Skip to content
Part 15 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Ƙara nutsuwa na yi jin kalamansa, a wannan daren na tantance maza daban daban ne, Tahir Sodangi cikakken namiji ne, na gane banbanci me yawa tsakaninsa da mijina na baya Abakar dan shi kam baya wuce minti biyar ya gama abin da zai yi ya kama gabansa. Amma Tahir wuya sosai na sha a hannunsa, dan ban saba da hakan ba ga kuma daɗewar da nayi rabona da abin, tsawon daren bai bar ni na huta ba ga gyaran da na sha, na gamsar da shi iya gamsarwa, ni ma kuma na gane maganin malama Jamila ya yi min. Na idar da sallar Asuba na ga shigowar sa, kaina na ƙasa na gaishe shi gado ya hau ya kwantaganin ba ni da niyyar tashi ya ce “Ke nake jira fa” jikina ba kwari na miƙe gefen gadon na zauna ya janyo ni jikinsa ya zare hijab din jikina da zanen da na daura da zan yi sallar sai ya rungume ni, “Zan kara ummulkhairi, ko kin gaji?

Jin nayi shiru sai ya ce “Ni ina so Ummu” Ya fara yamutsa ni muka ji ana buga ƙofa tsaki ya yi ya sake ni sai ya sauka ya fice, ina ji yana tambayar waye ban ji amsar da aka ba shi ba sai takun dawowarsa na ji, jallabiyar da ya tube shigowar sa ya shiga zurawa, a hankali na ce mishi”Lafiya” juyowa ya yi ya dube ni “Babban yayanmu ne ya aiko kirana, akwai wani gidan gona da nake so zan maida gidan kaji, shi ne yanzu ya aiko a shaida min me gonar ya zo gari dan shi ma ba anan yake ba in kuma ya tafi ya kan dade bai zo ba, shi ne za mu je yanzu dan yau zai bar garin”.Na ce “A dawo lafiya Allah ya yi jagora” ya ce Amin ki kwanta ki yi barci, zan dawo yanzu”.Na ce “To”Ya fita ya bar ni cikin ƙara kullewar kai game da shi.Na cigaba da juya tarin tambayoyin da nake da su a kansa nake kuma son samun wanda zai warware min.

Daga bisani barci ne ya sace ni. Ƙarfe takwas da rabi na farka, gane Tahir bai dawo ba sai na miƙe, wanka nayi ban ko tsaya wata doguwar kwalliya ba na zura hijab, da na fito sai na dauki bokitan alkaki da cincin wani yaro na yafito ya taya ni dauka, sai muka isa sasan Haj tana zaune, da fara’a take min sannu da zuwa “Kin fito ummulkhairi? Sai da na kai zaune na soma gaishe ta, ta yi min ya gajiyar aiki, kafin ta shiga godiyar kayan da ta ga mun shigo da su.Koko da kosai ta turo min da kayan shayi, ta ce “Aike na biyu ana cewa ba ki buɗe kofa ba, shi kuma Sodangi shiru ba su dawo ba.” Koko da kosan na sha sai nayi mata shara na gyara mata wuri.

Ta sa aka raka ni duka sasan yayyin tahir su huɗu, kowanne matansa biyu illa babban yayansu shi ne me mata uku. Sai da na shiga dakin kowaccen su kafin na dawo wurin Haj, na samu matan babban yayan su biyu uwargidan da me bi mata, sai kuma uwargidan me bi ma babban yaya suna raba kayan bikin da na zo da su. Sai da suka gama suka tafi na ce wa Haj ina neman yaron da zan aika ya yo min cefane. Murmushi sosai tayi ta ce “Yawwa ƴan nan Allah ya miki albarka, gara ki yi wa mijinki girki ko da matansa ya zo sai dai ya yi ta gararin sayen abinci.”

