Skip to content
Part 21 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Na roƙi Mama ta ba ni Hanan jin motsin ta zai rage mini kaɗaici ta ce idan ta ba ni ita da wa za ta zauna?

Na ce ga Husaini, ta ce makaranta za ta sanya ta, na ce zan sanya ta a can, sai da Baba Ali ya sanya baki wanda yake matuƙar ji da ni yanzu ta yarda. Samun Hanan ya rage mini kewa hidimarta da nake tana ɗauke mini hankali ga surutunta na kuruciya da take cika ni da su, wata private school na sanya ta, Basira ke kai ta ta ɗauko mini ita.

Nabila ta yi mini tayin komawa karatu na ce a’a haka ma Baba Isah watarana na je gida don Hassana ta haihu ta samu ɗiya mace daga gidan na biya poly in ga Nabila da ban samu a gida ba, Office din Baba Isah na fara zuwa na kuma ci sa’ar ganin shi yana yawan zuwa duba ni Aunty Larai ta ce cikin damuwa yake ƙwarai yana ganin kamar shi ya ja mini wannan auren

daga wata uku ya tafi ya bar ni da igiyar aure a ka.

Kallo na yake da damuwa a fuskarsa duk da fara’ar da nake, na gaishe shi ya ce “Sannu Ummu kin ji. Ki ƙara haƙuri.” Na ce “To Baba.” Ya ce “Ko karatunki za ki ci gaba da zaman jira?

Na yi ɗan murmushi na ce “A’a Baba,  karatun ma ya fita kaina ai ya kusa dawowa.”

Ya ce  “Watansa nawa yanzu? Na ce “Bakwai.” Ya ce “Kayya, ki dai ƙara haƙuri.” Na ce “To Baba.”

Ya tambaye ni ba ni da matsala na ce babu.

Na fita na tafi wurin Nabila da dama sun riga sun tashi na ce ne ta jira ni, muka gaisa na shiga motar da aka kawo ni ciki Nabila ta tafi da ƙawayenta.

Akai-akai yake turo mini kuɗi duk kuma ƙarshen wata nake yin list na abin da ba ni da shi na amfanin gida ya sa a kawo mini. Kuɗaɗen da ake kawo mini Mama nake yi ma hidima Baba Ali ma ina ajiye mishi abinci sai yan’uwa da abokan arziki ina yi musu gwargwadon iko.

Zuwa yanzu har kwana nake gidan Haj, saboda na shaƙu da su.

Ana ta mirginawa a haka tun ina damuwa da rashin shi har ya zame mini jiki na saba, illa ƙibar da na yi tuni ta gudu na koma yadda nake  sai dai jikina da ya bayyana hutun da nake ciki.

Muna waya da chart koyaushe yana faɗa mini damuwar da yake ciki ta rashi na kusa da shi .

Wata ranar Lahadi ina shiri zan tafi gidan Haj sai ga Nabila mun ɗan taɓa hira ta ba ni saƙon Mama da ta ba ta ta kawo mini na ce mata mu je gidan Haj.

Muka fita muka tafi Nabila na ba ni labarin aurenta da ya taso saurayinta da suka yi wata huɗu tare ya matsa da son a yi auren ma’aikaci ne a Abuja amma iyayensa na zaune nan Kaduna. Na taya ta murna da fatan alheri.

Watanni biyu suka rage Bashir Lema ya dawo  muka sha bikinta da angonta Zahraddin ya ajiye ta a unguwar Shanu kusa da gidan iyayensa yana tafiya wurin aikinsa Abuja Nabilar na samun hutun ƙarshen mako.

Wannan kenan da watan dawowar sa ya kama ruɓanya kuɗaɗen da yake turo mini ya yi  ya ce in yi shirin taryarsa, inda Aunty Larai ta kai ni lokacin aurena na je aka yi mini gyaran jiki da gashi da ƙunshi Aunty Ya gana da Lubna suka zo suka taya ni gyara gida .

Aunty Larai da ta zo faɗa ta yi ta mini a kuɗaɗen da yake turo mini ban canza suturuna daga matsakaita zuwa masu tsada ba na ce zan gyara daga wannan.

Ina ta murnar dawowar sa sai dai da na  tuna har da yaransa zai dawo sai murnar tawa ta koma ciki sai kuma idan na tuna idan tare za su dawo da mahaifiyarsu gidansu daban nawa daban sai in ji sassauci Mama ta karɓe Hanan tun ana saur kwana biyu ya dawo da na je unguwar kitso.

