Skip to content
Part 28 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

A tsanake na kammala ina jiran Aunty Laila. Tana zuwa wucewa muka yi, ita ke jan motar ina gefenta a Victoria Island iyayenta suke, tun daga shiga unguwar na tsinke, kafin mu shiga tafkeken gidan nasu wanda abin da za ka misalta shi da shi aljannar duniya.

Wuraren da muka riƙa wucewa dan isa falon babanta kusan rikicewa nayi, wato shi wanda ya gaji arziki daban yake ban taba tunanin arzikin iyayenta ya kai haka ba, dan yanda take simple wato dai shi wanda ya gaji arziki daban yake.

Kishingide muka same shi, na gaishe shi ya amsa min da fara’a, sai shi min albarka yake yi, kafin ta ja ni bangaren mamanta, bamu same ta a inda Lailar tayi zaton za mu same ta ba, wata cikin masu aikinta ta ce mana tana kitchen, can muka same ta ita da autar su su Laila Amira, Amirar tayo kan mu, ni ta rungume tana duban ƴar’uwarta “Wallahi Aunty, na gane ta, ita ce Aunty Ummunki.”

Nayi murmushin jin ta kira ni da Aunty duk da yake ba za mu wuce sa’anni da ita ba. Da ta sake ni sai na matsa kusa da mahaifiyar su, ita ma kamo ni tayi ta sa ni gefen jikinta, Oyoyo Ummun Laila.” ta ce min yayinda nake kokarin gaishe ta, Aunty Laila ta ce “Momi me kuke yi a kitchen? Murmushi tayi “Girki nake koya wa Amira” Dariya Aunty Laila tayi “Lallai ma autar Momi, har ma da kanta take koya miki? Momin ce ta ce “Ni ku bani wuri, kin zo da baƙuwa kin bar ta kitchen.”

Falo muka wuce, suka yi ta tarairayata. Har ɗakinta kafin tayi aure ta kaini, ina ta kara kakkaɓin halinta, dan ko inda take zaune take aure kai kasan arzikin gidan su ya fi ƙarfin nan. Kamar ta san tunanina, ta ce “Auren zumunci muka yi da Ahmad, Ummulkhairi” na kada kai. “Shi ɗin ya rasa iyayensa tun yana karami, a can garin su babanmu, Sumaila dake jihar Kano. Daddyna da Momi sun je garin, Momi ta gan shi ya yi matukar bata tausayi a matsayin shekarun sa ba shi da uwa ba shi da uba, mahaifinsa shi ne yayan Daddy, Momi ta roƙi Daddy su dauke shi su tafi da shi, lokacin Daddy yana aiki a Akure, suka tafi da shi Momi ta mayar da shi ɗanta dan sun jima basu samu haihuwa ba, an mayar da Daddy Sokoto aka haife ni, samuna bai sa sun rage komai daga kaunar da suke wa Ahmad ba, daga ni sai kanena Al’amin wanda na taɓa fada miki yana America yana karatu, daga nan sai auta Amira.

Mun tashi tare da Ahmad a gida ɗaya, kuma soyayya ta kullu a tsakanin mu, Momi ta so Ahmad ya karanci Business Administration saboda ya kula da harkokin kasuwancinta, dan ban da wurin da muka je da ke tana da wasu wuraren ma, har ma a Kano, amma Ahmad ya nuna ba shi da ra’ayi. Sai da na kammala Masters ɗina aka yi bikin mu.

Shigowar Amira yasa Aunty Laila yin shiru tana duban ta, “Amma kin ga da yake ita auta ce digiri na farko kawai ta kammala ta ce aure take so kuma su Daddy sun yarda za su yi mata. Cikin shagwaba ta narke fuska “Ai dai zan cigaba da karatuna.” Tare muka fito Aunty Laila ta jani bedroom din Momi, mun samu tana waya, ta ɗago ta dube mu kafin ta cigaba da wayarta, da hannu ta yafito ni na matsa kusa da ita, ta kamo hannuna ta zaunar da ni kusa da ita. Sai da ta kammala wayar ta kara matso da ni kusa da ita. “Laila ta ce min an yi miki abokiyar zama?

