Skip to content
Part 27 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Muna komawa ni da Aunty Laila, falon Aunty muka zauna ta ce “Kayan naki fa yaushe za mu kai ɗinki? Kaina na kwantar a bayan kujera, sai na girgiza kai “Idan dai an kara kwana biyu zan tambayi Kawu fita, sai in zo mu kwasa mu kai.”

Ta ce ” Hakan ma ya yi, amma dan Allah ina so ki cire damuwa a ranki ki yi hakuri, Aunty za ta gyara ki dan h… Shigowar Auntyn yasa ta yin shiru Flate ɗin da ke hannunta ta ajiye gabana, ƙamshin ya daki hancina fish wit vegetables spaghetti ne, “Ga shi nan ku ci ke da kawarki”. Ta dubi Laila “Ki yi kokari ta ci”. Ta ce “In sha Allah Aunty” ta juya ta fita, me aikinta ta kawo abincin rana, sa’adda Aunty Laila ta kai kifin nan bakinta sai ta runtse ido “Kai gaba ɗaya matar nan tayi, anya wannan kishiyarta ba ƴar rakiya za ta zama ba?

Murmushi nayi ko dai in sa miki waigi Aunty Laila? Hararata tayi “Meye nufinki santi nake?Na ce. “Da fa? Me aikin ta kuma shigowa da yankakkiyar kankana, ta ce “Aunty ta ce kina gamawa ki sha” na daga mata kai, Aunty Laila ta ce “Matar nan ta san ta kan gyara, kullum daga fruits sai vegetables take ba ki.”

Na ce “Kuma kullum sai ta yi min kunun Aya na musamman wanda ya ji kwakwa da dabino da madara.” Ta ce wadannan ai su ne gyaran, ba kinshe kinshen magungunan da ba ka san ingancin su ba”. Na ce “Akwai masu kyau, har kin tuna min da wata matar abokinsa da ta taba kawo min ziyara lokacin da ina Kaduna, ta bani magani. Nan na kwashe komai, labarin yanda muka yi da Haj Shema’u na gaya mata.

Na kara da cewa a lokacin sai nayi zargin wannan maganin da ta bani ne yasa ya yi ta yin abin har yasa cikina barewa” Aunty Laila ta dafe haba “Kuma yanzu ina matar? Na tabe baki “Oho wallahi, tun dai da ta kira ni ta ce tayi tafiya, ban kara jin ta ba” hannu ta kada “Gara haka, daga jin al’amarin ta akwai abin gudu a ciki.”

Na ce “Ni ma hankalina bai kwanta da ita ba”.”Amma, Ummu ya kamata ki rika shiga kitchen, tare da Aunty Kulu kina kwashe salon girkinta.” Kallonta nayi “Auntn ta ce sai na kara warwarewa, amma ko ni ma ai ina son koyon wasu girke girken nata, har wurin da ake gyaran jikin nan nata nake son zuwa kallo, ta ce a’a sai na kara kwari.”

Ta ce “Allah ya saka mata da alheri” tana surar jakarta “Dan Allah ki kwantar da hankalinki, Ummu kar ki sa tunani ki lalace, shi yana can yana holewarsa.” na daga mata kai “Na hakura Aunty Laila, in ma ban yi hakurin ba ya zan yi? da ya damu da halin da zan shiga ai da ya gaya min, ba sai an daura ba in tsinci labarin.”

Ta ce “Ba haka ba ne, kowane Namiji da irin tsarinsa idan zai kara aure” ta mike zan wuce Ummu, kasuwa zan leka, sai na kuma dawowa.” Na mike na dan taka mata sai ta wuce. Wunin ranar na dai yi shi ne amma zuciyata ba dadi. Abin mamaki a wurina da daddare zan kwanta sai na ji bakina yana furta addu’oin kwanciya barci, kamar yanda na saba a baya har suratu mulk da nake karantawa na karanta. Ina karatun ina hararar wayata da take haske dan na sanya ta a silent, kiran Tahir ne ke shigowa yana yankewa na kammala karatun zan ja abun rufa ta Aunty Kulu ta turo kofar ta shigo, mun hada ido ta zauna bakin gado sannu nayi mata, bata amsa ba ta jeho min tambaya.

