Mun dan tattauna maganar kafin ta ce tana so toye toyen da za a yi na Amarya ta kawo in ajiye. Na ce "Sai ta kawo" Da suka fita ni ma fita nayi zuwa dakin Haj. Nan na samu Amarya Saddiƙa sai razgar kuka take Haj na rarrashinta. Na tambayi abin da ya same ta, Haj ta ce "Ki bari, saitin da ubanta ya ƙuƙuta ya yi mata audugar sa ya sayar duka, amma ƴar nan, bata gode ba, tana ta famar kuka wai auren ma bata yi."
Na kamo ta zuwa jikina ina lallashi "Yi shirun ki. . .