Farkawata daga barci sai na ɗora idona bisa agogo, ƙarfe bakwai saura minti takwas na safe. Jikina na zare cikin na Tahir sai na fito, bathroom na fara shiga kafin na isa kitchen, ruwan Lipton wanda na zuba ma kayan ƙamshi na ɗora, yana fara zafi na fito, zane na ɗaura saman riga da wando na barci da ke jikina sai na saka hijab, bayan ɗakina na fita na dauko murhun gawayi na zuba gawayin kafin ya ruru na koma na kashe gas ɗin na juye ruwan zafin cikin flacks, da sauri na fasa ƙwai na soya wa Haj, na gasa mata bread.Wurin gawayin na koma ya ruru, na dauka zan wuce na ji muryarsa a kunnena “Ina za ki da wannan? Haj zan sanya ma wa a daki.”
Na ba shi amsa, sai na wuce, a uwar ɗakanta na same ta, na ajiye nesa da ita dan kar ya takura mata, na juya muka haɗa ido da Tahir na ratse shi na wuce, abin karyawarta na koma na kawo mata.Samu nayi suna magana, ban zauna ba kitchen na koma na kama aikina.Koda na kammala namu, dakin Haj ya nemi in kai mishi, dan haka can ɗin na kai, sai da ya shigo, yake tambayata me yasa ake kaiwa Haj wuta a daki.Ban ƙasa a gwiwa ba na ce “Saboda lalurarta, kuma ina ganin da za a daure da room heater aka sanya mata a ɗakin, bathroom ɗinta kuma a saka water heater saboda masu lalurar ba sa mu’amala da sanyi.
Idan aka yi hakan ina ganin ba ƙaramar lada za a samu ba” Daga haka bathroom na shiga dan na gama komai wanka zan yi.Shi ma da ya yi wankan Kano ya tafi. Ina sallar la’asar na ji yaran gidan suna ta sannu da zuwa, sai da Tahir ya shigo na gane shi suke mawa, sai kuma da na shiga wurin Haj kai mata abincin dare sai na ga aikin da ake yi.Water heater da room heater ake sanya mata, dan murmushi nayi a raina na ce sayen su ya kai shi Kano kenan.
Sai da muka nutsu a makwancinmu yake shi min albarka wai na tunasar da shi abin da yake wajibinsa ne. Ana gobe zai koma Kaduna, da safe duk da nauyin sa da nake ji sai da ya gane ɓacin raina, wunin ranar bai je ko ina ba muna daki sai dai ya fita sallah ya dawo.Ya dawo sallar isha’i aka kira wayarsa, ji nayi yana cewa ka shigo kawai, da shigowar baƙon miƙewa ya yi sai suka tafa, “Shegen bisa yaushe a gari? Tahir ya ce wa baƙon nasa, “Da magaribar nan mutumina, ai ina sauka nake jin kana garin nan har sati biyu, shiyasa ko abinci ban tsaya ci ba na ce bari in zo in ga wannan amarya da ta iya riƙe ka har sati biyu.” “Sharri ka shi zai kashe ka, wa ya ce maka ban taɓa sati biyu a ƙanƙara ba?”
Haba abokina ai rabonka da ka zo ka dade ina ga tun kana sakandare idan ka zo hutu”. Dariya suka yi Na ce “Sannu da zuwa.” Ya juyo yi hakuri amaryarmu, ya amarci? Na gaishe shi ya ce “A yi min afuwa amarya, ban samu halartar ɗaurin aure ba, muna wurin kwadago” Na ce “An dawo lafiya?” Lafiya ƙalau Alhamdulillahi”.Tahir ya buɗe abinci “Bismillah” Kallon abincin ya yi “Anya kuwa na ci abincin nan, ni ma nawa na can gida. Dan yau ni ma ɗin ango ne, kar in ci kasa a min bore.” Ya ce “Ci kawai malam, na rakaka har gaban Saratun, dama ai na ce kai mijin ta ce ne kullum kana fama da mace ɗaya.” Ya cika bakinsa da abinci ya ce “Dole ka yi ta zama abokina, ko da wannan daddaɗan abincin ai a riƙe ka.” Ya ce “Kai dai dan iska ne wallahi.” Duba na ya yi “Dan bani ruwa mara sanyi ummulkhairi.” Sai da na je na kawo mishi sai na koma kitchen din duba farfesun danyan kifin da na ɗaura, ji na shiru Tahir ya ce “Wai me kike yi ne? na ce “Ina duba girki ne.
