Skip to content
Part 34 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Shigowar Asiya wadda mijinta ne ya kira ta a waya ya katse mishi tunaninsa. Tana gaishe shi tana wucewa gaban gadon, ta kama hannuna ta riƙe cikin nata sama sama nake ganin ta dan barcin da ya soma cin ƙarfina “Me ya same ki fuska duk ta kumbura Ummulkhairi? Wani tube mijinta ya miƙo mata “Karɓi ki shafa mata.”

Ta karɓa ya dubi Tahir “Ina ganin fa za ka bar ta anan sai zuwa gobe” kai ya girgiza “Dan Allah Malam kayi mata abin da za kayi mata in ta sa abata mu je gida, sai ta gaya min abin da nayi mata ta ɓoye min wannan alherin da ya same ni.

Murmushi ya yi mishi “Amma dai ka haƙura ta warke ko? Kuma lallai ne sai ka bar ta nan ga Asiya sai ta kwana wurinta.” “Ni aikin me nake zan kwana da ita, bari in je gida in dawo.”

Cikin nishaɗi yake tuƙin tare da jera addu’a a cikin ransa Allah ya sauki Ummulkhairi lafiya ya kuma jikansa ya ba shi rayayye. Latifa gwanar zaman falo ita ya samu zaune. Shi ma zaman ya yi ganin fara’ar da ke kan fuskarsa yasa ta taya shi, tare da tambayar abin da ya same shi.

“Kin kusa yin ɗa ko ƴa” duk da faduwar gaban da ta ji sai da ta tambaye shi “A ina kuma? “Anan gidan daga wurin Ummulkhairi.”

Ba ita ba hatta Halima da ke fitowa daga ɗaki sai da tayi matukar kaduwa. Ganin kallon da yake mata yasa ta kirkiro fara’a, da saurin saita kanta daga daburcewar da tayi. Ashe kwanan nan za mu fara jin motsin yara, kai gaskiya na ji daɗi.”

Halima dai dan ta riga ta zo tsakiya ba halin ta koma ta iso ta zauna ita ma Allah ya raba lafiya ta ce wanda a ranta ji take ina ma duk su mutu wurin haihuwar daga ita har abin da ke cikin miƙewa ya yi zuwa dakin Basma, su biyun suka raka shi da kallo ransu fal baƙin ciki tamkar su binne kansu.

Yana tura ƙofar ya hango ta kwance riƙe da waya daga tsayen ya ce “Wai Basma ba ki gajiya da kwanciya? Birkitowa tayi tana kallonsa “To me zan yi? Dakin nata ya bi da kallo, duk da ba wani datti ya yi can ba, amma ya kamata a same shi a tsaftar da ta fi haka. Ko da dakinki kika tashi kika gyara bai fi ace kina kwance ba?

Taɓe baki tayi “Yar aikina ce, ka kore ta, ni kuma ka san ba zan iya ba” duban ta yake cikin mamakin ta “To kin kusa yin ɗa daga Ummulkhairi.” “Uhm” kawai ta ce ta maida kanta ta kwantar. Juyawa shi ma ya yi dan barin dakin, yana mamakin halayyar matan nasa wai duk mata haka suke irin wannan zaman?

Koko shi ne bai yi dace ba. Sam ba haɗin kai, ba me shan inuwa ɗaya da ƴar’uwarta, gara Halima da Latifa suma kuma hadin kan nasu bana Allah bane, kuma ba masu yawan tayar mishi da fitina a gida a sama da su. Ba wadda ya samu a falon ya wuce sama. Dr Muhammad ya kira ya tambaye shi ta farka? Ya ce “A’a amma Asiya na tare da ita” ya ce “Ok zai sa a dafa mata abinci sai ya zo da shi” Dr ya ce ya bar shi Hajiyarsa na hanya, za ta taho da shi.

Ya ce “To sai nayi sallah zan shigo” A dakin ya zauna har sai da aka kira magrib da ya dawo sallah ne ya ce masu zai koma Hospital dan an ba Ummulkhairi gado zai kwana wurinta. To kawai suka ce yasa kai ya fita, a hanya ya tsaya ya sayi lemo da Ayaba hada Kankana da Apple, kafin ya karasa asibitin.

