Tunkaro ni da hayaniyar take na fahimci abin da suke cewa faɗa take tana kuka kan ba za ta ɗauki abin da yake mini ba idan ta ɗauki ita abin da yake mata.
Ya ce ta ɗauki mataki ta yi abin da ta ga za ta yi .
Ta fito tana kuka ta biyo ni don na kama hanyar fita sai da na kai Gate ta cim ma ni da kyar ta samu na tsaya na ce “Dama Amina haka kike ma mijinki kina ɗaga harshe sama da na shi kina so ki zama mace ta ƙwarai?
Ta share hawaye “Sai ya wulakanta mini ke gaisuwa ba ki da arzikinta?
Na ce “Ba sai ya gaishe ni ba matuƙar zai riƙe ki da mutunci ki koma ki ba shi haƙuri ki kuma bar ɗaga harshenki saman na shi.”
Ta buɗe baki ta yi magana sai kuma ta fasa ta ce “Shi kenan zan yi yadda kika ce ki sauka lafiya .”
Na wuce har na fita tana tsaye a inda na bar ta na tafi cikin ruɗu mai yawa game da wannan aure da na zama sila ta ƙulluwar shi.
An ɗan kwana biyu ba wata matsala daga Amina wanda na yi ta murna don na dage da addu’a Allah ya zaunar da su lafiya, har Lema ya sake zuwa sai dai raina ya ɓaci da na gane bai faɗa ma matarsa Kaduna zai zo ba ta wayar da suke yi na gane da Dina ta zo kuma don ta saba zuwa wuri na ni ma na je sau biyu duk da son ya’ya irin nashi sai na gane bai ji daɗin zuwan ta ba ta ce Papi ka shigo KD ba labari muka yi waya da Mommy ta ce mini kana Bauchi? Ban tsaya sauraren amsar da ya ba ta ba na wuce kitchen na daɗe tsaye ina jin ba daɗi kafin na fito.
Dina ta daɗe da mu kafin ta tafi washegari kuma sai ga Suhaima da ɗanta ta zo wanda ya yi wayo sosai daga sannu da zuwan da na yi mata ta jefe ni da kallon banza ban kuma shiga sabgarta ba barin su na yi a falon ƙasa ita da papinta da ya haɗa ɗanta da Aman ya sa a jikinsa na tafi ɗakina na yi kwanciyata na fara barci ya zo ya tashe ni wai za ta tafi ni kaɗai na sauka tsaye na same ta ban mata magana ba sai ita ta dube ni a yatsine ta ce “An samu wuri har wani cikin kika kuma yi ?
Na rama Irin kallon da take mini na fara shafa cikina ta yi ƙwafa “Papi ya ce ma Mommy zai tafi Bauchi ya taho wurin ki sai Mommy ta yi da gaske za ta raba mu da ke.”
Na ja mummunan tsaki na juya na fara hawa sama ina ji tana jefo mini maganganu masu zafi da harshen nasara ko waiwaye ban yi ba na same shi kwance Aman na gefen sa ya yi barci hannu ya miƙo mini na shige jikinsa.
Wannan karon kwana biyar ya yi ya tafi yana tafiya sai ga Amina wai ta kawo mini wuni na yi murna da na gan ta cikin walwala ta ce mini kuma Abakar ya sauke ta bugu- da ƙari wani kyau na musamman da ta yi fatarta na ta sheƙi ƙurajen da suka ci mutuncin fuskarta sun duk sun ɓace kuɗi ta sanya akan ƙafata wai in ji Abakar a karo mata kayan gyara na Sunaf skin care na yi murmushi na nuna mata wayata “Ɗauki ki cire nombar Nafisa mai kayan.” Cikin hanzari ta ɗauka “Na ce “Ni na sha ma rabo muka samu ganin uban kyan da kika yi ?
Ta yi murmushi “Aikin kayan Nafisa ne kawai.”
Na ce “To Allah ya kawo mana cikin .”
Ta ce Amin a hankali.
