Bashir Lema ya koma motarsa fuskarsa na fitar da wani lallausan murmushi da alama kaya ya tsinke mishi a gindin kaba ba zai sha wata wahala ba zai mallaki Ummu Radiyya da yake jin kamar bai taɓa son wata ɗiya mace ba sai yau da ya ganta. Tun da ya ga yaron da ya fito a gidan suka tura shi kiran ta ya tabbatar da jinin Isah ne don tsananin kamar da matashin ke yi da shi, shi ya sa bai yi mata maganar komai ba Isah zai ja mishi gaba
Nombar da ta ba shi ya danna sai da ta kusa tsinkewa aka ɗaga “Bashir Ahmad ke magana.”
Daga ɓangaren Baba Isah ya shiga tunani “To wane Bashir Ahmad kenan?
“Bashir Lema tsohon abokin karatunka.”
Nan hira ta ɓarke don sun haɗu sau daya bayan dawowar Leman daga Turai kafin ya koma, ƙarshe ya shaida mishi ya ga ɗiyarsa Ummu Radiyya ya kamu da son ta shi yake so ya yi kamun ƙafa da shi a ba shi ita kafin ya koma London.
Baba Isah ya gwada mishi kar ya damu kamar ma ya same ta.
Bashir Lema ya ce zai fito da safe zai zo gidansa, suna gama wayar ban da goma da ya ga ta kusa da lokacin suka tafi gidan Isan, ya dai daure suka kama hanyar gida.
Bai iya wucewa wurin sa ba ya shiga wurin mahaifiyarsa ba ta a falo tana bedroom ɗinta ta idar da shafa’i da wuturi duban shi ta yi tana shafa addu’arta ya shigo sosai ya zauna bakin gado ta tambayi daga ina ya fito ganin ba kayan ɗazu ba ne jikinsa, kansa ya fara shafawa bai da buƙatar ɓoye mata ya bayyana mata komai da ya faru wani annuri ya mamaye fuskarta ta ɗaga hannuwanta sama ta yi ma Allah kirari ta yi godiya kafin ta fuskance shi da tambayar iyayen yarinyar, don ba za ta yarda ya ƙara irin auren Farida ba ko da ta matsu ya yi aure don saisaitar al’amuransa.
Ya faɗa mata jikar Ɗan Borno ce da yake sun san juna da iyayen su Baba Isa
“Su ɗin mutanen arziƙi ne Alh Ɗan Borno da matarsa Haj Ladi sai dai ita wadda za ka auran dole a yi binciken halayenta.”
“Ki tambayi autarki ƙawarta ce.”
Ta rufe bakinta da hannunta na dama alamar mamaki “Ƙawar Sa’ada kuma? Kai da ka ce ba ka son ƙananan yara?
“To ya za a yi haka Allah ya nufa.”
“Shi kenan Allah ya sa alheri zan yi Istikhara in sha Allahu a daren nan ka je ka kwanta da safe zan kira Sa’adan.
Ya tafi ya bar mahaifiyar ta sa wadda ba ta gushe ba sai da ta yi Istikhara tana neman zaɓin Allah kan auren ɗan nata ta kwanta zuciyarta na cike da farin ciki haka ma ta tashi da son al’amarin ta kuma kira Su’ada ta tambaye ta game da Ummu Radiyya kamar yadda ya faɗa mata sunanta, ita ma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta koma ga ƙawarta da ta ba ta bayanai kanta ta faɗa mata ko wace ce Ummu Radiyya har auren da aka yi mata watanni uku kacal iftila’i ya faɗa ma mijin da ya yi sanadiyar mutuwar auren.
Wayarta Hajiyar ta ɗaga ta kira shi ya ce mata ya fita.
Shi kuma ƙarfe tara na safiya yana falon Baba Isa, bai damu da kayan saukar baƙo da aka cika gabansa da su ba zancen Ummu Radiyya yake masa ya ce kamar yadda ya ji Ummu Radiyya ɗiyarsa ce da ɗan’uwansa ya haifa ya kuma rasu ya bar su, an yi mata aure watanni uku kacal da yi wani iftila’i ya faɗa ma angon ya sake ta.
Mamaki ya cika Bashir lema yarinyar nan har an yi mata aure ko ma dai mene ne bai nemi jin dalilin mutuwar auren ba sai ma daɗi da ya ji da ya zam ba aure a kanta.
Baba Isah ya ce “Bari na yi wanka sai mu tafi can gidan namu.
Ya miƙe ya shiga ciki Aunty Larai da ya samu tana gyaran gado ya ce ma “Ciro mini kaya bari na yi wanka.”
