Skip to content
Part 32 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

“Tahir” ta kira sunansa, bai amsa ba, bai nuna alamar ya ji ba ballantana ta sa ran zai waiwayo, tsaye ta miƙe “Tahir” ta kuma kiran sunansa tsaki ya ja ya shige dakin Basma. Ya ɗan jima ya fito, cikin rashin tsammani suka yi kacibis dan tana tsaye tana sauraren fitowar ta sa, ba zato idanunsu suka shiga na juna, wani sarawa ya ji kansa ya yi ya dafe kan, sai ya fasa shiga dakin Ummulkhairi da ya yi niyya dan Latifa bata gidan, juyawa ya yi ya nufi sama da shigar sa zama ya yi kawai hannunsa na dafe da kan har lokacin.

Halima kuma ganin halin da ya shiga da haɗa idonsu, ya firgitata, saurin juyawa tayi zuwa nata ɗakin tana shiga wayarta ta lalubo ta kira lambar malaminta cikin tashin hankali, ko gaisawa bata bari sun yi ba ta kora mishi halin da Tahir ya shiga da hada idonsu. Wata irin dariya ya kece da ita, “Shaidar aiki ya ci kenan, Hajiya, yanzu abu daya ya rage ya ci hadin maganin da na hada miki yana ci an gama, zai dawo mai jin maganar ki, kimar ki da darajar ki da kika rasa za su dawo, babu kuma wadda za ta sha gabanki.”

Murmusawa tayi tana zuba mishi godiya jin ana knocking yasa tayi mishi sallama ta bada izinin shigowa me girki ce, sai da ta gaishe ta cikin girmamawa kafin ta fada mata ta shirya tebur ok kawai ta ce tana fita ta bi bayanta, tana buɗe abincin tana tunanin yanda za ta zuba abin da aka bata Tahir ya ci shi kadai. Ta ɗan jima cikin tunani kafin ta samo dabarar da take ganin za ta fish she ta, falon ta koma ta zauna har aka kira sallar magrib sai da Tahir ya fito dan tafiya sallah sai ta koma ɗakinta, wanka tayi ta gyara jikinta, sai ta kuma fitowa falon ta samu Latifa wadda tun dawowarta sau daya su ka ga juna, sun gaisa sama sama.

Ni ma da nake zaune ɗakina ina ta sa ran Tahir zai shigo duba ni, har dai na ma cire, kamar in share fita cin abinci sai dai na fasa, ƴar kwalliya nayi sama sama sai na fito.
Duk kan su na same su zaune, mun gaisa da Basma da Latifa, Halima ce ko arzikin kallo ban samu ba, tana ta hura hanci tana shan ƙamshi.
Saukowar Ogan yasa duk aka miƙe zuwa cin abincin, kaɗan na ci dan cikina da na ji ya cushe, shi ma Ogan zama ya yi yana aikinsa a laptop ɗinsa.

Kowacce ta nemi wuri ta zauna, da kansa ya nemi Halima ta kawo mishi coffee abin da ya yi bala’in mata daɗi har mu ma sai da muka gane canjawarta, na miƙe tsam sai nayi musu sai da safe, ta kasan idanu ya bi ta da kallo sai da ta ɓace wa ganinsa.

Ina shiga ɗaki gado na faɗa na daɗe ina zubar da hawaye, dan da gaske raina ya ɓaci da rashin samun marabar kirki daga gare shi, kiran Asiyar Dr da ya shigo wayata yasa ni share hawaye na daga kiran muka shiga hira kamar komai bai faru ba.

A wannan daren Halima ta samu mijinta yanda take mafarkin samu. Ya kuma mallaka mata makudan kudade kamar yadda ta buƙata, ta ce ya saya mata sarƙa nan ma bai musa ba ya amsa.

Da safe da ya shigo dan mu gaisa babu wani sakin fuska a tare da shi, ni ma sai na daɗa kama kaina, dama zaune ya same ni inda nayi karatun Alkur’ani, ina Azkar, da ya fita ban wani bi shi da kallo ba.

