Skip to content
Part 44 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Da rana muna zaune a falo ni da Hadiza, Hadizar tana danna wayarta ta saka yaran a kekensu ta ajiye su gabanta, Daada na kitchen madarar da ake hada musu da ita ta je dama musu, knocking aka yi Indo da ke tare da Daada a kitchen din ta fita ta bude. Wani kyakykyawan mutumi ne dogo fari ya shigo, sannu ya yi mana sai muka gaisa ya tambaye ni Halima na ciki na ce mishi “E” ya shige na dan taba Hadiza wadda ko dagowa bata yi ba ballantana ta gwada ta san da shigowar sa.

“Meye haka kika yi saboda Allah bako ya shigo ki kasa daga ido ko sannu ya samu a wurin ki.” tabe baki ta yi “Ni ba shi ne damuwata ba, damuwata mu fita da sabuwar mota.” Na ce “In mun iya kenan” ta ce “Kai! Allah na ji Aunty Laila na cewa ta koya miki mota, zaman ki Lagos, ni ma zan soma koyo daga mun yi mota.” murmushi nayi na fadi “Allah ya temaka, amma ni kam kamar ma na manta tukin.”

Muna nan zaune Halima ta fito da mutumin yanzu ma sannu ya yi mana suka haye saman Tahir. Hadiza ta mike ta dauki Mimi ta wuce ciki. Daada na zaune tana ba Areef madarar Tahir suka sauko tare da bakon “Ya kamata yallabai ka saya wa Khadija foam a makarantar Hospital din mu, Tahir ya ce “Ai ni da har na saya mata dan ma bana nan ne.”

Ya ce “A’a dan Allah a saya mata a can” Ya ce “To zan shigo Asibitin naku sai ayi abin da ya dace. Ya yi min sallama ya fita. Kaina ya daure ina tunanin waye to wannan? Ban samu amsata ba sai da aka kwana biyu sai ga shi ya kuma dawowa da kuma ya tashi dawowa sai ga shi da form din makarantar da ya yi magana.

Ya same mu ni da Tahir da Halima ya mika wa Tahir foam din, sai da ya karba ya ce “Nawa ne? ban samu shigowa ba” kansa ya shiga sosawa “Ba sai an bayar ba ranka ya dade, a dai taimaka min in yi komai na shigar ta makarantar” murmushi Tahir ya yi ya ce in kira mishi Hadiza. Mun dawo tare da ita Areef na kafadarta Tahir ya ce ta miko shi.

“To ke Hadiza Kamal ya sawo miki foam yana roko ya yi hidimar makarantar taki, ki yi mishi godiya.” Kamar tana ciwon hakori ta ce “Na gode” ta tashi ta koma ciki Halima ta mike tana cika tana batsewa.” Kai yanzu Kamal dan karshen rashin zuciya har ka kara duban yarinyar nan? Ta wuce fuu! ta shige dakinta ta banko kofa, cikin sauri ya tashi ya bi ta yana shiga ya same ta tana huci, ai kuwa tana ganin sa tayi kansa da masifa.

“In ban da ba ka san ciwon kanka ba me za ka yi da wannan yarinyar? Sai yanzu na gane dalilin dawowarka garin nan, saboda ita ne ko? tun da ta dawo gidan nan ban taba kallonta ba saboda abin da tayi maka amma saboda kare ya cinye zuciyarkahar ka dawo mata” Jin ta numfasa ya ce “Hakuri kawai za ki yi Aunty, ban san inda zan kai son da nake mata ba nayi nayi in yakice ta cikin raina amma hakan ya faskara, ki yi min addu’a kawai.”

Tsaki ta ja “Kana saurayi ka rasa wa za ka aura sai bazawara dan ci baya sai ka ce ita kadai ce mace, ni ban ga wata tsiya da take da shi ba da ka ki aure tun gudunka da tayi ka zauna karatu.” Murmushin takaici ya yi ” Haba dai Aunty kya ce ba ki ga tsiyar da na gani ba, kamar ta daya fa da mijinki, kuma ke ma haka kika kafa zaman jiransa, kila dai mu jininmu ne haka.

