Miƙewa kawai ya yi ya shige ɗaki, na bi shi na kwanta kusa da shi ina tambayar shi lafiya? Bai amsa mini ba idanuwansa na rufe, ina kwance jikinsa muka yi barci sai la’asar muka tashi.
Abakar garas kamar ba shi ba ne ɗazu ya ba ni tsoro da yanayinsa.
Sallah ya fita ya shaida mini idan an idar zai wanke motarsa a waje ni kuma na yi amfani da hakan na sake wanka da wuri koma bayan na magrib in je ina ganin magen nan.
Na gama kwalliyata ya shigo muka zauna a tsakar gida saboda sakewar mu kaɗai ne, Abakar har yana zare t shirt ɗinsa ya zauna daga shi sai dogon baƙin wando hirarmu ta sabbin ma’aurata da suke gaɓar amarci muke yi kwatsam! Ba sanannen ciki muka ji motsi daga ƙofar shigowa a tare muka kai duban mu wurin
Haj Iyami ce da ta ce sai dare za ta dawo na bi ta da kallo ganin gabaɗaya hankalinta ya ɗauku ga kallon surar ƙirjin Abakar da ke tuɓe shi kuma ya yi hanzarin miƙewa ni kuma na ce “Sannu da dawowa Haj.” Wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke tana mai saurin duba na “Yawwa amarya, ashe Maigidan ya dawo. Sannu da hanya Allah ya ƙara tsare mana ku ya kawo kyakkyawan buɗi.”
Abakar dai bai tsaya ba ballantana ya amsa doguwar addu’ar da ta jera mishi.
Na ji mamakin kallon ƙurillar da ta yi masa amma na fi jin nasa, ina ruwan biri da gada ɗanta na uku kuma na ƙarshe shi ne ya yi aure shekara guda da ta wuce ko shi na san zai yi shekarun Abakar. Na tashi na bi shi.
A wannan rana ban ga mage ba ina ta murna har muka kwanta sai dai muna soma wasannin mu yana dab da cim ma burin sa komai ya lalace jikinsa ya saki ya kasa aikata komai lamo ya yi kafin ya sauka gadon ya fita ya dawo ɗaure da alwala ya fara jera sallah tun ina kallon shi har barci ya yi awon gaba da ni.
Tun daga ranar muka koma fuskantar kasa kusantata daga Abakar, ga mage da ke shigowa duk dare a lokacin da yake ƙoƙarin kusantata.
Tun Abakar na addu’a shi kaɗai har ya sanya ni ciki muna yi tare, ina jin barci cikin dare haka zai tashe ni mu yi sallah muna addu’o’i Allah ya kawo mana sauƙin wannan lamari.
Haj Iyami kuma na yi biyayya ga umarnin mijina na daina amsar abin hannunta duk yadda ta so kuwa, sai dai ba ta fasa ja na a jiki ba da alherorinta.
Ranar da na cika kwana ashirin da huɗu muka yi waya da babbar ƙawata Nabila ta shaida mini suna nan zuwa ita da ƙawayenmu su huɗu da muka yi karatu tare a kad poly.
Sanar da Abakar baƙin da zan yi yana fita don yin lodi zuwa Kano ƙarfe goma na safe na tashi barcina ina gyara ɗakina sai ga ɗan aike daga gare shi nama ne na saniya mai ɗan dama don zai yi kilo guda sai kayan miya da kayan haɗin Ginger.
Ban ƙasa a gwiwa ba na yi kitchen wake na wanke da niyyar yi musu alale da na san su ɗin mayun ta ne.
A blender ta na niƙa shi na yi mata hadi sosai na daffafen ƙwai da busasshen kifi ga wadatattun kayan miya da albasa da kayan ɗandano, gefe kuma naman nan na zage na yi miyar niƙaƙƙen nama.
A ƙarshe na haɗa Ginger na miƙa ma Haj Iyami ta sanya mini a fridge.
Alalen na kan wuta na tafi daki na yi shirin wanka, ina cikin wankan na ji muryoyinsu na gaggauta na fito shewa suka ɓarke da ita gani na, ni kuma na wuce na karɓo Ginger na iske su daki da ita na ba su na shige don in shirya ina jin su suna ta hirar tarayya ta da Abakar a poly ashe ashe mijina ne.
