Skip to content
Part 29 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Haƙuri nake ba shi bai ce komai ba, har ya sauya kayan jikinsa, ya zauna falo bai min magana ba. Haƙuri na ƙara ba shi sai na shiga ba shi labarin shawarar da muka yanke ta buɗe shagon ɗinki. Amsa min da ya yi yasa na gane ya haƙura, wayarsa ya miƙo min.

“Ga Hajiyar tudun wada, ta kira ni wai in haɗa ta da ke, dan kin kirata bata ji, na amsa sai da muka gama gaisawa da ita da Malam sai na ce ta bai wa su ƴan biyu, suka yi ta min shirmen su ina dariya.

Kwanakin da aka dauka ba masu yawa bane aka bude shagon ɗinki na zamani aka kuma nemi kwararrun teloli aka zuba, mallakin mu ni da Laila.Wani hantsi ina aiki a bed room ɗina, na shirya kayan guga, na hango tsayuwar motar gidan su Aunty Laila, ganin Mominta ta fito yasa mamaki kana kama ni dan bata taɓa zuwa ba.

Saurin kammalawa nayi dan in je in gaishe ta, hijab na sanya doguwa har ƙasa dan Ahmad yana gida, kasantuwar weekend ne, Tahir ma ya je kankara. Sai da na shirya mata dan abin taɓawa a faranti sai na isa wurin Laila, daga ita sai Ahmad na samu zaune suna magana, da Sallama na shiga na ajiye tiren a gabanta, sai na zauna kusa da kafafunta na soma gaishe ta, dafa ni tayi tana amsawa, kafin na gaishe da Ahmad.

Ban ga Laila ba ina tunanin tana kitchen, na fito na koma wurina. An shafe sama da awa biyu Momi ta fito za ta tafi, tare da Aunty Laila suka shigo wurina, ƙara gaishe ta nayi muka taɓa yar hira, da ta tashi za ta tafi wata leda ta ajiye min. Kayan yar Sokoto ne, “Jiya ta zo” na ce ,”Na gode Momi, Allah ya kara girma”. Sai da muka raka ta har inda motar da aka kawo ta take, ta shiga muka rufe kofar, motar Ahmad na bayan ta ta har suka ɓace wa idonmu. Wurina Aunty Laila ta bi ni, muna shiga ta miƙo min ledar yar Sokoto da Momi ta bata, iri daya da tawa. “Ga shi ki haɗa” Haɓa na riƙe “Wai sai yaushe za ki gane alfanun magungunan nan ki riƙa sha?

Gatsine tayi “Ke ni fa ba zan iya shan abubuwan nan ba” na wuce kitchen ina dauko kofi, “Da za ki san amfanin su Aunty Laila, da ba sai nayi ta rokon ki ba, za ki sha.” Kai ta girgiza tana kallona, na haɗa tsimi, da gumba da zuma na sha. ” Kin san labarin da na zo ba ki? Na ce “A’a” ta gyara zama “Daddy ne ya biya mana Saudiyya mu duka gidan mu, shi ne Momi ta zo rarrashin ɗan ta, ya ajiye aikinsa, dan ita dai aikin nan na Ahmad yana takura ta, duk inda za su sai dai su tafi babu Ahmad, saboda yanayin aikin sa, ta ce ya fadi duk irin sana’ar da yake so za su ba shi jari ita da Daddy, ya bar aikin.

To ya dai roke ta, ya ce ta dan ƙara mishi lokaci zai ajiye aikin kamar yanda take so. Ta ba shi keys na gidan da Daddy ya gina mishi, ta ce wannan umarni ne ba shawara ba, dole ya tashi anan.” Take hankalina ya tashi na ce “Yanzu tashi za ki yi ki bar ni anan, Aunty Laila? Murmushi tayi “Kin kuwa san kafiyar Ahmad? ba lallai mu tashi ba, zai san yanda ya yi ya lallaɓa ta. nayi murmushi “Mu’amalar Momi, da ya Ahmad tana burge ni, wani lokacin na kan yi tunanin kamar shi ta haifa ba ke ba.”

