Skip to content
Part 31 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Mun dan tattauna maganar kafin ta ce tana so toye toyen da za a yi na Amarya ta kawo in ajiye. Na ce “Sai ta kawo” Da suka fita ni ma fita nayi zuwa dakin Haj. Nan na samu Amarya Saddiƙa sai razgar kuka take Haj na rarrashinta. Na tambayi abin da ya same ta, Haj ta ce “Ki bari, saitin da ubanta ya ƙuƙuta ya yi mata audugar sa ya sayar duka, amma ƴar nan, bata gode ba, tana ta famar kuka wai auren ma bata yi.”

Na kamo ta zuwa jikina ina lallashi “Yi shirun ki ki kwantar da hankalinki, kayan ɗaki sai kin zaba in sha Allah.” Haj ta ce “A’a daina faɗa mata haka, ta dai yi haƙurin.” Sai ta kara fashewa da kuka na ja ta bed room din Haj ina ta gaya mata maganganu masu daɗi har ta haƙura. Sai da Tahir ya shigo muka nufi wurin mu tare, a falo muka samu Halima, na shiga kitchen na fito mishi da abinci bayan na ɗumama ya ce min bai jin cin komai indai kawo mishi black tea, ina fitowa kitchen na ji yana tambayar Halima da yaushe ta dawo ta ce sai da aka yi Isha’i.

Muna nan zaune, su hali dubu ana jira miji ya gama su shige daki sai ya ce “Nan dai ba kamar Kaduna bane, baƙunta muka zo, dan haka kowacce kwana ɗaya za ta rika yi har mu koma.” Sai Halima ta ɗauke wuta miƙewa tayi ta bar abincin da take ci, dan abincin da ya ce ba zai ci ba ita ta zuba tana ci.

Na kwashe kwanonin na kai kitchen. Sai da muka yi shirin kwanciya nake ba Tahir labarin Sadiƙa, shiru ya yi kafin ya ce “Ai idan za a aurar da yara gidan nan, ni ya kamata ace nayi musu kayan ɗaki ko? Na gyaɗa kai “Kwarai kuwa, abin da ya kamata kenan”. “Da safe ki kira min Sadikar.” Na ce “Allah ya kaimu”Da safe kafin ya fita Yaya Lawal ya aiko kiransa, godiya ya yi ta yi mishi kan Sabulu da omo da na kawo musu ya ce ka ga yanzu an samu sauki sai a ji da abinci.

Da ya dawo wurin da muke zaune za mu karya ka sa karyawar ya yi, har sai da Sadikar da na kira ta zo ta gaishe mu, kafin ta tsuguna “Ya ce Waɗanne irin kaya kike so? Shiru tayi ya ce “Ki buɗe baki ki yi min magana, Malama” dan zakudawa tayi. “Akwai a wayata” “To yanzu in haɗa ku da Direba ku tafi Katsina ke da Ummulkhairi ta taya ki zabe, ko in sa a turo min hotuna ki zaba?

Shiru tayi ya kara maimaitawa nan ma shiru gane ba za tayi magana ba yasa ya ce “Shi kenan ki je zan sa a tura min sai in tura wa Ummulkhairi ta nuna miki.” Ta ce “Na gode Baba” ta tashi ta tafi, Halima dai bata ce komai ba kamar ma bata wurin.

Sai da muka shiga daki ya ce “Kin ga ma na shafa’a da maganar saya musu abinci da muka yi, amma nayi magana za a kawo.” Godiya na mishi sai na tambaye shi yaushe zan wuce Dutsinma shiru ya yi min har sai da nayi ta yi mishi magiya kamar zan yi kuka, sannan ya ce sai an gama bikin gidan nan.

Shiru nayi sai ga hawaye yi ya yi kamar be ga me nake ba, ya shirya ya yi ficewar sa. Tun zuwana kankara yan gidan mu ke ta kira na su na tambayata yaushe zan taho, Sallamar Maman Sadiƙa da na ji yasa ni goge hawayen sai na fito, godiya ta min kan abin da nayi wa diyarta. An shiga hidimar biki.

Duk kuma wata ɗawainiya ni ake gaya wa ni kuma in gaya wa Tahir, baya ƙi sai ya yi anan na gane ba wai bai son taimakon ƴan’uwansa bane, me ɗora shi bisa hanya ne bai samu ba. Mota biyu aka kawo na abinci, mota daya yan’uwansa suka raba a tsakaninsu, ɗaya kuma aka raba tsakanin dangi da makota da mabukata, hakan ba ƙaramin dasa farin ciki ya yi ba a zuciyoyin jama’ar gidan.