Na gama na zo na same su suna ta cashe mini ina ramawa Nabila ce kawai ba ta taya su ba ba ta kuma shigar mini ba.
Abakar bai shigo ba ya yi mini text saboda su ba zai dawo ba, na shiga damuwar ina za shi ya samu ya huta ya ce kar in damu gidansu za shi.
Mun yi ta hira sai da muke idar da sallar la’asar ni da Nabila muka yi ƙarshe a ɗaki ta buɗe jakarta ta ciro saƙonnin Mamana ta ba ni daga bisani muka fita tare suka yi mini sallama turare hoda na yi musu kyautar su .
Ina dawowa daga rakiyar su na kira Abakar na ce sun tafi, ba jimawa ya shigo yadda ya kafa tumbler da na cika da Ginger sai da ya shanye ta kaf ya ajiye ga kuma yanayinsa sai na san bai samu ya ci komai a gidan nasu ba, tausayin maraicinsa na rashin uwa ya kama ni.
Ya shaida mini zuwa dare za mu je gidansu mu gaishe su na ce Allah ya kai mu.
Da wuri na kintsa yana fitowa sallar isha’i ya ce mu tafi, ina ganin ya fara rufe ƙofa na yi wuf na faɗa dakin Haj Iyami yi mata sallama don kar ma ya san me zan yi ya hana ni sai dai faɗa mata da na yi bagatatan ya zo da kallo, durƙushe take kan wani abu da ba zan ce ga shi ba tana ta yanka zufa, gani na kuma ta yi saurin ƙara danne abin da take a kan ni dai na yi mata sallama na yo baya zuciyata cike da saƙe-saƙen ko me take yi haka?
Harara Abakar ya balla mini ni kuma na jefe shi da kallo mai cike da karairaya bai ce komai ba ya wuce na iske shi muka jera.
Layi biyu ne tsakanin mu da gidan nasu don haka a kafa muka taka gida ne ginin bulo ƙofa ce tare da shago a waje mahaifinsa ya rayu can farkon rayuwarsa da abin duniya hakan ya sa ko yanzu da abin ya janye ga kuma girma da ya cim masa yana da yan kama sayar wanda ba a rasa ba shagon ƙofar gidan shi ke zama yana sayar da tarkacen kayan amfanin yau da kullum da ba su taka kara sun karya ba, mahaifiyarsa ta rasu shi kaɗai ta bari duk da kafin shi ta yi haihuwa da yawa suna rasuwa shi kaɗai ya tsaya.
Matar mahaifinsa da ta zo bayan mahaifiyarsa Hajiya Nasara yaranta mata ne har biyar ta ukun kuma ita ce sa’ar Abakar, an ce mahaifiyarsa mace ce mai zafi da faɗa kamar dage sai abin da ta ce ake yi a gidan sai da aurenta ya ƙare ta tafi ta bar Abakar Haj Nasara ta samu ta cewa a gidan mutane na ganin hakan ya sa ta yi ma Abakar ruƙo mai cike da ƙeta.
Mahaifiyarsa da ta bar gidan Kaduna ta bari ta koma can ƙasarta ta haihuwa wato Borno ta yi aure wurin haihuwa ta rasu Abakar ya tashi cikin maraici na rashin uwa da danginta, don wani abin mamaki ango ya kwana da ƙunzugu dangin mahaifiyarsa ba su ɗauki rabuwar da Alh Usman kuka sheƙa ya yi da ita da sauƙi ba hakan ya sa har Abakar ɗin sun ɗauki tsangwama sun ɗora mishi duk yadda ya so mu’amala da su dole ya janye ya rungumi mahaifinsa shi kaɗai da ya san shi kaɗai ya rage mishi.
Babbar ɗiyar Haj Nasara babbar ma’aikaciyar jinya ce hakan ya sa haj Nasara ke watayawarta ita kaɗai ko uban ba ta dangwala ma wa.
Ɗakinta da haske ke fitowa muka fara isa tana zaune a falonta muka shiga da sallama ta karɓe mu faran-faran ta kuma jagorance mu har ɗakin mahaifinsa tsohon na zaune an kunna masa rechargeable light saɓanin ɗakinta da solar ce wai bolb ɗin ne ba su isa ba shi ya sa ba a sa a nashi dakin ba.