Sake ya bar ta da baki jin maganar da ya yaba mata. Ya samu Tahir a inda ya bar shi, sun kara tattaunawa game da makarantar ta Hadiza sai ya mishi sallama ya bar gidan. Tun daga ranar ya maida gidan gidan zuwan sa, zai dauki yan biyu ya yi ta wasa da su amma ko sau daya wadda yake zuwa dan ita bata taba gwada ta san da zaman sa ba.

Har dai na gaji wata rana ya zo ya tafi duk dadewar da ya yi bata sa ya ga ko gilminta ba tana bed room tana barci, har kuma falona a ranar sai da ya shiga duka na dada mata a kafa ta tashi tana sosa wurin “Lafiya Aunty? Me yasa kike abin da kike yi din?

Kallon rashin fahimta tayi min “Ni kuma me nayi? Harara na bata “Saboda Allah abin da kike wa bawan Allan nan haka ya dace kayi wa wanda ke kaunarka? Murmushin yake tayi “Ni kam me zan ce mishi? Ni ban ma so dawowar sa gare ni ba, domin ban cancanci hakan ba, ban ma da idon da zan daga in dube shi.”

“Kuma ba shi zai sa ki ki ba shi fuska ba, ni ina ce ma godiya za ki yi wa Ubangiji da ya ba ki me tsananin son ki haka” shiru tayi kafin ta mike ta shiga wanka, sanda ta fito muna zaune da Daada a falona ina ba Mimi nono, Areef na bayan Daada, zama tayi tana sauraren mu dan labari nake ba Daada muka hadu da Daada muna ta bata shawara karshe ta ce ta amince.

Yana zuwa kuma a washegari ya aiko Hussaina wai yana son magana da ni wadda Tahir ya dauko da muka je tudun wada na ce ya shigo sai ga shi da sallamar sa mun gaisa yana rike da Areef ya ce “Wani taimako nake nema a wurin ki Maman yan biyu ” dan jim nayi kafin na ce “To Allah ya bani ikon taimakawa” ya ce “Khadija nake so ki yi wa magana tayi hakuri ta bani dama.”

Jin ya yi shiru na ce “Ba damuwa zan yi mata” ya mike yana min godiya. Yana kara zuwa kuma na shaida mishi ya mata magana a falona suka yi zancen ni da Daada muka fita can harabar gidan wurin rumfar shan iska. Halima dai bata nan dan wannan karon tafiyar ta ne, Basma kuma ta je Abuja ganin iyayenta, dama na ji Latifa na yi da ita Mata kamar mara hankali idan ta zauna bata taba sanin ya kamata ta je ta ga iyayenta ba.

Idan ta tafi kuma bata san ta dawo ba, shi kuma mijin da ba damuwa ya yi da ita ba, bai taba cewa ta dawo sai ta gaji. Dan haka wannan zuwan ma nike da shi tafiyar ma ni zan yi ta wadda nake ta tunanin yanda za ta kasance min ina fama da yan biyu, to na dai yi shiru in ga me ogan zai ce. Daren da ya zo muna kwance cikin dare bayan mun gama soyayyarmu, hannunsa na cikin gashina yana yamutsawa, “Na fa ajiye aikina Ummulkhairi.

Saurin raba jikina nayi da na shi na tashi zaune kamo ni ya yi ya maida “Saboda me za ka yi haka dan Allah? Akwai alheri a cikin aikin nan, me zai sa ka ajiye” Aikin nan ya nesanta ni da iyalina, na gaji da shi kasuwancina kara bunkasa yake a kullun, gidajen mai guda biyu zan bude ina ganin za su ishe ni rayuwa. Addu’o’i na shiga jera mishi kafin muka shiga barci.

