Skip to content
Part 24 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Don haka jikinsa ya yi masifar sanyi, ni kuma na soma magana cikin kuka. “Ka rabo ni da iyayena, ka kawo ni uwa duniya ka banzatar da ni.Kana saɓa ma Ubangijinka, duk da cewa ka sani, amma ka take, Ubangiji ya yi maka ni’ima, ya baka wadata ka mallaki mata har uku na sunna, amma godiyar niimominsa a gare ka, shi ne ka saɓa masa. Kuma kar ka ce ko ina daga cikin mata masu binciken wayar mazajen su, canjin da na gani a tattare da kai shi ya ingiza ni ga yin binciken.

Gobe in sha Allah, zan nemi hanyar garin mu zan bar ka ka ji dadin cin karenka ba babbaka. Ina zuwa nan na miƙe na soma sauke kayana, cikin karfin hali dan ba wani karfi ne da ni ba, jikina ba kuzari sam.Takowa ya yi daga inda ya ƙame tun daga fara sauraron kalamaina, kunya ce ke ɗawainiya da shi, ji nayi kawai ya riƙe hannayena na waiwayo na balla mishi harara da jajayen idanuwana da kuka ya rinar da su, hankalinsa ya ji ya ƙara tashi da yanda fararen idanuwanta suka koma, dan da ganin idanuwan ba yau ta fara kokawa da su ba, rashin kulawarsa ga al’amarinta yasa bai fahimci halin da take ciki ba.

Sakin hannayena ya yi ya ja baya kan gado ya zauna, dafe da goshinsa kafin cikin wata murya wadda ta fi kama da ruwa dan taushi ya shiga bani haƙuri, da alkawarin ya daina, karo na farko a rayuwarsa wanda ya tabbatar rudin sheɗan ne ya ingiza shi, amma ba halinsa bane. Ban ce mishi kanzil ba, ina gama haɗa kayana wuce shi nayi na kwanta, jin surutansa na kare kai sun kara min ciwon kai da nake ji kamar kan zai sauka.

Saukowa nayi daga gadon na fice dakin, dakin da ba komai sai carpet da labulayya na shiga na murza key. Na kwanta nayi matashin kai da hannuwana ƙirjina na min suya, ina jin muryarsa yana kiran sunana. Nayi nayi in tuna addu’ar da zan yi dan samun sauki, amma na kasa tuna komai daga cikin dimbin addu’o’in da na sani.

Sai gefin Asuba barci ya yi awon gaba da ni, muryarsa ta farkar da ni yana kiran sunana, ganin haske ta jikin labulai yasa ni fahimtar ba karamar makara nayi ba, cikin rashin kuzari na miƙe, bathroom din da ke cikin dakin na shiga na daura alwala, da na fito rashin hijab din da zan sa in yi sallah ya tilasta min bude kofar, yana tsaye hanya ya bani na wuce, na je nayi Sallah, idarwata jakar da na hada kayana na janyo, ja nayi na tsaya jin kofar gam! an rufe ta ta baya kan kujera na zauna na shiga wani sabon kukan yana saurarena, shi ya shiga kitchen ya daho min tea dan shi kadai ya iya dafawa, ko kallonsa ban yi ba, har sha daya na safe muna zaune, na gane ba ko Office ba za shi ba.

Knocking din da ake yasa shi tashi ya buɗe, Laila ce, ganinsa gaisawa suka yi, ya ce ta shigo ta ce,

A’a tana son magana da ni ne, ina jin su dan haka tasowa nayi, ya dawo ciki, tana tsaye riƙe da kwando, kallona tayi da murmushi a fuskarta “Haba Mmn twince, wannan fuska, ina ga babyn nan shi da kuka ya zo mana “Murmushin yake na saki ita kuma ta sha mur tana hararata, cikin rage murya ta ce,

“Oga na gida bai fita Office ba kike zaune haka jemai jemai ba ƴar kwalliya da kamshin da daga ka doso wurin zai tafi da kai, sai tsofaffin matansa sun karbe miki shi. Dan guntun tsaki na ja “Ke ta miji kike, ni duniyar ce gaba ɗaya bata min daɗi.” Ta rausayar da kai “Sai hakuri, shi ciki kowanne da yanda yake zuwa. Faten acca nayo miki da naji kina cewa bakinki ba daɗi.” Na amsa ta godiya ta wuce tana cewa “A daure a dau wanka da kwalliya Hajiyata.”

