Skip to content
Part 1 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Wata irin mage ce da tun da nake a rayuwata ban taɓa ganin kalarta ba, ruwan toka ce, idanuwanta su suka fi komai razana ni.

Tsugune take a ƙofar ɗakina ta zuraro mini idanuwan, bakina na rawa na kwashi gajiyayyun ƙafafuwana da na ji kamar ba za su ɗauke ni ba na runtuma ɗakin barcina angona Abakar da ke kwance kan sabon gadonmu na amarci ya miƙe,  hannayensa na tallafe da ƙeyarsa. Ya ce

“Lafiya Ummuna? Na dube shi sai na juya na dubi ƙofa, “Magen nan yau  ma ta zo wallahi.”

Na faɗi kamar zan rushe da kuka, ya sauka gadon ya bi ta gefe na ya fita.

Ina nan cikin rawar jiki ya dawo “Ni ban ga wata mage ba, na rufe ƙofa oya mu je mu kwanta.”

“Fitsari nake ji.” Na faɗi cikin wani sabon tsoron da nake ji yana daɗa lulluɓe ni.

Fitilar wayarsa ya kunna haske ya wadaci ɗakin don ba mu da wutar Nepa sun ɗauke.

Ina rawar jiki muka fita, banɗakin tsakar gida ba kowa duk da cewa gidan ba mu kaɗai ba ne, akwai mai gidan da muka kama haya kuma daga mu sai ita.

Ina duƙawa yana tsaye, ɗif hasken wayar ya ɗauke take kuma na yi ido biyu da Magen nan ta kafe ni da ido.

Da sauran fitsarin na miƙe a guje na yi kansa na ƙanƙame shi daidai da dawowar wutar lantarki, wurin ya haske.

Wai aka ce amarya ba kya laifi, ina ganin shi ya sa bai hasala ba ya kama ni da karsashi muryarsa ba amo ya raɗa mini “Wai mene ne? Na ƙara riƙe shi “Mu je ɗaki mag…. Ai  ban samu ƙarasawa ba muka yi ido huɗu tana zare mini idanuwanta.

Na rufe idanuwana gam ina tura shi tare da kokowa da harshena ya furta addu’a kowace iri ce amma abin ya ci tura, a haka muka shiga ɗaki ya rufe muka yi ciki duk abin nan ina maƙale da shi ya kunna rechargeable light na yi shirin kwanciya.

Mun kwanta ya fara wasanni da ni sai da ya zo cim ma burin sa jinin da ya zo mini ranar da aka yi buɗar kaina na kuma tabbatar da ɗaukewar sa ɗazu da na yi wanka kafin shigowar angona, yanzu kuma ya dawo.

Haƙura ya yi daga wasannin muka yi barci.

Ban ƙara farkawa ba sai gabanin asuba, , na gode ma Allah da ban yi mafarkin mage ba sai Abakar da na gani kan sallaya ya yi sujjada ga mahalicci,

na rufe ido na koma barcina.

Na farka na gan shi kan sallaya yana ƙirga tasbihi da wayarsa ya ɗago ido jin motsina muka haɗa ido ya sakar mini murmushi yana miƙo mini hannunsa na sauka na isa inda yake da rarrafe,  na kwantar da kaina kan ƙirjinsa ya ɗora hannunsa kan kitson aurena yana shafawa.

“Har kwana nawa kike yi kafin abin nan ya ɗauke? Na ɗaga kai muka haɗa ido na mayar da kaina ƙasa

“Kwana uku.”

Amma yau har kwana bakwai ya ƙi tafiya abin nan yana takura ni. Zan je Abuja ko Tea ne ki ba ni, wanka kawai zan yi.”

Na tashi da sauri jin tafiya zai yi buta na ɗauka na yi waje.

Kamar dare yanzu ma ba kowa tsakar gidan sai hijabin Haj Iyami da ke kitchen ta juya baya.

Na wuce bayin da sauri, sai da na gama lalurata na fita na shiga kitchen ɗin da nufin dafa mishi Indomie sai in haɗa mishi da Tea ɗin da ya ce.

Haj Iyami ta juyo ta dube ni cikin fara’a “Har kin fito amarya?

Na ɗan sunne kaina “Ina kwana?

Na gaishe ta ina wucewa gaban ɗan Gas ɗina da aka sanyo mini a kayan sa rana.

Ina ƙoƙarin ɗaukar tukunya in ɗauraye sai na ji muryarta “Kar ki wahalar da kanki Amarya, ga tray nan na shirya muku ɗauki ki kai maku.”

Na dubi inda take sai na saki yar  fara’a kafin na rusunar da kaina na fara mata godiya na ɗauki faffaɗan tray mai ɗauke da kwanonin ci bari kallo don matuƙar haɗuwar su, a duk kulolin aurena ba masu tsadar su.

