Skip to content
Part 10 of 42 in the Series Ummu Radiyya by Maryam Ibrahim Litee

Muna ɗaki mun ɗaga labulai mai kauri don mu sha iska muna cin abinci ina hangen Baba yana cika baki da shinkafar nan ga nama wadatacce Mama ta sanya mishi.

Wani irin annuri ne a fuskarsa sau biyu yaransa na zuwa  na farko ya ce mamansa ta ce ba a ga butarta ba? Na biyu ya ce a san ma mamansa gishiri ni na zargi ƙamshin da ya kai ziyara sasansu suka turo a gane musu duk da Mama ta sanya Hassana ta zuba ma yaran.

Bai kammala ba sai ga aiken kiran shi bai tashi ba sai da ya yi hani’an ya sha ruwa da zoɓon da Mama ta tanadar masa ya tafi.

Tsiya ce ta tashi suna kukan rashin adalci da Baba ba ya musu ya ba Mama shinkafa har da nama su kuma kudin da ba su taka kara sun karya ba ya ba su.

Duk yadda ya so fahimtar da su ba da kuɗinsa aka yi ba kasa amincewa suka yi lamarin da ya janyo dagulewar al’amura, har ya ce Mamansu Samira ta tafi ta bar mishi gida, ya kuma tsaya kai da fata sai ta fita.

Don ita Aya da ta ga abin zai yi zafi noƙewa ta yi ta bar Mamansu Samira da faɗan.

Ita kuma tana yafa mayafi wurin mu ta yo tana kuka kamar ƙaramar yarinya maganganu take sakewa Mama ta karɓe musu miji, ba wadda yake kallo a mace sai ita.

Lokacin da take ta sakin maganganun ni kuma ina zaune a kofar ɗaki kallon ta nake ta yi, duk da Mama ta girme mata a haife amma duk ta koɗe ta ƙojale ga ba gyaran kirki sun sanya kansu masifar cin bashi idan suka karɓi na wannan sai a je a karyar a biya wannan da haka bashi ya yi kwance-kwance ya haye musu ita yan’uwanta sun taɓa haɗa kuɗi suka biya mata amma ba a ɗauki lokaci ba ta koma.

Daga ita har Ayar ba komai a ɗakinsu yan bashi sun gama kwashewa, tun Baba yana kawo abinci danye ya ajiye, yana ajiyewa za su kwashe su sayar suka koya mishi ko yana da shi bai iya kawowa dama kuma shi ɗan cin dare daya ne kumburin ciki duk abin da ya samu dare ɗaya za a cinye a tashi.

Mama kuma tashin Maiduguri sun saba da gyara jiki da ƙamshi ga jiki ta mora ga ta da hasken fata koyaushe cikin ƙunshi take, ba mu cimar banza neman da take sai dai idan ta kulle mata ga Lubna tun da ta yi aure tana taimakowa, ɗakinta kullum tsaf yake cikin ƙamshi saɓanin su da har hana su shiga mashi wuri yake kar su ɓata mashi, farkon dawowar mu yana sanya ni gyara mishi tsiyar da hakan ta janyo shi da matansa ga yaransa na barazanar sai sun zane ni Mama ta hana ni zuwa.

Tana cikin masifar Baba ya isko ta ya ce ta zo ta fice da shi take yi ba da matarsa ba ita ba abin da ta yi mata.

Haƙuri Mama ta hau ba shi ya ce wallahi ya gaji da tashin hankalinta.

Ta ce ya dubi yaranta ya bar ta cikin ya’yanta.

Ya ce Ai ita ba ta kallon yaran nata idan ta tashi yi masa rashin mutunci.

Mama da ta ga ya ƙi, nata lulluɓin ta ɗauko ya ce ina za ta? Ta tafi ya bi ta, hakan Maman su Samira ta samu ta koma ɗakinta.

Wani Malami da ke kusa da mu Mama ta kira, shi kuma ya zo ya tara su ya yi musu nasiha ya ba Baba haƙuri da cewar da ya yi sai Maman su Samira ta tafi, ina za ta tafi ta bar yaranta goma? cikin goman daya kaɗai ta yi aure.

Ya ce shi kuma duk mai son ɗorewar zamanta da shi ta daina ɗora mishi zargin yana ba Hauwa ba ya ba su, duk abin da suka gan ta da shi bai ba su ba sana’arta ta ba ta sai ɗiyarta da ke kawo mata.

Malam ya karanta musu kuskurensu ya sanya su ba Baba haƙuri , suka ba shi magana ta ƙare.

Da safe ina sanya ran zuwan Abakar hakan ya sanya ni yin saƙar zanen gado har ƙarfe uku na rana kafin na fara shiri.

Wanka mai kyau na yi na gyara jikina ƙamshi kuwa bayan nawa turaren har na sayarwar Mama na bulbule jikina na tsaya gaban mirrow ɗakin mama ina kallon kaina, lallai kam na yi kyau.