Da na koma ciki wankan nayi, wanda a yanzu wahala yake min, mai kawai na murza na zura doguwar riga.sai na dawo falon.Sa’a kawai nake nema in cika wa rigata iska, na sha faten na koma na kwanta kan kujera.A takaice ranar a nan muka wuni yana gadina.

Bai fita ko nan da can ba. Washegari ya kulle ni ta baya ya nufi wurin aiki.Da Laila ta zo tana knocking ƙofar na zo na ce ta zagayo ta window, ta zagayo ta ce “Lafiya?Na cije lebe “Kulle ni ya yi” murmushi tayi har tana daga gira “Mutanen nan salon soyayyar ku na burge ni” ta fada cikin salon basarwa na wayayyu, dan na san ta fahimci akwai matsala “Abinci na kawo miki.”

Na buɗe window ta miko min, na koma na ci. Da la’asar ya shigo, ya maida kofa ya rufe. Ban mishi magana ba, shi ma bai min ba, na lura ma kamar nauyi na yake ji. Da daddare yana falo ina ɗaki, na ji wayarsa na ƙara, ba a dauki lokaci ba ya shigo “Ga Haj tana son magana da ke.” tsayawa ya yi kaina kila yana tunanin zan faɗa mata kamar yanda na saba gaishe ta cikin nutsuwa da girmamawa haka na gaishe ta, ta ce “Tun jiya nake sa wa a kira wayarki, sai a ce min kafiran nan sun ce a kashe take” nayi murmushin jin maganar ta, (wayar tun jiya Tahir ya dauke ta)amma sai na ce mata “Ruwa ta fada.”

Ta ce “Ash sha shi ne ba a nemi wata ba? Na ce “Za a gyara Haj” ta ce “Kuna lfy ko? Na ce “Lafiya lau muke Haj” ta ce “Idan Sodangi ya zo zan ba shi magani ya kawo miki na sammu ne, dan yanzu mutane ba tsoron Allah suke ba, sai ka tashi tsaye da neman tsarin jikinka, da kuma na zaƙi.” Na ce “To Haj, Allah ya kara girma.” Na tambaye ta mutanen gidan, sannan nayi mata barka, dan maman Ummi ta faɗa min Usaina ta haihu.

Mun gama wayar na miƙa masa a bar sa, ya juya ya fice dakin. Na kai hannuna na shafi cikina, ni ma dai bana in Allah ya so zan riƙe nawa ɗan, zan samu me ɗebe min kewa, duk da ba wani uban girma ya yi ba na ciko, ramar da ta addabe ni ta sake ni na murje. Sai kuma na koma jin dadi na dacen da nayi da suruka me sona, mu’amalar da take yi da ni bata Suruka da Surukarta ba ce, mu’amala ce irin ta uwa da ɗanta. Kwanciya na gyara na lumshe idona.

A falo ya kwana, ni kuma na kwana a daki, yana gudun ya shigo in tafi ɗayan dakin in kwana a ƙasa. Washegari ma lokacin tashin sa office nayi sai ga shi ya dawo, nan ma bai ƙara fita ba, kamar hadin baki irin lokacin da Haj ta kira waya sai ga kiran Ummata, duk kararta ta kasa jure rashin ji na har na kwana biyu, ga halin da nake ciki, dan Hafsa na ba labarin ina da ciki ita kuma ta taka har gida ta fada musu. Ita ma dai gaisawar muka yi, na ce mata muna lafiya, dan tausayinta da nake ji, bata da juriya kan matsala idan ta same ni, ko bata yi magana ba ramar da za ta shiga yi za ta fallasa abin da ke cikin ranta.