A falo saman Carpet ɗin da aka shimfiɗa mini a tsakiyar ɗaki na ajiye tray na wuce  na ɗauki bokiti na fita, ruwa na tara saboda zafin da ake ba ya yi da ba sanyi, na kai mishi na koma ɗakin na sanar da shi ya fita.

Na janyo wayata ina dannawa ina jiran dawowar sa da ya shigo wuce ni ya yi ya shiga ciki sai da ya fito ya zauna gaban abincin, buɗewar da ya yi sai ya kira sunana da irin furucin da ban taɓa ji ya yi amfani da shi ba.

Na ajiye wayar da azama na taso “Ina kika samo wannan abincin? Na dubi kwanonin da ya buɗe farfesu ne na naman kai da ke fitar da tururi da ƙamshi, sai ƙaramin kwanon soyayyar agada da ƙwai sai ƙaramin flacks da na tabbatar ruwan zafi ne.

“Haj Iyami ta ba ni.”  Ya zura ma  abincin ido kafin ya ɗago, hassalar da na ga ya yi ita ta sa na langaɓe kamar zan fashe da kuka.

Ya sassauta “Me ya sa ba ki ji ?

Rannan da ta ba ki ban ce ki daina kawo mini ba ? Ke wata ce za ta dinga ba ki abincin da za ki ba mijinki?

Daga gama faɗin haka ya miƙe da azama ya yi ciki, na bi shi kayan da ya fiddo ya fara sanyawa ina kallonsa har ya kammala na yi saurin dauko turare na fara fesa mishi.

Ya dubi agogon da ya gama ɗaurawa a hannunsa “Na makara Ummu Radiyya.”

Na yi murmushi

“Ka ƙi cin abinci, za ka tafi da yunwa b…

Hannunsa ya ɗora saman laɓɓana, ya cire hannun sai ya kama hanyar fita na bi shi a sanyaye, Haj Iyami na tsaye ƙyam a ƙofar kitchen da ta zam santar ƙofata, a yanzu ba hijab kuma cikin kwalliya take ta wata ɗanɗasheshiyar atamfa ɗinkin riga da zane da suka zauna mata dam, ga ta yar duma-duma jawur gayu da jin daɗi sun taka muhimmiyar rawa wurin ɓoye shekarunta, don idan ba faɗa maka shekarun nata aka yi ba ko ka ga yaranta da suke duka maza kuma kowa da matarsa mijinta ya mutu tuni za ka ce ita ɗin matashiya ce yar talatin da biyar, ga ƙamshi mai daɗi da ya cika gidan ko ni da na kasance jinin kanuri tushen ƙamshi ina mubaya’a da ƙamshi mai sanyaya rai na Haj Iyami.

Ta san sirrin girki ta san na ƙamshi.

Idonta na kan mu har muka gifta ta, abin haushi nama na jan kare Abakar bai ko dubi tsayuwar ta ba sai ita ce ta ce “Ina kwana? Ya amsa kamar yana ciwon baki.

Har zaure na raka shi ya fita don zuwa inda yake ajiye motarsa da yake ɗaukar shata zuwa Abuja ko Kano.

Ƙa’idarsa sau ɗaya yake ɗaukar fasinja a kwanakin da muka yi aure.

Na juya na koma ciki, ba Haj Iyami a kitchen na shiga na ɗora ruwan wanka ina tsaye har ya yi zafi na juye zuwa bayi wani abin mamaki da ya sa ni tunani jinin nan ya tafi dama abin da yake mini kenan da Abakar ya fita zan duba in ga ba shi bai tashi dawowa sai ya buƙace ni.

Na yi wankan ba karsashi na fita zuwa dakina, sai da na yi kwalliyata na fito falo dabgen da Abakar ya ƙi ci na zauna na gyara ma zama har na kasa cinyewa juyewa na yi a nawa wurin na fita don wanke mata nata, ina gama wankewa na shiga kitchen na ji ta bayana, “Amarya ba kya laifi irin wannan kwalliya haka, abin har ya ɗauke ne? Wata wawuyar waiwaya na yi muka haɗa ido sai na ga ta ɗan diririce. “Ga kwanonin nan na gode.”

Na faɗi ina neman hanyar fita “Kun ci kenan? Ta faɗi maganar da na ji ta ƙara ƙulle mini kai.

Na koma ɗaki na hau dogon cushion na lumshe ido ko wayata da nake ƙulafuci ban kalla ba “Ke wata ce za ta dinga ba ki abincin da za ki dinga ba mijinki? Kalmomin da suka yi ta yawo cikin kaina kenan ina kuma laluben abin da ya sa Abakar ya ƙi yarda da abincin da Haj Iyami ke ba mu musamman da safe, alhali matar nan ba yarinya ba ce daga ni har shi ta haifi waɗanda suka fi mu.

