Skip to content
Part 20 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Sai a na ukun nayi ta maza. Ban haɗu da kowaccen su ba har na taka step zuwa saman, da keyn nayi amfani wurin buɗe kofa wani wani kasaitaccen niimtaccen falo na soma taraswa sai dakin barci da bathroom ke manne cikin sa.

Nayi yan kakkabe kakkabe da goge goge, sai na canza zanen gado na fesa room freshener, kafin na shiga bathroom, shi ma na daɗa tsaftace shi, na fito na rufo ƙofar. Na kusa saukowa Halima ta shigo da alama daga wurin aiki take dan sanye take da kayan malaman jinya riga da wando sai dan guntun hijab iya kirjinta, tana rataye da jaka.

Gabana ya buga dam! dan duk cikinsu na fi ganin jin zafina a ƙwayar idonta, sannu da zuwa nayi mata, wucewa kawai tayi tana juya jiki, kitchen na shiga amma sai na shiga tunanin me zan dafa, anya idan nayi tuwo wadannan ƴan iyayin za su ci? wata zuciyar ta ce “Ba dai mijinki na so ba sai ki ƙi yi mishi dan wasu.

Da wannan ƙarfin gwiwar na yi tuwon Semo miyar kubewa danya, dan na ga kubewa fresh a kitchen din, na yi pepper soup, sai kunun aya na haɗa ƙarshe.Sai da na kammala komai nayi wanka sai nayi salkah. yau kwalliyar ta musamman nayi na sa ƙamshi sosai a jikina, riga da skirt na sa na English wear, rigar fara skirt din pink rigar ta kama ni, hijab na sa iya gwiwa na fito falo
dan yanda na ga suna yi me girki kan zauna ta jira shigowar megidan.

Zama nayi idona na kan TV da ke ta aiki, amma gaba ɗaya na gundura da zaman, dan bana so wata cikin su ta fito ta same ni, ina nan zaune kamar wadda ta yi ƙarya jin fargaba ta yi min yawa na tashi na gudu daki.
Na zare hijab din na zauna zan soma latsa wayata, ya turo kofar bakinsa dauke da wata makalallar sallama, na amsa nayi masa sannu da zuwa “Ya ba ki zauna na shigo ba?
Ya jeho min tambaya, shiru nayi sai ya miƙo min hannunsa “Mu je ɗakina”.

Bayansa na bi har saman, sai da ya yi wanka muka sauko, sun hallara idonsu kafe kanmu ni nayi saving din megidan na ɗaga manshanu “Kana so in zuba maka?
“So kai, ko kin manta Hajiyata bafulatana ce?

Na zuba mishi su kam sai kallon tuwon su ke suna taba baki, tunanina ba za su ci ba, sai ga shi kowacce ta cinye wanda ta zuba, aka zuzzuba pepper soup shi wannan kam tasa aka gama da shi.

Har Ogan na tambaya akwai saura zai ci da safe. Na ce sai dai idan Allah ya kaimu safiyar in yi mishi wani. Na zuba mishi kunun ayan ban jira me aiki ba na soma tattara kayan,

Da mug din ya miƙe zuwa kan sopa labaru yake kallo a CNN. Sai da na gama kwashe komai sai na dawo na zauna ina latsa wayata, dan yau ban ga ta gudu daki ba, daga ni ke da Ogan.

Goma daidai na tashi na wuce ɗakina, kayan jikina na cire da ƴan kunnaye na rage daga ni sai bra da wani wando baƙi skin tight da ya lafe da fatar jikina.

Gaban fridge na wuce Kankanata wadda na zuba ma madarar ruwa peak na ɗauko abin da na wuni ina sha kenan gyaɗata da na sarrafa ita kyakykyawan sha nayi mata tun safe.

Na fara shan Kankanar kenan Tahir ya shigo “Lafiya kika dawo nan”
langabe kai nayi “Barci nake ji” “To barci anan za a yi shi?

Ya miƙo min wayarsa Haj za ta yi magana da ke na miƙa hannu na karɓa daidai lokacin da kiran ya shiga Hajiyar ta daga bata tsaya amsa sallamar da nake mata ba, ta shiga korafi.

“Lafiya Ummulkhairi duk yau an kasa samunki duk wanda na ce ya kira min ke, sai ya ce wayar ba ta zuwa.”

“Wayar ce yau take bani matsala am….