Ballantana wannan matsala da nake ciki ba zan iya fallasa ta ga kowa ba, dan idan na fadi na asirin mijina na tona, na san dai tun da na shekara garin nake ma Tahir nacin ya kai ni gida, shi kuma sai ya ce ba yanzu ba sai na warke wannan ramar ta sake ni, dan ba zai kai ni yana laluben amsar da zai bayar na zargin da za a yi masa. Mun ɗauki tsawon sati guda a haka. Office kadai ke fitar da shi sai Sallah, har na fara murna kila Allah ya shirye shi, sai dai ranar da muka cika kwana tara a haka, ya shiga wanka sai na saci wayar tasa in ga da gaske ya daina din, sakonninta ne kala kala tana mishi magiyar ya zo gare ta, amsar da na ga ya bata Madam ɗinsa ce ba lafiya ko zai zo sai ta warware.

Ta ce to ta zo Office ta same shi? Ya ce A’a” kalaman fitsarar da take mishi ya nemi ta turo mishi ba kalaman kaɗai ba hada nude picture ɗinta ta turo , ai ban tsaya tantance abin da nake ganin ba na rufe wayar, na kwanta a falo ina sharar hawaye.Har ya fito ya shirya, damunsa ake tayi da kiran waya daga wurin aikinsa, sai tsaki yake zabgawa dan ya makara, garin sauri ya manta bai rufe ni ba, na tashi, sai na ga keys a jiki, wani farin ciki ya lullube ni, na koma ciki na suro jakata, wadda dama har yau ban kwance kayan ba.Hijab na sa sai na fito, na daɗe tsaye ina kallon flat din Laila, kallo irin na karshe, anya idan na bar garin nan ban ma Aunty laila sallama ba nayi wa kaina adalci? Nayi abin da ya kamata dan halak ya yi?

Cigaba da tsayuwa nayi ina tunano alheran Laila a gare ni.Can wata zuciyar ta rada min “In dai kina son barin garin nan, to ki hanzarta bacewa a wurin nan kafin ta gan ki, dan kin san tana ganin ki gudun nan da kike yunkurin yi zai zama tarihi.

Takawa nayi da sauri a kokarina na bacewa daga wurin, tafiya sosai nayi kafin in samu dan acaba, ko a Dutsinma ban faye hawan sa ba, haka na haye na faɗa mishi ya kaini inda zan shiga motar Kaduna, muna tafe ina sakawa ko ya zan yi idan aka shiga Kaduna cikin dare.Inda wata taxi ke lodi wani dan Union ya kaini, akwai mutum uku a ciki, wanda na nakalci yan kasuwa ne, mutum ɗaya suke jira ya fito daga cikin kasuwa. Sai zuci zuci nake mutumin ya fito dan yanda gabana ke faduwa, hamdala nayi ganin isowar mutumin, an karbi kuɗaɗen mu, cuku cukun direbobi da yan Union shi suka tsaya yi, na jingina kaina jikin kujerar na lumshe idona, ina me jin farin cikin zan ga Babana da Ummata, da ƴan’uwana hada Hafsata.”Ga ta nan Yallabai” Muryar namiji ce ta ambaci hakan gabana ya yanke ya fadi, nayi saurin bude idona, ban sauke su kan kowa ba sai kan Tahir da ke tsaye ya harɗe hannayensa a kirji.

Shi ma ni yake kallo, cikin farin glass ɗinsa, a kallon da nayi masa na fahimci ransa ya yi mummunan ɓaci. Dan kamashon da ya karbi kayana ya kuma rako ni shi ke yi wa Tahir wannan maganaar. “Lafiya? direban ya zo yana tambaya, “Wannan baiwar Allar, Yallabai ya zo nema.”

An yi cirko cirko dan Tahir ya ki magana ni kuma ban fito ba, Direba ya shiga mazauninsa, Tahir ya zagaya dan ni daga karshe nake sai dai ji nayi kawai ya ɓalle murfin motar, hannu yasa sai ya janyo ni waje take na soma hawaye Direba ya fito “Yallabai ya za ka ciro ta, za mu tafi? Dan kamashon ne ya matso ya ce,