Ƙarar wayata ta katse ni daga duniyar tunanin da na lula, mahaifiyata ce Haj Hauwa, cikin jin daɗi na amsa wayar muka gaisa da muka yi sallama maimakon komawa na kwanta ciki na shiga na gyara gadona na ɗan goge wuri sai na fito na share falo ina son sanya turaren wuta amma ba rushi, wayata na janyo na kira mamana shaida mata na yi a sawo mini abin kunna turaren wuta, ta ce bunner fa da aka sanyo mini? Na ce ta ƙi yi, ta ce shi kenan idan an kawo mini abin kunna turaren in bayar da bunner ƙawata Nabila da muka sawo bunner tare sai ta mayar ta canzo mini wata.

Ina ajiye wayar kiran Abakar ya shigo shaida mini ya yi har ya shiga Abuja, wani babban mutum ya ɗauka murnar maƙudan kudin da ya ba shi ya sa ya ce da ƙyar zai iya jiran wasu fasinjan zai juyo ya kasance da amaryarsa.

Murmushi na yi kafin na soma  ba shi baki ya daure kogi bai ƙi yayyafi ba, kar ya ƙona mai a banza.

Muka yi sallama kwanciya na yi don ba ni da yunwa shi kuma sai ya taso ya yo nisa sai ya kira ni in ɗora mishi abin da zai ci.

Ƙarfe sha biyu ya kira ni ya ce ya yo nisa yana gadar Malam Mamman.

Da azama na fita na faɗa kitchen sai dai yanzu ma Haj Iyami tare ni ta yi da tambayar angon zai dawo ne? Na ce “E.  Ta ce “Bar girkin ga abinci na kusa saukewa sai na zuba mishi.”

Na dubi tukunyar, abincin na fitar da tururi mai sanya haɗiyar miyau, ga nama zunduma-zunduma ya ji kayan lambu.

Kamar na karɓa kar in faɗa mishi sai dai kuma na ce “Ki bar shi Haj na gode.”

Ban saurari maganar da take ba na fara ƙoƙarin ɗora nawa girkin, da busasshen kifi na yi amfani ina shiryawa kuma na kai ɗaki, Abakar ya shigo.

Wanka ya fara yi sai ya zauna cin abinci, kiran da Haj iyami ke yi mini ya sa na fita, riƙe take da jug mai garai-garai da ya ba ni damar ganin zoɓo da ke ciki ganin zoɓon kuma ya tuna mini da wanda ta kawo mini da kanta ranar buɗar kaina “Ga shi Ummu Radiyya, kina amarya duk ba ki da dabarar da za ki tarairayi angonki ya sha wannan yadda ya ɗebo rana da gajiya zai sanyaya ransa ya sa shi ya wattsake.”

Na karɓa da godiya zuciyata ɗaya, sai kuma ta miƙo mini wani turaren wuta “Ki sanya wannan a ɗakinki, irin naku ne amare.” Na amsa ina cewa “Bunner ta ta ƙi yi, kuma ba ni da abin da zan kunna turare.”

“Ina zuwa.” Ta ce mini tana juyawa.

Nan na tsaya saƙare har ta dawo ɗauke da wata kyakkyawar Bunner da ta fi tawa kyau da tsada “Ki yi amfani da ita.” Na ɗan yi turus ina yaba kirkin ta ya isa “Ki amsa mana.” Ta tunasar da ni, na miƙa hannu na karɓa ina mata godiya murya ƙasa-ƙasa kar Abakar ya ji, zan juya ta ce “Fita zan yi sai dare ƙila, ko zan dawo.”

Na yi mata fatan dawowa lafiya na shiga ɗaki.

Ban tunkari Abakar da zoɓon ba saboda kallon da na ga tana yi mini, Bunner kawai na fara ƙoƙarin jonawa na sanya turaren, take ɗakin ya ɗauki wani fitinannen ƙamshi mai sanyaya rai sai ƙara buɗe hancina nake, na wuce zan shiga ciki ya ce  “Ina za ki? “Alwala zan yi.” Na ba shi amsa fuskarsa ta washe bai yi magana ba ya ci gaba da cin abincinsa.

Na fita har na yo alwalar na dawo na kabbara sallah ƙamshi mai daɗi ke fita ta Bunner, saɓanin na fara  sallah salo ya sauya, wani irin ƙauri mai sanya sarawar kai ya koma, kafin in idar da sallar maganar Abakar biyu “Ki idar ki raba mu da abin nan.”

Ina sallame wa ko addu’a ban tsaya yi ba na zare Bunner na dube shi ya dafe kai gabaɗaya jikinsa ya saki na isa ina taɓa shi.

Ummu Radiyya 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×