"Mai jego kin sha ruwan dimi." murmushi nayi me sauti "Ko ba haka ake cewa ba? Ban amsa ba na soma tambayarsa hanya ya ce "Alhamdulillahi, sai yanzu ake gaya min haihuwa, an ta kira na ba ta shiga wai wasu Sodangin sun iso.
Na ce ni ban yarda sunan su Sodangi ba korau sunan su dan sai da suka kore ni suka iso, ya ya lafiyar ku ƙalau? Kai na gyaɗa kamar yana kallona. "An ce min a gida kika haihu, akwai wata likita abokina zai kawo ta anjima ta duba ki sosai har yaran.
Na ce mishi. . .