Skip to content
Part 35 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Ganin sakon daga Haj Fanna ne na tashi na tafi ɗaki kan tafiyata take faɗa mini ba ta ji daɗi ba da ta dawo ta samu na tafi, tana fata ba zan sanar da Lema ba.

Na goge saƙon na yi kwanciya ta ina ƙara mamakin ta ni wane karen hauka ya cije ni da zan saki jiki mu yi mu’amala ta sirri da ita ta har yau ita ɗin tana ƙaunar Bashir Lema, ko danganar da take cewa ta yi bugawa da ta yi abin ya gagare ta amma ko gobe ta samu dama babu abin da zai hana ta aurensa.

Shigowar sa ta sani tashi CCTV Camera ya kunna da ban san san da aka saka ta ba abubuwan da suka faru a gidan suka yi ta zuwa suna wucewa rashin gani na ya sa na gane tafiya ta gidan Haj Fanna aka maƙala ta sai dai ko sau ɗaya ba a nuno Khalil ya shigo ɗakin ba.

Ƙwafa ya yi ya ce lallai yaron nan amma zan kama shi.

Ni dai ajiyar zuciya na fitar ina mai gode ma Allah da ya sa ya ji da kunnensa na fita a zargi.

Sati guda da faruwar rikicin Dina da Taj ɗinta aka sake wata wannan karon ya ƙi amsa wayar ubanta ta shiga wani irin tashin da ya kwantar da ita har sai da ya kai ta asibiti.

Na fito wani hantsi zan shiga kitchen saboda aiken Vicky ko in ce Amina kasuwa mutanen gidan sun aiki Easter sai na ce ta je su tafi tare.

Dina na gani kwance male-male ta yi amai a inda take kwance ga Amal da Suhaima zaune amma suna faɗin ba za su iya taɓa amai ba sai idan Easter ta dawo ita da Vicky su wanke mata su kuma su kai ta hospital.

Na koma na samo tissue na goge aman sannan  na kamo ta da ƙyar na samu ta miƙe don nauyin cikin jikina muka soma takawa har ɗakinta toilet na wuce da ita na haɗa mata ruwa da taimakona ta wanke jikinta na fito na bar ta ta yi wanka da ta idar ta kira ni na sha mamakin kalmar Aunty da ta shiga kunnena wadda ta yi amfani da ita.

Na shiga na taimaka mata muka fito na ciro mata riga ta sanya sai ga su Suhaima sun shigo isowa suka yi suka kama ta har suka fita Amal na masifar kan wani za ta kashe kanta ya ce bai yi sai me?

Ganin ɗakinta na bukatar gyara na gyara mata kafin na fita.

Ina isa suna gama zaunar da ita a mota wani kallon wulaƙanci Amal ta yi mini ta ce “Lafiya?

Na juya ta shiga Suhaima na gefen ta suka bar gidan, Bashir Lema na kira da na koma ɗaki na sanar da shi ban fito ba sai da Amina ta dawo ta kira ni a waya na fita na duba sayayyar ta ce tana son yi mini wata magana kitchen ɗin na baro na koma falo na zauna a kujerar da na fi zama sannan na ce ta faɗa mini maganar a hankali cikin nutsuwa ta ce islamiya take son shiga idan zan bar ta a ranakun ƙarshen mako.

Na ce ba damuwa za mu je tare sai a yi registration ta yi ta mini godiya na ce ba komai.

Da tafiyar ta wayata na ɗauka na kira Bashir Lema tabbaci ya ba ni an ba Dina gado na ce yaushe zai dawo mu je ya ce Iliya zai dawo sai ya zo da ni.

Cikin shiri na zauna har Iliyan ya dawo muka fita tare da Amina da na ce ta shirya mu je tare.

Mun samu tana jin jiki an ce jininta ne ya hau. Sai juye-juye nake kan kujerar da nake don ta ishe ni na gaji, Bashir Lema da ke tsaye ya naɗe hannaye a ƙirji har na ji mamakin ko ba ya gajiya ƙafafuwansa ba za su gaji ba.

Ya kira ni da hannunsa na tashi na isa gaban shi ya ce “Mu je Iliya ya mayar da ke gida.”

Na ɓata fuska na ce “Zan zauna da ita, idan na tafi wa zai zauna da ita?

Ya ce “Mutanen Kaduna sun kusa shigowa.”

Ya kama hannuna “Mu je.”

Na zame hannun na isa gaban gadon na yi mata addu’a duk da barci take su Amal na zaune bisa gadon.