Na daga mata kai “To ki yi hakuri kin ji Daughter? Na kuma daga mata kai “Ki yi kokari ki kama mijinki, ba ruwanki da wasu kishiyoyi, ki gyara kanki.” Ta mike ta fita kafin ta dawo da wasu kaya a hannunta “Ga kaya nan nayi miki tsaraba ki yi ma in law ɗina kwalliya.” Ta miko min wasu turaruka.

“Wadannan na sirri ne dan maigidanki kawai za ki yi amfani da su, ki kasance kodayaushe cikin tsafta, ka da ki sake ya rika ganin ki a yamutse, sai girki ki iya girki me dadi, ko ta nan za ki sace zuciyar miji, kin ga Amirana aure za tayi, da kaina nake shiga kitchen Ina koya mata da na gane bata so.”

Haka tayi ta yi min nasiha wadda na ji dadinta kwarai sai godiya nake. A karshe Aunty Laila ta ce “Sana’a take son farawa Mommy, shi ne na ce ta bari ki zo mu nemi shawarar ki, dan ke ce business woman.” daƙuwa tayi wa Lailar ita kuma Lailar ta kama dariya, “Ina ganin ku haɗa hannu ku buɗe wurin sana’a guda, akwai ginin wata plaza da ake yi ina ganin zan ba ku shago Daya sai ku zuba kaya, sai ku je ku yi nazari ku ga me za ku sa ka.” Godiya muka yi mata.

Sai da ta fita Laila ta buɗe jakar da ta bani dogayen riguna ne guda huɗu, sai riga da wando su ma hudu, sai riga da siket su ɗin ma huɗu, duk kan su kuma haɗaɗɗu ne masu asalin tsada. Da muka yi shirin tafiya kudade irin kyautar su ta manya babanta ya bata ya ce ta riƙe min. Sai yamma likis na koma. Inda Aunty Kulu ta ce “Hala kin manta da wankan? Na ce “A’a Aunty” ta nuna min toilet “To yi maza ki shiga.”

Sanda na fito missed call din Tahir uku na samu na kira ya daga yana tambayata ina na shiga. Na ce “Wanka” ina jin ajiyar zuciyar da ya fidda “Har yau ba a gama sa miki tafasasshen ruwan nan ba? Kai na daga kamar yana kallona “Dama kira nayi in ji kin dawo.”

Na ce “Na dawo” ya ce “Ya yi kyau, kina lissafin kwana nawa ya rage in dawo.” Idona na runtse na dafe goshina “E” wata tambayar ya kuma wurgo min “Kin warke ko yanzu, ba ki jin wata matsala a jikinki? Na ce “Na warke Alhamdulillahi” “To ma sha Allah sai ki yi shirin tara ta.”

Ya katse wayar ya bar ni sake da baki, dan sosai na gano inda zancen sa ya dosa. Namiji kenan, kana da mata uku reras a gabanka amma kana harin wata, cikin ukun ma hada Amarya. Aunty Laila ta kawo min dinkunana wadanda suka yi matukar yin kyau har ba magana dan wuri ne na gwanaye, kuma kwararru. Aunty Kulu ma a nata fannin ta ƙara ƙaimi wurin gyara ni da kanta, gashina ma ya sha gyara, jikina kuwa har sulbi yake ban da kamshin da ya kama jikina, nayi wani irin kyau ga cikar jego.

Saura kwana biyu ya dawo na tafi gidana da masu aikin Aunty Kulu mata biyu, muka gyara wurina, an wanke abin da ke buƙatar wanki na gogewa an goge, komai an gyara shi tsaf har labulayya da zanen gado an sake. Ana gobe Tahir zai dawo, wata cikin masu aikin Aunty Kulu tayi min kunshi ina zaune zaman jiran ya bushe, wasu ƴanmata suka zo yin ƙunshi, wadda tayi min tayi wa daya a cikin su dan su biyu ne kuma ɗayar kawai za a yi wa. Sai da ta gama saka mata lallen ta fita, wadda aka yi ma wa ta dubi wadda suke tare, “Kin san nan wane gida ne ƙawata? Girgiza kai tayi dan hankalinta na kan wayarta. “Gidan su gayen nan ne da ya auri Latifa.”