“Matarsa ce, tafiya za tayi bai sani ba” “Subhanallahi”. In ji Direba, take sauran mazan da ke wajen suka dauki salati wani cikin su ya ce “Sai hakuri zaman aure, baiwar Allah”.Ni dai sai share hawaye nake na ki bin Tahir, dan kamashon ya ciro jakata, “Yallabai ya za a yi da kudin motar da ta bayar? Ya ce “Ta bar maka” Direba ma ya zaburo “Alh yanzu sai na ƙara zaman jiran wani fasinjan? Wadannan bayin Allah daga Kaduna na dauko su, mutum ɗaya zan cika mu dau hanya. Hannu Tahir ya zura aljihunsa kudade ya ciro da bai tsaya dubawa ba ya mika wa dan Union, ya kama godiya kamar zai ari baki, “Mu je Malama, Tahir ya ce min yana kara daure fuskarsa, hannuna na ji ya fincika ganin bani da niyyar bin sa ta lalama bai tsaya ko’ina ba sai inda ya adana motarsa, buɗe ta ya yi ya tura ni ciki, ya maida ya rufe ya zagaya zai shiga, dan Union ya iso “Ga jakarta Alh” Boot ya buɗe mishi ya jefata ciki.

Da mugun gudu ya finciki motar masifa ya fara min, “Ke yanzu da an bar ki haka za ki isa har Kaduna zaune jikin kato?Sai kuma ya sassauta murya “Me ya ja miki wannan aikin? Kin san tun fitowarki mala’iku ke tsine miki, kin fito bada sanin mijinki ba? Meye ribar ki idan kika isa gaban iyayenmu da wannan bakin labarin, ke fa Malama ce Ummulkhairi memakon guduwa ki bar ni addu’a ya kamata ki taya ni, abu daya zan faɗa miki ki ji tsoron Allah, daga yau zan daina rufe ki, amma ki sani igiyar aurena na kanki, ban Kuma yarda ki taka ko’ina da ita ba.

Yanzu da kin samu nasarar gudu ba ki tunanin wani abu ya same ki a kan hanya? me za ki fada wa Ubangijinki.Sosai maganganun suka ratsa ni tsoron Allah kuma ya cika zuciyata, sai na ƙara sautin kukana.Da muka isa ma shi ya ciro ni dan kin fitowa nayi, har daki ya kaini ya kuma ki fita, na takura kwarai da zaman namu wuri ɗaya sai na tashi na shige bathroom, da na rasa abin yi sai na ji sha’awar yin wanka ta kama ni, Ruwa me zafi na haɗa na sa turarukan wanka masu dadin ƙamshi wanda har na manta rabon da in yi hakan na kwanta cikin ruwan nayi wanka me kyau, na wanke sumata, na sha mamakin yanda gashin ya kara haukan cika da tsawo, dama an ce gashi bai faye zuwa inda ake lailayarsa ba, ya fi hauka inda ba a damu da shi ba.Tawul na daura, na kuma daura karami a kaina ina goge sumata, ban damu da ganin Tahir a zaune bakin gado ba kan mirror na wuce, mayukana da na manta rabon da in shafa su na shiga shafawa, na fesa turare kadan, hand dryer na kunna ina busar da gashin kaina kafin na shafe shi da mayuka.

Tahir wanda ke zaune ya yi mugun dauke wuta, yaushe yarinyar nan ta koma haka? Wai ma watanni nawa kenan rabonsa da ita me ya dauke mishi hankali da bai lura da canzawarta ba, kirjinta ya dada bunkasa, ta kara ajiye mazaunai.Taku ya yi zuwa inda nake zaune ina ta je sumar tawa wadda ta sauka kan kafadata. Haɓar mutum kawai na ji kan wuyana ta mudubin muka haɗa ido na bata rai, hannuwansa yasa ya rungume ni, na shiga kici kicin kwace jikina, ya gwada min kashi ya jefa ni gadon, duk da rashin karfin jikina dambe na shiga yi da shi sosai dan kwatar kaina, shi kuma ya yi amfani da karfinsa ya gamsar da kansa da kyau. Kafin ya tsallake ni ya shiga bathroom, hawaye ne ke ta gudu bisa kuncina, har ya fito, tawul ya wurgo min “Ɗaura ki mike.”

Na bi tawul din da harara ina cigaba da kukana, cikin kukan barci ya yi awon gaba da ni, mafarkin da nayi jini na bin jikina yasa ni farkawa a firgice, sai zufa ke wanke mini fuska, jikina ko’ina rawa yake.

<< Wa Gari Ya Waya 23Wa Gari Ya Waya 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×