Sosai ya ji dadin samun familyn Dr Muhammad bayan mahaifiyarsa hada kannansa sun zagaye Ummulkhairi, mahaifiyar Dr ke riƙe da Ummulkhairi ta matsa mata ta ci tuwon Semon da ta yo mata. An gaisa sun tambaye shi me jiki shi kuma sai godiya yake sun yi shirin tafiya suka bar su daga Asiya sai shi sai Dr da ya shigo daga baya. Kusa da ni ya dawo, “Ya jikin? Kallon sa nayi da kumburarren idona, ban yi magana ba.

Ya dubi Dr Muhammad “Wai ba abin da za a sa ma idon nan jan ya yi yawa? Wani kallo ya jefa ma shi dan har lokacin yana jin zafin sa kan abin da ya yin. Hannunsa ya kai kan wuyana “Babu zafi” sai sannan Asiya tayi magana “E zazzaɓin ya sauka”. Sai goma Dr ya tafi kai Asiya gida, tare muka kwana da Tahir, duk kuma kokarin Dr sai da na kwana da zazzaɓi, ciwon kan ne dai na ji sauki.

Tilas washegari ya fasa sallamata. Asiya ta dawo da safe da abin karyawa, haka ma na rana da daddare kuma ta kwana wurina dan ina ganin Latifa me girki ba ta amince da kwanan Tahir wurina ba. Sai da na kwana biyu sai ga su su duk kan su, daga irin kallon kurullan da suke bi na da shi, na gane labarin cikina ya je kunnuwansu, basu jima ba suka tafi.

Ranar da na cika kwanaki uku na ji sauƙi kwarai. Wanka nayo da ruwan da Asiya ta haɗa min dan duk kwanakin nan ma Tahir da sassafe yake zuwa idan ya duba ni sai ya wuce makaranta, sai kuma ya tashi sai ya dawo anan kuma yake hirar dare.

Asiyar na duƙe jikin gado idonta na kan wayarta tana latsawa na wuce ta na hau gado ina goge jikina da karamin tawul din da na rufe jikina, ƙasa nayi da zanen jikina na soma murza mai ina wa Asiya mita “Ni fa wallahi mijinki ya sallame ni, na warke” “Ai idonki bai gama washewa ba.”

Ta fadi ba tare da ta ɗago ba “E wannan kuma ai sai a hankali.” na bata amsa ina tuna duk a yan kwanakin nan take so ta ji me ya same ni a ido sai in bugar da ita. Murɗa handle din ƙofar da aka yi tare da shigowa gaba ɗaya yasa duban ƙofar a razane dan halin da nake ciki, sai dai haɗa ido da Tahir da nayi yasa na saki wata munafukar ajiyar zuciya kusa da ni ya zauna yana jifana da wani irin kallo ni kuma na daure fuskata, ci gaba nayi da abin da nake yi kamar ma baya dakin suna gaisawa da Asiya na mike na sanya kaya shi ma fita ya yi suka dawo tare da Dr Muhammad, Sallama ta ya yi bayan an bude min file na awo.

Muka dunguma zuwa gida sosai nayi mamakin rashin ganin Haj Hajara amma na bar shi a bata sani ba. Ba mu samu kowa gidan ba abin mamaki har Haj Basma, ni da Asiya muka wuni har kusan magrib sai ta koma gida na bi ta da dinbin godiya me yawa a bakina.

Ban san dawowar mutanen gidan ba sai bayan magrib suka rika shigowa da daidai suna gaishe ni. Wanka na lallaɓa nayi da ruwa me dumi sai nayi sallar Isha’i, mai na goga da turare na dan mutsutstsuka hoda wata doguwar riga mara nauyi Pink color an mata ado a kirji guntun hannu take da shi, da dan gyalen ta na yane kaina. Falo na dawo na kwanta ina duba wayata, shigowar Tahir yasa ni daga kai kamar yanda na koma mishi tun da ya mare ni bana mishi magana dan haka daga kallon ban ce mishi komai ba, ya ce “Ya jikin? Na ce “Da sauki.”