Faduwar gaba na ji jin zancenta sai na ƙara kasa kunnena, idanuna na kan wayata dan kar su gane ina sauraren su, ita kuma saurin barin kallon wayar tayi ta fuskance ta, “Dan Allah? ya aka yi kika sani” “Ai na dade da sani” Ƙwafa waccan tayi “Allah ban yarda yarinyar nan ba abin da tayi wa gayen nan ya aure ta, da ganin su ma ajin rayuwar su ba iri daya bane, meye ban yi ba dan in samu ya dube ni kawai, ke bama ni ba gaba dayan mu duk wacce ke zuwa wurin na su wace ce bata yi fatan ya kula ta ba amma ba wacce ya taba kallo, sai ita daga zuwan ta, wai ya Aure ta.”

Ta ƙarashe maganar da takaici me yawa a muryarta. Ɗayar ta karɓe “Ke ita fa ba a garin nan ta san shi ba, nan ɗin ma da kika gan ta shi ta biyo.” Waccan ta buɗe ido “To! ita kuma daga ina take? “Yar Kaduna ce, a yanda na samu labari, tun bai yi auren fari ba take bibiyar sa tayi tayi su buga duniya ko da ba zai aure ta ba amma bata samu nasarar hakan ba kin dai ga gidan su, Babansa shahararren malami ne, maido shi aiki garin nan ta biyo shi tana da yan’uwa na jone jone ta zauna gidan su, tana barikinta shi kuma ta da ɗa manne mishi. Anan ne ma ta samu hankalinsa, kin ga har ta dace ya aure ta.

Cikin matukar jin zafi waccan ta ce “Ta dai taki sa’a asirinta ya ci.” Shigowar wadda ta sa mana lallen yasa su yin shiru, nawa ta duba ta ce mu je in wanke, na tafi na bar yammatan, zuciyata cike da tunani kan maganganun su. Da daddare muna zaune da Aunty Kulu. Nasiha take min game da zaman aure, har ma da yanda zan mu’amalanci kishiyoyina. Kuɗaɗe ta miƙo min, na dube ta dan neman karin bayani ta ce “Malam, ne ya bayar ya ce in saya miki abubuwan da suka dace, shi ne na ce bari in ba ki ko da abin da kike sha’awa sai ki saya in kuma babu sa abin ki a banki.”

Na ce “Yanzu dai ban da bukatar komai, ki ajiye kuɗaɗen a hannunki.” ta ce “Sam ki karbi abin ki ke ya ba” wasu kwalaben humra ta dauko guda biyu “Ni kuma ga gudunmuwa ta nan, Ummu na musamman ne, ki tabbatar duk sadda za ki yi amfani da su, za ki wurin megida ne, dan Namiji duk taurin kansa ya shaƙa sai ya biyo, ki adana su da kyau su ne makamanki.” Na ce

“To” kiran Kawu da ya shigo wayarta yasa ta tashi da sauri ta ce min tana zuwa. Kwanciya kawai nayi, zuciyata na jinjina tsantsan karamci na wadannan bayin Allah. Dan haka da safe da muka yi waya da Ummata, ta ce in hada ta da Aunty Kulu, godiya sosai tayi mata bisa karamcin su a gare ni. Na je nayi wa Kawu Attahiru bankwana gami da godiya,

Aunty Kulu ce ta raka ni gidana, bata jima ba ta ce min za ta koma dan tana da ayyuka, har ƴar ƙwalla nayi ta sabo da muka yi.