Mun daɗe gaban tsohon yana ta sanya mana albarka kafin na ajiye mishi dan madaidaicin kwanon da na dafa farar shinkafa na rufe ta miyar niƙaƙƙen naman, ya sake yi mana addu’a, Haj Nasara kuma ba ta yi shiru ba sai da ta ɓara “Shi kaɗai kika sani kika kawo ma abu to Abakar dai ba shi da uwar da ta fi ni.”
Dukkan mu ba wanda ya tanka sai miƙewa da Abakar ya yi ya ce mu je.
Muka yi musu sallama a raina ina ƙudurta duk na yi girki sai na lulluɓo kaina na kawo ma dattijon ban kuma yi ƙasa a gwiwa ba washegari ina kammala girkin rana wanda taliya ce da ta ji kifi da kayan lambu na zuba a madaidaicin kwano na sanya lulluɓina na yi saurin barin gidan ba tare da shaida ma Abakar ba a nufi na zan yi sauri na dawo kafin ya shigo.
Cikin shagonsa gaban kayan da yake saidawa na hango dattijon na shiga da sallama ya amsa da yalwatacciyar fara’a, na ajiye kwanon a kusa da shi ina gaishe shi albarka yake ta sanya mini da godiya mai yawa kan wannan alheri nawa ya sanyaya jikina da wani irin tausayi mai tsanani ban jinkirta ba na ce mishi zan koma.
Na kama hanya ina.duba agogon wayata , motar Abakar da na gani ta a ƙofar gida ta sa ni fara raba ido na yi ta maza na tura ƙofar zauren me zan gani ni Ummu Radiyya Abakar ne tsaye naɗe da hannaye ga Haj Iyami ta sha kwalliya kodayake ita ɗin ma’abociyar kwalliya ce da ba ka taɓa raba ta da ita.
Abakar ya ba ƙofar baya ita kuma tana kallon mai shigowa duk da fuskarta cikin fara’a mai yawa take wata fara’ar ta ƙara tana faɗin “Kin dawo amarya?
Maganar da ta sa Abakar saurin waiwayowa , ban tsaya ba wuce su na yi na isa ɗakina kaina a ƙulle ina shiga Abakar na take mini baya kan kujera na faɗi kwajab kamar tsohuwar jaka ya tsaya kaina “Ina kika je?
Wani duba na yi masa sai na ɗaure fuskata “Baba na kai ma abinci.”
Ya saki fuska “Amma me ya sa ba ki faɗa mini ba?
Na ƙara yi mishi kallon sai na furta “Ka yi haƙuri.” Na miƙe na shige daki na haye gadona ya biyo ni “Wai me kike yi haka Ummu?
Na tashi zaune duban ido cikin ido na yi masa na ce “Mene ne haɗin ka da Haj iyami?
Ɗan murmushi ya yi “Me kike son ki ce mini kina tunani tsakanin mu?
Wani sabon takaicin ya lilluɓe ni sai na fashe da kuka ya hau gadon ya kama ni ina turjewa “Me kike yi haka Ummuna?
Me za ki yi tunani zai haɗa ni da wannan mata da ta haifi wanda ya fi ni?
Me zai sa ka kasa gaishe ta a shekarunta? Kuma ka hana ni mu’amala da ita? Yanzu kuma na dawo na same ku tare?
Ya shafa kitson kaina har zuwa bayana “To shi kenan ki yi haƙuri,ni ba komai tsakani na da ita dawowa ta kenan na gan ta.
Shiru na yi ina sauraren abin da yake mini ba don na gamsu da abin da ya ce ba har ya samu nasarar raba ni da rigar jikina kalaman rarrashi ya yi ta faɗa mini har ya samu na biye mishi sai dai kamar koyaushe mu’amala ta auratayya ta gagara tsakanin mu, cikin damuwa mai yawa ya tsallake ni.
Sai da na gama kwanciyata saboda laushi da jikina ya yi na sauka gadon na mayar da rigata na fita falon zaune yake yana cin abinci hannu ya miƙo mini na matsa kusa da shi na zauna muka cinye abincin da ya rage ya kara mini wani shi kuma ya koma saman cushion ya kwanta muna yar hira har na kammala ɗaki muka koma muka yi barci.