“Ya ba ki fito cin abinci ba? Kaina na langabar “Zan fito” “To taso” ban musa ba na mike ina bayan sa muka isa falon matan da ke zaune suka bi mu da kallo kadan na ci na mike “Ya ba ki ci da yawa ba? In ji Tahir kai na girgiza.

“Ya ishe ni” ban tsaya biye kallon da matan ke antaya min ba na koma ɗakina. Kafin in kwanta ya kuma shigowa, sai da ya ga nayi shirin kwanciya sannan ya ja min ƙofa ya fita.

Da safe ma yana dawowa Sallar Asuba ya shiga ya duba yanda na kwana ya ce min zai shirya ya fita zuwa makaranta, in ci abinci.” na daga mishi kai, na fito na ci abincin da su Laraba suka girka, ina ɗakina har rana mun yi waya da Asiya sai Aunty Kulu da ta kira dan jin lafiyata.

Har daki Laraba ta shigo sai da ta ƙara gaishe ni da jiki sai ta shaida min an kare abinci, na dan bata lokaci sannan na fito Latifa da Halima na kan dinning kaɗan na zuba na ci Halima ta turo mun jug din kunun Aya, raina na ji yana so, dan haka na tsiyaya na sha, na mike zuwa ɗaki gado na hau dan in yi barci kafin La’asar, na soma lumshe idona na ji marata ta tsira kan kace me mara ta hau ciwo mirgina mirgina na shiga yi ina kiran sunayen Allah can na ji bul! In duba sai jini na gani kuka na fashe da shi na rarumo wayata Tahir na kira yana dagawa na fashe da kuka “Me ya faru? Ban yi magana ba na cillar da wayar, ina ci gaba murƙususu banko ƙofar da aka yi da ƙarfi bai sa na ɗago ba sai muryarsa da na ji yana tambayata abin da ya same ni ganin jini a kafafuna ya kara daga hankalinsa, ciccibata ya yi ya fita dakin, sai da ya zaunar da ni kafin ya ja motar a sittin ya bar gidan.

Asibitin Dr Muhammad ya mayar da ni cikin gaggawa suka amshe ni suka shiga min taimakon da ya dace, sun samu nasarar tsaida jinin aka gunguro ni zuwa dakin da na kwanta. Office ɗinsa suka nufa da Tahir wanda ke cikin yanayin da indai kana da imani sai ka tausaya mishi, da lallami ya samu ya zauna, “Me ya samu matata? Shi ma wannan cikin na rasa shi ko?”.Ya kare fadi da damuwa me yawa a fuskarsa, “Ba ka rasa shi ba, mun yi iya bakin ƙoƙarin mu jinin ya tsaya kuma abin da ke cikin yana lafiya, sai dai akwai abin da matarka ta ci ko ta sha wanda yaso fidda cikin” take ya dau zafi.”

Me nawa yarinyar nan za ta yi min haka? In dan marin da na mata sau nawa zan gaya mata kuskure ne kuma na bata haƙuri. Cikin mamaki Dr Muhammad ke duban sa “Wa takan kai dai matan kawai ka tara amma ba ka san hallayar su ba. Akan me za ta zubar da cikinta?

Tun da take da abin ta tsawon watanni ka kama ta da wata alama ta son zubar da shi sai yanzu kwanaki uku da sanin ka, ba ma kai ba kowa ma, yarinyar nan ko Asiya bata gaya wa abin da ya same ta a fuska ba, duk kuwa yanda taso ta sani.” Jin zancen Dr yasa Tahir rage zargin ɗora min laifin zubar da cikina tunani me zurfi ya faɗa har bai san sa’adda Dr ya fita ba, kiransa a waya da ya yi yasa shi dawowa hankalinsa ya dauka Dr ya shaida mishi ya same shi dakin da aka kwantar da Ummulkhairi. Ya samu har Asiya ta iso dan gidan nata babu nisa da Asibitin, tana zaune kamar ta fasa kuka. Wasa gaske dai sai da na shafe tsawon sati guda a Asibitin. Kuma a zaman da nayi ne Dr Muhammad ya kuma min scanning ya gaya min abin da ya gani a cikina. Na roke shi da ya yi shiru kar ya gaya wa Tahir, ya ce shi ma akwai abin da yake hasashe wanda ya san tahir bai fahimta ba dan haka ba zai faɗa mishi ba.

