? Ta girgiza kai ta ce a’a.

Na ƙara girmama matsananciyar ƙauna ko in ce makahon so da yake ma ya’yansa, kaico na faɗi a raina ni kam ba zan bari abin da zan haifa ya tashi ba kwaɓa ba, tarbiya wajibi ce ga mai haihuwa akan abin da ya haifa, ayar Alkur’ani ta ce kullukum ra’in wa kullu ra’in mas’ulun arri’ayata.

Dukkan ku masu kiwo ne kuma kowanne mai kiwo abin tambaya ne ga abin kiwonsa .

Amma mene ne abin burgewa ga tarbiya Irin ta Bashir Lema ta baiwa ta haifi uwar gijiyarta ya’yanka su zama ya’yan agwagwa ba dai ku bi uwarku ba sai dai uwarku ta bi ku.”

Wayata na ciro na kira mamana da muka gaisa na roƙe ta ta yi ta mini addu’a Allah ya tsare ni.

Ta ce  Ina yi Ummu. Na ce na gode zan turo kuɗi a sayi abin sadaka a dinga ba almajirai su yi mini addu’a.”

Ta ce “Me yake faruwa ne Ummu?

Na ce “Ba komai, halin yau da rikicewar zamani na ba ni tsoro.”

Ta ce “Za a yi in sha Allah. Allah ya tsare mana ku ya shiga lamarinku ya raba ki da cikin da kike ɗauke da shi lafiya.”

Na kasa faɗin amin sai dai na ce a zuciyata.

Hirar ɗan gidan Lubna da aka yi ma shayi muka yi na ajiye wayar na gyara zama na mayar da hankalina ga TV.

Ina nan zaune har su Dina suka fito ba wanda ya ce mini ci kanki har ita Dinar da kan ce mini sannu, anan na yi sallar azahar Amina ta kawo mini abinci ina cikin ci Bashir Lema ya shigo mamaki ƙarara ya bayyana a fuskarsa da gani na bai dai tambaye ni ba har sai da muka je daki don yana gama magana da ya’yansa ya tashi ya tafi na bi shi yana shiga waiwayowa ya yi ya ce “Me ya dawo da ke?

Na turo baki na isa gado na zauna ya zauna kusa da ni “Me ya sa kika dawo?

Na ƙara tura bakin bayan kicin-kicin da na yi  “Ba zan zauna gidanta ba, ka san bu…

Maganar maƙalewa ta yi na kasa furta kalmar budurwarsa da na yi nufi don sai na ji abin ya yi mini ganɗanɗan ko in ce banbaraƙwai.

Uhmmm.

Ya faɗi yana tsare ni da idanuwansa na kauda fuskata ka san kuna son juna da ka rasa wurin kai ni sai wurin ta .”

Yar dariya ya yi wadda ba zan riƙe sau nawa ya yi ta ba tsawon sani na da shi .

Ya sa hannu ya kamo ni ya sanya jikinsa dole na bi shi muka kwanta “Kishi kike da ita ?

Ya raɗa mini a kunne na tura baki ya ƙara yin dariyar “Ni da ita ba soyayya, mun zama aminan juna zamani mai tsawo abokiyar karatuna ce. Wa ya faɗa miki muna soyayya?

Ido na ɗaga na zabga mishi harara ya ƙara dariya da alama nishaɗi nake ba shi “Ki yi haƙuri ki tashi mu koma ta san kin fito?

Na girgiza kai “Ta fita na fito, ni wallahi ba zan ƙara komawa gidanta ba zan zauna anan har ka samu gidan.”

“Za ki kula da kanki,? Ya tambaye ni kai na ɗaga mishi “Dama Haj ta ce bai kamata na ɗauke ki na bar su Dina su kaɗai ba, ni kuma na ga Mommyn su ta kusa zuwa saboda bikinsu.”