“Me yasa kika ki amsa wayar Tahir? Baki na kumbura “Babu komai” “To akul kika yi haka, ya kira ni yana fada min, yana ta kiranki, ba ki picking, ki zama cikin wayayyun mata, Ummulkhairi nuna mishi abin da ya yin bai dame ki ba.” Kai na gyada mata sai ta turo min wayarta.”

“Ya ce zai kira” kamar jira wayar ta shiga kara na dauka sai ta mike ta ja min kofar muryarsa ce ta ratsa kunnena “Ranki ya dade, duk fushin ne? Baki na tabe ina jin wani takaici na kulle ni, “A’a fushin me kuma? Ango ka sha kamshi.” Murmushi na ji ya yi me sauti “A’a to ko dai ana fushi da ni na ji ba me tsanani ba ne, amma me yasa aka ki daga wayata? wayar na harara “A silent take, kuma na sa ta karkashin pillow, ban ji ba, Allah ya sanya alheri ya kade fitina.”

Cikin wata murya me bayyana tsananin jin dadi yake fadin “Amin na gode Ummulkhairi” mun ajiye waya na kuma janyo abin rufata na ji shigowar sako cikin wayata, na dauko ta na duba Alert ne, yawan kudaden da na gani yasa ni tashi zaune, ban yi wata wata ba na kira Tahir a waya, kamar yana jira, tana shiga ya daga ” “Ya aka yi? Ya soma tambayata “Dama kudade na ga sun shigo na ce ko kayi mantuwa ne? Murmushin sa na ji cikin kunnena, “Ba mantuwa nayi ba, naki ne na faɗar kishiya, ki sayi duk abin da kike buƙata, sauran yan’uwanki ma na ba su.”

Kai na kada, kafin na shiga yi mishi godiya. Da safe Malam ya umarce ni in yi sadaka da hannuna domin sadaka maganin masifa ce, sai da na karya sai na kira Ummata, na bata labarin auren da Tahir ya yi, kamar yanda na zata cewa tayi “To mene ne? Ya canza miki ne daga yanda yake miki? Na ce “A’a” ta ce,

“To ki yi hakuri ki yi ta ma mijinki biyayya” na ce “To” labarin kuɗaɗen da ya turo min na bata, na ce zan turo su a raba duka gidan mu.Ta ce “A’a ki raba kudin uku, ki aiko da kashi daya, sauran ki adana abin ki, so samu ki samu sana’a kina yi ba wai duk abin da kika samu ki ce za ki turo mana ba.

Na ce “To Ummana.” Da daddare kamar jiya sai ga kiran Tahir, hira muke a hankali, a cikin hirar yake gaya min maganganu na lallashi “Ki yi haƙuri, ban yi aure dan cin zarafin kowaccen ku ba, ko dan ban samu wani abu da nake da burin samu wurin ya mace kaddara ce kawai, kuma idan na ɗauki shawarar ki gara mu yi auren.”

Wata irin faɗuwar gaba na ji gane wace ce ya aura, cikin rawar baki na ce “Wai ya sunan Amaryar taka? Dan jim ya yi kafin ya ce “Latifa” Ai ji nayi tamkar zan yi fitsari a wando, zufa na ji tana tsatstsafo min. “Wani abu ne? Muryarsa ta maido ni cikin hayyacina.

“Ba komai” na fadi kamar zan fasa kuka. Daga nan duk zantukan da yake min ban fahimtar komai, har ya gaji ya ƙyale ni, wanda ni ma ba fi so. Tagumi na rafsa hannu bi- biyu na tashi zaune tsakiyar gado, “Ni ba ta garin nan ba, yaƙi ya ci kwartuwa, ni Ummulkhairi ina zan tsoma gulmata?

