Skip to content
Part 42 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

“Mai jego kin sha ruwan dimi.” murmushi nayi me sauti “Ko ba haka ake cewa ba? Ban amsa ba na soma tambayarsa hanya ya ce “Alhamdulillahi, sai yanzu ake gaya min haihuwa, an ta kira na ba ta shiga wai wasu Sodangin sun iso.

Na ce ni ban yarda sunan su Sodangi ba korau sunan su dan sai da suka kore ni suka iso, ya ya lafiyar ku ƙalau? Kai na gyaɗa kamar yana kallona. “An ce min a gida kika haihu, akwai wata likita abokina zai kawo ta anjima ta duba ki sosai har yaran.

Na ce mishi To” “Abin da duk kuke bukata ki rubuta mishi zai kawo, Aunty Kulu za su taso gobe zan aika akai mata key na ɗakinki ta kwaso sauran kayan dan Hadiza ta ce min kin dauko wasu, ni ma idan Allah ya tashe mu lafiya zan wuce port Harcourt, an tutturo min hotunan yaran” murmushi na ƙara yi.

Mun jima kafin na ajiye ina wa Latifa sannu wadda tun soma wayata ta shigo, gaishe ni tayi Hadiza ta kwaso mata yaran ta ce a bar su ta gan su, ta juya ta fita. Da daddare bayan kowa ya wuce sai bakin Haj na nesa suka rage, su ma suna falonta, daga ni sai Hadiza taba ni ta rika yi daga kwanciyar da nayi na juya baya.

“Ki tashi ki ga yaran nan, daga ba kowa dan ina kula da ke ba ki kalle su ba.” Zaune na tashi ina duban inda take miko min namijin, na karbe shi ina kare mishi kallo idan ka ji kalmar bahaushe da yake fadin kwabo da kwabo to yaron shi ne kwabo da kwabo da mahaifinsa ko da yake jariri. Addu’a na tofa mishi sai na kwantar da shi na karbi yar’uwarsa, ba a mamaki da ikon Allah ban da haka da nayi mamaki ita kam kamar an tsaga kara da mahaifiyar Tahir yanda Haj take farar bafulatana kyakykyawa haka yarinyar take.

Tahir shi mahaifinsa ya biyo shi da Hadiza, sauran yanuwansu ne ke kama da Haj. Ita ma na kwantar da ita ina ta kallon su ina jin dadi wai yau ni ce rike da dan kaina abin Allah har ma guda biyu. Washegari yan gidan mu suka zo. Yayyena ne gaba daya sai gwaggo wai matan yayyena su sai gobe dan kar su yi yawa, Hafsa ta riga su zuwa ita da malam har falon Haj ya shigo aka kwaso mishi yaran na fito muka gaisa ya dauki jariran ya yi musu Addu’a.

Yayyena sun wuni har yamma kafin suka tafi sai babbar yayata Aunty Maimuna aka bari za ta zauna da ni zuwa suna. A wannan haihuwa na ga jama’a dan yadda family su Tahir su ke da yawa mu ma namu haka, zuwa kawai ake daga Dutsinma. Ko da Tahir baya nan hidima sosai yake kan haihuwar.

Haj Hajara ta tafi Aunty Kulu ta iso ita da Kawu Attahiru wanda da ya dauki jariran hada kwalla ya share wai yau yayan Tahir ne a hannunsu, kamar yanda Haj ma tayi. Duk wani shirin suna Laila da Asiya ke gudanar da shi dan haka sai ana gobe suna suka iso, Su Halima da Basma ma sun iso tun da rana amma ni dai ban gan su ba sai da me gayya me aikin ya iso da yamma suka biyo shi suka shigo tare, Basma dai ta ce tana son su amma ita bata iya daukar yara ba, Halima dai ganin idonsa ta dauka, ba su wani jima ba suka mike suka fita.

Kallona ya yi bayan fitar su ” Kin yi kyau Maman biyu jegon ya karbe ki” murmushi nayi “Ya ya ba wata matsala ko? Kai na girgiza “Ba ka bar mu da ita ba” macen da ke hannunsa ta bude ido ya ce “Mamana ta tashi ” ya mike tsaye da ita tana kallon kwan lantarki “Me yasa ba ki koma dakinki ba? Ya jeho min tambaya dan shiru nayi kafin na ce “Na riga na haihu anan shiyasa ban koma ba.”