Na koma wurin shi muka fita a mota na samu Vicky da ba ta wani daɗe a dakin majinyaciyar ba ta ce za ta koma mota ta jira ni na shiga ya rufe ƙofar muka tafi ya koma ciki.

Sai dare su Haj suka zo gidan, Su’ada suka bari asibitin ta kwana da ita.

Sosai family ɗinsu suka yi ta zuwa duba Dina hakan ya sa na ce ma Mamana su zo su gaishe ta daga nan su ga inda nake Mama Aunty Larai Lubna Aunty Ya gana da Aya suka zo , kwana biyu suka yi suka koma na ji daɗin ganin su na kuma ji daɗin sha tara ta arzikin da Bashir Lema ya yi musu.

Dina ta ji jiki sosai don haka ko da ta dawo lallaɓawa take Mamanta da ke can ta tayar da hankalinta kan Mama Zulai ta zo ta kula da Dina, mijin Mama Zulai kuma a wannan karon ya nuna kwanjinsa ya hana ta zuwa. Na yi iyakar ƙoƙarina wurin ba ta kulawa duk safiya da na fito wurin ta nake fara shiga in duba ta abin karyawa nan nake sa wa a kawo na tasa ta sai ta ci nan uban zai shigo ya same ni zan lallashe ta mu fita Main parlor a maimakon daki da take kwanciya .

Da rana ma sai na tsaya take cin abinci shi kuma ya yi da daddare sai ya ga ta ci abinci ya raka ta ta kwanta sai ta yi barci zai fito.

Da haka ta warware sai na daina zuwa zazzaɓi na yi, kwana biyu ban fito ba ina kwance ɗaki na ji knocking daga kwancen na bayar da umarnin shigowa tunanina Amina Vicky ce ga mamakina Dina ce na yunƙura na tashi zaune  na sauka gadon na ce shigo mana ganin ta tsaya daga bakin ƙofar, ta tako cikin nutsuwarta don dama ita ɗin mai nutsuwa ce.

Ta zauna a kujera ta ce  “Morning Aunty.”

Na yi murmushi na amsa mata ina zama  ta ce “2 days kin bar fitowa.” Na ce “Ban jin daɗi ne na yi zazzaɓi.”

Ta ce “Sorry. Irin hijaban da kike sanyawa nake so .”

Na yi saurin duban ta da mamaki, ta yi murmushi “Yes ina so. Sai Abayas irin waɗanda kike sanyawa idan kin samu time mu fita ki taya ni na saya.”

Na ce “Ba damuwa kowane lokaci ni ba na yin komai. Hijabai kuma zan yi ma ƙawata magana a ɗinko miki a Kaduna.”

Ta ce “Thanks.”

Ta miƙe na raka ta da ido har ta fice na koma gado na kwanta cike da tunanin sabon sauyin mu’amala da aka samu tsakani na da Dina.

Tun daga ranar kuma idan ba ta gan ni ba za ta biyo ni ɗaki duk da ba mai son magana ba ce muna ɗan yin hira.

Mun fita ta sayi kayan da ta ce an ɗinko hijabai Nabila ta zo da su na ba ta sosai dressing ɗinta ya sauya da ta sanyo wata abaya cikin waɗanda

muka sawo ta yi matuƙar yi mata kyau ga ta ita ɗin mai kyau ce ta shigo wuri na na ce ta yi kyau ta yi murmushi sai hawaye suka zubo mata na ce “A’a mene ne na kuka?

Ta share hawayen “Bad dress na daga cikin abin da ya sa Taj ya ce bai aurena.”

Na girgiza kai don a yadda ta furta kalaman ta ba ni tausayi sosai

“Yana yawan yi mini tambaya kan Islam ban sani ba rabuwar mu ta ƙarshen nan tambaya ta ya yi kan farillan alwala, da na ce ban sani ba ban kuma so yana mini irin haka, shi ne ya ce ya haƙura da ni ba zai ɗauke ni ya kai ni gidansa ban san komai ba kan addinin islama ba ba kuma na so a koya mini. Har yana cewa ka tabbata ka auri mai tarbiya ita za ta taimaka wurin gyara taka tarbiyar.”

Ta share wasu hawayen “Muna yara Papi na kai mu wata Sch ta addini duk Weekend muna yin wayo muka ce ba ma so sai ya ƙyale mu.

Za ki fara koya mini karatun?

Na ɗaga kai ta ce “Na gode. Na ce “Kar ki damu .

Sai girki ya ce yana son matarsa ta yi masa girki ta zauna ta rarrashe shi sai ya ci sai ya tambaye ni wane Dishes na iya, nan ma na ce ban iya ba shi ne yake cewa ba mace.