Gabana na ji ya buga jin furucin sa na Mamansu Amal za ta dawo nan kusa hannunsa ya kai kan fuskata yana shafawa ya gangaro zuwa sassan jikina aka fara dukan ƙofar kamar za a karya ta tare muka kai duban mu ga ƙofar ya zare jikinsa ya nufi ƙofar na gyara rigata ina kallo tare da sauraren abin da zai faru Suhaima ce ta bayyana da buɗewar sa hannunta a sama ta fara ƙara da ambaton Dina ta faɗi! Hannunta ya kama suka tafi ni ma na dira na bi su.

Yau ne rana ta farko da na shiga wurin su, matsakaicin falo ne sai ɗakuna uku biyu a jere sai daya na kallon biyun mai kallon biyun suka shiga na bi su, Dina na kwance tana juyi ta dafe ƙirjinta shi ya kamata yana tambayar me ya same ta kuka ta fashe da shi ta ce Taj ya fasa aurenta uban ya shiga lallashi da tambayar abin da ya faru har ya fasa cikin kukan ta ce ya ce ba ta da tarbiyyar da zai zaɓa ma ya’yansa ita, ya nemi ta canza dressing ɗinta ta ce ita ko sun yi aure ba za ta canza ba.

Da ƙyar ya samu ta yi shiru bayan ya ce zai kira Tajuddin, ganin ba shi da niyyar tafiya na juya na fita.

Ɗaki na koma barci ya fara ɗauka ta ya shigo ina jin shi ya yi waya da saurayin nata ya ce yana neman shi ya yi masa alƙawarin zuwa gobe.

Washegari bai fita ba yana jiran isowar shi tare muka fita falon da Easter ta zo ta shaida mishi isowar shi, su biyu ne shi da abokinsa cikin girmamawa suka gaishe mu ba ɓata lokaci ya tambaye shi dalilin sa na fasa auren Dina sai da ya ƙara nutsuwa ya yi masa bayanin idan suna magana duk abin da zai ce mata ba ya so kai tsaye za ta ce duk abin da take so shi ba zai hana ta ba tana da yancin yin abin da take so kamar yadda shi ma ba za ta hana shi yin abin da yake so ba.

Bashir Lema ya ce to yana so ya wuce suna son junan su haka bai kamata ba.

Ya ce ya wuce amma a yi mata faɗa ta san girman miji.

A raina na ce can abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa Bashir Lema ne zai ma ɗansa faɗa?

Amal da Suhaima suka fito Amal daga ira sai wata yar riga tsawonta kadan ta wuce gwiwa hannunta na shimi ne kanta ba komai sai gashinta da ya sha gyara yana sheƙi ta sa dogon takalmi.

Suhaima riga da skirt ne skirt din mai tsagu har kusan cinyarta, rigar ƙarama ta kama ta ita ma kai buɗe suka samu wuri suka zauna na saci kallon Tajuddin dogo ne kyakkyawa mai cikakken saje da ya ƙara mishi kyau da ka gan shi kasan akwai nutsuwa da kamala a tare da shi ga masu gidan rana idan Dina na taƙama da su shi ma babban gida ya fito.

Suka yi sallama ba tare da sun taɓa komai daga daga ababen ci da sha da Peter ya yi ta sintirin jera musu, suka tafi Bashir Lema ya miƙe ya shiga wurin su ya fito tare da Dina yana riƙe da ita duk ta zama wata iri kujera daya suka zauna yana yana lallashin ta. Tajuddin ya dawo ta kwantar da hankalinta cikin shagwaɓa ta ce ba ya ce dole sai ta dinga rufe ko’ina a jikinta ba? Na saki kunne na ji me zai ce sai na ji yana ci gaba da rarrashin ta.

Amal na ta taɓe baki da sakin tsaki tana faɗin kan wani ta shiga wannan halin kawai ta manta da shi.

Suhaima dai ta nutse cikin kujera da ear piece tana waya.

Shigowar saƙo a wayata ganin daga Haj Fanna ne na tashi na tafi ɗaki.

<< Ummu Radiya 33Ummu Radiya 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×