Da mamaki ta dube shi “Fita kuma tun da safen nan yau Sunday?
Kai ya kaɗa mata “Wannan tsohon Abokin nawa na sha ba ki labarinsa tun rabuwar mu a Secondary ban ƙara ganin shi ba sai a shekarun baya ya ce mini yana zaune a London, to yau kuma ya zo gare ni ya ga Ummu yana so.”
Aunty Larai ta riƙe numfashinta tana fiddo ido waje “Mazaunin London ɗin ke son Ummu? Da fa ganin shi Naira ta zauna kai ma sha Allah Allah ya yi ma ‘yata canji.”
Ta kama hanci ya zabga mata harara “Me za ki yi ? To yana dai falo idan kika yi yana jin ki.”
Toilet ya wuce ya bar ta tana murna sai da ya shirya ya fita ya same shi suka shiga motar Bashir Lema suka nufi unguwar Sunusi.
Da safe da na tashi na manta da mutumin da ya zo neman Baba Isha, yau ma a aljihuna na yi mana abin karyawa kunun gyaɗar na kuma damawa har da ƙosai, Baba ma nan ya shigo ya karya duk da sai yamma Mama za ta karɓi girki.
Ni na gyara ɗakin na sanya ƙamshi, kamar in kwanta sai na tashi sai in yi wanka in ci gaba da aikina na zanen gado, sai dai jin da nake yi duk na yi wata iri rabona da wanka tun jiya da safe a gidan Baba Isah.
Ruwa na surka saboda sanyi da ya fara sallama na yi wankan na murza mai na goga turare na sanya riga da zane na atamfa, kamar in janyo aikina in ci gaba sai na ji kwanciyar kawai nake so na kwanta na shiga barci.
Da tsayuwar motar Baba Isah ya ce mishi zai shiga ya yi musu magana.
Ya sauka ya shiga gidan fannin Baba ya fara shiga suka gaisa da su Aya ya tambayi Baban suka ce yana ciki.
A falonsa ya same shi sai da suka gaisa da ƙanen nasa ya ce “Yanzu kuwa zan fita rabon za mu haɗu.”
Baba Isah ya labarta mishi ɗan gidan Alh Ahmad Lema ne ya zo da zancen son auren Ummu Radiyya.
Baban ya ce su je wurin Hauwa’u a yi maganar gaban ta.
A falonta suka same ta Baban ne ya yi mata bayani kamar yadda Baba Isah ya labarta masa, ta tambayi halayyarsa Baba Isah ya tabbatar mata mutumin kirki ne matarsa daya da yara uku.
Mama ta cika da murnar wanda Allah ya kawo ma Ummunta.
Ta ce “Ummun ta fita su yi magana sai dai ba yanzu za a yi maganar aure ba, saboda hidimar auren Hassana maganar Ummu sai nan gaba.”
Baba Isah ya ce “Shi kuma nan kusa yake so.”
Baba Ali da ya san kayan Ummu na wuyansa ya ce “Auren Ummu ba zai yiwu yanzu ba, don ba mu shirya ba.”
Baba Isah ya ce ” A tayar da ita ta je ta same shi.”
Mama ta shigo ta tashe ni sai da na wattsake ta shaida mini mutumin jiya ne ya dawo kuma wurina ya zo abokin Baba Isah ne, in tashi in same shi a waj.
Amsa mata na yi bayan fitar ta hawaye suka yi ta gudu kan fuskata ina ambaton kalmar ƙaddara ita ce ta yi aikinta a kaina na auri saurayi yaro ɗanye sharaf da nake mafarkin mu gina rayuwarmu tare, to ƙaddara ta riga fata ta raba ni da Abakar har tsararrakin Baba Isah sun fara zuwa nema na.
Na share hawayena jin Mama na kiran sunana hijab din jiya na zumbula na fita, na gaishe da Baba Isah na wuce su.
Inda suka ajiye motarsu jiya yau ma nan na hango ta karkashin wata bishiyar maina na ƙarasa ina jin wani yanayi na lulluɓe duniyata.
Yana cikin motar ya buɗe ƙofa gami da zuro ƙafa ɗaya waje murfin gefen sa ya buɗe mini yana faɗin na shigo na ce nan ma ya isa fitowa ya yi ya zagayo inda nake kaina ƙasa na gaishe shi don kwarjinin da ya yi mini mutumin ya haɗu ƙarshe ya gabatar mini da kansa take na gane yayan Su’ada ne da buƙatarsa ta son aurena nan kusa.
Ban ƙwauron baki ba na ce mishi ba zan yi aure yanzu ba karatu zan yi.
