Muna ɗaki mun ɗaga labulai mai kauri don mu sha iska muna cin abinci ina hangen Baba yana cika baki da shinkafar nan ga nama wadatacce Mama ta sanya mishi.
Wani irin annuri ne a fuskarsa sau biyu yaransa na zuwa na farko ya ce mamansa ta ce ba a ga butarta ba? Na biyu ya ce a san ma mamansa gishiri ni na zargi ƙamshin da ya kai ziyara sasansu suka turo a gane musu duk da Mama ta sanya Hassana ta zuba ma yaran.
Bai kammala ba sai ga aiken kiran shi bai tashi ba sai da. . .