A ranar da na koma gida Tahir da ya rako ni ɗakina sai da na hau gado na kwanta ya ajiye min wata yar jarka me ɗauke da ruwan zam zam daga Kawu Attahiru addu’a ce ya tofa ya ce a kawo min, sai kuma wata jarkar zuma ce me kyau mara gauraye ya ce “Baba ya ce ki rika sha safe da dare, sai zumar ita ma ki rika sha shan ta na sa a haifi yaro me hazaka.

Ki taimake ni, Ummulkhairi ki bar cikin nan shi ne cikon farin cikina”, ya juya ya bar dakin na raka shi da ido cikin matukar mamakin kalamansa da suka daure min kai. Me yake nufi da in taimake shi in bar cikin ni kenan nayi yunkurin zubar da shi, take wani takaici ya mamaye ni, dama ina lura da take taken shi a Asibiti sai ya yi ta wani cin magani baki na taɓe na isa gaban mirror ina kallon cikina wanda kamar jira yake a fallasa shi gaba ɗaya ya fito ko dan na rame ne? nayi fayau a yan kwanakin nan.

Na dade wurin kafin na koma na kwanta. Ban fita cin abinci ba duk da cewa ina jin yunwa, da wuri nayi shirin kwanciya cikin wata yaloluwar riga iyakacin tsawon ta gwiwa, kaina Calabar ce da Asiya ta min a Asibiti. Jin knocking yasa na nufi kofar tare da mamakin ko waye Tahir ne baki na tura na kauce daga kofar ya shigo “Me ya hana ki fitowa ki ci abinci? Ya tambaye ni yana kallona tura bakin na ƙara yi “Ba komai” “Ah ya ba komai? “In ci wani abu ya same ni, ace ni na zubar da cikina.”

Na fadi cikin kunkuni. Sai dai na gane ya ji dan kallon da yake min ledar hannunsa ya bude gasashshen naman rago ne yana fitar da tururi da ƙamshi “Oya zo ki ci, in kin ƙare rashin kunyar.”

“Rashin kunya kuma? Na fadi ina kara tura bakin, ban ƙi ba zaman nayi dan gaba ɗaya yawuna ya tsinke ya fidda juice din Exotic ya ajiye kusa da ni “Ki karbi girki gobe” ya fadi yana miƙewa tsaye sai ya bar dakin na bi shi da kallo ina taɓe baki, sosai na ci naman ina korawa da juice din wanda ko tsayawa neman cup ban yi ba, sai da na ji nayi kat sai rufe sauran na kulle kofata. Ko da safe ban fito yin break past ba sai da ya shigo da kansa ya ce ba fa zan karya mishi dokar gida ba kan wani tunani nawa na shirme. Ko da na fito yi nayi kamar ina ci nan kuwa ban ci komai ba, yana miƙewa ni ma na shiga kitchen dan dafa abin da raina ke so, hayaniyar da na ji falon ya dauka ne ya sani leƙowa, wasu mata ne su huɗu daya ce ke ta bala’i sauran na taya ta da ƙyar na gane kan me suke yi bashi take bin Halima wanda take ta bin ta ta ƙi biya,

Latifa na zaune tana kallon su, Basma ma na tsaye ta wurin kofarta. Mai gidan ne ya rika takowa steps cikin wani yadi yake da akayi ma dinki guntu half jamfa sai farin glass ɗinsa na rai da rai manne a idonsa bai sa hula ba sai takalmi cover shoes. Ya yi min kyau kwarai kallo yake bin matan da shi har ya karasa saukowa, ankara da sauran matan suka yi da shi yasa su yin shiru sai wadda ke bala’in, har sai da ya isa gaban su ta ankara shiru tayi ita ma tana girgiza jiki “Me ya faru? Ya tambaya cikin dakewa “Haj Halima nake bi bashi sai wahalar da ni take ta ki biyana.”

<< Wa Gari Ya Waya 33Wa Gari Ya Waya 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×