Wuni ta yi mini sosai ita da Hassana da ta zo ta same ta.
Cikina na ta girma ina jin daɗin zama a Kaduna illa rashin Lema wanda idan ya tafi ya kan daɗe ban gan shi ba wani lokacin har sai Haj ta yi faɗa Haihuwar Dina Amal da Mamanta suka zo shi ma ranar suna sai da aka yi sa’insa tsakanin ɓangaren ta da na Lema, sai matsalar zaman Amina da Abakar da idan ta yi sauƙi kwana biyu sai kuma ya dawo da tsiyar sa ranar da na yanke yi masa magana na tafi gidan da hantsi ranar ta kama asabar Amina na zuwa islamiya na tura mata text kafin zuwa na tunanina ba za ta fita ba idan ta samu saƙona sai dai shi kaɗai na samu a falonsu na ɗaure fuska matuƙa muna duban juna na ce “Me ya sa ka san ba za ka riƙe auren Amina da kyau ba ka karɓi tayin da na yi maka?
Ya taɓe baki ya noƙe kafaɗa na yi ƙwafa don na kawo iya wuya
“Mene ne dalilinka na wulaƙancin da kake mata? Don na fara gajiya?
Wani murmushin rainin wayau ya yi “Magana ai ɗaya ce Ummu kin sani na sani ke kaɗai ce nake so kuma ke kaɗai zan ci gaba da so a….
Kunnena na toshe na ambaci A’uzu billahi minash shaiɗanir rajim. Wace irin magana kake yi haka ? Ina matar wani kana faɗa mini wannan maganar?
Hannu ya ɗaga mini “Ya isa Ummu, ki kawo karshen wasan nan ki rabu da mutumin nan da bai damu da ke ba sai uwarsa ta matsa masa yake zuwa gare ki, ki tarbe ni ni ne nake son ki ki bar inda ba a san muhimmancin ki ba na yi tunanin zan iya rayuwa da wata ɗiya mace ba ke ba amma abin ya ci tura.”
Na share zufa da ke wanke mini jiki da fuska “Ina zaman jiran ki dubi abin da kika koma kika sake ɗauko wa .”
Ya faɗi yana nuna cikina da ya yi girma gabaɗaya kaina ya ƙulle na rasa tunanin da zan yi ko abin da zan kuma cewa tsaye na miƙe na juya don barin falon muka yi ido huɗu da Amina da ke sanye da dogon hijabi har ƙasa ban san tun san da take tsaye ba haka ban san iyakar abin da kunnenta ya jiye mata ba na ratse ta na wuce ba ko waiwaye.
Na isa gida ban saurari Ma’u da Aman ba na haura sama na kwanta bisa gadona rasa inda zan sa kaina na yi laifn kaina nake gani ni ce sila kuma kanwa uwar gami a haɗin aure tsakanin Amina da Abakar Da zuciya ɗaya na yi haɗin nan Allah ka sani.” Na faɗi a hankali sai kuma na shiga addu’a da ƙarfi Allah ya dube ni don karfin mulkinsa ya daidaita tsakanin waɗannan ma’aurata.
Ban san iya lokacin da na ɗauka a haka ba juyin da ɗan cikina ke yi ya sa ni tashi zaune na share fuskata da ke ɗigar gumi na ɗauki wayata na sauka ƙasa ga mamakina Amina na gani tsaye a falon ƙasa ta juya baya tana waya wani mummunan faɗuwar gaba ya ziyarce ni don na san ko me ya kawo ta ba lallai ya zamo alheri ba, a inda nake na tsaya cak jin abin da take furtawa “Zan dawo gida Mommy gara mini Daddyn ya kashe ni na huta da wannan rayuwar.”
Ta yi shiru cikin saurare amma ba ta bar shessheka ba sannan ta ce Tun da kin ƙi zan tafi wani wurin.”
