Skip to content
Part 33 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Shi kuma megidan ganin har sha biyu ba ni ba labarina yasa mishi ɓacin rai dan bai san dalilina na yin hakan ba. Ga ɓacin girkina a yau wanda ya rasa shi ma abin da ya ja hakan. Ko da gari ya waye ban yi yunkurin fitowa dan samar da abin karyawa ba.

Knocking din da na ji ana yi muna tsaka da chat da Asiya ya daure min kai, na dai mike na buɗe, Laraba ce mun gaisa cikin mutunta juna kafin ta nemi izinin a akan me za a yi yanzu da safe? Na ce tayi yanda ta saba yi na maida ƙofata na rufe. Tahir na tashi da safe haushin rashin shigowata yasa ya fita da wuri zuwa makaranta, bai tsaya sauraron kowa ba ko wani abin karyawa.

Sai da na gama duk abin da na saba yi a ɗakina, kafin na tura mishi txt zan shiga gidan Kawu Attahiru, tsarabar da na dawo da ita na debi me yawa dan kai wa Hajiyar, da zuwa na ban wani jima ba na juyo kitchen na shiga dan dama kunun gyada da na ji ina sha’awa, Sallamar da na ji ana yi ta sa ni leƙowa, wata dattijuwa ce, gajera me jiki, kayan jikinta sun dan sha jiki hijabin ta ma a juye ta sanya shi.

Suna riƙe da hannun juna ita da wata yarinya da ba za ta haura shekaru sha uku ba. Sannu da zuwa nayi mata fuskarta ta washe da fara’a, tana amsawa fitowa sosai nayi ina gaishe ta, muna cikin gaisawar Latifa ta fito, kallo ɗaya tayi wa inda muke tsaye na ga tayi kicin kicin dattijuwar ta kara fadada fara’arta tana duban latifa, magana tayi cikin yaren su wanda ban taba jin tayi ba, sai dattijuwar ta bi ta a baya zuwa dakin Latifar.

Dogon tsaki Halima da ke zaune a dinning tayi “An dai tafka asara, kana cikin wannan daular uwarka tana yawo haka a tsiyace. Wani iri na ji jin zancen Halima, dan ko bata yi gwari gwari ba na gane wannan dattijuwar mahaifiyar Latifa ce.

Komawa nayi cikin kitchen din, cike da madaukakin mamaki magana ta gaskiya bai dace a ce an ga mahaifiyar Latifa a yanda na gan ta ba, to ita ko me take ci da abin da mijinta ke bata da ba za ta taimaki mahaifiyarta ba.

Na ga dai duk girkin da za ki yi na kwana biyu zai dauki kudade masu kauri ya baki, duk da cewar ba abin da za ki saya, haka zalika duk karshen wata zai dauki wasu kuɗaɗen ya ce kowacce ta sayi abin bukatunta, ko nan ina ganin za ka taimaki har yan’uwanka ba ma uwar da ta kawo ka duniya ba.

Na gama dama kunun na dauko na fito daki na shiga na sha, gama sha na sai duk kasala ta sauko min carpet kawai na bi na kwanta barci ya ɗauke ni. Na farka nayi saurin duba agogo lokaci ya yi nisa dan an kusa Sallar Azahar na fita dan kai cup din da na sha kunu kitchen in kuma ɗora abincin rana.

Latifa ta tare ni ta ce ogan na neman mu a sama. Saman na wuce Inda na samu Halima da Basma sai Latifa da muka shiga tare. Zaune yake a wata kujera da na ga yana zama ya yi karatu. Sannu nayi musu shi kuma na gaishe shi, wasu fararen ledoji da ke saman wani dan stool ya nemi Halima ta dauki daya ta miƙe ta ɗauka sai Basma sai ni Latifa ce karshe wadda na fahimci duk sadda za a yi rabo irin wannan sai ka gane bakin cikin ta a fuskarta na zamantowar ta ta karshe.

Ni dai godiya nayi mishi da fatan kara samun budi na alheri a wurin Allah. Na taso na tafi sai da na shiga daki na bude ledar, dankareriyar sarƙa ce, Dubai da ke ta sheƙin ɗauke idanu da yan kunnayenta ha da zobe.