Da muka tashi Abakar ya yi alwalal la’asar tare da shaida mini daga masallaci zai kai gyaran motarsa a hanya sai da ta lalace mishi lallaɓawa ya yi ya dawo gida.
Sai da aka yi isha’i ya dawo, washegari ma da ya fita bai samu zuwa Abuja ba da ya yi niyya saboda gyaran motar bai yi ba yana fita Kaduna ta maƙale sai da ya samo bakanike ya taɓa ta.
Tun daga nan motar ta ƙi mishi hannu mai mishi gyara kuma ya ba shi shawarar da zai sauya ta don ya gano ita wannan motar an samu hatsari da ita babbar matsalar an riga an buɗe injin ɗinta sai aka yi mata kyakkyawan gyara da kai da ba ka san sirrin mota ba za ka ce ita ɗin sabuwa ce dal, rashin lafiyar motar ya shafi cimar mu ba ta abinci ba don ina da gara ta ababen sarrafawa masu daɗi da gina jiki sai dai maneji amma ban fasa kai ma tsohonsa duk abin da na sarrafa har kuma lokacin bai bar ni zuwa gidanmu ba ya ce sai ya samu kuɗi da zai yi mini sayayya na kai ma mahaifiyata tilas na haƙura duk da kewar ta mai yawa da nake cikinta ƙannena dai sun zo da yayata ta gidan aure mai suna lubna masu bi mini Hassana ne da Husaini sai autarmu Hanan.
Ina sakandare Allah ya dauki ran mahaifina sanadiyyar ciwon ciki kafin rasuwar sa ma’aikaci ne a hukumar ruwa ta jihar Kaduna muna zaune a tudun Wada wani gida na kakanmu mahaifin babanmu babanmu su biyu ne a ɗakinsu shi da ƙanensa, a wurin mahaifinsu kuma su huɗu waɗanda suke Uba daya Gwoggo Maimu da ita ce babba sai ƙanenta sa’an babanmu Baba Ali tare suka taso da babanmu komai nasu daya in ka ɗauke hali da kowa da nashi Baba Ali mai son fantamawa kuma ya yi sa’a ya shiga cikin dukiyar mahaifinsu don bai yi dogon karatun boko ba da mahaifin nasu ma ya rasu shi ya shige gidan iyayen nasu ya tare da iyalansa inda mahaifansu suka rayu babanmu ya samu wani gefe a cikin gidan da kuma gidan da muke ciki bayan rasuwar babanmu Baba Ali ya zo da zancen son auren Mamanmu da ta ƙi sam ya sha wahala ƙwarai kafin mahaifinta ya taso tun daga Maiduguri ya ba ta ba ki ta amince da ɗan’uwan mijinta ta ci gaba da ruƙon ya’yanta tamkar a gidan ubansu ta yi ma mahaifinta biyayya amma ko da aka yi auren idan ya zo gidanmu bai samun taryar kirki a wajen ta yau da gobe ta sauko har ga Hanan nan ta haifa ya kuma kalallame ta aka sanya yan haya a wancan gidan.
Matansa biyu ne da ya’ya kuɗaɗen gadon da kowa ya shaida shi ya yi rub da ciki a kanta ba ta je ko’ina ba ta kare ya dawo babu da yawa ɗawainiyar gidan sai dai kowacce ta ji da kanta yin auren mahaifiyarmu da shi ya kawo rashin jituwa mai yawa tsakanin mu da iyalansa a unguwar Sunusi gidan yake ƙaton gaske ne irin na attajiran da bayan matuƙar yalwa da yake da shi ga kuma shuke-shuke masu ban sha’awa musamman wurin mu flat house ne da zamanin masu gidan baƙi ake saukewa akwai tazara mai nisa tsakanin mu da sasan iyalan Baba Ali mahaifiyarmu ta yi tsaye kan cigaban karatunmu da abin da za mu ci ta sana’ar da take fafutuka ta sayar da turarukan wuta da na jiki kasantuwar ta mutuniyar Maiduguri daga ita har mahaifinmu daga can ƙanwar mahaifiyarta ke aiko mata da kuɗi ko babu.
Baba Isa shi ne suke daki daya da babanmu lacture ne a kaduna polytechnic mata daya gare shi ba su haihu ba
Gwoggo Maimu a Zaria take aure tana can da iyalanta.