Wayar ta sauke ta share fuskarta daidai da fara ɓurarin tawa wayar na duba Maman Amina ce na ɗaga kiran na gaishe ta da girmamawa ta ce Vicky ta kawo mata wasu zantuka yaran nan idan ba ya son ta tana so ya rabu da ita amma ba ta yarda Amina ta rabu da ni ba na taimake ta na je inda Amina take na dawo da ita wuri na gobe tana nan tafe.
Na amsa mata ta yi mini godiya na sauke wayar Amina da ta zuro mini ido ta fara takowa na sauka muka haɗu kasa ce mata komai na yi na zauna a kujera ta zauna ƙasa kusa da ƙafafuna ta haɗa kai da gwiwa “Ki yi haƙuri Amina.”
Ta ɗago ta dube ni “Na gama zama da Abakar, a yau ya sanar da ni ke ce matarsa ta farko da yadda kuka haɗu har kuka rabu.
Ta haɗiyi yawu”Ya kuma sanar mini ke ce Ummun da yake kira a shimfiɗarmu.”
Ta yi shiru don yadda ƙirjinta ke sama da ƙasa “Ba zan iya haɗa soyayya da ke ba na bar shi har abada na so na nisance ku Mommy ta hana.
Tagumi na rafka na rasa abin cewa mun zauna jugum-jugum na tsawon wani lokaci kafin na tashi na shiga kitchen abincin da na yi kafin na fita na fito da shi Amina kasa cin komai ta yi da na matsa mata ta sha yoghurt kaɗai.
Tare muka kwana na samu saƙonnin Abakar kala-kala da yake faɗa mini na kashe aurena na dawo gare shi .
Mahaifiyar Amina ta zo ta ƙara roƙona na riƙe mata Vicky na yi haƙuri da ita, na ce in sha Allahu zan yi iya yi na.
Kwana uku kaɗai komai ya gallabe ni, Lema na kira na shaida mishi zan dawo Abuja, gidanmu da gidan Haj kaɗai na je sauran jama’a na kira su ta waya ne kayan sana’ata su suka fara gaba ta mota muka bi jirgi ni da Amina da Aman na yi blocking din Abakar ya sake layi ya kira na yi masa rantsuwar ya sake kira na kotu za ta raba mu sai ya shafa mini lafiya.
Mun isa gidan yana nan yadda yake haka ma mutanen cikin sa, ba wanda ya kula mu muka shiga harkar mu sai dai Amal da ta dawo daga club ta yi ta ƙankanci tana zagina da ambaton sai na fita ɗaki na shiga na yi shiru cikin kakkaɓi gaba kura baya siyaki na baro Kaduna nan ma ga abin da na guda ita kuma uwarta ta tsaya kan ba zai shigo ɗakina ba sai da suka kwashe ta ba daɗi ya shigo wannan ya hana mararin da muke da juna yin armashi yana gama yi mini kwana biyuna ya tsiri tafiya da ta yi matuƙar ɓata ma uwar su Amal rai sai zage-zage take wunin ranar abin da suka wuni yi kenan ni da Amina sai dai kallo da yamma Amal ta yi shiri ta fita sannan uwar ta shiga wurin ta shi ne muka samu muka sake.
Na idar da sallar asuba na yi karatun Alkur’ani da azkar na miƙe na koma gado cikina ya yi nauyi sosai don haka komai cikin ƙarfin hali nake na fara barci ban ji buɗe kofa ba da na bari a buɗe saboda Amina ko za ta kawo mini Aman ko wata buƙatar ta kawo ta sai dai zafi da na ji ya ratsa allon kafaɗata na buɗe ido ba shiri Amal ce tsaye kaina da wuƙa ta ƙara kawo mini sarar duk da cikin jikina kaucewa na yi ba shiri hakan ya sa ta same ni a baya ba saurarawa ta kawo wata da ta sauka kan hannuna da na tare wukar ƙara na ƙwalla daidai da shigowar Amina ta baya ta damƙe Amal ɗin ba shiri ta wurgar da wuƙar ganin jinin da ke zuba jikina Amina ta haukace tana kai mata duka me ta tuna kuma ta sake ta ta tura ta waje ta rufe ɗakin ba ta taɓa wuƙar da ke yashe a ƙasa ba sai da ta ɗauko tsumma ta ɓoye ta a drawer ta murza key ta zare shi sannan ta nufo ni ko’ina jini ke zuba kafaɗata bayana hannuna ta kamo ni na sauko gadon ina cewa ta taimake ni na canza kaya mu fita zuwa hospital din ta ce a’a haka za mu tafi ta kama ni muka fita jini na ɗauka ta ina tambayar ina Aman ta ce uniform ɗinsa ta zo ɗauka ta samu wannan abin.
