A haka muka yi ta gungurawa har muka tasamma watanni uku da aure bayan matsalar shimfiɗa da muke fuskanta ga ta mota da ta sanya shi gaba mahaifinsa ya samu ya yi mishi bayanin matsalar da yake fuskanta shi kuma ya yi alƙawarin sayar da rumfar kasuwa da yake da ita Abakar ya sayi mota ya mayar da wannan da aka ba shi.
Sai dai ba nan gizo ke saƙar ba jin labarin ya haifar da tashin tarzoma daga Haj Nasara wallahi ba za ta yarda ba duk yaranta wacce ya taɓa saida wani abu na shi ya yi mata hidima sai Abakar don shi kaɗai ne ɗa.
Wata safiyar laraba mun wayi gari Abakar ba shi da ko sisin kobo ruwan lipton na dafa mana ya fita ya dawo da bread muka karya na gyara gadona ina shirin hayewa in yi kwanciyata ya ce “Kar ki kwanta Ummu, shirya mu je gidanmu.”
Ban musa mishi ba na wuce na yi wanka sai da na kammala shiri na shi ma ya shirya sai duban shi nake yadda duk ya yi wani iri a cikin yan kwanakin nan da ba ya fita saboda tsayawar motar gabaɗaya.
Jerawa muka yi muka bar gidan har gidan nasu mahaifinsa bai riga ya fita ba yana ɗakinsa nan muka shiga muna zaune gaban shi yana ta sanya mana albarka Abakar ya ce zai tafi nan zai bar ni sai yamma zai dawo mu tafi.
Ya fita zuwa dakin Haj Nasara ni ma na fita bai jima da tafiya ba sai ga yaran Haj Nasara da ɗai ɗai suna shigowa har da babbar su Aunty Habashiyya da ta sanar da su ba ta da aiki yau .
Ita ta bayar da kuɗaɗe aka yo cefane mai rai da lafiya wanda duk da haka mahaifiyarsu sai da ta aika ma tsohon ya bada kuɗin cefane.
Ni ta umarta na yi girkin suna daki suna ta hira, ina gamawa aka turo fauziyya wadda tsarar Abakar ce ta raba ina gefe idan ta zuba sai na kai har ta kusa gama kason na yi mata tunin ba ta zuba ma tsohon nasu ba.
Wani kallo ta tayar da kai ta yi mini na ke kuma a wa? Sai kuma ta zuba ta ba ni, na isa ɗakin da aka zube lemuka masu sanyi na daukar masa ɗaya na fita yana zaune a shagonsa na kai masa sai sannan na zauna cikin su gani na kuma bai hana su zancen fifita Abakar da mahaifinsu ke yi a kansu, Aunty Habashiyya kaɗai na ji tana hana su.
Sai magrib Abakar ya dawo yadda na gan shi kuma na tabbatar bai ci abin kirki ba, abinci na haɗo na ajiye gaban shi na yi kamar ban ga kallon da Haj Nasara ke yi mini ba na mamakin ƙarfin hali na.
Sai da ya kammala muka isa gaban mahaifinsa haƙuri ya ba shi kan sayen mota a ranar na ga tashin hankali a tare da Abakar damuwa sosai ya shiga muka koma gida ina ta ba shi haƙuri.
Washegari ma da na san ba shi da kuɗi na ce ya yi haƙuri yau dai ya bar ni in je gida ya ce in jira shi ya je ya dawo sanin ƙarshen ta ba shi zai ciyo ma kansa na hana shi ta hanyar roƙonsa ina da wasu yan kuɗi, su na ciro na nuna masa zan yi kuɗin mota sabulai kuma na akwatina zan cire na kai ma Mama da ƙyar na samu ya gamsu ya haƙura da fita ya ciyo ma kansa bashi.
Tare muka tafi gidan namu Hassana da Husaini da Hanan na ta murnar gani na na shiga sasan Baba na gaishe su Nabila ta zo muka wuni tare.
Na so zuwa gidan Lubna da ya gana ɗiyar yayar Mama sai dai Abakar ɗin ya ce in bari na je ba yau ba.