Ina ta zumuɗi da rawar ƙafa, ranar dawowar sa Abuja ya sauka Iliya Abujar ya kwana suka juyo tare sai dai me zan gani da na fito da murnata Amal ce ta fara fitowa sannan Suhaima sai Dina shi ne karshe ganin su ya hana ni rugawa na rungume shi fara’a dai ta samu matsuguni a fuskata ina ta masu sannu da zuwa na taki sa’a dai sun amsa sau ɗaya shi kam isowa ya yi inda nake tsaye ya kama hannuna muka wuce ciki

suka yi wurin su inda na sanya Basira ta gyara da kyau  na ce musu ga abinci nan idan sun huta.

Zare hannuna na yi a nasa na ɗauko masa ruwa da lemon da na haɗa masa muka hau sama na so ya haƙura ya ci abinci bai yarda da hakan ba babin ma’aurata muka faɗa bayan na sanya ma ɗakin key sanin rashin tunani na Amal,  duk yadda yake faɗa mini ya yi kewata ta chart din da muke haɗuwar mu ta nuna mini fin haka.

Sai da aka kira magrib ya bar ni muka yi wanka da alwala na san anan zai ce zai yi Sallah na ce da ya fita jam’i bai yi musu ba ya fita.

Na yi tawa sallar na sake sabuwar kwalliya na sauka ƙasa daidai yana shigowa na yi masa tayin abinci ya ce ko zan kira su Dina  na ce shi kenan.

Ba a son raina ba na tafi na murɗa ƙofar ɗan corridor ne za ka fara wucewa zai sa da ka da madaidaicin falo wanda ya raba ɗakunansu suna zaune ɗaiɗai kayan abincin da na hana kaina sakat Basira ke zuzzuba musu na yi duru-duru idan ba idona ke gizo ba ba abin da aka rage mini,  gabaɗaya sun zubo mini ido in ban da Basira da ke ta ɓare-ɓaren zuba musu.

Juyawa na yi ƙafata na rawa wani ɓacin rai na taso mini.

Da fita ta kan dinning na hango shi wayam, na ƙarasa kamar wadda aka zare ma laka “Ka yi haƙuri ka ba ni 30 minutes na dafa maka wani abin, abincin d na dafa gabaɗaya Basira ta kai ma su Suhaima.”

Na faɗa cikin rauni mai yawa a fuskata “Kar ki damu mu fita kawai mu ci daga can mu gaishe da Haj.”

Daga haka miƙewa ya yi ya kama hannuna muka koma sama kaya ya canza zuwa ƙananan kaya ya ɗaura agogo da takalmi kallonsa na yi ta yi don ya yi kyau ba kaɗan ba,  ni ma na sauya atamfar jikina zuwa abaya sai ranar na ji haushin kaina da duk kuɗin da yake turo mini Abaya uku kaɗai na saya duk yadda take burge ni duk da ba laifina ba ne  tun tafiyarsa na ɗauke duk wata ɗawainiya ta Mama ci da sha da abin amfani na yau da kullum sch da na sanya Hanan Husaini ya shiga K.A.S.U ni na yi duk ɗawainiyar makarantar tashi haihuwar Hassana na yi iyakar kokarina wurin yin komai da ake yi.

Ga bikin dangi za a ce wance ta haihu biki gidan wane .

Muka fita na karɓi key hannun Iliya ya ja motar wani wurin cin abinci muka fara zuwa sannan muka yi gidan Haj.

Anan muka yi hira har cikin hirar su da Haj na ji suna zancen uwargidansa ta ce ba za ta dawo Nigeria ba ta zauna da wata, shi kuma ya kwaso yaransa ya bar ta ita da ƙanenta.

Haj dai tana ta jaddada mishi ya samu ya faɗa ma ya’yansa su fito da maza a yi musu aure.

Mun koma ba motsin kowa shedar gajiya ba ta bar su ba, ni na rufe ko’ina muka hau sama, ina cire kayana ya kamo ni muka zauna bakin gado tambaya ta yake me ya ramar da ni? Na ce ba komai, ya ce idan shi ne matsalar to ga shi nan ya dawo shi kenan? Na rufe fuskata da tafukan hannayena.

Da safe ba mu fito da wuri ba kuma na rufe ƙofar kamar yadda na yi zato an zo ana  buga ƙofa  na ƙara narke mishi, tilas ya fasa tashi mai bugun ya gaji ya juya.