Sai ana saura kwana biyu biki su Aunty Kulu suka iso, zo ka ga murna wurina, gidan Kawu Attahiru da ke garin suka yi masauki, ni na shirya musu abinci, barci kawai ya raba mu. Zagewa nayi duk wata hidima da ni ake yi, duk ma abin da za a yi sai an neme ni,

Halima dai tuni ta gudu ta bar min wurin ta koma gidan su. Kwalliya sosai na sha da bikin, ga gwala gwalai na da na fiddo nayi ta caɓa ado, duk inda na bi sai an kalle ni, balle da Aunty Kulu ta fiddo kayan gyaran ta ta kuma gyara ni. Ranar buɗan kai ya ce zai kai ni gida daga can ya wuce Kaduna. Nayi Sallama duka da matan gidan da Haj, har na shiga mota zai ja wani matashi ya zo gaishe da Tahir ya yi kafin ya faɗa mishi Malam Lawal na kiransa, ya ce yana ina.

Ya ce yana gidan su mai waina, mamaki ne ya rufe shi sai dai ya bi bayan yaron. Dan gidan su Halima ne gidan su mai waina me wainar kakarta ce. A dakin Mahaifiyar Halima ya kuma shan wani mamakin, Yayun shi ne Maza duk kan su ke zaune a dakin, ga mahaifiyar Halima da mahaifinta, sai ita Halimar da ke zaune tana rusa sharbar kuka tana rattafo rashin adalcin Tahir, ya kwashe dukiyar sa ya ba wannan yarinyar da ya auro a Dutsinma, sai yanda ta ga dama take yi.

Tahir da ke duban ta cikin mamaki ya ce “Kuma duk ni ke yin wadannan abubuwan da kika lissafa? Cikin daga murya ta ce “E mana, E mana, nan da ta je aikin Hajji, dukiya ka na ɗa mata ta sawo gwala gwalai na miliyoyi, duk wanda ya zo bikin nan ai ya gani, ban da suturu na alfarma da take sawa. Sai ta fashe da wani irin kuka.

Yayansa Babba ya shiga mishi nasihar girman adalci, a tsakanin iyali. Sai da ya gama bai katse shi ba sannan ya rantse da girman Allah kan bai ba Ummulkhairi kwabo kan gwala gwalai ko suturu da take fadi ba, da dai za ta tafi na ƙara mata kudi kan guzurinta, kuma ke ma da muka je tare na ba ki, abin da dai na sani akwai wata makociyar mu a Lagos tare suka yi tafiyar da iyayenta, Ummulkhairi ta shaida min basu bari ta kashe ko kwabonta ba, sayayya su suke mata har kudi suke bata nan ta sayi gwala gwalan da kike magana.”

Nan dakin aka ɗauki salati ana wa halima fadan zargi. Tahir ya shiga kwance abin da Halima take mishi, da yanda bai jin daɗin zama da ita yana haƙuri ne albarkacin iyaye ana tare. Amma yanzu daga ta kawo kararsa to su bar ta ta huta. Ca! aka yi mishi ana ba shi haƙuri, Halima sai ido ya raina fata, ya bar ta a gidan nan na su ai da ta shiga uku, tunda bakin cikin Ummulkhairi yasa ta baro mata can ta dawo gidan su, komai a aljihunta take ma kanta hada gidan nasu ma, ƴan kuɗaɗen nata ma sun kusa karewa. Tana cikin tunani ta ga Tahir ya juya ya fice. Nan aka yo kanta ana ta mata faɗa ita kam ta gwammaci ko dukan ta za su yi su sa Tahir ya tafi da ita kar ya bar ta a kankara.

Mota kawai ya buɗe ya shiga yanda na ga yanayinsa yasa ni kama kaina. Ajiyar zuciya me ƙarfi na fidda ganin motar ta tsaya a kofar gidan mu, sai ware ido nake, da Nura kanena na fara haɗa ido wanda na ga ya wuce cikin gida da sauri. Matasan da ke zama kofar gidan suka taso ganin na fito, suna mana barka da zuwa. Ina gaba Tahir na baya na muka shiga gidan. Gwoggo ce ta kama ni ta rungume, yayyena mata duka suna gidan suna ta ma Tahir Barka da zuwa, ni dai bakina kamar gonar auduwa bai wani jima ba ya sallame ni bayan ya ci abincin da Ummata ta shirya mishi, da yaro aka haɗa shi ya raka shi kasuwa ya gaishe da Babana, ya tafi bayan ya cika su Ummata da yaran yayyena da kuɗaɗe.