Miƙewa nayi na koma sasan Tahir, can wani ɗan matashi ya bi ni na lissafa mishi abin da zai sawo min ya karɓa ya tafi.Na koma ciki ina gyara wurin duk da ba wani datti ya yi ba, na dai ƙara tsaftace komai, na saka turaren wuta. Ina yan goge goge a kitchen yaron ya dawo, Farar shinkafa na dafa da miyar ƙoda, sai kuma na shirya Spanish poiled cheaken, kaji uku nayi amfani da su wurin yinsa, wanda na ba yaron ya siyo min. Zuwa ƙarfe ɗaya na kammala komai, Hajiyar su Tahir na ware wa kaza daya sai na shirya mata abincin a wani katon tray na dauka na kai mata, ni da Tahir kaza daya na cire mana sai na shirya kaza daya da abincin a wani tray na aika wa uwargidan babban yaya ta raba ma jama’ar gida.

Wanka nayi na gyara jikina, nayi kwalliya da shaddar da na dinka ta cin biki, dinkin fitted gown ne da ya yi matukar karba ta ya fidda surata,mayafi na sa sai na isa sasan Haj, na samu tana buɗe kwanonin sai sa min albarka take, tana cin abincin ina gefenta Tahir ya shigo, “Kai Haj ina kika samu abincin nan?dan na san ba na surukanki bane”.Ɗagowa tayi tana duban sa”Ai kam na surukaina ne”Cokali yasa ya ci sau ɗaya sai ya lumshe ido abincin ya yi Haj” Ya koma kan naman ya yaga ya sa baki “Uhmm delicious” ta ce “Ka ga malam kar ka cinye min ga naka can a daki” Wani duban mamaki ya yi min dan maganar da tayi ta sa ya zargi ni nayi.Na sauke idona, Haj ta ce “Daga yanzu yanzu sai muka ji ka shiru sai yanzu” ya ce “Bayan mun je gidan gonar an yi ciniki wasu filaye suka ja ni wai yana da kyau in saya in gina wa iyalaina, ni kuma ban da wannan ra’ayin, indai kina raye na fi san na shigo garin nan in sauka wurinki”Ta ce “Ba laifi sayen ma yana da amfani”Duk a gajiye nake, taso mu je ” ya fadi yana juyawa dan barin dakin, na miƙe na bi bayansa.

Zama kawai ya yi na zuba mishi sosai ya ci, sai ya sha juice din kwakwa da abarba da na hada mishi.Sai sannan ya nemi sanin inda na samu kayan cefanen, na mishi bayanin na aika ne sai aka sawo min. Kai kawai ya gyaɗa sai ya mike wanka ya yi da ya fito na ji yana kirana, kwance na same shi bisa gado daga shi sai wando gajere, “To zo mana in ga kwalliyar in kuma bada tukuicin girki me daɗi da aka yi min” a hankali na taka kusa da shi da ƙafafuwansa ya nade ni sai ya janyo ni jikinsa, bayan gama abin da za mu yi daga bisani barci muka yi,sai dai ni nawa barcin bai yi nisa ba dan hankalina na ga komawa ta gida.Ana fara kiraye kirayen sallar la’asar na soma taɓa shi a hankali, har ya buɗe ido na ce “An soma kiran sallah kar dare ya yi ka maida ni har ka dawo”.Ya tashi zaune “To bari in dawo sallah sai mu yi maganar.”

A gurguje ya yi wankan sai ya wuce masallaci, ni ma nayi wankan nayi salla, na idar kenan cikin yaran gidan wani ya zo ya ce Haj na kirana.a baya na bi shi har wurin HajiyarTa ce “Garin dawa ne na ce ko za ki yi wa mijinki tuwo dan yana so”Kaina ya ɗaure da zancen girki ni ita Hajiyar bata san yau zan koma gida ba?Amma ba zan iya musa mata ba, na amsa da “To” ta ce “Yawwa ga daddawa nan me kyau ce ta kalwa ga kaza can na sa a yanka, sai ki yi amfani da ita.Na dubi inda take nuna min, jikanta ne ke gyaran kazar.Ta cigaba”Mijinki na san abincinmu na gargajiya duk da dadewarsa a bariki, to mata ne duk maƙyuyata, sai abincin ƙarya”.ganin nayi ɗan murmushi ta ce “E man girkin zamani ai girkin ƙarya ne, zuwa na na farko gidan Sodangi, matarsa tun la’asar take ta kai da kawo, sai dai ka ji kwas ƙwas ana ta yanke yanke a raina ina faɗin za mu ci daɗi, wai sai da magrib ta zubo min latas da abarba da lemo wai su ne abincin dare”.Ina son yin dariya ina kuma jin nauyinta, jikanta me gyaran kaza ya kwashe da dariya. “Kai Haj cream salad da fruit salad fa aka kawo miki.”