Ba mu fito ba sai sha ɗaya ai kam na sha harara wurin Amal da Suhaima, yau ma tebur wayam an kwashe an kai musu na yi ma Basira magana ta ce su suka ce ta kai musu.

Na ce ya ɗan jira ni, na faɗa kitchen ɗin na samar mana abin kari mara wahala.

Da gamawar mu rakiya ya nemi in masa  wani Company muka je sai yamma muka dawo don mun biya gidan Haj.

Ai kam ya’yan Baba ban da harara yau har da sakin magana, ni dai na ɗane sama na ƙyale su.

Washegari abin da ya girgiza su gidan Haj ya ce su koma zan mishi rakiya Abuja

Kwanaki uku muka yi a hotel muka yi masauki iyaka ya kan fita abin da ya kai shi idan ya dawo ya fita da ni mu zaga gari.

Mun dawo Suhaima da Amal suka tayar mishi da rikici su gidan nan ya ishe su ba za su zauna Kaduna ba nan a takure suke.

Baya iya ƙetare buƙatar su don haka ya samu Haj da zancen komawar, ba ta so ba don ita buƙatar ta ya aurar da ya’yansa wani dare ya shigo ya yi mini bayani in fara shiri sati mai zuwa za mu koma Abuja wani banbaraƙwai na ji zancen take na shiga zullumi da tausayin kai, idan na koma garin da ba ni da kowa.

Ganin na yi zugum ya ce “Ki shirya zuwa dare za mu tafi gidanku mu yi masu sallama.”  Na amsa a sanyaye ya miƙo mini kuɗi “Ki ba House girl ɗin nan ranar da za mu tafi sai ta wuce.” Na ɗaga mishi kai ina juya kuɗaɗen a hannuna fita ɗakin ya yi ni kuma na yi ta kwanciya a wurin ina tunani.

Duk da fargabar komawa Abuja garin da ban san kowa ba zan zauna ne daga ni sai waɗannan bayin Allah ya’yan miji kulawar da na samu daga Bashir Lema ta kwantar da hankalina.

Tare da shi kamar yadda ya ce muka je gidan namu muka yi musu sallama Mama ta ce me nake so a yi mini in tafi da shi na ce markaɗaɗɗar gyaɗa don ina son kunun gyaɗa.

Da muka bar gidan na ce mu biya gidan Baba Isah a’a ya ce wai ko ɗazu sun haɗu.

Na ce ni ai zan yi musu sallama kallona ya yi na gane bai son zuwa na langaɓe kai sai ya juya kan motar.

Na daɗe tare da Aunty Larai tana yi mini nasiha yadda zan riƙe mijina ta mini kyautar magungunan sanyi da ta ce su na fi buƙata a yanzu ta tambaye ni ba za a yi mini rakiya ba?  Na ce haka ya ce sai dai bayan na tafi ku zo mini Aunty.

Murmushi ta yi ta ce “Dole mu je mu ga inda kike.

Mun koma gida har mun yi shirin kwanciya na ji ƙishi sauka na yi gadon a hankali ya tambayi inda za ni idonsa na kan wayarsa na ce ruwa zan sha

Ban damu da ɗaura zane saman riga da wandon  barcin da ke jikina ba na fita ga mamakina Suhaima da Amal na zaune a falon ƙasa ban kuma gan su ba sai da na sauka, yi na yi kamar ban gan su ba na wuce kitchen “Gara mu bar garin mu huta da tarkacen baƙi kullum sai sun zo suna sa mutane tashin zuciya.”

Zancen Amal kenan daidai zan shige ta bayan su “Shi ya sa na ce maki mu ce ba mu zama garin nan, can dai ai ba a san kowa ba.”

Suhaima ta faɗi lokacin da nake fitowa daga kitchen ɗin,  sama na haura cike da tunani sanin da ni suke.

Da safe na samu Basira na ba ta kuɗin da ya ba ni na ba ta na sallama har da kayana kala biyu na haɗa mata.

Kuka ta yi ta yi ta ce mu yi mata rai ta ci gaba da aikinta ta bi mu Abujar, miji ya sake ta har da ya’yanta iyayenta ba ƙarfi dole take aikin nan saboda ya’yanta.

Ta ba ni tausayi matuƙa na ce ta bari zan yi mishi magana idan ya dawo don ya fita a lokacin.

<< Ummu Radiyya 20Ummu Radiyya 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×