Skip to content
Part 41 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Haka na daure har sai da na ji ta lafa min sai na shiga barci. Gabanin Asuba na farka marar ce ta ci gaba da tsungula min Tahir na kan sallaya ya yi sujjada ga mahallicinmu.

Har ya fita sallah ban samu na tashi ba, da kyar ta sakan nayi wanka hade da alwala, sai da na gabatar da Sallah na zauna nayi kwalliya Atamfa nasa ɗinkin doguwar riga.

Sa’ilin ya shigo “Lallai ma me cikin nan akwai kokari har kin yi wanka kin sha ado? Murmushi nayi ina gyara daurin dankwalina na gaishe shi ya jani zuwa bakin gado, hira muka yi ta wani lokaci kafin muka kwanta. Wayarsa da ake kira ta tayar da mu ya sa ta a kunne sai na ga ya mike ya fita kafin ya dawo ya ce in zo mu ci abinci na ji dadin abincin dan haka sosai na ci sai sha biyu ya yi wanka ya shirya sai muka bar gidan, shi ma damunsa aka yi tayi da kiran waya, ana tambayarsa yana ina?

Sashen mu ya shiga ni kuma na wuce na Haj Wanda na samu ya cika da jama’a. Hadiza da na hango ta sha kwalliya cikin wani rantsatstsen less na nufa muka yi wa juna murmushi “A kwana a hantse.” ta fadi tana kama hannuna zuwa dayan dakin Haj da ba kowa dan rufe shi Hadizar tayi ta nuna min kayana da ta kwaso min ta kuma gabatar min da duk abincin da aka yi na bikin, da ta diba ta ajiye min.

Na ce “Yanzu dai na koshi sai dai ko anjima.” Da ganin fuskar Hadiza akwai magana sai dai akwai yar nauyi tsakanin mu, ta dai ce min “Yaya Sodangi ya ninke matarsa” sanin inda zancen ya dosa sai nayi murmushi kawai canza kayan jikina nayi zuwa shadda ɗinkin doguwar riga, tun daga wuya kunnuwa da hannayena sun sha adon gwal walkiya kawai nake dan shaddar ba me ƙananan kudi ba ce takalmi da jaka na sa sai mayafi da na rataya a kafaɗata.

Muka fito Haj na ta nuna ni ga yan’uwanta da suka zo da jama’ar ta “Wannan ita ce matar Sodangi wadda ta ke riƙe min Autata.” Sai ka ji ana fadin Allah sarki. Karfe uku duk jama’a sun koma tsakar gida inda ake ta cashewa. Daga ni sai Haj da Hadiza Tahir ya shigo ya cire babbar rigar da ya sa sai ƴar ciki da wando yana zama Haj ta miƙe hurar da na ga tana ta damu ɗazu ta dauko mishi yana sha yana lumshe ido.

“Kamar ko kinsan ban ci komai ba Haj tun karin safe” ido ta fiddo “Duk abincin da aka fitar waje? Bari in dubo maka ba za a rasa abinci ba” “Huta Haj, ku ci abincin ku zan fita in nema, Hadiza kira Latifa” Ta tashi ta tafi text na mata na ce ta hado abinda za mu yi wa yayanta girki.

Sai da ta tsaya tayi blending din kayan miya kafin ta dawo, dan haka latifa ta riga ta shigowa an sha kwalliya cikin less kusa da Tahir tana gaishe da Haj. Na mike zuwa kitchen din hajiyar Hadiza ta mara min baya, jallop muka yi cikin sauri wadda ta sha kayan lambu da wadataccen naman rago, Hadiza ta markada min Aya muka hada kunun Aya wanda na jefa ma kankara na juye madara peak. A tire na jera na fito Hadiza ta biyo ni da wani dan stool na dora mishi abincin, Haj ta rike baki “Yanzu dan Allah zaman nan namu har kin yi girki?