“Na shiryo musu na dauko maganar da na ji suna yi cikin rage murya ta sa ni tsayawa sai na sa kunne.Wallahi kar ka ga magiyar da Latifa take min in kawo mata kai, har kudi ta bani na ce ta riƙe kudinta za ka same ta har inda take.” Ai kam za ta daɗe bata gan ni ba abokina.” Tahir ya ba shi amsa ya ce “A’a dai abokina, ƙarshe dai zaƙin amarci ke dibarka.” “Ba za ka gane ba kai kam.” Tahir ya ce mishi Sallama nayi musu na ajiye musu farfesun, sai na ji sun sauya fira zuwa ta wurin aiki. Miƙewa nayi Tahir ya ce “Ina za ki?Na ce “Zan kwanta ne”.Ya dubi agogo.” Kwanciya ko tara bata yi ba? Shiru nayi. Ya dubi abokin nasa”Yau tun tashin ta fushi take zan tafi gobe in bar ta.” Ya ce
“Kawai ka tafi da a bar ka.” Kai ya girgiza “Idan na tafi da ita can su nawa ke jirana? ka san basma ma ta dawo kaduna, an maido ta aiki nan.Nan kuwa ita kadai ce. Dariyar shakiyanci abokin ya saki. “Kafin ka harbeta ko? Jin furucinsa ban ko tsaya ce mishi sai da safe ba, na shige da sauri har ina tuntube.” Tahir ya dube shi “Daga ka kore min amarya kai ma sai ka tashi, dan ka san ango baya doguwar fira.” Dariya ya yi har yana buga kafa. “Allah sarki ni daɗin abun dai ni ma Allah yasa ina da matar nan, yau da na mutu da takaici. In ka gama amarcin muna nan muna jiranka, duk da dai har na fara tunanin duk aurenka ban ga wadda ka ruɗe har kake min irin maganganun da kake yi yau, anya?Tahir ya buɗe ido “Anya me?
Sharrinka dai kai zai kashe.”Tare suka fita abokin na dariya. Na kwanta cikin jujjuya maganganun nasu, ban so zuciyata ta yarda da zargin da take na jin zantukansu, ina ta kokowa da zuciyar tawa ya shigo, gadon ya hayo sai da ya sanya ni jikinsa sannan yake bani labari. “Wannan ɗin da kike gani, abokina ne tun na kuruciya, sunansa Shehu, tanki yake tukawa a ma’aikatar mu.” Da safe ma da muka tashi fuskata ba walwala, ina haɗa mishi abin karyawa sai rarrashina yake.
Ganin ina hawaye sai ya mike kayana ya soma haɗawa, da na ce mene ne ya ce tafiya za mu yi. Na yi saurin duban sa”Tafiya kuma zuwa ina? Gira ya dage min “Kaduna”Ido na zaro “Ba za ni ba”Dole kuwa ki je, dan ba zan bar ki kina kuka ba.” Na share hawaye to kayi hakuri na daina.” Ya kamo ni muka zauna bakin gado maganganu masu daɗi yake gaya min har sai da ya ga na hakuran da gaske, sai ya ce in raka shi wurin Hajiyarsa, na raka shi, suka yi sallama sai dai duk yadda ya so in mishi rakiya wurin motarsa kasawa nayi, dan duk mutanen gidan sun fito mishi bankwana.