“Shi ne ba ki ba shi an gyaro ba? ko a sawo wata, ina Sodangin?

“Bai sani ba Haj, ai yau ne.”

“To ba shi, in gaya mishi, a nemo wata ko a gyaro.”

Murmushi nayi “To Haj”

Sai na miƙa mishi,

Sun ƙare wayar ya juyo inda nake “Me ya samu wayar?

Na ce “Daukewa take”

“Shi ne ba ki gaya min ba?

Na ce “Yau ai ta fara”

“Kawo in gani” ya amsa ya gama daddanna ta ya miƙo min.

“Ki wuce ɗakina” daga haka ya juya.
Na karasa yan kintse kintsena sai na saka hijab na fito,na rufe ƙofata, suna nan zaune inda na bar su, ban waiwayo ba har na shige.
Na fara barci na ji motsin shi, sai da ya gama komai ya rage hasken fitilar zuwa dream light ya hawo gadon, ba ka jin karar komai sai ta Easy da take ta aiki, jawo ni ya yi jikinsa, rada min ya yi “Wa ya ce yau za ki yi barci? za ki rama tsawon kwanakin da na ɗauka ba ki.”

Wani kishi na ji ya taso min,,jin maganarsa mutumin da ke da mata har biyu amma yake wannan maganar.

Ajiyar zuciyar da yake ta fiddawa yasa nayi tunanin ko da gaske yake kewar tawa da ya ke faɗi ya yi? tsawon lokaci muka dauka yana nuna min kaunarsa a gare ni, daga bisani mun yi barci.

Asubar fari na ji ya zare jikinsa, sai da ya gama shirin fita Sallah sai na sauko, wanka na yi haɗe da alwala, anan dakin nayi Sallah, sai da nayi karatun Alkur’ani ina Azkar ya shigo, gaishe shi kawai nayi na sauko ƙasa, break fast na shiga haɗa mishi. Ina ciki kowacce ta shigo neman abin da za ta ci ta wuce wurin aiki. Farfesun kayan ciki nayi masa iyaka dan wanda zai ci, sai ruwan tea na soya chips da ƙwai, kan dinning na shirya mishi komai na haura upstairs na samu yana shiryawa, tare muka sauko na bar shi yana karyawa na wuce dan in shirya.

Ina kwalliya ya shigo ya ce min “Shi ya shirya zai wuce.”

Addu’a nayi mishi ya ce “Ba za ki raka ni ba?
nayi narai narai da fuska.

“Ban sa kaya ba” agogonsa ya kalla “Ina jiranki.”

Doguwar riga baka me adon duwatsu a wuya da hannu nasa, na ɗauko hijabi, ɗago idonsa ya yi daga kan wayarsa, “Wannan hijab din, kullun kamar kin zo baƙunta na meye?maida shi nayi jin maganarsa ya ajiye min kudi sai ya juya.

Ina biye da shi har gaban motarsa, “Me zan taho miki da shi?

Murmushi nayi “Komai ka kawo min na gode”
ya ja motar, motarsa na bayan ta Halima suka bar gidan.

Na kama hanya dan komawa ciki “Kar ki yarda ki zama ƴar tsaron gida” maganar Baƙuwa Haj Shema’u ta faɗo min, wasu maganganun fa da ta gaya min akwai ƙamshin gaskiya a cikin su, sai dai wasu sun fi kama da zuga, idan na biye mata za ta kai ni ta baro.

Jin na kusa karo da mutum yasa ni dawowa nutsuwata, Basma ce cikin sauri take tana rike da takardu da makullin mota.

Nayi aikina na kwana biyu. Ina shirya mishi abinci me rai da lafiya da safe da rana haka nan da daddare.

Ranar da na fita ya kai ni gidan Kawu Attahiru, can na wuni har sai yamma sosai ya je muka dawo tare.

Wata rana ya dawo aiki muna cin abinci, kamar yanda muka saba. Wayata tayi ƙara sabuwa ce fil ya kawo min, tun bayan da muka yi waya da Haj.

Ganin sunan me kiran yasa gabana bugawa, har rawa hannuna yake na daga kiran, gaishe ta na yi tayi dariya “Ban ji ki ba Ummulkhairi, magani ya yi kuwa? ya amsa zai nemo miki makarantar? ta jero min tambayoyin da suka sa na ji kamar zan saki fitsari, na saci kallon inda yake, cin abincinsa yake kamar ma bai san ina waya ba, na ce “Ban tambaya ba tukun” ta ce “To me ya hana? kar fa ki sake ki zama sakarai cikin kishiyoyi, ki yi kokari.