Ni ko da nake ta jin kamshi ban kawo nan bane.” Na ce “Dan dai girkin plate daya Haj ai ba wani bata lokaci” kitchen din na koma ina sauraron farfesun kazar da na dora ma Haj ya karasa. A Flack’s na juye na dauko zuwa falo na dire shi gaban Haj, lokacin Tahir ya kusa tashin abincin gabansa, Haj ta bude tiriri da kamshin naman suka buge ta ta dago.

“Ma sha Allah, sannu Ummulkhairi Allah ya shi albarka, kina fama da kanki kika dora wa kanki aiki” murmushi nayi na zauna ina sauraron zancen da Tahir yake wa Haj kan tafiyar da zai yi gobe zai biya Kaduna su wuce tare da Halima, a Lagos din ma ba zama zai ba za shi wani aiki Port Harcourt. Latifa dai tana zaune kamar bata wurin jin anan Tahir zai bar ta sai na ga fuskarta ta canza. Ya juyo gare mu “Gobe idan Allah ya kaimu za a kawo furniture’s na dakunanku, kowacce sai ta je ta zabi daki a sabon gidan can, Sati guda za ku yi inna kammala aikin da ya kaini zan dawo mu tafi tare.”

Dan murmushin su na manya Haj tayi “Wannan cikin har zai kai satin? Tahir da kamar bai fahimci zancen nata ba ya ci gaba da maganarsa, kiran da aka aiko ana mishi yasa shi mikewa,

Latifa kamar tana bisa wuta yana fita ta bi bayansa. Tana shiga bedroom, dankwalinta da ta bata lokaci wurin daurawa ta fincike ta wurgar gadon kawai ta fada zuciyarta kamar ta fashe hoton Ummulkhairi kawai ke mata gizo shigar da tayi ta matukar sa ta kaduwa bata yi la’akari da tsadar nata less din ba. Ga zaman kauyen nan da Tahir zai ja mata, wai ta zauna har sati.

Wayarta ta jawo kawarta Fadila ta kira tana kora mata damuwarta hakuri ta bata, sai dai cikin zafi ta soma fadin “Wancan karan ma da ya sayi mota bai saya min ba cewa kika yi in yi hakuri kika hanani in yi magana, to wallahi yau zan yi maganar motar duk abin da zai faru ya dade bai faru ba.” Duk yadda kawar tata taso nuna mata su bi komai ta siyasa latifa birkicewa tayi.

Ana sallar Isha’i Tahir ya shigo sama ya same ta yana tambayar ta ci abinci tana maganar mota cikin mamaki ya ce “Wane irin zancen mota kuma za a yi anan, tun can ba a yi ba? Tana wani daga hanci ta ce “Na ga ba ka da niyya ne” ya ce “Ina da niyya zan saya idan lokaci ya yi, dan yanzu dai kina ganin hidindimun da ke gabana gini biyu nake, ko da na gama na nan, akwai na Kaduna. Daga murya ta fara ban yarda da sai wani lokaci ba a bani hakkina kawai yanda aka saya musu a saya min.”

Kallo sosai ya yi mata “Latifa, girma da arziki na dauko ki zuwa gidan mu, ka da ki neme ni da magana.” juya ido tayi ta ci gaba da fadin maganganunta san rai mikewa ya yi yana neman rigar da ya cire. “Ba zan iya kwana kina nema na da fitina ba, kuma ba zan biye miki ba dan gidanmu na kawo ki.” Ya maida rigar “Sai da safe” sai ya fice Wayata ya kira bata shiga ba, sai ya kira ta Hadiza lokacin muna dakin Haj da ba kowa daga ni sai ita, ni dai daga yin sallar Ishai da kyar na rube kayan jikina sai na sa wata riga iyakarta gwiwa, na kwanta ina kallonta tana amsa waya sai ta miko min jin muryar ogan yasa ni fasa tambayar ta waye.