Gadona kawai na haye da na koma daki, wunin ranar ban fito ba, sai dai in tashi in yi sallah in koma in kwanta.Ban tabbatar da shakuwar da nayi da shi me yawa ba ce dai da ya tafi ya bar ni. Haka na koma kan al’amuran da nake yi, amma kewar Tahir na tare da ni duk da yawan wayar da muke yi. Ranar da ya yi kwana uku da tafiya, ina dakin Haj ina yi mata goge goge, na daga received na ɗaga dan in goge kasanta, wasu hotuna suka bayyana, cikin mamaki na dauka ina dubawa, dan abin da na gani a cikin su, wata budurwa ce jikin hotunan me matukar kama da Tahir, dan dai kawai ita ɗin mace ce, duk a yan’uwansa ban ga wanda suka yi kama haka ba, Su duk Haj suka biyo, shi kuma Tahir da mahaifinsa yake kama, dan akwai hoton mahaifinsa kafe a falon Haj.Yarinyar yayansa da ke zaune a falon na nuna ma hoton “Salma wace ce a hotunan nan?Ta taso daga inda take tana leka hotunan “Anty Hadiza ce, ita ce autar su babanmu”.A ina take? Na tambaye ta cikin mamaki dan ni dai ban taba jin wanda ya yi maganar ta ba.”Tayi aure ba a daɗe ba, mijin dan Nijar ne ya tafi da ita can”.Shiru nayi cikin kakkaɓi ina ƙara duban hotunan. Da daddare na kai ma Haj fira, akwai jikokinta a dakin suna kallo, ni ba kallon nake ba wata yar wansa da ke fama da dan’uwanta ya koya mata sarfu an basu aiki bata iya ba, ganin har ta soma hawaye sai na yafito ta, ta iso gabana a hankali na shiga koya mata har ta gane, sai na nuna mata tayi aikin da aka basu a makarantar.
Tun daga ranar duk wanda bai gane aikin da aka yi musu ba sai ya zo wurina, iyayen ma samuna suka yi suna so in rika koya musu karatu na ce ba damuwa sai su zabi lokacin da suka ga ya dace mu riƙa yi daga su ne masu yawan aiki.Da Tahir ya samu keɓewa zai kira ni, bai zo ba sai da ya samu kwanaki goma sha biyu da tafiya.Ya ce min gashi nan zuwa, dan haka shiri sosai nayi na tarar sa, ranar da zai zo tun da na tashi ban koma ba, sai da na gyara ko’ina kafin na shiga girki, Dambu nayi na shinkafa sanin shi ɗin me son cin nama ne kamar yanda Hajiyarsa take yasa na tanadi kazata, kai da kafa kawai aka cire mata dahuwar shinkafa cikin kaza nayi sai nayi mishi juice din abarba da kwakwa.Da na kammala wanka nayi me kyau na gyara jikina sai da na ji na dauki ƙamshi ko ta ina cikin doguwar riga, ban je sasan Hajiya ba a ɗakina na yi zamana, isowar yara da ledoji ya bani tabbacin Ogan ya iso kenan, ya ɗan jima bai shigo ba na san yana wurin Haj.Ƙamshin turarensa na fara shaƙa kafin na ga shigowarsa, jamfa da wando ne sanye a jikinsa na wata ɗanyar shadda, farin glass ɗinsa na rai da rai manne a idonsa mayatattun idanuwansa a kaina, sauke nawa idon nayi dan duk ya daburta ni, kawai sai na samu kaina da zubewa gabansa, ya ɗago ni sai ya manna ni a kirjinsa, bedroom muka wuce duk da tuna mishi da nake ya ci abinci tukuna.Sai la’asar ya janye daga gare ni ya wuce masallaci.