Amma Aunty na ga Papi bai damuwa sai an yi masa girki, idan ma Mommynmu Europe take ke anan ban taɓa ganin ya damu da sai kin yi masa ba.”

Ɗan murmushi na yi  “Ƙila ko don ni yarinya ce ƙuruciyata yake lallaɓawa ta ce ba ta gane ƙuruciya ba me nake nufi? Na yi dariya sai ta ce  Allah wata maganar idan muna yi ba ta gane me nake nufi.

Na ce “To kamar yau sai ki dinga tambaya ta.

Daga ranar na fara koya mata abin da ya shafi addini, ta iya sallah wadda ta ce papinsu ya koya musu tun suna yara na shawarce ta da shiga makarantar da Amina ke zuwa, ba ta ƙi ba sai Papi ɗin nasu ne ya ce a kira makamin ya dinga zuwa gida yana koya musu har su Amal, ita ɗin da take so ita kaɗai ke fita.

Cikina ya tsufa hakan ya sa Bashir Lema rage tafiye-tafiye duk yamma muna fita in motsa jiki ina dan koyon mota duk da cikin ya yi girma sosai ya sa ba buɗe bai faye yi mini nauyi ba na fi jin nauyin sa idan na tashi barci kafin na wattsake.

Mun yi sayayyar kayan haihuwa na Baby zuwa nawa ya so lallaɓa ni in yarda mu je tare da Haj Fanna wai za ta fi zaɓar mana masu daraja na ce a’a.

Ya ɗaga bikin Suhaima ya ce sai na haihu ai kam shi da matarsa kamar su cinye juna saboda bala’i ta waya  ta ce Date din da ta sanya sannan take cikin hutu shi ne saboda wata haihuwa da za a yi masa zai ɗaga mata bikin yarinya?

Sai na yi ta mamakin masu faɗin ta mallake shi ita ke juya shi shi ya sa aka ce mata da miji sai Allah.

Wani hantsi na fito na yi mamakin samun Khalil shi ne ke yi ma  Amina Vicky bayanin abin da za ta dafa da dare, Amal da ke gefen sa ta kama dariya ta ce  “Mene ne laifin na Peter ya ce A’a na musamman ne abokinsa zai sauka daga Turai nan Abuja zai sauka kuma wurin sa zai fara sauka .

Na wuce suna maganar na shiga kitchen nan Amina ta same ni na ce ba za ta makaranta ba ta ce saboda girkin boss ba za ta je ba, na jinjina kai lemon abarba da na soma haɗawa ta ce in bar shi ta yi mini.

Falo na koma na zauna jiran ta Khalil ya sanya Easter zuwa ta gyara mishi daki ina sauraren hirarsa da Amal har da Suhaima da ta fito ba jimawa, Amina ta kawo mini zan tafi ɗaki Dina ta fito direct kuma wuri na ta yo yan’uwan kuma suka haɗe rai don sun tsani mu’amalarta da ni, fasa tashi na yi na zauna muka gaisa tana tambayar ba yau zan je asibiti ba,  na ce ba yau ba ne kaɗan muka yi hira na ɗauki jug dina na tafi .

Na samu Yallaɓai Lema na duba laptop na zauna kusa da shi ina mishi zancen son komawa Kaduna na haihu a can.

Laptop din ya kawar ya fuskance ni lallashina ya yi  in haƙura da komawa Kaduna yana da tarin ayyuka a Kaduna da ba zai yiwu mu koma gabaɗaya ba shi kuma ba ya son yin nesa da ni a wannan halin don yana son ɗansa ko yarsa ya iso akan idonsa.

Kuka na fara yi masa  har ya yi banza da ni sai kuma ya ce abu daya zai mini sai na haihu sai ya kai ni Kadunan a yi suna.

Dole na yarda da wannan tsarin ba don ya yi mini ba.

Yamma na yi muka fita kamar yadda muka saba kafin sallar magrib muka dawo ni ce gaba ina tura cikina da ya yi matuƙar girma yana biye da ni da ledar da ya sawo ma ya’yansa abin da suka ce mishi suna so.

Dukkan su suna zaune har Khalil a falo shi da wani da tunanina ya ba ni abokin nasa ne, Khalil ya taso yana mana barka da dawowa tare da gabatar ma Bashir Lema abokinsa Abbakar Usman kuka-sheƙa, ƙirjina ya doka jin  sunan baƙon na khalil baƙon ya tunkaro mu ba ko shakka Abakar ne.

<< Ummu Radiya 34Ummu Radiya 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×