Ita ma ta murmushin tayi “Kafin ke mutane da yawa sun faɗi haka, wata irin kauna ce tsakanin su.” Mun jima muna hira kafin ta koma sashenta. Da Tahir ya dawo nake ba shi labarin tafiyar da su Laila za su yi zuwa aikin hajji. Na haɗa da rokonsa ya kai ni gida, ya ce ba yanzu ba. Har na manta mun yi maganar zuwa aikin hajjin su Laila sai ga shi da takardu wai za mu je in yi passport ya biya min za mu tafi tare da su Aunty Laila, har ya je ya yi ma mahaifinta magana za su tafi tare da ni.

Murna sosai nayi jin ni ce za ni kasa me tsarki sauke farali. Amma har kamar Laila ta fi ni jin dadin za mu tare, dan ita wannan ba shi ne zuwan ta na farko ba. Na ƙara roƙon Tahir ya kai ni gida in yi Sallama da su, ya ce A’a sai na dawo” jin da nayi yana waya na fahimci idan na tafi wata daga cikin matansa zai kawo, dan Mmn Ummi ta bani labarin matan nasa sun bar aiki, wai tun zuwan da ya yi ya yi wata guda, ya tada musu balli, ya ce dole duk wadda ke son zama da shi ta ajiye aikinta ta kula da aurenta.

Sun girgiza duk kan su amma tilas suka haƙura. Sai na dauke duk wani abu nawa, har Suturu na na kai wa Aunty Kulu, ina dai ta fargaban idan ya tambaye ni abin da zan ce mishi, sai bai ma tambaya ba. Bamu tashi da wuri ba, dan mu ne jirgin karshe. Ranar da zamu tafi muna Sallama da Tahir duk da idon mutane sai da ya kama hannayena ya riƙe cikin nashi, “Ki kula da kanki Ummulkhairi, Allah ya tsare min ke.”

Na kasa cewa Amin dan zuciyata da ta tsinke har sai ga hawaye. Handkerchief ya fiddo ya goge min, sai ya ciro wasu kudade Dalar Amurka ya damka min a hannuna, “Kar ki ce za ki yi wata tsaraba, Ummulkhairi ki ci abinci me kyau, kar ki dawo a rame, ki yi ibada. Na daga kai muka haɗa ido, “Kuɗaɗen nan fa sun yi yawa, za a bani na guzuri” murmushi ya min kafin ya kai ga magana sai ga Laila ta karaso akwai ƴar kunya tsakanin su, dan haka sallama ya mata muka wuce ina jin ba dadi a zuciyata.

Aikin hajinmu me daɗi muka yi, dan kasancewar iyayen Laila a tare da ni. Hotel din da muka yi masauki na musamman ne kuma yana kusa da harami dakin mu daya da Laila, Momi da Amira, sai Daddy shi kadai, Ahmad dai ya zille bai zo ba, ya ce sai za su dawo Umara. Mahaifiyar Laila, Haj Asma’u, mace me kwazo da sanin ciwon kanta, wayayya me dimbin ilimin addini da na zamani. Bata barin mu haka nan, kullum muna wurin ibada, har muka kammala aikin Hajji.

Daga Saudiya Dubai za su wuce, daga can su shiga China za a yi ma Amira sayayyar kayan aure. Daga ni sai Aunty Laila ne masu komawa Nigeria, samun mahaifinta tayi ta ce ya roki Ahmad da Tahir su bar mu mu tafi tare da su. “Anya Lailata aka yi haka ba a shiga hakkin mazajenku ba? Kafa ta buga kamar wata yarinya karama, “Haba daddyna ba wani shiga hakki duka sati nawa ne? Ya ce “Shi kenan.”

Tsalle tayi ta mika mishi wayarsa da ke kusa da shi da ɗai ɗari ya kira kowannen su ya nemi alfarmar barin matan nasu su tafi tare da su, wanda duk kan su dauriya me yawa suka sa wurin amsa wa dattijon. Aunty Laila ta same mu tare da Momi da Amira da murnarta ta bamu labari. Kai Momi ta girgiza “Ai da ina wurin ba za a yi wayar ba, Alh ya yi ta biye miki da shirmen ki, da wane ido za mu kalli yaron nan Tahir in shi Ahmad ba yadda zai yi da Daddy. Wani kallo Aunty Laila ta fakaici idon Momi tayi min “Oya taso mu je.”