Wata budurwa da ke zaune tana daddanna waya ta fadi. Baki Hajiyar ta taɓe “Shiriritar banza dai, haka dambu Sodangi na sonsa sosai”.Kirana aka aiko yi wai in zo an kawo sako,na isa kayan abinci ne jibge wai in ji Tahir, na store na sa suka shigar can, na kitchen aka sa kitchen.Ban koma wurin Haj ba girkin na shiga yi, daga ban ma gan shi ba ballantana in yi zancan komawata gida, kuka na kaɗa ita ma Hajiyar ce ta bani, na zuba wa Hajiyar na ci nawa sai na shirya mishi na shi.Bayan har na yi wanka ya shigo, ya ce “Kin ji ni shiru ko?. Idan na shigo garin nan jama’a ba sa bari na zama”.Ya zauna ya soma cin abincin, ya ce “Dazu Hafsa ta kira ni, ta ce In Haɗa ku ta kasa samunki” na ce “Kashe wayar nayi saboda masu kirana su yi min tsiya, baran ma ita Hafsa, ina son kiran Ummata amma ina jin kunya”.Karamar wayarsa ya janyo umman ya kira ina jin muryarta dan yasa hands free, sai da ya gama gaishe ta sai ya min alama da hannu zan yi magana da ita?Kai na girgizaYa yi sallama da ita ya kashe wayar.Na ce “Ina ta jiranka ka zo ka mayar da ni gida, ba ka shigo ba sai yanzu.” Kallona ya yi “Gida kuma? wane gidan?” Gidan mu mana” Sumar kansa ya shafa Ai nan ne gidan ku, kuma kin zo kenan, in ma za ki tafi wani gidan sai dai in za ki koma Kaduna.” Shiru nayi raina ya ɓaci sai na miƙe,” Ina za ki kuma? Ban waiwayo ba na ce “Sallar isha’i zan yi”Ko da na idar da sallar ban fito ba kwanciya ta nayi can sai ga shi “Kwanciya kika yi ba za mu yi firar ba?”Barci nake ji” na faɗa ba tare da na buɗe ido ba.”Amma ba ki kwashe kwanonin abincin naki ba” Na sauka na je na kwashe sai na dawo, kwance na same shi ya rufe rabin jikinsa, hannayensa ya buɗe da niyyar in shiga cikisai na ɗauke kai, nesa da shi na kwanta na juya mishi baya.Mirginowa ya yi ya haɗa jikinmu sai ya rungume ni a kunnena yake rada min “Fushin me kike Ummuna?Ke ɗin ai Malama ce, ya halatta mace ta juya wa mijinta baya a shinfida? Shiru nayi “To yi haƙuri ko bani bane? Kaina na kara kwantarwa kan kirjinsa “Ba ka ce ba zan koma gida ba?