Washegari da sassafe muna barci bayan idar da sallar asuba abokin Abakar Amiru ya kira shi a waya ya cire ni a jikinsa ya fita bai jima ba ya dawo hannu ya sa ya tashe ni na buɗe ido cikin matuƙar barci da ke cin idona “Albishir Ummu.” Na ƙara buɗe idon ina kallonsa “Goro.”
Na amsa mishi “Amiru ne ya zo yake shaida mini za mu je wurin ubangidansa mu roƙe shi ya saya mini mota, kafin nan kuma zai dinga ba ni ta shi ina samun na cefane.”
Murna sosai na shiga yi wanka ya yi ya shirya a gurguje ya fita ni kuma na koma barcina da na tashi na ga kayan Tea a leda da bread na san bayan fitar sa ya dawo ya ajiye mini.
Kitchen na fita na ɗora ruwan zafi Haj Iyami ta shigo ta same ni na gaishe ta, ta rage sakar mini fuska yanzu, da ba ni abin ta daga ta san ban amsa amma yau wani farfesu da ke ta tafarfasa duk da ban sha’awar da ya yi a ido ina juye kofin ruwan zafina ta miƙo mini a wani ɗan bowl tsigar jikina na ji ta tashi hakan ya tilasta ni canza niyyata ta farko idan ta ba ni karɓa zan yi kai na girgiza ta ce “Saboda me ba za ki karɓa ba? Ta tambaye ni tana ɗan ƙafe ni da ido.
Na ɗan yamutsa fuska “Na ƙoshi.” “To, to, ko an samu mara son nama ne? Gabana ya faɗi jin zancen ciki da ta yi mini na ɗauki kofin da sauri na bar kitchen ɗin.
Ta sa Tea ɗin da na haɗa na yi na gaza sha maganar da Haj iyami ta yi mini sai ta dawo mini da damuwa ta ta kasa kusanta ta da Abakar ya yi ko ranar da na je gida an ta yi mini zancen ciki da kowa ke zaton ina da shi.
Hannu na ɗaga sama ina roƙon Allah ya kawo mana ƙarshen matsalolinmu ina sauke hannun kofin na ɗauka na fara sha a hankali sai da na idar na fara gyara ɗaki sannan na samu wayar Abakar bayani ya yi mini sun je wurin ogan Amiru ya amsa ba matsala zai ba shi mota akwai wata da ya karɓe wurin wani da bai son kawo balance za a duba ta zai ba shi.
Na yi murna ƙwarai ya ce na duba ƙasan pillow ya ajiye mini kuɗi na yi cefane godiya na yi da muka ajiye wayar na ɗaga pillow gudar dubu daya na samu na fita na yi ma Haj Iyami magana idan mai yi mata aike ya zo zan ba shi saƙo ta ce ba damuwa.
Da na gama girkin na sanya lulluɓina na kai ma Baban Abakar bayan na yi masa text zan je in kai.
Da na dawo ko abincin ban ci ba na kwanta barci da na ji kamar ina riƙe da shi a hannu sai dai ina yin nisa a barcin na fara mafarkin magen nan tana lasar ƙafata ina ta kuka cikin mafarkin a haka na farka na gan ni na jiƙe sharkaf da gumi, wani irin tsoro ya lulluɓe ni na baro ɗakin na dawo ƙofar daki na zauna cike da zullumi.
Ban gusa ba har sai da Abakar ya dawo ya yi mamakin gani na a birkice ba kwalliya kamar yadda na saba ya miƙo mini hannunsa na kama jikina ya ba ni kamar ana kallon mu na waiwaya a ba zata sai Haj Iyami na gani muka wuce daki a jikinsa ya sanya ni ina kuka ina ba shi labarin mafarkin da na yi ya hana ni ya kwantar mini da hankali da cewa mafarki ne kawai saboda na sa magen a raina in dinga addu’a idan zan kwanta.
Da ƙyar ya ciyo kaina na ci abincin tare da shi sai na yi sallah ko da zai fita sallar magrib waje na fito na yi tawa a ƙofar ɗaki har sai da ya dawo muka shiga ciki.