Miƙewa nayi dan dama a shirye nake, ta dubi Mominta, “Saura ke Momi ki tashi mu je” “Ku je abin ku, zan huta ne” marairaicewa Laila tayi har ta samu Momin na ta ta yarda za ta. Kama hannuna tayi “Mu je mu yi wa Daddy Sallama, kafin Momi ta shirya”. Inda Aunty Laila ta bar shi nan muka same shi, muka shaida mishi za mu fita sayayya, kuɗaɗe ya ciro ya damka ma Lailar ni ma ya bani kamar yanda ya bata, muka yi godiya muka fito.

Mahaifiyar Laila na gaba muna bayanta, wani katafaren wurin saida turaruka muka shiga, mu wurin na sawa a daki muka nufa, Momi kuma magunguna irin na su na can ta saya mana ta haɗa kuma har sayayyar da muka yi ta biya kudaden. Daga nan sai wurin sayar da kaya, laffaya muka saya kala kala ko in ce Momi ta saya ta saya mana, har Aunty Kulu na zabar ma masu kyau.Mun taho bisa hanya ina ta wa Aunty Laila mita, “Kullum za mu sayayya sai kin uzzura wa Momi, ko bata da sha’awar fita, dan wayon ta biya kudaden duk abin da muka dauka. Shi kuma Daddy dole sai kin kaimu yi mishi sallama shi kuma duk zuwa zai dumbuzo kudi ya bamu, ni kam tun zuwa na ban kashe ko kwabo ba, komai su Daddy ne da Momi.”

Maimakon ta bani amsa sai ta shashantar da maganar, ta hanyar nuna min wani shagon dogayen riguna, haka muka shiga kuma Momi ta biya duk abin da muka dauka. Ban gane me Aunty Laila take nufi da abin da take yi ba sai ana saura kwana uku mu bar garin ina zaune a masallacin Annabi, karatun Alkur’ani me tsarki nake. Wayata ta shiga vibration dan na sa ta a silent, dubana na kai inda take sunan Aunty Laila na gani na ɗauka ina magana can kasan makoshina “Ki yi sauri Ummulkhairi ki dawo za mu fita.”

Kashe wayar nayi na soma tattara nawa ya nawa, na rataya jakata, cikin nutsuwa na riƙa takawa har na koma masaukin mu, na samu dama Laila jirana take. Yau dai bata ce wa Momi sai ta bi mu ba, ko Amira ƙanwarta da ta ce za ta raka mu, cewa tayi “Kwanta abin ki ki huta ƴanmata.” Amma sai da ta kaimu wurin Daddy muka yi mishi sallama, shi kuma ba fashi ya ciro kudade ya bamu ya ce mu kara sayayya. Bata kai mu ko’ina ba sai wani katafaren wurin saida kayan ƙarau na adon mata, dukiya ce iya ganin idon ka. Duba na tayi “To Hajjaju me son kashe kuɗin ta, ga lokacin kashe su ya yi, Allah ma yasa su ishe ki. Murmushi nayi ina naɗe da hannuna a kirji.

“Me kenan za a saya malamata? Ita ma murmushin tayi “Ina son ki sayi sarƙa da ƴan kunnaye kamar set uku ko hudu iya dai inda kudinki suka tsaya, sai bangul ina son ki saya, sannan akwai wasu awarwaraye na gwal sirara ne guda goma sha biyu, Momi ta taɓa saya min, sai zobuna na gwal guda takwas.Girgiza kai nayi “Tirkashi! babbar magana, duk ina na ga kuɗaɗen sayen waɗannan ababen da kika lissafo?