Ya ce To ki yi haƙuri, ki bari idan na je Kaduna na dawo sai in mayar da ke” A haka muka rufe maganar na haƙura kan ba yadda zan yi.Washegari Bakori ya tafi shi da yayansa me bi ma yaya Babba.Haj ta bani kayan da zan yi dambu ni kuma na zauna na yi shi me daɗi ya ji zogale da wadatacciyar gyada, sai hanta da na yanka gutsi gutsi.Da nayi wanka sai na shiga tunanin kayan da zan sanya, tunawa da jakar da ya ce akwai kaya a ciki in yi amfani da su yasa na janyo ta dogayen riguna ne dakakku yan gaske wannan tana wane wannan wannan tana wane wannan har kala goma sha biyu, akwai takalma da mayafai sai rigunan barci daya na dauka na sanya nayi rolling da mayafinta.Motsin da na ji yasa ni fitowa falo, Tahir ne kallon da nayi masa yasa na shafa’a da yi masa sannu da zuwa, sai kallon suturar da ke jikinsa nake wata rantsatstsar shadda ce da ke ta masƙi hular nan ta zauna mishi a shatara, yana kokarin kwance agogon hannunsa ya ce “Ke lafiya kallon fa? Yar kunya na ji na yi mishi sannu da zuwa.Yana cin abinci yana santi, ni kuma ina kan sopa na haɗe kafafuna idona na kan TV amma hankalina ya yi nisa wurin tunanin da na fara tun shigowarsa.Ban san kammalawarsa ba sai dai na ji ya ruko ni, na miƙe tsaye sai da ya kwanta ya kifa ni kan cikinsa ya ce tunanin me kike tun shigowata ?Na ce “Ba komai”ya ce “Yi hakuri ki gaya min, ko kina da wanda ya fi ni anan ɗin?Na girgiza kai “To gaya min” yana fadi yana jan hancina sai da na kara tura kaina a kirjinsa sabuwar kaunarsa da na tsinci kaina cikinta na ƙara fizgata har ina jin ina ma ace shi ɗin nawa ne ni kaɗai.Sannan na ce “Ina tunanin sanin da nayi maka a ustazu, yanzu kuma ka rikide min wani mutum daban, da yawan lokaci kuma na kan so sanin dalilin zuwanka makarantarmu da niyyar koyarwa”.Jin nayi shiru yasa shi yin wani murmushi me sauti, yanda abin ya faru ya soma mishi yawo a ido.Ranar wata asabar ce da ba zai yuwu ya manta ranar ba, ya kai wa Malam Mas’ud ziyara a garin su Dutsinma lokaci na farko da ya yi hakan tun haduwar su a aikin hajji, wanda suka yi abota, ko bayan dawowar su zumunci me ƙarfi ne ya kullu a tsakaninsu.

Daliban malam Mas’ud suka rika fitowa cikin nutsuwa suna wucewa gidajensu, wani tunani ne ya darsu a ransa yayin dayake duban su cikin sha’awa, dan sun burge shi.Ya maida duban sa ga malam, ina ma cikin daliban nan naka mata in samu daya me hankali da nutsuwa in aura”.dan nutsuwarsu ta bani sha’awa, malam Mas’ud ya ce “Ai in kana son hakan sai a nema maka me hankali”.Ya ca “A’a malam, ina so yanzu idan zan kuma aure in auri wadda nake so take sona a ni din take so ba wai abin hannuna ba”.Malam Mas’ud ya ce “To yanzu ya za a yi ka gan su har ka samu wadda kake so?Nan ya faɗa mishi tunanin da ya yi zai rika zuwa duk weekend zai zama malami, da haka zai gan su. Malam Mas’ud ya ce To za a ba shi darasi a ajin masu fita yammata, ya je ya zo mishi da jadawalin darussan da suke yi, sai ya zabi sharhur risala, dan ita ce darasin da ya fi kauna sa’adda yana ɗaukar karatu a gaban uban goyonsa wanda ya kasance babban malami ne, shi ɗin ma har ya zama saurayi ya kan taɓa koyarwa a makarantar uban goyon nasa.Jin shirun shi ya yi yawa yasa nayi tunanin ko barci ya ɗauke shi, motsi nayi sai na ji ya daɗa makale ni, sama sama ya bani labarin. Shiru nayi cikin nazari tare da juya ɗayar tambayar da ke min yawo a rai.Tahir me fadin kwana uku zai yi ya koma Kaduna, sai ga shi yana neman yin sati biyu, kullum sai dai in ji shi yana waya da matansa.Ni kuma ban gajiya da shirya mishi abinci, wani abincin gargajiyar ma ban ko iya shi ba Haj ke koya min, wadda sai a sannan na fahimci lalurar da take fama da ita ta ciwon Athma da pnimonia dan haka ban gajiya da temakonta, dan yanzu ne lokaci me wahala ga masu lalurar wato lokacin sanyi.Na lura Tahir yana jin daɗin mu’amala ta da mahaifiyarsa. Wayata kuwa tuni na kunna ta iyaka duk wanda ya kira ni ya gama sherin shi ina ji, ba kamar Hafsa sharrin duniya ba wanda ba tayi min ba,Kullum nake kiran Ummata dan ba kaɗan nake kewar ta ba.

<< Wa Gari Ya Waya 14Wa Gari Ya Waya 16 >>

4 thoughts on “Wa Gari Ya Waya 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×