Ƙayataccen girki nayi wa megidan da abin sha, jirgin yamma ya biyo. Wanka nayi na sha kwalliya da riga da siket na wani haɗadden less me ƴan ƙananan hudoji, da duwatsu, kayan sun zauna jikina sun fidda halittata, na murza humrar da Aunty Kulu ta bani ana sallar magrib ya shigo dan haka alwala kawai ya yi ya nufi masallaci, ni ma sallar nayi na daɗa gyara kwalliyata. Har ya dawo na zuba mishi abinci, a lurar da nayi zuciyarsa a ɓace take, dan ya tsare gida, ƙara nutsuwa nayi tun da na tambaye shi yanda ya baro su, dan Ummata ta ce min har gidan mu ya je.

Kammalawar sa wanka ya yi da ruwan da na hada mishi, ina zaune falo amma gabana sai faduwa yake sai addu’o’i nake dan ban san dalilin da ya sa ya ɗaure min ɗin ba, jin yana kiran Sunana yasa ni miƙewa kwance na same shi ya yi ɗaiɗai daga shi sai guntun wando, “Yi shirin kwanciya ki zo mu kwanta.”

Umarnin da ya bani kenan. Falon na koma na kashe komai sai na rufe kofar na cire kayan jikina na mayar da na barci humrar na ƙara sawa kadan sai na hau gado addu’o’in kwanciya na shiga karantowa na gama sai na shafe jikina na lumshe idona na ji ya mirgino inda nake sai ya rungume ni, ajiyar zuciya muka fidda a tare.

Abubuwan da suka faru a tsakanin mu a wannan dare masu tsayawa a rai ne, daren yana cikin dararen da ba zan taba mancewa da su ba a tarihin aurena da Tahir. Da safe mun tashi yana ta ji da ni sai zuciyata tayi min sanyi, sai gobe zai koma wurin aiki dan haka tare muka wuni, da na leƙa wurin Aunty Laila dan mu gaisa sai tsiya take min na baro ta ina cewa ki dai ji da sharrinki Aunty Laila.

Da daddare yana zaune ina kwance jikinsa, hotunan ginin gidan da yake yake nuna min ina ta yabawa tare da addu’a.Haka rayuwa ta juya min, na samu lafiya da walwala ina kokari wurin kula da ibadata da mijina, na goge na waye zama da Laila, na koyi gyara jikina da nakaltar yanda ake kwalliyar, kashe min kudi kawai Tahir ke yi daga suturu zuwa kayan gyaran jiki da na kwalliya. Inda duk Laila za ta za ta gayyace ni, shi kuma bai taba hanani ba har gidan su Laila mun je tare da shi dan ni tuni na zama ƴar gida.

Duk sati biyu yake tafiya Kaduna saboda gininsa, idan ya tafi ni kuma zan kai wa gidan Kawu Attahiru ziyara inda Aunty Kulu za ta gyara ni ciki da bai. Wata ranar Laraba da yammaci na shiga wurin Aunty Laila. Girki take haɗawa ni kuma ina zaune kan wata drower jikin window ina latsa wayata, ɗagowa nayi na dube ta.

“Aunty Laila na samo mana sana’ar da za muyi ta waiwayo da ludayi a hannunta “Wace sana’a ce? Na ce “Mu sa kekunan dinki, sai mu samo kwararrun teloli mu zuba suna ɗinki muna biyan su” ta ce “Good idea dama shagon da Momi ta bamu jikin wanda take saida material ne” wayarta ta jawo momin nata ta kira ta shaida mata shawarar da na kawo ita ma tayi na’am ta ce mu hada kuɗaɗen mu za ta neme mu.

Muna cigaba da maganar na hango shigowar motar Tahir ta window da nake zaune, kasa na duro “Na tafi Aunty Laila” ta ce “Habibi ya dawo kenan? Na fito yana kokarin parking kallon da yake jifana da shi bayan fitowar sa, yasa na sha jinin jikina wuce ni da ya yi ba tare da ya yi min magana ba yasa na bi shi cikin sanyin jiki, dan gano laifina ya hanani shiga wurin Laila ba mayafi, jikina na duba wando da riga ne na material rigar karama ce sai wandon falazo sai baby hijab da na sanya.

<< Wa Gari Ya Waya 27Wa Gari Ya Waya 29 >>

2 thoughts on “Wa Gari Ya Waya 28”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×