Nabila ta shigo tarar Abakar ta zo taya ni, muka zauna zaman jiran isowar shi har abincin da Hassana ta yi na ɗibar masa amma har yamma ta ƙwace shiru ba Abakar Nabila ta gaji ta tafi gida ta ce ko sai dare zai zo.

Na idar da sallar magrib haƙurina ya ƙare asalin lambarsa na kira ba ta shiga na kira Amiru da muka rabu da gaisawa shi ma ta shi a rufe, na haƙura na tashi na tuɓe hijab na fita wurin su Mama.

Washegari ma na yi ta zuba ido sai dai  kamar ta jiya ba shi ba labarinsa sai dare na ɗebe tsammani ban ƙara gwada kiransa ba don na gane ya kamata ya neme ni, cikin wani irin sanyin jiki da na zuciya na fara zare awarwaron hannuna sannan na cire sarƙa da yankunne, na zare doguwar rigar atamfar da ke jikina na mayar da wata mara nauyi na fita tsakar gida na zauna gefen su Hassana da Husaini da ke mata tsiya kan Malam Mahir, zama na wurin ya hana ta ci gaba da ramawa, ni ma tawa damuwar da ta dame ni ta hana ni sanya musu baki har lokacin kwanciya ya yi muka shiga barci rashin ji daga Abakar ya hana mini samun barci mai daɗi da safe da ciwon kai na tashi.

Sati guda aka shafe ban ji daga gare shi ba gabaɗaya na yi sanyi damuwa ta samu matsuguni a zuciyata da gangar jikina.

Ranar kuma Lubna ta zo kan maganar Hassana da Mama ta kira ta, Malam Mahir ya turo magabatansa yana so ya kawo sadaki a sanya mishi rana watanni uku da za su yi daidai da kammala jarabawarta ta WAEC.

Mama da Lubna sun yi na’am kamar yadda Hassanar ke matuƙar son Malam ɗin, Baba Isa ne kaɗai da ya zo kan maganar ya ce ya so Hassana ta ɗan taɓa karatu ko da SCH of Health ɗin da ta taɓa ce mishi tana so.

Da ya tashi tafiya ya yafuto ni daga inda nake zaune ina jin kowa ban sanya musu baki ba tun bayan gaishe shi da na yi, na bi shi waje har inda ya adana motarsa muna tsaye jikin motar ya ce  “Har yanzu ba labarin mijinki ko?

Na girgiza kai “A’a Baba ya dawo.”

Da matuƙar mamaki ya ce “Ya dawo amma ban ji ba yaushe?

Na ba shi labari ya ce “To shi kenan, ko an mayar da aurenku ki yi ƙoƙari ki ci gaba da karatunki kamar yadda aka yi alƙawari da shi zai bari ki cigaba.

Kai na ɗaga masa, mun ɗan yi hira ya shiga motarsa na tafi gida.

Ina shiga Lubna ta ce “Ya kamata Abakar ya zo a yi magana a haɗa bikin komawar ki da auren Hassana.”

Wani takaici na ji  kamar na ɗora hannu a ka na yi ta kwarma ihu, ban yi mata magana ba na shige ɗaki na kwanta bisa katifarmu don ma kar ta ci gaba da yin maganar, ina sauraren su ita da Mama suna zancen yadda za a haɗa mana kayan ɗaki ni da Hassana.

Zancen auren Hassana  ya kankama an sanya rana kamar yadda Malam Mahir yake so, Lubna ta karɓi kuɗin sadakin da na gaisuwa sannan kyauta sosai yake ma Hassanar daga kuɗaɗe zuwa kayan kwalliya kasantuwar shi Mutum mai hali yana da Private Sch da ake karantar da boko da Arabic sannan ya mallaki shaguna da ya zuba yara ana gudanar da sana’o’in hannu, makarantarmu ta islamiya anan shi ma ya yi nashi karatun ya kuma fara koyarwa, ko da ya mallaki tashi ba ta hana shi koyarwa a tamu ba.

Na cire rai da dawowar Abakar gare ni, duk da zuciyata da ke mini zugar in tafi gidansu in gano amma da na faɗa ma Nabila hana ni ta yi ta ce in yi haƙuri.

Mama na ta faɗi tashi yadda za ta haɗa kayan ɗakin Hassana, don ni kam sun haƙura ita da Lubna saboda fitowa da na yi na faɗa ma Lubna gaskiya ban ƙara ji daga Abakar ba tun ranar da ya zo wuri na,sai suka haƙura Lubna na ce mini “To kin gani ke da kika ƙwallafa rai a kansa yanzu sai ki dawo nutsuwarki ki fita batunsa ki koma yadda kike da.

A baki na amsa mata amma a zuciyata ina kasa gaskata Abakar ya bar ni to saboda me?  Gidansu na shirya na tafi ni kaɗai sanin Nabila ba za ta ba.