A wannan dare ban samu barci mai daɗi ba saboda mafarkin mage tana lasa ta da na farka kuma kukanta na ji ya cika mini kunne.
A daddafe na ga safiya bayan Abakar ya ɗauki mabugi ya fita neman mage ya buge ta kowa ya huta.
Daga sallar asuba ya fita saboda Amiru da ya ce ya zo ya karɓi motarsa.
Ina zaune a falo kan sallaya na yi tsuru ko gyangyaɗi na gaza yi ballantana a kai ga batun komawa barci saboda tsoron in yi barci in je ina mafarkin mage, ina nan a inda nake na ji kukan wayata a tsorace na tafi bedroom na ɗauko ta don har ɗakin ma tsoron shi nake, Abakar ne ya shaida mini ya samu wani babban mutum zai kai shi Abuja na yi addu’ar Allah ya tsare ya sa a dawo lafiya.
Dole na ɗaure zuciyata na shiga harkokina sai kuma Allah ya taimake ni ga ƙannena Hassana da Hanan, ba su jima ba sai ga Yayata Lubna ita da ya gana wuni mai daɗi muka yi sai da suka tafi Abakar ya dawo yana cin abinci ina ta kallon wata yar kyakkyawar Brief Case da ya shigo da ita ko ganin kallon da na yi mata ya yi yawa ne ya ce mutumin da na ɗauka ne ya mance da ita ba mu kai ga shiga Abuja ba mota ta zo ta ɗauke shi ina kyautata zaton ɓadda kama ya yi ya shiga motar haya na duba ciki na samu wasu lambobin waya na kira, wanda na samu makusancin mutumin ne mun yi da shi jibi zan shiga Abuja zan kai mishi a bar sa.
Na ce “Allah ya rufa asiri taka motar fa Ogan Amirun bai kira ka ba?
Ya girgiza kai”Kin san lamarin masu shi ɗin nan bai kira ba.”
Da zamu kwanta na maƙale Abakar sosai duk wata addu’a da na sani na yi ta yi ina shafe jikina shi ma na ce ya yi mini har yana mini dariya na yi kamar zan fashe da kuka na ce don ba kai ake tsoratawa ba ya shiga shafa kaina yana rarrashina.
Ranar na kwana lafiya Amiru kuma da ya tashi da zazzaɓi ya kira shi ya ce ya zo ya ɗauki motar.
Ya ɗauki Brief Case ɗin nan ya tafi da ita.
Sai da ya dawo yake ba ni labari ya kai amma bai samu mutumin ba tafiya ta kama shi amma ya ce Abakar ya bar lambar wayarsa idan ya dawo zai tuntuɓe shi ya yi masa godiya bisa ga alherinsa na maido masa muhimman takardunsa.
Na ce “Kash na so ka same shi.” Ya tsare ni da ido “Saboda me?
Na yarfe hannu “Irin waɗannan mutanen na san da ka same shi alheri zai yi maka.”
Ya girgiza kai “Ya manta kayansa na mayar masa shi kenan ko bai ba ni komai ba na sauke nawa nauyin da ya hau kaina .”
Na ce “Haka ne.”
Yau tun ina shirin kwanciya na ga magen nan ta kuma kafe tana ta kuka jikina ya ɗauki rawa daga inda nake tsaye Abakar ya tashi daga kwancen da yake bisa gado ya ɗauko mabugin da ya dauko shekaranjiya cikin sa’a yana kai bugu ya sauka bisa kan mage ta yi wata irin ƙara sai ga ta ta faɗo cikin ɗakin za ta fece ya kuma doka mata ta ɗiba a guje jini na zuba na dubi wurin da ya ƙwala mata da jini ke kwance jikina ya kuma ɗaukar sabuwar rawa na hau gadon na kwanta na dunƙule wuri guda bakina na rawa shi ya gyara wurin ya rufe ko’ina ya hau gadon ya sanya ni jikinsa a kunne yake raɗa mini maganganun da tsoro ya hana su yin tasiri a gare ni, sannu a hankali ya faɗa wata nahiyar da tun ina jin wancan tsoron har saƙon da yake aika mini ya yi tasiri cikin mamaki sai ga Abakar ya cimma manufarsa.