Na dai san san da ta sanya ni a mota daga haka jini ya ɗauke ni na suma na farka ne na gan ni na sha adon bandeji a inda na samu raunukan na dubi hannuna ƙarin jini ake mini gabana ya ce ras! Sa’ilin da na dubi cikina babu komai na dubi gefena Haj ce na ƙara duban daya bangaren Mama ce da Aunty Larai na rufe idona gam raɗadin ciwuka da na zuciya na daɗa dabaibaye ni ba dai cikina ya mutu ba ? Na tambayi kaina
Sannu suka shiga rige rigen yi mini Aunty Larai ita ta ba ni amsar abin da nake son ji sakamakon tsorata da kika yi jini ya fara zubar miki likitoci sun tabbatar abin da ke cikinki yana haramar fitowa duk da lokacin sa bai yi ba suna shirin yi miki aiki Allah ya yi ikonsa suka ciro shi an sanya shi cikin kwalba.
Na saki ajiyar zuciya ina ma Allah godiya Namiji kika samu.” Ta ƙara fadi Haj ta matso
“Sannu yan nan kin auna arziƙi.” Sai ta fara kuka “Yau ga ranar da nake guje ma wannan yaron yau ina ranar wannan kafurci da Amal ta aikata? Da da ƙarar kwana ta kashe ki me zai ce ?
Mama da Aunty Larai suna ba ta haƙuri tana kuka a haka Leman ya shigo ya yi sanyi sosai da alama yana cikin alhini mai yawa da ɗaiɗai suka fara barin dakin a ka bar ni daga ni sai shi karo na farko ya ba ni haƙuri kan abin da ya’yansa suka yi mini tare da alƙawarin kare mutuncina ba zai ƙara bari ya’yansa ko uwarsu su kuma taɓa ƙima ta duban shi kawai nake a raina ina faɗin ta baya ta rago an yi wa goɗiya tsarki.
Su uku suke jinyata Mama ta koma gida bayan na ji sauƙi sai jiran Babyn ya yi ƙwari a sallame mu.
Wani yammaci mun fito shan iska saboda gajiya da zama wuri ɗaya da na yi ni da Amina ne take taya ni zagayawa labari take ba ni ranar da abin ya faru ta ce ita da Iliya Direba suka kawo ni hospital amma ba a karɓe ni ba duk da magiya da roƙon da suka yi ta yi sun ce sai sun zo da Police, sun canza asibiti ba ta canza zane ba ta kiɗime ta rasa yadda za ta yi sai ta kira mahaifiyarta ita kuma ta kira wani ƙanenta Spetan yan sanda ne da ke Imo State shi ta kira shi kuma ya kira hukumar yan sanda ta nan Abuja suka turo yan sanda biyu sannan aka karɓe ni a ranar Bashir Lema ya juyo saboda kiran da ya samu duk ƙoƙarin da ya yi wurin fahimtar da yan sanda Family Issue ne ba su yarda ba an kai bincike gidansa da kamo Amal sai dai ta tsere.
Na jinjina kai ina ɗan murmushi “Ke fa kika dace da hukuncin Amal don ke ce kishiyarta ba ni ba.”
Ita ba ta yi murmushin ba siririn tsaki ta ja “Ki bar mara hankali ai kam da na nuna mata ta ta ƙwayar ta ƙarya ce wai uban na faɗa Maman ta dage ba cikin hayyacinta ta yi ba a bige take.