Da ya dawo ne ya ci abinci sai kuma ya janyo ni wai in ba shi labarin kewar sa da nayi.Kwanaki uku ya yi min wadanda suka yi matuƙar yi mana daɗi.Ranar Monday da sassafe ya yi sammakon tafiya, ko da na tuna mishi mayar da ni Dutsinma daure fuska ya yi ya ce yana sane, tilas na haƙura.Haka ya yi tayi ya zo Friday ya koma Monday, har na samu wata biyu, kafin cikar watanni biyun na samu ziyarar ƴan’uwana dukan su hada matan yayyena, Hafsa ma ta so biyo su lokacin kuma Ramlarta bata da lafiya, sai dai koyaushe tana ce min tana nan zuwa.Wani zuwa da ya yi zai tafi na raka shi wurin Hajiya zai yi mata sallama yake ce mata “Sati me zuwa in Sha Allah zan tafi da ummulkhairi Kaduna”.Hajiya tayi dan jim kafin ta ce “Ina sha ka bar min ita nan kenan?Ya ce “Na dai bar ta ne ta ga dangina ta saba da su”. Sai ga Haj tana matse ido yana bata hakuri.”Saboda Allah ka san ba bar min ita za ka yi ba ka kawo min ita?Sai da na shaku da ita, yarinya me hankali da kirki da ganin girman mutane, Allah kaɗai yasan ƙaruwar da mutanen gidan nan suka samu zuwanta.Ka ga ga karatu tana koya musu su da yaransu, daidai da girki zuwanta matan nan sun gyara girkinsu, ga ta bata da rowa komai ka kawo mata sai ta cire ma kowa, ni nan abin da nake so shi za ta girka min, kullun sai ta dafa min nama, ta gyara min daki, ta kwance min kai tayi min kitso,zannuwana ta wanke min.Sai ta shiga kuka sosai tana fyace hanci, ya ce “Ki yi haƙuri Haj, nayi wa Fati magana (ɗiyar wansa ce) duk safiya ta zo ta gyara miki ɗaki ta kuma rika yi miki kitso, wanki da gugar kayanki kuma Na matazu zai rika aikowa a karɓa, nama da kwai za a cigaba da kawowa umma ta rika dafa miki, tun da kin ce duk matan ta fi su tsafta da iya girki.In kuma duk hakan bai yi miki ba to ki shirya mu tafi tare.Nan kuma tayi tsalle ta ce “Allah ya tsare ta da komawa gidansa.Ya ce “To cikin sauran matana ki zaɓi wadda kike so zan kawo miki ita.”
Nan ma ta ce ya rufa mata asiri bata son ko daya.Ya ce ki fahimce ni Haj na ɗauko ummulkhairi da nufin kwana ɗaya za tayi, in mayar da ita, yan’uwanta sun je Kaduna sun yi mata jere.Ita kanta kullun korafin da take min kenan,sai iyayenta da ƴan’uwanta su ji ta shiru daga tafiyar kwana ɗaya,ki yi haƙuri Haj ayi mata biki irin na al’ada in yaso bayan ta tare a Kaduna sai in dawo miki da ita.Da alama dai Haj bata da niyyar fahimtar sa, lallashinta ya shiga yi ya ce ya bar ni.Kudade ya ciro ya ajiye mata, sai muka fito sai da ya shiga motarsa ya leƙo da kansa “Kina ji na da Haj? auren nan kamar ita nayi mawa”.Ni dai murmushi nayi.
Na cigaba da zama a ƙanƙara, a matan yayyensa mun fi shiri da matar yayansa wanda yake bi mawa yaya Abubakar, uwargidansa sunanmu daya da ita, amma ita Umma ake ce mata ni kuma ina kiranta maman ummi sunan yarta ta farko, ɗanta na biyu me suna Faisal ba shi da ƙyuya ko’ina zan aike shi dan haka ni kuma komai zan ci da rabonsa sanadin sa kauna ta wanzu tsakanina da ita.Sai na lura a gidan matar babban yaya ta biyun wadda yaranta ke kira da Amma da sannu sunan ya bi bakin kowa, ita ke faɗa aji a gidan ko a wurin yaya babban ita ce mandiya.Ɗakinta nan ne majalisa ta yan gidan, ni dai ban zuwa haka ma maman ummi, domin amaryar maman ummi usaina yar dakin Amma ce.Amma mutumniyar maradun ce ta jihar Zamfara, tana sayar da magungunan mata wanda idan ta je garin su ta kan saro ta taho da shi.
Bayan tafiyar Tahir nayi wanki, shanya ita tafi kaini tsakar gidan, ina cikin shanya naji yarinyar Amma tana ce min “Aunty Innarmu tana kiranki”. na ce ina zuwa sai na cigaba da shanyata, sai da na kammala sai na isa ƙofarta nayi mamakin rashin samun kowa a ɗakin, na shiga da sallama ta amsa tana min fara’a, na soma gaishe ta ta ce “Haba ummulkhairi sai ka ce wata baƙuwa zauna man”. na zauna ina kallon abubuwan da ta baza a gabanta.
Thank you
Update pls