Miƙewa kawai nayi na kunna Tv na koma na zauna na ɗauki wayata, WhatsApp na shiga, sakonni suka yi ta antayowa daga kunna Data ta, duk yawancin su daga ƴan’uwana ne bin su nayi ina ta mayar musu da amsa, kafin muka shiga hira da Aunty Laila, magana muka yi tayi kan shagon mu na ɗinki, tana min bayanin yanda abubuwa suke tafiya, da shawarar da Mominta ta kawo mu bude Branch a Kaduna. Na ce zan yi wa Tahir Magana ya samo mana wuri.

Ta ce Manager na wancan wurin namu na Lagos shi zai nemi ma’aikata duk wanda aka yi wa interview ya haye shi kenan sai a ɗauke shi idan Allah yasa wurin ya daukaka kamar yanda na Lagos ke samun cigaba, sai mu raba kawai kowa ta ja ɗaya. Na ce “Hakan ya yi Allah ya shige mana gaba. Ta ce tana nan zuwa min kwana biyu. Na ce “Na dai ji ki Aunty Laila, Allah yasa da gaske kike” mun ɗauki dogon lokaci kafin na kashe datar.
Ɗakina na gyara zuwa bathroom, nayi wankana na gyara jikina. Bani da niyyar fita dan yin break fast, kwanciyata kawai nayi bisa sopa.

Tahir na barin gidan, Halima da ta dawo rakiyar sa ɗakinta ta faɗa ta lume a kujera tana kaɗa ƙafa cikin nishaɗi sai sakin murmushi take.

Knocking din da aka soma yasa ta tsuke fuska, tana bada umurnin shigowa, Latifa ce ta shigo ganin ta bai sa ta saki ranta ba, hakan bai damu Latifar ba sai ma murmushi da ta saki “Hutawa kike kenan? Ta faɗi tana kokarin zama, kallo Halimar ta bi ta da shi bata yi magana ba, bata damu ba ta cigaba “Yarinyar nan da ta dawo jiya, ita za tayi girki koko waccan shashashar, sauna me daɗin kishi? Kyaɓe baki tayi “Ke ma kin san dole ita da ta dawo tafiya ita za ta karɓa”. Siririn tsaki ta ja kafin ta farga da wayar da Halima ke miƙo mata.

“Meye a ciki? Ta tambaya tana mika hannu “Ki duba” Halima ta faɗi tana wani shu’umin murmushi. Zumbur Latifa ta mike kafin ta koma ta zauna tana share zufa kamar ba sanyin Ac a ɗakin. Ashariya ta lailayo ta antaya “Lallai ma a gaida Namiji munafiki, duk cikin mu wake da irin wadannan mahaukatan gwala gwalan? Koko zai ce ba shi ya saya mata ba.”

“Kema kya fadi, haka tayi ta ke ce raini da bikin nan, ta saka wannan ta fidda wannan”
“Lallai ma in ni ce, idan na yarda Allah ya tsine min, kuma girkin da za ta yi yau sai na bata mata daren.”

“Me za ki yi mata? Halima ta tambaya “Girkin zan lalata, yanda ko uwar su ɗaya da mijin ƙarshen soyayya ba zai iya ci ba, dama ina da takaicin yanda yake buɗe ciki a duk ranar girkinta, ita ga gwana”, ƙwafa tayi sai ta miƙe ta bar dakin. Wani malalacin kallo Halima ta bi ta da shi ta fara magana ƙasa ƙasa “Gaba ɗayanku, zan gyara wa kowa zama, duk kan ku sai kun fice kun ban wuri, dama wuyarta in kama Tahir a hannu.”

Sai ta janyo wayarta, malaminta ta kira ta fada mishi aiki ya ci fiye da tunaninta dan haka ya turo acc no ta ingiza mishi sauran kuɗaɗen aikinsa. Ta ajiye wayar da sauran murmushi kan fuskarta tana kara yaba iya aiki na sabon malamin nata, jininta na al’ada kawai ya nemi ta kawo da shi ya haɗa mata maganin da za ta rika zubawa Tahir a abinci, sai wani ruwa da ya bata ya ce ta shafa a fuskarta, suna haɗa ido da Tahir an gama. Tuna wani tayi da ya sa ta ta rika tsarki, ruwan ta rika dafa wa Tahir abinci duk da tabbacin da ya bata mallaka ce ta gaske bai hana Tahir ya subuce mata ba, dan haka dagewa za tayi wurin wannan mutumin bakin rai bakin fama.