Yanzu ma kiranki nayi in ce miki tafiya ta kama ni, mahaifiyata ce bata da lafiya, zan je in dubo ta zan ɗan kwana biyu, idan na dawo zan shirya ki tsaf sai kin tsere ma wadannan matsiyatan.”

Wani irin kaduwa cikina ya yi, ji nake kamar Tahir na jin abin da take cewa. Nayi wa mahaifiyarta fatan samun lafiya, tare da mata Allah ya tsare. Sai na ajiye wayar na dawo inda na tashi sai dai na kasa cigaba da cin abincin, sai Ginger da na hada nake ta faman banka wa cikina, turo ƙofar da aka yi yasa muka kai duban mu wurin Halima ce cikin uniform take “Ina son ganin ka daga ka san ni ke da girki ba ita ba.”

“To ki je ina zuwa” ya fadi ba tare da ya bar cin abincin da yake ba, ta juya ta banko ƙofar.

Sai da ya gama ya fita ashe tana kofar dakin, muryarta na ji na fara bambamin masifa tun bai tayata ba , har ya soma maida martani tsiyar bata ƙare ba har sai da ya fita ya bar gidan.

Ɗakina ta dawo kashedi ta min da in kiyayi Tahir ballantana har in ba shi abinci matuƙar ba ranar girkina ba ce.

Har dare bai shigo ba ita ma bata yi abincin dare ba.

Ni dai nayi zuru a daki, komai ban ci ba kuma tsoro ya hanani fitowa in dafa, sai sha dayan dare na ji shigowar motarsa, Komawa nayi na kwanta ina so barci ya ɗauke ni.

Washegari sai da suka fita na fito nayi girki, na boye abu na na ci ni kaɗai. Ko da ya shigo tambayata ya yi ban yi girki ba ne na ce “E” ya ce “To me zan ci? na ce zan fita in yi, ya ce ko ban da lafiya na ce Aa.

Ƙarfe uku ya kira wayata ya ce In same shi falo, hijab na sa sai na fito, su duka ne, fuskantar mu ya yi “Wace magana ce kuka zo da ita? shiru duka suka yi har sai da ya maimaita.

Sannan Basma ta ce “Mun ce bamu yarda tana ba ka abinci a ranakun girkinmu ba”
wani kallo ya watsa musu wanda na tabbata kowacce ta shiga hankalinta “Meye dalilin da zai hana ni cin abinci idan tayi?

“Saboda ba hakkinta ba ne” nan ma Basman ce ta ba kuma ba da amsa.

“Good, ku masu hakkin me ya hana ku zama ku bani abincin?

Cikin gunguni ta ce “Mu ba aiki muke zuwa ba.”

Halima dai da alama ba su shirya da ogan ba, dan ko zamanta a rabe tayi shi ba da ba da take zama tana hura hanci.

Ba zai yiwu ina da mata har uku ba, amma ina yawon sayen abinci kullum, kamar wani gwauro. Wadda kuma ke yi ina ci kuna ganin ba a yi muku adalci ba, to kowacce ta bar zuwa wurin aikin ta zauna ta kula da aurenta.”

Kowaccensu ta zaro ido suka bi shi da kallo, dan yana gama fadi miƙewa ya yi ya haura sama.

Ranar ni zan karbi girki. Kitchen na shiga, megidan dai bai kuma bi ta kan kowa ba yana sama Sallah kawai ke sauko da shi, har na gama girki na yi wanka ba motsin kowa zaman da suke yi wanda dama na fi danganta kishi ke sa su yin sa yau kowacce ta nabba’a ɗakinta.

Na ɗauki abincin zuwa sama, ban same shi falon ba sai na wuce ciki yana kwance daga shi sai gajeren wando ya tallafe keyarsa da hannayensa fuskarsa na kallon sama, ganin bai ko motsa ba tun shigowata yasa na zare jallabiyar da ke jikina sai na isa zuwa inda yake pillow da yake kai na sa hannu na zare ya yi firgigit ni kuma na yi maza na maye gurbin pillow da hannuwana sai na sa kansa a ƙirjina na rungume shi da hannayena, hakuri na shiga ba shi da wata murya da ban ma san ina da ita ba.