Sai dare Babana ya dawo shi ma sosai ya ji daɗin gani na. Hafsa ma a daren Malam Mas’ud ya kawo ta, ai kam da ƙyar muka rabu, nayi mata alkawarin gobe ina nan zuwa mata wuni. A gado daya muka kwana da Ummata, muka raba dare muna hira tana bani labarin bayan ba ni, ni ma na bata labarin nawa bangaren yanda ta kasance min, iya abin da na ji zan iya faɗa mata. Da safe na fidda tsarabar kowa na ɗauki ta Hafsa da diyarta na nufi gidanta. Muna cikin hira ta kewaye ni da kayan daɗi ta ce “Amma dai Ummu ciki ne da ke? Hararar ta nayi “In ji wa ya faɗa miki? Ta ce “Idona, a yanda na gan shi ma ya fara nisa” gyara kafafuwana nayi “Ba ke kadai ba, Ummata ma ta gane.”

Kin fara zuwa Hospital ne? Na girgiza kai “Ban ma san ta inda zan fara shaida wa Ogan ballantana har in ziyarci Asibitin.” gaba ɗaya ta zaro ido “Wace irin magana kike gaya min Ummu sai ka ce wata yar fari? Kina nufin bai sani ba? “Hafsa, saboda yanayin wadanda nake tare da su. Nan na shiga labarta mata zamana da kishiyoyi, da yanda nayi ta fama da barin ciki a Lagos.”

Sosai ta nuna razanarta “Yanzu cikin wadannan iblisan Allah ya kai ki zama? Na ce “To ya zan yi? Ta jinjina kai “Allah ya daɗa kare mana ke, yasa ki sauka lafiya, amma dai ki yi kokari ki je asibiti ” Na ce “Ina ta tunanin haka, kuma in sha Allah zan je.” Kiran Tahir da ya shigo wayata ya katse mana hirar mu, mun ɗan jima kafin muka yi sallama.

Amma dai na fahimci yana son ki Ummulkhairi, kina da matsayi a zuciyarsa, dan haka za mu dage taya ki da addu’a, daga ba ki nufin kowaccen su da sharri Allah zai ɗora ki kansu”. Na ce “In sha Allah” Da Azahar Malama ya shigo da kaji ya ce Hafsa ta gyara min, dan haka sai yamma sosai na koma gida dan fitowa nayi na taya ta aikin. Kwanakin da suka biyo baya ziyara nayi tayi, har yaya Sani ma ya zo, na ce bi shi ya ce In nemi izinin mijina na tambaye shi ya ce A’a tilas na haƙura.

Ranar da nayi kwana tara na samu wayar Tahir da daddare ina kwance a dakin Ummata, su kuma suna tsakar gida suna hira. Ya ce “Kina kuwa kirga kwanakin da kika yi? Na ce “E” ya ce “Ba ki ga ya dace ace kin dawo dakinki ba? Ido na zaro kamar yana kallona “Haba duka kwana fa tara nayi? To shi kenan ki shirya gobe direba zai iso, sai ku wuce ƙanƙara ku kwana jibi ki dawo gida, ganin gidan ya isa ni ma ina bukatar matata a kusa.”

Kunya na ji kamar yana gabana na shiga ba shi haƙuri babu wanda ya san zan tafi gobe ban ma kowa sallama ba. Da kyar dai ya kara min in ƙara kwanaki huɗu anan sai mu isa ƙanƙara in kwana daya. Godiya na mishi na ajiye wayar, ina tunanin gidan da na baro, na shafa cikina wanda ya fara motsi ina jin sonsa da kaunarsa tare da fatan Allah ya bani rayayye me albarka kifawa nayi nayi rub da ciki ina tuna ya zan ji a ranar da na gan ni da yaro ko yarinya? “Anya Ummu, maza ki tashi daga rub da cikin nan, ko bayan babu kyau a musulunci kin sani, masu ciki basa yinsa yin sa ke sa a haifi yaro da cibiya ta nade mishi wuya, da kwanciya ki kalli sama, in kuma za ki juya kwanciya sai kin tashi zaune.”