Murna nayi sosai tare da ƙara mishi addu’a sai na adana abi ta wurin da na adana sauran. Sai na fita dan yin girkin na fara aikin Halima ta shigo tsaki na ji ta fara ja ban waiwayo ba ballantana in san abin da take wa tsakin “Ke Malama wa ya ce miki yana da bukatar wannan jagwalgwalon naki? da kika shigo ki yi wa mutane.

Na waiwayo na dube ta ban magana ba na maida kai na ci gaba da aikina. “Dama kin daina ba kanki wahala ki fita ki bani wuri, dan Ogan ya turo ni in sama mishi abin da zai ci.”

Ko da ban juyo ba hakika na ji abin, dan tsaki na ja “Dan Allah ki yi abin da ya kawo ki kawai, ba ruwanki da abin da nake yi.”

“Iyee lallai samun wuri, to nan in gaya miki gidana ne, ku ɗin nan duk raɓowa kuka yi ku ci arziki, kowacce sai da ta ga an tara ta zo a ci da ita, saura na aka samu ehee! Murmushi me ciwo nayi jin zancenta, “Ai sai ki zagi ƙaddara, Halima dan ita tayi aikinta har kika gan ni anan kike min gorin na zo kwadayi ko na tarar da sauran ki, dan ban da kaddara irin wannan matsayin da kike alfahari da shi ni ma shi na baro kuma…….Wani irin mari da ya shiga cikin idona yasa ni ganin wuta tare da daukewar ji na na wucin gadi yasa ni yin dif!

Bayan ƴan sakwanni na buɗe idona dan ganin wanda ya yi min wannan aikin. Tahir ne tsaye yana huci “Ke har kin isa kiran aurena da ke ƙaddara ce ta kawo ki? Shi wancan sakaran me ya fi ni? Ganin yanda har jikinsa ke tsima yasa na raɓa ta gefensa na fice kitchen din.

Latifa na gani cikin sauri tana niyyar barin kofar kitchen din, kai hatta Basma da bata shiga shirgin kowa na gan ta kusa da kitchen din, kenan duk murna suke da abin da aka yi min? Ɗakina na wuce idanuwana na zubar da hawaye, na hau gado na zauna tokare da kafafuwana, hannuna daya dafe da bangaren da Tahir ya mara wanda nake jin azaba na ratsa ni.

Nayi kuka tamkar uwata ce ta mutu, har na ba uku lada.Tahir shi ma fitowa ya yi daga kitchen din, ya nufi waje dan ficewa daga gidan, dan dama fitar zai yi ya leƙo kitchen dan ce ma Halima ta bar girka komai shi fita zai yi, dan bayan tashin kowaccen su Halima ta koma tana mishi kisisina wai da ganin shi bai ci komai ba, ita ba za ta iya barin sa da yunwa ba, bari ta shiga kitchen tayi mishi girki.

Duk da mamakin da ya rufe shi wai shi yau Halima ta damu da rashin cin abincin sa, sai ya ce kawai ta bari fita zai yi, ta dai dage shi ne ta fito, shi kuma ya isko ta kitchen din ne ya ce ta bari fita zai yi. Ya tsinkayi muryar Ummulkhairi tana fadin kaddara ce ta raba ta da tsohon mijinta, wanda yake jin bala’i bala’in kishin sa, ta haɗa shi da ita, shi shi Ummulkhairi za ta buɗe baki ta ce ƙaddara ta haɗa su.

Yasa key dan tashin motar ya bar gidan, amma ya kasa tashin ta, kwantar da kansa ya yi kan sitiyari wai shi yau da hannunsa ya mari Ummulkhairi, take nadamar kasa saita kansa ta shige shi. Fitowa ya yi sai ya rufe motar, ciki ya koma sama ya hau, zama kawai ya dafe kai, ya ɗauki tsawon minti talatin kafin ya yi amfani da abin da zuciyarsa ke gaya mishi ka duba yarinyar nan.

