A tsanake na kammala ina jiran Aunty Laila. Tana zuwa wucewa muka yi, ita ke jan motar ina gefenta a Victoria Island iyayenta suke, tun daga shiga unguwar na tsinke, kafin mu shiga tafkeken gidan nasu wanda abin da za ka misalta shi da shi aljannar duniya.
Wuraren da muka riƙa wucewa dan isa falon babanta kusan rikicewa nayi, wato shi wanda ya gaji arziki daban yake ban taba tunanin arzikin iyayenta ya kai haka ba, dan yanda take simple wato dai shi wanda ya gaji arziki daban yake.
Kishingide muka same shi, na gaishe shi ya amsa min. . .
I love to read
Hakikanin rayuwa