Na girgiza kai na ce “Kaico!
Jama’a daga familyn Lema da nawa suna ta zuwa gaishe ni mun koma gida da baby na da babansa ya sa mishi sunansa ban so yin taro ba don kula da jikin Bashir Karami amma dangin Lema sun ce sai sun yi taro mota-mota haka suke zuwa suna aka yi na ji da gani fiye da na Aman Maman Amina da ita aka yi bayan ta zo duba ni ina hospital ta dawo taron suna.
Maman su Amal kamar ba ta gidan duk habaici da zagi da dangin Lema ke mata shiru sai bayan suna da kwana biyu ciwo ya tashi ashe ta daɗe da cutar Cancer ta ƙwaƙwalwa Allah ya ɓoye abar sa sai yanzu, asibiti nan cikin Abuja suka fara zuwa ganin abu ba sauƙi ya shirya fita da ita waje watana biyu da haihuwa suka fita zuwa Canada wata guda suka dauka suka dawo na ƙara tsorata da lamarin Ubangiji Mai mayar da Sarki bawa an canza hallittar wannan baiwar Allah ta koma ba uhmm ba uuhm wata aka samo tana kula da ita don yan’uwanta da ya je ya yi ma magana kowa ya zuƙe.
Daga ni sai Amina muke shawagin mu a gidan tana kallo na da Lema ba yadda za ta yi sai lokacin ya yi mini maganar Amina zaman me take ina mijinta na ce saɓani suka samu ina jiran sai ya zo. Na ja bakina na yi shiru sha’awar komawa karatu Amina ta nema na ce akwai igiyar aure a kanta dole ta nemi iznin mijinta ta ce a’a, ta yi magana da Mamanta ita ta kira Abakar ta ce yarinyarta na son komawa karatu ya ba ta takardarta wai ba kunya sai ga shi ya fara kiran Amina a waya ba ta ɗagawa sai ya fara turo saƙonni nan ma ba ta reply wani Weekend sai ga shi ba ita ya nema ba oga Lema ya nema shi kuma ya kira ni na fito na same su zaune a falo na yi kamar ban gane shi ba, Lema ya fuskance ni ya ce “Ya zo bayar da haƙuri ne sai ki shiga ki shirya masa matarsa su tafi.”
Na girgiza kai “Ba za ta koma haka kai tsaye ba sai ya janye abin da yake mata ya yi maka alƙawarin riƙe ta cikin mutunci da girmamawa.
Ya yi mini duban rashin fahimta sai kuma ya ce “Shi kenan ku shirya kai da matarka.”
Ya miƙe na tashi na bi shi muka tafi muka bar shi.
A ranar bai samu ganin Amina ba ya juya, wasa-gaske Abakar ya dage biko ni da ita muka yi ta gara shi har sai da na tabbatar son ta yake kuma zai gyara sai da na shirya ta tsaf sannan na raka ta daga nan na yi yawon arba’in.
A gidan Haj na ji ana maganar Suhaima a wani suna da ake yi a gidan ta koma Abuja ko gidan da ta kama haya ita ta kama saboda ɗan banzan neman matan mijinta.
Lema na ta da na sani na soyayyar da ya nuna ma ya’yansa yau ga inda ta kai shi Amal ta shige ƙasashen waje ba wanda ya san inda take ya koma neman ilimin addini ka’in-da-na’in Suhaima ma duk san da ta zo ya dinga mata nasihar ta shiga islamiya ta san Allah da yadda za ta bauta masa. Tun da Amina ta koma sai hamdala Abakar ya sauya ya riƙe ta ruƙo na tsakani da Allah kamar yadda na yi fatan ya yi tun farko har ga shi tana ɗauke da ciki.
Sai da Bashir Karami ya shekara uku na samu wani cikin wannan karon mace na samu da ya yi ma Haj takwara rayuwata sai hamdala na samu farin ciki a gidan aure bayan rayuwa da na yi da tarin ƙalubale a farko.
Tammat