Ɗakin Haj Nasara na shiga saboda rashin ganin shagon Baban a buɗe sai da muka gaisa ta yi mini iso ɗakinsa,  ashe kwana biyu bai ji daɗi ba,  ya ce mini shi ya sa bai zo duba ni ba kamar yadda ya saba. Na gaishe shi tare da ajiye mishi lemo da Ayaba da na saya mishi yana ta shi mini albarka ya ce “Kun yi magana da Abakar ɗin? Na girgiza kai ya ce “Ai yaron nan ba ƙaramin taimako ya yi ma rayuwar Abakar ba, bayan fitar da shi ga kuma karatu da ya yi sanadin zai koma wanda shi ne burinsa. Jin Baban kawai nake ba don na gane maganganun ba abu ɗaya na fahimta Abakar ba ya garin,  sallama na yi mishi na tashi yana ta sa mini albarka, na leƙa na yi ma Haj Nasara sallama ita ma.

Keke napep na tare da na gani za ta gifta, na faɗa kaina kawai na tura tsakanin cinyoyina hawaye na mini zuba da ƙyar na saita kaina na share su na ɗago fuskata ina kallon hanya.

Kafin in isa gida na yi ta ƙarfafa ma kaina gwiwa da haƙurƙurtar da zuciyata Abakar bai waiwaye ni ba yanzu da na zo gaban mahaifinsa ba wata magana tawa sai ta murnar burin Abakar zai cika zai koma karatu. Shi kenan aurena ya ƙare daga watanni uku kacal da ɗaura shi, anya Abakar ya yi mini adalci da ya bar ni ya mayar da ni ƙaramar bazawara?

Na share hawaye na sauka napep ɗin ina ƙara ƙarfafa ma kaina gwiwa yakice shi a raina daga yau.

A tsakar gida na samu su Mama na yi mata sannu zan wuce Hanan ta taso ta maƙale ni, kanta kawai na shafa ban ɗauke ta ba kamar yadda na sabar mata na wuce ɗaki ma’ajiyata na wuce na ciro kuɗaɗen da na tara sai da na zauna na ƙirga su na ware kuɗin registration na mayar da su inda na ɗauko su na miƙe da sauran na san kafin samun admission ɗin in sha Allah na tara na acceptance feeda sauran ƙananun matsaloli.

Sai da na zauna kusa da Mama na miƙa mata da rashin fahimta take duba na tana duban kuɗin na ce “Kudaɗen da nake tarawa ne na ayyukana na zanen gado har da dubu ashirin din da Abakar ya ba ni na ware wadanda zan yi Registration sauran ne waɗannan ki ƙara Mama a yi ma Hassana hidima.”

Ina jin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciyar da ta fidda ta fara sanya mini albarka, shigowar Nabila ya sanya ta yin shiru muka nufi ɗaki.

Zaman mu na zayyana mata zuwa na gidansu Abakar da yadda muka yi, tsaki kawai ta yi ta ce “Kin faye naci Ummu Radiyya.”

Sai dai ta ji daɗi sosai da jin yadda na nuna zaƙuwa ta kan in fara karatu.

Kwanakin da suka biyo baya ana ta shirin bikin Hassana muna kuma  ta shirin komawar mu karatu ni da Nabila.

Wani hantsi Nabila ta shigo, aikin zanen gado ta same ni ina yi ta ce zuwa ta yi ta faɗa mini zan raka ta biki.

Ina ci gaba da saƙata na ce masu aikin nan yau suke so Nabila, zuwa yamma zan kammala.”

Ta ɓata fuska “Su haƙura ki raka ni kawai Ummu.”

Na ce “Wai wane biki ne wannan? Ta kanne ido “Ƙawata ta poly Sa’ada Ahmad Lema.”

Na jinjina kai “Lallai za a sha biki. Ko ba ita ba ce kika taɓa ba ni labari yar auta ce ba? Kai ta gyaɗa “Ita ce, shi ya sa nake so ki zo mu je za a gwangwaje gobe ne ɗaurin aure yau Bridal shower za a yi.”

Na ɓata fuska “Amma kin san ban ɗinka kayan da za ku sa ba don na san dole ku yi anko za ki kama ki gayyace ni.”

A kayan akwatinki akwai material irin sa, ki sanya kawai kala ɗaya ne.”

Na mike na nufi wurin kayana sai da na ciro kayan ta nuna wanda take nufi doguwar riga ce sau daya na sanya a watan farko na aurena shi ma da daddare na yi ma Abakar kwalliya.

Nabila ta riƙe a hannunta tana yaba kyan ɗinkin na ce “Yanzu ya kike so na yi da mutane? Ta ce “Ki ba su haƙuri sai gobe.” Na gyaɗa kai “Shi kenan ƙarfe nawa ne?  “So nake 2;30 mu bar gidan nan kin san unguwar sarki ne akwai nisa kafin mu kai.”

<< Ummu Radiyya 8Ummu Radiyya 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×