“Daga bakin da yawa a kai yan’uwanki dakinki” kai na daga mishi Namijin ya fara kuka saurin kwantar da macen ya yi ya dauko shi “Gyara to ki ba shi nono” nuku nuku na fara kafin na ciro ya sanya min shi a cinya na soma ba shi, shi kuma sai kallon mu yake macen da ya dauka ita ma ta sa ka kuka na ciro na hada su na shayar da su kamar yanda na koya.

Ya dauki tsawon lokaci tare da mu har sai da aka kira shi. Cikin lokaci kadan Hafsa sun saba da su Laila. Sai da muka yi barci Aunty Laila ta ciro sarkokina da ta tafi da su tun zuwanta ta canzo min wasu, da kuma kayan da zan yi kwalliyar suna, dan ita na ba kudade ta sawo min kayan ta kuma bayar da dinki. Su uku muka kwana Hafsa, Laila sai Asiya.

Safiyar suna yaran sun amsa sunan Zainab sunan mahaifiyar sa da Tahir sunan Kawu Attahiru Attahiru bugu da kari kuma da ya cinye sunan ubansa. Ya yanka wa yaran ragunan su biyu, sai Sa da ya ce ayi abincin suna da shi an kira ni dan tambayata yanda za a yi da naman san na ce a kira masu gashin nama su yi ta gashi a tsakar gidan duk wanda ya zo akwai masu rabo su kai mishi Laila da Asiya sun yi hayar wani shahararren gidan Abinci daga Kaduna su suka zo tun daga can an shirya runfuna da kujerun Canopy su suka yi ta raba abinci ga mahalarta sunan, an raba abubuwa da dama masu dauke da hotunan yaran, ya yin da nake ta shiga ina fita cikin shiga ta alfarma, kishiyoyina dai tun fitowa daya da suka yi ba su kara fitowa ba sai dai masu kai musu gulma su kai musu labari a wannan rana nayi kyau har na gaji na kuma samu alheri ko maman Laila Abin hannu na gwal da yankunne ta aiko wa Zainab sai kayan jarirai da zannuwa.

Kanwar Aunty Laila ma ta zo daga Katsina, Matan abokan Tahir sun zo sosai. Washegarin suna yan’uwana soya nama suka yi aka raba suka shirya tafiya zuwa gida, da gwaggo za ta ci gaba da zama da ni, sai ta bi su suka tafi ta ce zaman me za tayi uwar mijina da yan’uwan sa na tsaye a kaina. Na roki Hafsa ta kara kwana ta ce “Cab! dan ma ke ce Malam ya bar ni kwana biyu.”

Sun tafi sun bar ni da kewar su da tarin alherin da na yi musu ni da Tahir, Laila da Asiya ne suka rage sai gobe. Ranar da su Laila za su wuce nayi wankan safe kwalliya na yi cikin wata farar super riga da zane rigar ta zauna a jikina ga cikar jego nayi kaina kitso ne two step aka yarfa min sun zubo har kafadata takalmi na zura na yafa wani yala yalan mayafi sarkar da nayi ado da ita daga karshe ran suna English gold na sa a wuya da kunne sai bangul da zobuna suna ta sheki.

Na fito zuwa falo, yaran tun da aka yi musu wanka Haj ta goya Takwararta Mimi Hadiza ta goya Areef, ihu Aunty Laila da Asiya da ke zaman karyawa suka saka Wallahi me jegon nan kin hade, ko dai yau za a maida mahaifa.”

Kai na dafe duk da sanin da nayi Haj bata sasan, Hadiza kuma ta kauda kai, wuri na samu na zauna Asiya na daukata hotuna da wayarta “Dole ne angon karnin ya ga wannan kwalliyar.” ta tura mishi hotunan. Sai dai a daidai lokacin da hotunan ke shiga wayarsa yana zaune a falonsa na sabon gidan sa su Halima sun sanya shi tsakiya wadanda tun tashin sa suka ce suna son magana da shi abin da bai sani ba tun ranar suna matan uku suka hade kansu, dan shigar da me jegon tayi tayi musamman gwalagwalan da tayi ta sakawa da kayataccen shagalin sunan da aka yi ya daga hankalin Halima da Latifa, suka karanta ma Basma suka nemi hadin kanta, sun shawarta su ritsa shi kan ba za su yarda da wannan rashin adalci, Ummulkhairi ita kadai ce matarsa da zai rika kashe mata dukiyarsa su ko oho.