Sai wuraren Azahar na fito na nemi abin da zan saka ma cikina, ina kuma gamawa na koma ɗakina, ban ga kowa ba sai sabuwar me aikin nan tana ta kokarin haɗa abincin gida, duk da dai Indo ta bi ni har daki mun gaisa.

Da cin abincina barci na shiga yi, cikin barcin na ji ana knocking ba da so na ba na tashi na buɗe, Latifa ce cikin murmushin ta da za ka rasa in da ta dosa tayi min godiyar tsarabar da na aika musu, ta ce “Na ji ki shiru shi ne na ce matar nan ba za ta shiga kitchen ba? Dan murmushi nayi Zan shiga, barci ne ya kwashe ni, na gode. Ta juya, na shiga ɗaki ruwa na sha sai na ɗaura dankwali fitowa nayi zuwa sama kamar yanda nayi zato dakin Tahir ba shi cikin kintsi, kwashe komai nayi boxes ɗinsa nasa a laundry na wanke na canza bedsheet din na share ko’ina na goge na fesa air freshener kafin na kunna turaren wutar da na ruko.

Sa’adda na sauko uku tayi dakina na wuce saboda haushin da Tahir ya bani na kudurta ba zan yi girkin ba yau me aikin tayi.
Da daddare ma kamar in ki fita cin abinci, sai na yi gudun ja ma kaina laifi, ina kuma gama ci na koma dakina, wanka nayi dan tun na safe ban ƙara ba, nayi yan shafe shafe sai na hau gado, shigowar saƙo cikin wayata yasa ni duba wayar, daga Tahir sakon yake “Ina jiranki” shi ne abin da sakon ya kunsa. Na harari wayar kamar Tahir din ne gabana ya iya min wulaƙanci amma kuma ya san ina da amfani a wurinsa ai da sai ya riƙe ginshirar tasa, cikin sauri na ƙara gyagygyarawa sai na fita zuwa saman.

Ban same shi a falo ba sai na wuce bedroom kwance na same shi ɗaiɗai bisa gado daga shi sai gajeren wando kirjinsa da ke kara dulmiyar da ni a kaunarsa waje, waya ce aje kusa da kunnensa a hands free take yana amsawa, kirjinsa yake shafawa da hannunsa, dakin ya ɗauki sanyi da ƙamshi me daɗi. Hannun ya miƙo min alamar in zo gare shi kawai sai na ji tunani ya zo min wai duk sauran ma haka yake musu ko? jin raina ya soma jagulewa yasa na fara addu’ar neman tsari da shaidan, na yaye hijab din da na ɗora saman wata sakaryar rigar barcin da na sa da dan rashin kirkinta ko hannu bata da shi.

A hankali na ƙarasa yasa hannun ya janyo ni, ya kwantar da ni gefen kirjinsa sumar kaina yake shafawa, yayinda ni kuma nake shaƙar daddaɗan ƙamshin da ke fitowa jikinsa, wata irin kaunarsa tana fizgata, ina kuma sauraron hirarsa da abokin wayar tasa. “To yanzu dai ya ka ji girkin na ta? Muryar na cikin wayar ta ratsa dodon kunnuwanmu, dan tsaki Tahir ya ja “Ta iya abokina, amma ni mutum ne da na fi son in ci abincin da matata ce ta girka ba wata macen ta daban ba.”

“Daga dai an samu nasara girkin Laraba ya yi maka, shekarar ta kusan shida tana yi wa Habiba girki, na haƙura na bar maka ita ne dan ka samu maslahar rigimar girki a gidanka, ka haƙura da dole sai ka ci abincin da matanka suka girka maka, ba dole komai kake so kake samu ba, daga dai Allah ya yi maka gata ya baka matan nan har huɗu kawai yi ta cin duniyar ka da tsinke mutumina ka bar mu da ɗaiɗai, ko fa goyo ka ce kana so rige rige za ka ga a…”

