Da rana muna zaune a falo ni da Hadiza, Hadizar tana danna wayarta ta saka yaran a kekensu ta ajiye su gabanta, Daada na kitchen madarar da ake hada musu da ita ta je dama musu, knocking aka yi Indo da ke tare da Daada a kitchen din ta fita ta bude. Wani kyakykyawan mutumi ne dogo fari ya shigo, sannu ya yi mana sai muka gaisa ya tambaye ni Halima na ciki na ce mishi "E" ya shige na dan taba Hadiza wadda ko dagowa bata yi ba ballantana ta gwada ta san da shigowar sa.
"Meye haka kika. . .