Zaunen na tashi ina duban Ummata da ban san sa’adda ta shigo ba. Kwanon hura ta miƙo min da ake damawa Babanmu, “Ko za ki sha? Kai na girgiza “Na koshi Ummata cikina ya cika, wai kin ji shi Umma, nan da kwana hudu zan tafi” ajiye kwanon hurar tayi “To ai babu laifi, an gode mishi, Allah ya kaimu.”

Daga ranar kuma shirin komawata Umma ta shiga yi ta kuma aika wa ƴan’uwana ranar da zan tafi, mazan kuma duk wanda ya shigo za ta shaida mishi. Kamar yanda suka zo ranar da na zo, haka ranar da zan tafi ma suka dawo kowacce kuma da tsarabarta.

Sai Azahar direban ya iso muka dau hanya wanda da rarrashi na fito gidan har kuma ya fara gudu a titi hawaye bai daina gudu akan fuskata ba, na sa kwallen da Yaya Mustapha ya miƙo min na share fuskata. Da isar mu Haj kawai na shiga na gaida na koma wurin mu nayi kwanciyata ban ga Halima ba, sai nayi tunanin ko ita ma ta koma Kaduna, sai da na shiga wurin maman Ummi mata uku na samu a ciki ana ta hira anan nake ji suna labarin abin da ya faru da Halima har ma na ji ba ƙaramin artabu aka sha da Tahir ba ya kafe sai ta zauna a gidan su.

Sai da aka haɗa shi da Kawu Attahiru shi ya yi mishi magana jiya tayi shatar mota ta koma. Ni dai iyaka ta sauraro ban yarda na tofa tawa ba, gudun me zai je ya zo, na dai yi musu sallama Haj har da su matse ido. Mun shiga Kaduna ana sallar la’asar raina na ji ya yi duhu tuna gidan da zan koma kiran Tahir na samu wanda tun tasowar mu yake kirana na ɗauka na shaida mishi mun iso yanzu.

Na samu falon shiru kamar yanda nayi tunani, na wuce ɗakina nayi sallah, duk kuma da halin da nake ciki na gajiya bai sa na zauna ba gyaran ɗakina na shiga yi, sai da naga ya yi min yanda nake so sai na yi wanka, riga doguwa ta wani yadi me taushi nasa, jin ƙwanƙwasa ƙofar yasa ni miƙewa na karasa dan budewa cike da mamakin ko waye, wata baƙuwar fuska ce a gare ni, riƙe da tray a ladabce ta gaishe ni tare da min bayanin sunan ta Laraba sabuwar me girkin da aka dauka. Na karba nayi mata godiya sai da na amsa wayoyin da ake ta kirana sannan na ci abincin, ina tunanin ni kam zan yi wa mijina girkin da zai ci duk da girkin nata da dad’i, ba zan zauna yar aiki ta bawa mijina abinci ba.

Da na gama na kwashe kayan zuwa kitchen ruwa na dauko na zo fitowa muka yi kacibis da Tahir har kirjin mu na haɗuwa na matsa, muka kalli juna tare da tattausan murmushi tsakanin mu hannuna ya kama “Kin dawo?

Ya fadi cikin wata murya da sai da na ji ni cikin wani yanayi na daga mishi kai sai karaf idanuwanmu suka shiga cikin na Halima da ke maƙale tana kallonmu.Tunda ta dawo tana ɗakinta tana aiwatar da surkullen da sabon malamin da ta ziyarta a Ƙanƙara ya bata ya ce kuma wuyarta su haɗa ido da Tahir dole zai shiga taitayinsa sai yanda ta ce, duk da cewa tun dawowarta jiya aka bata miji kamar yadda ake yi a gidan to ita dai kam ka bata samu kwarin gwiwar fitowa ba, duk da tabbacin da malamin ya bata, ko kudin aikinsa rabi ya karba rabi ya ce sai ta ga biyan buƙata, wani mugun kallo ta bi mu da shi, ganin kamar ya manta inda muke yasa na bi ta gefensa na wuce hannayensa ya rungume a kirji ya bi ni da kallo har na shige, hakan kuma duk a idon Halima ta maza tayi ta karfafi zuciyarta ta tako zuwa ainahin cikin falon ta zauna, sai a sannan ya lura da ita, ƙara tamke fuskarsa ya yi, ya bi ta gefenta zuwa dakin Basma.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya 30Wa Gari Ya Waya 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×