Ya mike cikin sa’a yana tura ƙofar ta ta buɗe bata sa key ba, bata falon sai ya wuce bedroom kuka take tana sheshsheka yanda bangaren fuskarta ya kumbura ya ba shi tsoro, ya taka har gaban gadon hannunsa ya kai jikinta ta ture hannun ta matsa, gadon ya hau sosai ya kamo ta buge buge na fara ina ture shi, jin yanda jikina ya dauki zafi ya kara ruda shi. “Dan Allah ka ga Tahir ka ƙyale ni.”

Saurin kallona ya yi jin na ambaci sunansa, abin da yasan ba nayi sam sai dai ganin yadda kwayar idona wadda ya mara ta koma ya kara daga hankalinsa.

“Yi haƙuri Ummulkhairi raina ne ya ɓaci ina jin kishinki me tsanani, ba zan juri kina ambaton wancan sakaran ba.” ta karfin tsiya ya samu nasarar matse ni jikinsa, sai rokona yake in yi shiru. Ni kuma kamar yana ƙara zuga ni, ga wani uban ciwon kai da nake ji wanda na san yawan kukan da nayi ne ya janyo shi.

“Ki tashi mu je Hospital” “Ka bar ni ba za ni ba idan ma mutuwa zan yi in mutu, dan na san bani da gata, ni ɗin kuma ba komai ba ce a wurinka.” “Ke ɗin ce ba komai ba a wurina? “E mana akwai wadda za ka yi wa tozarcin da ka min? Ka mare ni gaban kishiyoyi, duk cikin su wace ce za kayi wa haka. Sai na ƙara fashe mishi da kuka.

Saki na ya yi ya mike wardrobe dita ya bude ya soma ciro kaya, har ya dauko wata bak’ar abaya haɗe da gyalen ta, ya dawo gare ni ta karfin tsiya ya zura min, duk da zazzaɓin da ya rufe ni rokona ya shiga yi in shige mu je.

Na wuce yana biye da ni, shi ya rufe min kofa ya zura key aljihu har inda motarsa take ajiye, sai da na shiga na zauna ya zagaya ya shiga.Latifa wadda ke kallon komai ta window ta, tayi wurgi da dankwalin ta, “Kan bal balin bala’i” ta furta tana barin dakin.

Dakin Halima tayi wa tsinke, wacce ke kwance rub da ciki, farin ciki na ɗawainiya da ita. Karon farko daga yi wa Tahir maganar sarƙa ya saya ya kawo, duk da dai ba ita kadai ya saya mawa ba ta san zai yi wahala ya saya ita kadai, koma dai meye ta fada kuma anyi, ga kuma babban farin cikin ta marin Ummulkhairi da ya yi, duk da da ta tuna kishi ne me tsanani yasa shi yin marin, farin cikin ta kan ragu, kai ba za ta manta wannan rana ba.

Shigowar Latifa yasa ta daga kai, yanayin da ta gan ta yasa ta ce “Lafiya? “Ina fa lafiya” ta fadi tana wani uban numfashi “Kin san shegiyar yarinyar nan, tun shigowarki daki Sweety ya fada ɗakinta, yanzu kuma ya fito tare da ita sun shiga mota.”

“Haba dai? In ji Halima da ta mike zumbur! Baki ta taɓe, “Za ki iya lekawa window ki dan ban yi tunanin sun fita gidan ba” ilai kuwa, Halima wadda har hannunta ke rawa wurin buɗe window ta hangi ficewar Tahir gidan hada Ummulkhairi zaune ɗare ɗare gaban motar. Faduwa kawai tayi kan sopa tana da buƙatar kadaicewa a halin da take ciki, sai dai Latifa uwar san ganin kwakwab ba za ta bar ta ba. Jin shirun ta ya yi yawa yasa ta miƙe ta bar dakin tana wani killer smile.

Tahir na hawa titi ya dubi inda nake zaune na takure, hawaye na min zuba Wai ba za ki yi haƙuri ba Ummulkhairi? Banza nayi da shi wayarsa ya ciro bayan sun gaisa da wanda ya kira na ji yana tambayar ina zai same shi.Wata haɗaɗɗiyar Asibiti me zaman kanta ya kai ni, ko da tsaida motar sai da ya yi ta rokona in dai na hawayen ko dan jama’ar da ke kai kawo a wurin. Na share hawaye da gyalen rigar sannan na fito na bi bayan sa. Mun ratsa reception kafin muka wuce Office din likita, likitan na zaune a ƙayataccen Office din nasa ya zura wa system ido.