Wannan kwarkwararrar yar duniyar Tahir ya aura, shi kenan ni kam na sare, dan ban ga ta inda zan fara in iya karawa da wannan yar barikin ba.Tahir ya dauko mana fitina. A wannan dare in na ce na rintsa nayi karya, haka na tashi da safe ido ya yi zuru zuru, saboda rashin barci. Gatan da Aunty Kulu ke min ban yarda da shi ba a wannan rana, kitchen na bi ta duk kuma yanda ta kai ga cewa in koma in kwanta ƙi nayi, tare muka yi komai da ita, ina nakaltar yanda take sarrafa komai.

Na bi ta wurin gyaran jiki muka haɗa humra tare, wani abu da na tuna yasa ni komawa daki da sauri na ɗauki wayata, WhatsApp na shiga wani link na wani grp da Aunty Laila ta turo min ta ce in yi joining, ban ko bi ta kan shi ba, group ɗin na sayar da Supplement ne na gyaran jiki, nan take nayi joining. Saƙo na tura mata.

“Ina son ganin ki Aunty Laila, ina cikin matsala”. Ba a yi kwakwkwaran awa daya ba ta ga sakona sai ga kiranta ta ce “Mene ne? Na ce “Kan wadda Tahir ya aura ne” na bata labarin wadda ya aura, amma sai na sauya zancen na ce mata sanda ina Ƙanƙara na samu labarin yana tare da ita, wurin matar yayansa, wata kwantagwalalliyar, yar duniya ce. Kwantar min da hankali tayi, tare da gaya min maganganu na karfafa gwiwa, da shawarwari wadanda zan taimaki kaina.

Na bata labarin kuɗaɗen da ya turo min, ta ce na gayawa Aunty Kulu? Na ce A’a dan ni dai gaskiya ina tsoron dangin miji, duk dadinka da su.Ta ce “Haka ne, dama za ta ce in yi shiru kawai. Na ce “Sana’a nake so in fara Aunty Laila” ta ce mu bari Mamanta ta dawo wadda shahararriyar yar kasuwa ce, sai mu nemi shawarar ta.”

Na ce “Ina so idan kin shigo in bi ki, in kwaso kayana mu kai ɗinki” ta ce. “Ba kin ce sai an kwana biyu ba? Kai na girgiza. “Ba a bori da sanyin jiki Aunty Laila, in dai kin shigo sai ki taya ni rokon Aunty Kulu ta bar ni mu je mu kwashi kayan.Yar dariya Aunty Laila tayi.

“Matar nan dai ta kidima ki Ummu”Na ce “Ba kaɗan ba.” Tana min dariya muka aje wayar. Sai washegari ta shigo, muka roki Aunty Kulu ta ce Mijina bai sani ba. Na ce “Zan mishi text” ta ce “Ba laifi” Ina yi mishi text ɗin ce min ya yi Allah ya tsare.

A motar Aunty Laila muka tafi.A ɗakina ina ciro kayan Aunty Laila tana tsaye riƙe da haɓa, Allah Ummulkhairi kina da wadannan kaya masu tsada kika bar su kina ta ajiyar su? Murmushi nayi, na janyo wata drower, “Sai mun fara biyawa shagon Momina mu canza wasu kayan.”

Na ce “To” “Kai! yanzu dan Allah tunda nake baki magungunan (Supplement) ajiyar su kike ba ki sha? na ce “Ai yanzu ga shi zan sha” ta murmusa “Ai na ga kin ma yi joining da grp ɗinmu (beauty wit supplement) dan tsaki na ja ina taɓe baki “To ya zan yi? daga ina zaman lafiya an haɗa ni da rakai.”