Washegari Hadiza ta soma zuwa makaranta. Ban yi wanka da wuri ba sai da aka gama karyawa, ina gaban mirror ina kwalliya na ji muryarsa suna gaisawa da Daada labulai ya daga na dago na dube shi “In kin gama shiryawa ki same ni mota, ba sai kin dauko yara ba. Kai na daga mishi na gama zura kaya na fito na ce ma Daada za mu dan fita ta ce “A dawo lafiya” Kan bonet din motata na gan shi ina karasawa ya ce “Koma ki dauko keyn.”

Na juya sai na dawo dauke da shi ya shiga ya yi mata key, na bude na zauna a gefensa. Filin koya mota muka je ya gama min bayani sai dai ina rike sitiyarin ya ce “Anya na yarda ba ki iya tuki ba? Murmushi nayi masa “Aunty Laila ta soma koya min a Lagos, sai dai a tunanina na manta.

Mun dade a wurin kafin ya ce mu je gida, hancin motar na shiga cikin gidan Hadiza na fitowa daga motar kamal, kallo daya ya yi masu ya fita ya nufi masallaci shi ma Kamal din jirana ya yi na karaso muka gaisa ya fada motarsa dan barin wurin.

Tare muka shiga da Hadiza, Halima da muka gani tsaye tana huci Latifa kuma na zaune kan kujera, kan Hadiza tayo “Ke yarinya ki kiyayi kanki ki kuma kama kan naki ki fita rayuwar kanena, dan ba abin da zai yi da bazawara yana saurayi.”

Wani kallon banza Hadiza tayi mata “Ai sai ki fara fada ma kanen naki ya rabu da ni, ba ni za ki zo kina ma gayyar hakori a ka ba.” “Ai wallahi ya ci baya ya aure ki, dan ba zan taba bari hakan ta faru ba.” Wata shewa Hadiza tayi “Ai wallahi kuskure kato kika tafka da kika nuna min ba ki so, da kin yi wayo da ba ki bari na gane ba ki so ba, dan wallahi na saurari Kamal ne dan wadanda nake gani da daraja sun roke ni kan hakan, amma wallahi tun da kika nuna min bakin cikin ki a fili sai na auri Kamal kika ga hakan bai kasance ba to ki kaddara Allah ne bai yi ba, amma ba wani kulunbotonki ba.”

Shigowar Tahir sai Halima ta saka kuka ta nufi wurinsa tana fadin an sanya Hadiza tana mata rashin kunya tana zaginta, har tana ce mata mara wayau” “Ki dai ji tsoron Allah a ina na zage ki? Hadiza ta fadi “Ki yi min shiru! Tahir ya fadi ma Hadiza cikin daka tsawa ya haye saman shi Halima ta take mishi baya.

Muna zaune har mun manta sa’insar Hadiza da Halima sai ga Tahir ranshi a hade, fada sosai ya yi wa Hadiza kan abin da tayi wa halima ni kuma ya ce min bai kamata ina goya wa Hadiza baya tana ma wani rashin kunya a gidan nan ba.

Na bude ido “Ni kuma? Magana dai ai ta Kamal ce da bata son sa da Hadiza, mun shigo dazu sai ta tare ta, ni me na ce? Gyada kansa ya yi sai ya fice. Latifa ta iske Halima dakinta. Wani irin shiri suke a yanzu wanda ta kai har hada sirri suke, Halimar ta dube ta “Wai kuwa anya na yarda da ke ba abin da ke faruwa tsakanin sa da Ummulkhairi kina ganin yanda yake wani nan nan da ita, tsaki Latifa ta ja.”

Ni ma na fara shakkar abin, ina ganin sai mun hada hannu ko za mu yaki yarinyar nan, ki bari Basma ta dawo” wani mummunan tsaki Halima ta ja “Dan Allah kina maganar mutane ki bar sa wannan, in za mu yi abin mu mu yi kawai” kiran da ya shigo wayar Latifa yasa ta mikewa tana amsawa sai ta bar dakin. A daren ranar Har Tahir ya fito cin abinci Latifa me girki bata fito ba, tsaki ya ja bayan ya zauna dan fita yake son yi, a waya ya kira ta shiru bata fito ba bayan ta ce ga ta nan zuwa, kara kiranta ya yi Latifa da ke dakinta tana laluben glashinta da ya subuce dan yanzu an kai da magrib tayi in har ba glass din bata gani, tsoron fushin Tahir yasa ta laluba hanya tana fitowa dan tana so ta ce mishi bata ga glass dinta ba, ya kashe wayar.