Hakan ko aka yi da wannan ta sauka sai wannan ta dauka yana sauraren su, wayarsa kawai ya jawo ya shiga kira. Su Aunty Laila suna ta min tsiya kiran sa ya shigo na dauka zan soma gaishe shi na ji ya ce “Ki zo yanzu ki same ni.” “Lafiya?

Na tambaye shi kit na ji ya katse kiran. Cikin jimami na sauke wayar ina fada musu abin da kenan. Sannu a hankali na fito mun gaisa da wadanda na gani a tsakar gidan har na isa kofar da aka yi wadda ita za ka shiga ta kaika sabon gidan na Tahir sai a sannan na ga sabon gidan, babu laifi tsakar gidan na da girma dakuna ne guda hudu kowacce ciki da falo da bayi sai na ogan shi ma haka, ban san wanne ne na shin ba sai na kira Hadiza a waya na tambaye ta, ta fada min sai na isa, da sallama a bakina na shiga falon, sai dai shi kadai nake tunanin ya amsa su ukun kowacce zaune take tana kada kafa.

Zama nayi kujerar da ke fuskantar wadda yake kai, shi na soma gaidawa, kafin na hade su duka na ce ina kwananku? “Ku maimaita abin da kuka ce” ya fadi yana duban su, shiru duk kan su suka yi, ya maimaita sai dai ba alamar akwai wacce za ta tanka ya maido dubansa gare ni “Ke Ummulkhairi ki ji tsoron Allah, ki sani akwai ranar da za ki tsaya gaban Ubangijinki na taba saya miki sarka ta gwal? ban da wadda na ba ku gaba daya?”

Kai na girgiza “Tsakanina da Allah ba ka taba saya min wani abu, ba ma sarka ba, sai ka hada mu ka bamu tare.” “Good to wadannan bayin Allan sun sa ni gaba kan na saya miki gwala gwalai kin yi fitar suna su ban saya musu ba, nayi miki zannuwa masu asalin tsada su ban musu ba, ko wancan zuwan sai da muka samu matsala da Halima kan na saya miki gwalagwalai ” Na fidda ajiyar zuciya “Ni ba ka sai mini zannuwa ba, kudade ka bani ka ce in sayi kayan da zan yi fitar suna, su kuma gwala gwalai ba lallai in tsaya fadin yanda na same su ba dan sirrina ne, amma ni bai bani kudin sayen su ba, sa’adda na saya ma bai sani ba.

Su ya duba “Lokacin da na saya muku mota wace ce ban ba kudade ba? Suka yi shiru ya tambayi adadin kudaden da ya ba ni ban ko numfasa ba na fadi ya ce wacce ce ban ba haka ba? Suka kara tsit dogon tsaki ya ja ya tashi ya fice, ni ma mikewar nayi na baro gidan na koma sasan Haj, na samu su Aunty Laila sun tafi gidan Aunty Kulu sayen turaruka, sai Azahar suka wuce tare da dinbin kayan suna da hada musu sai kalmomin godiya da nayi ta jera musu.

Bayan tafiyar su sai na ji duk ba dadi, daga ni sai Haj sai Hadiza. Da yamma nayi wanka jariran ma an musu suna ta barci zaune muke ni da Haj da Hadiza kamshin turaren wuta falon ke ta yi, Tahir ya shigo da sallama, gaida Haj ya yi muka gaida shi ni da Hadiza ya karasa inda suke kwance ya dauki Areef ya ce Hadiza ta dauko mishi Mimi bayani yake wa Haj gobe zai koma ta ce hada iyalin naka? Ya ce “Hada ma Ummulkhairi daga an yi suna.” salati ta rafka.

“Kai yanzu sai ka dauki wadanda yan bayin Allan, ka kwasar musu cuta, to ko za su koma sai yaran nan sun yi kwari, an nema musu magunguna su da uwarsu.” Bai kara magana ba amma a halin sa da na nakalta na san ransa ya so su da hukncin Haj, zama ya ci gaba da yi har sai da aka kira sallar magrib, ya fita zuwa masallaci. Washegari kuma ya tattara matansa suka koma.

<< Wa Gari Ya Waya 41Wa Gari Ya Waya 43 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×