“Dalla wuce mutumin banza kai dai dan iska ne Usama”. Dariya Usama ya kwashe da ita Tahir ya katse kiran. Yasa hannuwansa ya rungume ni “To ya aka yi” ya ce min cikin rage murya kai na girgiza gane hira yake so muyi dan sai cewa yake in ba shi labarin tafiyar, sai na ga bari in yi amfani da wannan damar in roke shi shawarar da na yanke sa’adda na je Dutsinma, ina so ya bar ni in rika zuwa makarantar Isamiya ta Kawu Attahiru, kusa da gidan Kawun take babbar makaranta ce da matan masu hannu da shuni da yaran su ke karatu. “To ai iyakarta Sanawiyya, kuma ke kin gama Ummuna” Na ce “E zan riƙa shiga Alhamis ne da juma’a duk littafin da kake so za a yi maka. Ya ce “Har yanzu karatun duk da kika yi bai ishe ki ba? Na daga kai “Karatu ai baya isa kuma ba a gamawa” ya ce “Haka ne” mafari kenan da na soma zuwa karatun zaure a makarantar Kawu Attahiru.

Zuwa safiya na nemi haushin da nake ji na Tahir na rasa dan tarairayar da na sha a wurinsa. Dan haka washegari zagewa nayi nayi mishi abinci wanda na san zai kayatar da shi zuwa magrib na kammala komai, ɗakina na shiga dan in shirya wanka nayi na fesa kwalliyar daukar magana dan wani dakakken less na sanya da aka yi wa dinkin da ya ƙara fitar da shi, na fiddo sarƙa da yankunnayena da zabba da awarwaro na ƙara ƙayata kwalliyar, nayi ɗauri me kyau ga sassanyan ƙamshi ina yi na zura takalmi na fito bakina ɗauke da addu’a.

Fitowata tayi daidai da shigowar megidan kallo ɗaya ya yi min ya nemi haurawa saman sa, na dan ƙara sauri na karbi ledar hannunsa na bi shi a baya muka haura tare, ban bi ta kan Halima da Latifa da ke zaune muna shiga kayansa ya shiga cirewa yana gamawa ya juyo inda na zauna shiru ina duban sa, kamo ni ya yi sai ya sa ni jikinsa, al’amuran da ya shiga gudanarwa ban tsammaci zuwan su a lokacin ba kan ba yanda zan yi na biye mishi har ya samu nutsuwa, da gamawarsa tsallake ni ya yi zuwa bathroom dinsa, ni ma miƙewa nayi ina diban kayana da ya ciccillar na maida a jikina sai na sauka kasa dan komawa ɗakina, ban kalli inda su Halima suke ba dan zargin da na san za su yi da daɗewa ta a dakin nasa, ina shiga bathroom ni ma na shiga nayi tsarki da ruwa me dumi ban da lokacin wanka kayan ma ina tsoron canza su sai na fito kawai fitowata ta kara yin daidai da ta megidan dan haka sai na isa dinning nayi saving ɗinsa, su Latifa ma kowacce ta zuba wa kanta, watso da lomar farko da Latifa tayi kowa ya yi saurin duban ta kafin Halima da Basma su ma su bi bayanta megidan ne na karshe dubana ya yi.

“Me kika sa wa girkin ne Ummulkhairi? “Me nasa kuwa? Na fadi cikin mamaki “To ai sai ki ci ki ji” ya fadi cikin hasala cin nayi kuma a take na maido shi, dan kasa ce hade da kalanzir.

“Kasa kalanzir a girkina? Na fadi kamar zan fashe da kuka “Sai a kula a san irin kwamacalar da za a rika baiwa mutane da sunan girki.” Cewar Halima tana barin wurin. “Ina ruwan gwanaye”. Latifa ta fadi da wata yar dariya da za ta fahimtar da kai nishadin da take ciki. Tahir ma miƙewa ya yi ya haye saman sa kafin ya sauko riƙe da keys ɗinsa a hannu Basma dai umarni ta baiwa Laraba ta daho mata indomie ta kawo mata ɗakinta. Halima da Latifa na zaune cikin falon na wuce su zuwa ɗakina zuciyata na tafasa na tausayin kai irin zaman kaddarar da Allah ya doro min, na jima kafin na shiga bathroom na tsarkake jikina na fito na sanya kayan barci Addu’o’i nayi tayi iya sani na har na samu gwanin iya sata ya sace ni.

Latifa da Halima kasa barin falon suka yi har maigidan ya dawo sai sha biyu saura da suka tabbatar ba za ni turaka ba kowacce ta nufi ɗakinta cikin farin ciki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya 31Wa Gari Ya Waya 33 >>

2 thoughts on “Wa Gari Ya Waya 32”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×