“Ki fito ina waje” abin da ya ce min kenan ya kashe wayarsa bin wayar nayi da kallo cikin takaici ko tausayi ban ba shi ya ta do ni da daren nan siririn tsaki na ja sai na cicciba Hadiza da ke kallona ta ce Lafiiya? “Wai yayanki ne ya ce in same shi waje” cikin tausayawa ta miko min hijabi dogo har kasa na zura zan fito ta ce da kin dauki kayan da za ki sauya.”

Kai na girgiza bar su kawai.” Na sa kai na fita yana cikin motar, na bude na shiga ganin ya fara ribas na ce “Ina ce wurin Latifa za ka kwana yau? Wani kallo ya yi min nayi sauri na kauda idona, “Idan ba za ki ba in tsaya ki sauka malama, kema kar ki kara bata min rai.

“Shiru nayi gane ransa a bace yake. Hadiza ta iso jaka ta miko min tana mana sai da safe. Har muka je ba wanda ya kara magana. Ni dai gado kawai na nema ina zare hijab din sai na kwanta. Ina tunanin yau ba zai saurare ni ba, ganin yanda yake cika yana batsewa na soma barci sai jin mutum nayi a bayana, yau ma kamar jiya ciwon mara ya tado min, na kuma ta fama da shi har safiya, ko da ya ga yanda nake yi ya ce ya ya dai na ce ba komai.

Karfe takwas muka bar nan din, kudade masu yawa ya sallame ni da su, ya nufi wurin Latifa. Kamar yanda ya ce za a kawo kayan dakunan mu an kawo na tashi daga barcin da tun dawowata ya dauke ni dan na samu marar ta lafa Hadiza ta ce in zo mu je in zabi dakin ga Latifa can ta tafi, na ce ta zabar min dan wani ciwon marar da ya dawo sabo.

Tun ina yi ba wanda ya fahimta har Hadiza ta gane Haj ta kira nan take Haj ta kidime matar babban Yaya maman Sadika aka kira sai uwar gidan Yaya magaji suka tsaya kaina. An kawo mota ana cewa a fito da ni na ji wani ruwa ya keto gabana “Alhamdulillahi faya ta fashe in ji Maman Sadika in sha Allah an kusa bata rufe baki ba na fara wani uban nishi sai ga kai gaba daya sai dan ya fado, an dauke shi ana jiran uwa ta biya sai ga wani kan ya fara tahowa nishin na duka sai ga wani dan kasa sai mahaifa ta biyo shi.

Take gida ya rude da murna yau Sodangi ya yi yaya har guda biyu suma kuma Sodangin ne, kamar yanda Haj ta je biki gidan su ta haife shi mace ce da namiji. Ruwa aka dora matar babban yaya ta ce in hau gado in dan huta na girgiza kai na fi so in yi wankan da taimakon su na shiga bayin dan jin da nayi kamar iska za ta wancakalar da ni sa’ilin da na tashi. Na gasa marata da jikina da kyau kafin na fito na samu nurse din da yaya magaji ya turo ta iso duba ni tayi ta bani magunguna, na shirya cikin riga da zane na kwanta bisa gadon, yaran aka kawo min wadanda har an gama shirya su, yawan jama’ar gidan da baki yan biki yasa ban iya kallon su ba.

Kiran waya ya rika shigowa yan gidan mu ne, da wata ta tsinke wata za ta shigo Hafsa ma ta kira, can sai ga kiran Laila da na Asiya, su na san Hadiza za ta kira su. Gasashshen Nama aka kawo min wai in ci maganin kan baki Hadiza ta hado min tea na sha sai na gyara kwanciya kiran Aunty Kulu ne karshe sai na shiga barci. Bayan La’asar na farka.

Abinci Hadiza ta kawo min na ce ba zan ci ba sai ta kira Haj, lallashina Hajiyar ta kama “Abinci shi ne jego tashi ki ci” na tashi na ci, na gama na wanke hannu Hadiza ta miko min waya “Ogan bisa layi” na kai hannu na karba ina murmushi. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya 40Wa Gari Ya Waya 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×