Kowa ya hallara ana jiran me girki fitowar da tayi tana laluben hanya ya sa hankalin kowa ya koma kanta, Tahir ya ja tsaki “, Meye haka? Ta ce “Glass dina ne ban gani ba” wai sai ga mutumniyarta Halima na dariya kasa kasa, wani kallo Tahir ya mata ta gintse dariyar tana kauda kai. Halimar yasa ta je dakinta ta nemo mata glass din ta dawo dauke da shi a hannu tana dariya.”

Ke malama makauniya ai glass din da ka shiga yake.” latifa ta zaburo jin Halima ta kira ta makauniya, nan suka kama bala’i Tahir bai ce musu uffan ba tsaki ya ja ya bar gidan. Zuwa safiya sun shirya radam, dan Latifa bata da ruko da kanta ta nemo Halima.

Tahir kuma ya tattara su ya yi Asibiti da su, Latifa kan matsalar idonta, Halima kuma wai tana jin motsi a cikinta. Latifa aka fara dubawa, sai ya koma inda Halima take ganin nata likitan, scanning ya yi mata nan take kuma ya tabbatar musu da zargin da yake na ciki a jikin Halima har ma ya soma kwari.

Daga ita har Tahir kamar su ki yarda ya ce su je asibitin Dr Muhammad, ta ce “A’a su dai je wani wurin shi ma ba tare da latifa ba, ta roke shi kar ya fadi ma kowa. Sun taho bisa hanya ta fadi tana son Maltina latifa kuma ta ce tana son pad wani super market da ke bisa hanyar tasu ya yi shawarar tsayawa cewa ya yi su zauna ya shiga ya fito yana shigewa Halima ta hango wata mata tsaye rike da jaka Latifa take nuna ma ita “Kin ga waccan matar?

Matar abokin Tahir ce kawata ce sosai, sai mijin ya nuna yana son wata kanwata mafarin watsewar kawancen namu, kuma abin haushi da auren yar’uwar tawa ko shekara ba a yi ba ya watse, dan Haj Shema’u Shu’uma ce shiyasa wata ran da na tuna ta sai in ga da muna tare da tuni ta yi mana maganin shegiyar yarinyar nan.”

Latifa ta ce “Dan Allah? To mu kirata mana” Halima ta kara duban inda take tsaye kamar tana jiran wani “Anya za ta yarda? Sosai fa ta ji zafin abin nan” “Ke dai dan Allah mu je mu same ta” suka balle murfin motar suka fita zuwa inda take, ga mamakin su da fara’arta ta tare su suka gaggaisa ta tambayi Tahir Halima ta tambayi Engineer ta ce sun rabu shekaru biyu da suka wuce. Su Halima suka jajanta tare da tambayarta inda take a yanzu ta ce tudunwada sun yi musayar lambar waya suka rabu da alkawarin ziyartar juna.

Sun koma inda motar take Halima tana kallon wani kayataccen shagon dinki da aka rubuta Ummulkhairi fashion design ta taba Latifa “Ke kin ga wani hadadden wurin dinki latifa ta kalla suka ci gaba da yaba kyawun wurin da irin dinkunan da suka gani har Tahir ya fito yaran shagon na rike mishi da kayan da ya saya motar ya shiga yaron ya sa mishi kayan a boot.

Har ya ja motar yana jin matan suna santin wurin dinkin da zancen za su kawo dinki. Sai da ya juya ya dubi wurin kafin ya ce “Ai ta kwana gidan sauki dan yaruwarku ce me wurin.” har suna hada baki wurin fadin wace yar’uwar tamu kafin kwakwalensu su tuna musu sunan wurin.

<< Wa Gari Ya Waya 43Wa Gari Ya Waya 45 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×