Na yi masa sallama na yi tafiyata.
A falon na wuce su Baba na shiga ɗaki.
Baba Isah ya miƙe ya ce musu bari ya je ya same shi cikin motar ya same shi ya yi mishi bayanin yadda suka yi haƙuri baban ya ba shi ya ce abin da ya sa ta ce ba za ta yi aure yanzu ba karatu za ta koma, nan da sati uku za a yi bikin ƙanwarta gaskiya ba su da halin yi mata kayan ɗaki nan kusa, sai dai a yi haƙuri har nan gaba.
Ya ce shi in dai don kayan ɗaki ne ya shirya nan da sati ukun a haɗa da shi yana da kayan ɗaki idan ma ba su yi mata ba ta zaɓi waɗanda take so har kayan kitchen.
Daɗi ya lulluɓe Baba Isah Ummu ta samu inda za ta huta ya ce “Ba damuwa zan shiga mu yi magana da mahaifiyarta da yayana da a halin yanzu shi ke auren mahaifiyarta, zan turo maka yayan nawa.
Baba Isah ya shiga ya kwashe duk yadda suka yi ya zayyana musu Baba Ali jin kayan ɗaki sun sauka a kansa wani son auren ya baibaye shi dole ma Ummu ta yarda ya ce ma Baba Isah ya shigo da shi falonsa.
Hakan aka yi can suka shiga aka ƙara magana ya nemi a faɗi mishi abin da zai biya sai ya tura musu suka ce ya dakata tukuna.
Baba Isah ya kai shi falon Mama ya gaishe ta kwarai ta yaba da mutumin, nan ya bar Baba Isah ya tafi suka ƙara zama kan maganar, Baba Isah ya kira ni yana kwaɗaita mini auren Bashir Lema ganin ina zumɓura baki ya fara zagina abin da bai taɓa yi mini ba na ce “To Baba karatuna fa ga shi har na yi Screening.”
Ya ce “Ƙyale karatun nan tukuna auren mutumin nan ya fi miki komai a yanzu.”
Na ƙara ɓata rai tuna kuɗaɗena da na wahala wurin tarawa suka tafi kan faɗi tashin karatun na ce “Baba kuɗaɗena fa da na kashe a karatun?
Ya ja wani mummunan tsaki “Ke yar dubu arba’in ɗin ce za ki wani tsaya tunani?
Ya tafi ya bar ni da Mama yana ce mata ta faɗa mini gaskiya.
Baba Ali ma ya ce mini ya yi na’am da mutumin na yi miji na nuna ma sa’a Allah ya yi mini sakayya na abin da ya same ni a baya.
Mama kuma Lubna ta kira da Aunty Ya gana suka tasa ni suna cusa mini son auren Baba Ali ya zo ya same su ya ce su shawarta nawa za a ce ya kawo don ya ce a faɗa mishi gabaɗaya sadaki da kayan akwati.
Da ya fita suka yi ta shawara Aunty Ya gana ta ce Dari biyar Lubna ta ce sun yi yawa zai fa yi kayan daki da na ga ba ma ta tawa suke ba na fito na ce “Ni fa ba zan aure shi ba daga zuwan Mutum jiya-jiya sai a kama batun aure kamar wata kaza?
Mama ta fara yi mini faɗa sosai ƙarshe ta rufe da cewa tun da ni sakarya ce kan Abakar zan yi ma kaina sagegeduwa to ko Abakar ya dawo in dai ita ta haife ni ba ni ba aurensa ta fice ta bar ni da su Lubna suna nuna mini alfanun auren mutumin nan, tun daga nan Mama ta daina yi mini magana.
Washegari Nabila ta shigo wuri na ganin duk yadda na yi wata iri kallon ta kawai na yi na koma na kwanta ta dafe ƙirji “Kar ki tsorata ni Ummu me ya same ki?
Na zubo da hawaye sai na soma ba ta labarin abokin Baba Isah da ya zo neman aurena kuma ta ƙarfi suke so dole sai na aure shi don Baba Isah sai da ya dawo da daddare ya tabbatar mini idan na watsa mishi ƙasa a ido to ba ni ba shi.
Ga Mama da ke matsanancin fushi da ni Nabila ta kama hannuna ta damƙa mini wayar gallery ta shiga hoton da na gani sai na dube ta ta ce “Ki ci gaba da dubawa na yi yadda ta ce hotuna ne na Bashir Lema da wasu Ajebo ɗin yammata a wurare daban-daban na shakatawa masu daraja waɗanda da ka gani ka san a ƙasashen masu jajayen kunnuwa ne.”