Hannuna ta kama “Za ki gani” sai dai wani jiri da na soma ji yasa ni kasa cire kafa. Duba na tayi “Yaya dai? Na ce “Jiri nake gani sai zuciyata da na ji tana tashi, kamar zan yi amai” A taƙaice dai ka sa tafiya nayi sai da taimakon Laila, taxi ta tare mana zuwa gida. Hankalin Momi da Daddy ya tashi ganin halin da nake ciki, sai da suka kai ni asibiti, binciken larabawa kuma ya bada sakamakon karamin ciki da nake dauke da shi wanda bai cika watanni biyu ba. Bayin Allan nan suka shiga murna, da tarairayata, Asibitin suka riƙe ni suka ce sai na kwana. Muna zaune a dakin daga ni sai Aunty Laila, Ayaba nake ci tana zaune gefena.”

Ina ganin dai wannan ɗan namu ɗan bankwana ne, aka maƙalo aka taho da shi.” Rufe ido nayi na ce. “Na shiga uku Aunty Laila” ta kwashe da dariya. Tsokana ta tayi tayi, har na gaji na kwanta na juya mata baya. Washegari na tashi garau, suka sallame mu. Ba mu koma wurin sayayya ba, Aunty ta ce mu bari sai mun isa Dubai. Mun bar Saudiyya muka shiga Dubai, sati guda muka yi anan ɗin na sayi duk abin da Aunty Laila ta lissafa sai dai set na sarƙa biyu aka samu, kuɗi suka kare kaf, har na account ɗina da na canzo na taho da su wa’anda na ce mata ban so in karar da su ina so in yi alheri da su idan na koma na je gida.

Ta ce Allah zai kawo na yin alherin. Daga Dubai sai China nan kam yawo muka yi sosai dan na gane Laila sani ba na wasa ba tayi wa garin, ana gobe za mu bar kasar dan sati biyu muka yi, a Guangzhou muka sauka sai muka wuce yiwu muka yi kwana hudu daga nan muka wuce shon-hai muka yi kwana hudu, nan ma sai muka dawo Guangzhou idan muka kwana washegari sai mu wuce.

Mun je kasuwa mun dawo daga kasuwa zuwa hotel din da muka yi masauki babu nisa, takowa muka yi a ƙafa, muna tafe muna hira Laila ta ce “Kika ce oganki ya ce Kaduna za ki sauka? Na daga kai “Haka ya ce dan an tura shi wani course na wata tara a Kadunan, amma ni kam ban san haduwa da matan nan na shi.” Wani kallo ta min “To ina fata dai ba tsoron su kike ji ba?

“Haba dai tsoro? fitina ce kawai bana so””Yawwa, yanzu ba tsoro tsakaninki da su, ai kin gane? na daga mata kai. “Duk wata haɗuwa da mace za ta yi takama da ita ke ma kin haɗe, in bokon su ke ba ki tsoro, to kema yanzu da kowa za ki yi turanci, in kika haɗu da su kwalliya sosai za ki rika dauka dan su san yanzu ba da ba ce, da ba ki iya fita sai da hijabi, uwa uba mijinki na sonki.”

Ajiyar zuciya na fidda “Haka ne” sai kuma na shiga tunanin halin da muke ciki da Ogan tun rokon da Daddyn Laila ya yi mishi sai ya dauki fushi da ni, ya daina kirana in kuma ni na kira shi a dakile yake amsawa. Abin yana damuna amma sai na sa hakuri na bar wa raina, ina ta addu’a. Ranar da zamu taho jirgin Ethiopia muka hawo, zaman awa goma sha bakwai muka yi hada yada zangon da muka yi a Ethiopia, Abuja muka sauka karfe daya agogon Nigeria, daga cikin jerin motocin da suka zo taran Daddy muka shiga daya, nan ma Daddy waya ya yi wa Tahir ya roke shi zan kwana da su anan idan Allah ya tashe mu lafiya zai sa a kawo ni Kaduna.

Shiryayyen gidan Daddy na Abuja muka yada zango, ni dai cikin fargaba nake yanda za ta kaya mana ni da Ogan dan an kara mishi laifi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya 28Wa Gari Ya Waya 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×