“Tun da na taso Ummulkhairi ban taba sha’awar tara mata ba, amma ya zan yi abin da aka rubuta kenan a allon kaddarata, yau an wayi gari matana uku, bana son kowace ta zarge ni da yi mata rashin adalci.”

Jijjiga kansa nake ina kuma taba duk inda na san zan motsa shi, har na samu nasara ya fara maida martani sai da ya kamu sosai muka yi soyayyarmu.

Ganin da ya yo wanka ya dawo zai kuma kwanciya na shiga mishi magiya har da yar kwallata ya zo ya ci abinci, mun fito falon na zuba mishi ya ci abinda ya sa ni jin daɗi daga bisani mun kwanta.

Da safe da na gama haɗa abin kari na hau sama samu na yi ya shirya muka sauko ƙasa tare, abin da yaso bani dariya kowacce zaune muka same ta cikin shirin tafiya aiki, ganin su yasa shi shan mur, ya wuce dinning ni ma ganin sun ya sa na mike zan gudu dakina, wani kallo ya min na koma na zauna muka karya tare, da daidai suka sulale kowacce ta nufi ɗakinta.

Wasa wasa fushi sosai yake da matan nasa, aiki kuma ba wadda ta kara zuwa kamar yadda yasa doka, wurin Kawu Attahiru suka kai karar sa, aka kira shi ya je ya same su.
Dole Kawun ya sa shi ya janye dokar hana su fita aikin su, kamar yanda suka rokai, shi ma kuma ya ce lallai duk wadda ke da girki sai ta ba shi abin karyawa kafin ta fita, ta dawo kuma ta ba shi na rana.

Ranar wata Asabar na tashi da amai da jiri.
Sai da ya shigo ya same ni a hakan, take ya ce in shirya mu je Hospital.

A hankali na shirya ya gaya wa matan nasa abin da kenan,sai muka fita. Wata asibiti me zaman kanta ya kaini, yanda ma’aikatan ke ba shi girma, suka karɓe ni a mutunce yasa na gane wurin zuwan sa ne. Family card ɗinsu aka fiddo aka kai ma Dr tare muka shiga likitan wanda ba Bahaushe ba ne hada miƙewa tsaye ya yi dan nuna girmamawa, suka gaisa da Tahir ya juyo gare ni muka gaisa. “Meke damun Madam?

Ya tambaya da bagwariyar Hausarsa na fadi jiri da amai, ya cigaba da min tambayoyi ina ba shi amsa, Nurse ya kira ya ce mu je ta debi jinina a gwada yanzu a kawo mishi result, har aka diba na dawo suna zaune suna taba fira, bayan wani dan lokaci Nurse ta dawo ɗauke da sakamakon gwajin likitan ya karba ya duba kafin ya ɗago yana ma Tahir murna da albishir.

Ya mishi murna da albishir ina da shigar ciki.
Hamdala ya shiga yi da roƙon Allah ya inganta mishi.

Likita ya yi rubutu ya ba Nurse din takardar, ta karba ta fita cikin sauri. Tahir ya juyo inda nake wani kallo yake jifana da shi wanda yasa kunya dabaibaye ni, na kudundune cikin hijab ɗina, can sai ga Nurse din ta dawo da magunguna likitan ya karba kafin ya mika wa Tahir, musabaha suka yi har ya mike ban motsa ba, sai da ya ce “Ko nan zan bar ki? na miƙe ina sussunnewa. Da muka shiga mota na sha maganin, sai ya tada motar muka bar harabar asibitin.

Ya hau kwalta hankalinsa na kan titi ni kuma ina satar kallonsa, wani farin ciki na ratsa zuciyata, ina ma Allah tasbihi tare da gode masa, cikin rahamominsa ga bayinsa ya bani Tahir a matsayin miji.

Ko a mafarki ban taba tunanin samun namiji me tsada irin sa ba, sanye yake cikin wani lallausan yadi fari hular kansa tangaran wadda ta tsaya a kanshi take fidda sheƙin da ke bayyana ita ɗin me tsada ce, agogon invicta daure a hannunsa.