“Ai ba abin da ban ba ki ba, sai dai da yake ana turo sabbin kaya, kika fara amfani da su da kanki za ki bani labari.” A jaka na sanya su muka fito sai na rufe wurin. Na sha mamakin katafaren wurin da Laila ta ce min na Mamanta ne. Duk wani abu na kwalliyar ya mace ba abin da babu. Shugabar wurin, wadda ta zam mace ce, ita Lailar tayi wa bayani, za ta musanya kaya, ta juyo wurina ta ce in zaba, ta kuma taya ni zaben. Da muka gama Aunty Laila ta zabo min wasu saitin mai ta ce in gwada amfani da su. Daga nan sai wurin telan da ke mata ɗinki, muka bayar, sai la’asar na koma gida.Na sa wa raina dangana sai dai na dage da addu’a a sujjadata, na kan ce “Ya Allah wannan al’amari da ya same ni, ban gaya wa kowa ba kai na gaya wa, ina rokonka Ubangiji ka zame min bango abin jingina ya hannanu ya mannanu ya badi’us samawati wal’ard, ya zuljalali wal ikram.

Na dage kuma da shiga kitchen tare da Aunty Kulu da taya ta ayyukan sana’arta. Ni ma ta soma min gyaran jiki, Kawu Attahiru yana ta bani addu’o’i na dage ina tayi, gaba ɗaya nake jin canji a tare da ni. Muna waya da Tahir, ya kira ni sau uku a rana. Iyayen Laila sun dawo dan haka roƙi Aunty Kulu zan je, ta ce “To in sanar da mijina” Na kira shi da safe, lokacin yana zaune a Hospital an kwantar da sarautar mata, wadda tun daura auren Tahir ta shiga tashin hankalin da bata samu sa’ida ba har sai da ta dangana da gadon likita. Kwance take sharkaf wanda gaba ɗaya jikinta da zuciyarta ciwo suke mata.

Tahir na zaune kujerar gaban gadon nata, Amarya Latifa na tsaye ita da kawarta Fadila wadanda basu jima da zuwa ba, ba kuma kowa ya gayyato su ba tun dai da ta kwana biyu bata ga Tahir ba, ya ce ba zai samu zuwa ba, Uwargidansa na kwance Asibiti.

Kasa haƙuri tayi sai da ta nemi abokinsa Shehu, wurin sa ta ji inda aka kwantar da ran gidan, sai suka yo mishi tsinke, yanda take ji a jikinta ya hana ta tashi tayi musu korar kare. Har suka gama gaishe gaishen su, bata ta da kai ba, tana dai kallon su, zuciyarta na tururi, wayar Tahir ta shiga ƙara yasa hannu ya ciro ta a aljihu, ganin me kiran ya ba shi mamaki dan ba kiran sa take ba “Ya aka yi? abin da ya fara ce min kenan, ban amsa ba na shiga gaishe shi, kafin ɗora da cewa “Dama iyayen Aunty Laila ne suka dawo shi ne nake so mu je in gaishe su.”

“Yawo ko? Kai na girgiza kamar ganina “Allah ba yawo bane” “Sai kun dawo, ki kula da kanki.” na ce “In sha Allah, na gode” Latifa suka kalli juna ita da kawarta Halima kuma na kallon su, dan duk sun fahimci da wa ya yi wayar, cikin magana me kama da subutar baki Amarya Latifa ta dube shi “Ba bata da lafiya ba? har tana iya fita? Shiru ya mata kamar ba zai tanka ba, kafin ya jefe ta da idanuwansa “Wa ya ce miki bata da lafiya?

Take ta gane kuskuren da ta tafka, kame kamen da ta shiga yi yasa Halima zura mata ido tana nazarin ta, ita Sarkin karantar mutane tuni ta gano Latifa, a ranta ta ce “Wato ban da asirin zubewar ciki da na yi wa yarinyar nan, ita kuma na rashin lafiya tayi mata kenan? Kamar yanda malaminta ya ce mata ita ma Latifa tun kan ta shigo gidan neman kowa take, lallai yarinyar nan ta  kawo kanta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya 26Wa Gari Ya Waya 28 >>

1 thought on “Wa Gari Ya Waya 27”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×