Dr Muhammad ya juyo gaba ɗaya yana duban mu, glass din idansa ya zare “Kai ba dai Madam ce ba lafiya ba? Tahir ya shafa kansa “Ita ce wallahi” “Zauna Madam Sannu da zuwa” sai kuma ya dubi fuskata “Subhanallah! Zama nayi kujerar da ya nuna min “Meke damun ki? Ya tambaye ni bayan ya karbi wata folder da wata Nurse ta shigo tana mika mishi “Ina jin zazzaɓi, sai kuma kaina da ke ciwo” “Fuskar kuma fa me ya same ta ta kumbura? Shiru nayi ban amsa ba ya Tahir “Me ya samu Madam a fuska kansa ya kara shafa “Tsautsayi aka samu marinta nayi” da sauri ya kai duban sa gare shi “Mari kuma? Marin lafiya ada fa na san kana shan maganin karfe, shi ne za ka hau yar mutane da mari so kake ta makance?

“Daina min wannan fatar da na shiga uku.”

Tahir ya furta a hankali kamar ba shi ya yi maganar ba. “Ba ka shiga uku ba sai ka ƙara, kana duban yanayin da take ciki ai komai tayi a yafe mata, mata masu juna biyu ai haƙuri ake da su ko? Gaba ɗaya Tahir ya zare glass din idonsa.”

Zancen juna biyu na ji kana yi wa kake magana me ciki? “Za ka ce min ba ka san tana da ciki ba? “Ciki kuma,? Tahir ya tambaya cikin matukar mamaki. “In kana tantama ai sai a gwada” “E a gwada, amma ina zaune da matar ka ce min wai ciki ne da ita.”

“Kwarai ciki ma har ya miƙa” Nurse din da ta fita ya kira ya ce mu je ta debi jinina a gwada a kuma yi min scanning, yana son result yanzu. ta amsa ta wuce na bi ta da ƙyar. Yana ganin mun fice ya ɗaure fuskarsa tamau “Amma saboda Allah me ya ja maka aikata abin da kayin? Dan tsaki ya ja “Na fada maka Tsautsayi ne” ya ba shi labarin abin da ya faru. Kai Dr ya girgiza “Dama mata na cewa mu maza wadda muka ga tana bin mu mun fi sauke sharar mu akan ta, in ba haka ba me tayi na duka?

“Ni fa idan Ummulkhairi tana son zaman lafiya ta daina maganar sakaran nan, dan da na tuna kafin ni Ummulkhairi ta san wani na kan ji kamar in hadiyi zuciya. Amma wallahi ina nadamar abin da nayi mata. Sai da ta debi jinina ganin halin da nake ciki yasa ta ce In kwanta. Anan aka yi min scanning, Sai ta je ta samu Dr ta gaya mishi halin da nake ciki sai ga su shi da Tahir, magungunan da ya rubuta ya aike ta ta karbo mishi, da taimakon ta na sha magungunan barci ya fara fizgata na ji ta kawo mishi result.

“To kai me musu kana kallon me matarka na ɗauke da ciki har ya kai watanni shida ba ka sani ba? Anya Tahir kana kula da Madam ɗin nan taka yanda ya dace? Iska ya furzar “Wallahi ba ta gaya min ba, ni kuma da ba sanin kan abin nayi ba. Indai ba ganin ciki nayi ya yi katoto ba” wayarsa ya zaro ya yi mata albishir bai bari ta gama murnar ba ya kira Kawu Attahiru da suka yi sallama ji ya yi kamar ya kira mahaifiyarta dan ya kamata ta sani sai dai yana jin nauyi ba zai iya gaya mata zance irin wannan ba.

Sai kuma ya tuna abin da ya yi wa Ummulkhairi idan ta fada wa iyayenta fa? Wata fargaba ya ji ta rufe shi sai kuma ya rika karfafa zuciyarsa Ummulkhairi matar rufin asiri ce, tun da suke bata taɓa kai kararsa ba, wannan ma in sha Allah ba za ta fadi ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya 32Wa Gari Ya Waya 34 >>

2 thoughts on “Wa Gari Ya Waya 33”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×