Dan kidan da wayarsa ta ɗauka ita ta katse min tunanin da na lula, bai ɗauka ba hannu kawai ya kai ya amsa kiran, “Yallabai barka da hantsi” muryar namiji ta fito daga cikin wayar, “Yawwa Usman an tashi lafiya?
Lafiya lau yallabai, dama zan ce har yanzu ba ka shigo ba” agogon hannunsa ya kalla, “Anya Usman zan samu shigowa yanzu? Daga Hospital nake”. “Ash sha yallabai, waye ba lafiya?

“Iyali na ce” Addu’a mutumin ya yi ta fatan samun sauƙi, ya kashe wayar. Sai kuma na ji ya ja tsaki, ya sauka titin da take ya sauya hanya.

Wata tafkekiyar plaza ya tsaida motar.
Gini ne hawa biyu, har ya bar ni ciki, sai kuma ya dawo ya buɗe ƙofar, “Fito mu je” ya bani umarni, “Ko kina jin jirin? na girgiza kai, sai na bi bayansa a hankali. Wani tafkeken wuri ne, da aka loda yadikan hijabai na miliyoyin nairori, masu kula da wurin suka yo kanmu suna miƙo gaisuwa, wanda na lura shi ne Babba shi, suka koma kujerarsa yana nuna mishi takardu da computer da ke gaban tebur ɗinsa, sai dubawa yake, suka gama lissafin su ina inda nake zaune ina sauraren su, Tahir ya juyo ya dube ni “Sorry ko Ummulkhairi”. murmushi nayi mishi, ya mike yana duban Manager “Amma Usman ba ka da kirki, in kawo maka Amarya har shagonka ka kasa bata ko hijab daya.”

Dafe kansa ya yi da hannunsa, “Tuba nake Amaryarmu” ya fuskanci Tahir, “Yallabai ko za mu shiga ta duba ne? “Bata da lafiya Malam, ba za ta iya wani zaban hijab ba.”
Daga haka ya tako zuwa inda nake duƙowa ya yi gabana “Me ya ba ki sha’awa a wurin nan in ɗauko miki? Kai na girgiza ya ce “A’a fa, kar fa ki ce nayi miki rowa.”

Murmushin jin zancansa nayi, wasu hijabai sakar ƙasar Jordan da suka burge ni, na nuna mishi, kowace kala sai da aka daukar min daya, Usman ɗin ya yi mana rakiya har inda Tahir ya ajiye mota.

Mun shiga har ya soma tashin motar, wani matashi ya karaso cikin sauri “Haba boss, kaina bisa wuya, yanzu nake jin ka shigo, amma mu ba a leƙo mu ba, kuma cikin satin nan nake son shiga China, ga kayanmu da suka taho ta jirgin ruwa jibi za su iso” Tahir da ya zuba mishi ido tun soma maganarsa ya ce “To yanzu ya kake so a yi?
ya ce “Ka daure boss mu koma”. girgiza kai ya yi “Ba ni kaɗai na shigo ba malam, sai dai idan Allah ya kaimu gobe.”

Sai sannan hankalin matashin ya kai inda nake zaune, zagayowa ya yi inda nake ya gaishe ni cike da mutuntawa, sai ya koma wurin Tahir, “Sai goben Boss.”

Ta da motar ya yi sai muka bar wurin.
Muna tafe shiru babu mai magana, har muka shiga wata unguwa da ya ce min sunanta Tudun wada, ya tsaya daidai wani gida ginin da, sai dai na bulo ne shafaffe da siminti, hada dakali guda biyu a kofar gidan. Ya fita kafin ya min izinin fita, zauruka biyu muka wuce kafin muka tarad da tsakar gida wanda yake malale da siminti a share tas, kai ka ce babu dan adam ɗin da ke taka shi. Sallamar da yake ta fiddo da wata dattijuwa, “To to ka zo? ta faɗa tana takowa inda nake “Shigo kishiyalle, daga dai na san ita ce Amaryar tawa.”

“Amaryarki ko dai tawa , baki ta dafe “Au tsiyar da za ka yi min kenan dan na kira kishiya da tawa? Shigo kin ji ki ƙyale Sodangi” na bi bayanta, har cikin dakin wanda yake a gyare fes yana fidda ƙamshin turaren tsinke. Kamar ba na tsohuwa me irin shekarunta ba.

<< Wa Gari Ya Waya 19Wa Gari Ya Waya 21 >>

1 thought on “Wa Gari Ya Waya 20”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.