Halima ta ci gaba da jinya a Asibiti cikin mawuyacin hali, gaba daya ta lalace. Wata biyu ta share aka sallame ta ba dan ta warke ba sai dai likitocin sun ce sun yi iyakar kokarin su sai dai ko zai fitar da ita waje, dan haka cuku cukun fitar da itan ya fara. Ranar da aka dawo da ita mahaifiyar ta da kannenta suna kokarin taimaka mata ta fito, Latifa ta fito daga ciki an sha gayu za ta shiga motarta ga glass din nan ya yi das ya zauna a fuska, sun kalli juna ita da Halima wadda ke kara jinjina rashin amana irin na kishiya tun kwanciyar ta Asibiti sau biyu kacal Latifa ta taba zuwa duba ta. Latifar kuma ta hade su duka tayi musu kallon hadarin kaji kafin ta ce “Sannun ku.” sai ta wuce abin ta.
Cikin wheel chair suke tura ta da Tahir ya saya mata dan saukaka mata wahalar tafiya, mahaifiyar ta na rungume da jaririn me suna Abubakar Sadiq sunan babban yaya an cire shi daga kwalba sai dai baya shan nono dan nonon ba ruwa duk yadda aka yi kokarin nemo mata abinda za ta sha dan ruwan nonon ya zo hakan ya faskara kawai sai aka ci gaba da ba shi madara aka bar ta ta ji da kanta. Latifa ta hau titi zuciyarta bakikkirin da ganin dawowar Halima kullun addu’arta Allah yasa idan gaban nata ya karasa rubewa ta mace a can kowa ya huta dan yanzu gidan ba karamin dadi yake mata ba ba Halima ga Basma ma bata nan ba ruwan ta da wannan dogon jiran kafin girki ya zagayo kanta, Basma ta kusa wata da mahaifinta ya zo ya tafi da ita wai waje zai fita da ita a duba ta kan matsalar rashin haihuwar ta da kuma lalurar ciwon kanta.
Ita ma fata take da shige shige Tahir ya aika mata da takardarta, sai ta ji da wannan shegiyar yarinyar da har yau ta kasa samun yanda za ta sanya mata amma dai a juri zuwa rafi ta bugi sitiyari “In Allah ya yarda sai kun bar min Tahir ni kadai, sabon gidan da ya kankara babu me shigar sa. A bakin Indo muka ji dawowar Halima na cicciba dan cikina ya fara nauyi ga gajiya da nake ciki ta sintirin zuwa gidan Asiya da ta haihu aka yi suna jiya, ta samu ya mace Hanifa. Sai da nayi wa Hadiza magana sau uku kafin ta yarda za ta wai kunyar mahaifiyar Halima take ji. Da sallama muka shiga falon duk kan su suna zaune cikin mutunci suka amsa gaisuwar mu dan su kam suna taya Kamal son Hadiza dan yanzu shi ne komai a gidan su, shi ke musu abin da mahaifin su zai musu shi ya zame musu uba duk da uban na su yana nan. Sai wani sussunnewa Hadiza take yi, ba mu jima ba muka mike da muka fito na sa Laraba ta kai musu abinci. Da daddare Kamal ya zo, wurin yayarsa ya fara isa kafin ya dire falona wurin Hadiza, mun gaisa za mu bar musu wurin ni da Daada ya ce yana son magana da ni sai na tsaya rokona ya yi in shawo mishi kan Hadiza ta bari ayi bikin su ba kamar yanda take cewa ba sai ta kammala karatu.
Na ce kar ya damu zan mata magana. Sai da muka yi shirin kwanciya nake mata maganar ta ce Ita wallahi tsoron auren sa take sai ta ga kamar dan ya rama abin da tayi masa yasa ya matsa lamba sai ya aure ta. Na ce kuma in haka ne sai ya ki aure tun tafiyarki sai ma karatu da ya koma? tayi shiru sai na bata shawarwari ta kuma amince dan haka washegari nayi mishi waya na sanar da shi amincewarta, bai yi kasa a gwiwa ba ya tura yan neman aure a gidan su na Kankara, sai dai yayyen Tahir sun ce sun bar komai a hannunsa daga shi ke rukonta. Shi kuma ya ce Kamal ya je ya shirya duk ranar da Allah ya sauke ni lafiya ranar suna sai a daura aure, Halima dai duk da halin da take ciki an ce bata so. Kwana uku da tsaida maganar na fara nakuda daga ni sai Hadiza muka nufi hospital na ce wa Daada tayi hakuri ta zauna da yaran dan Tahir baya gidan.
Cikin gajeruwar nakuda Allah ya yi ikonsa na sauka lafiya na samu da namiji shi ma din kamar sa daya da Areef duk sun dauko Tahir har dan wurin Halima duk kamar su daya. An sallame mu mun dawo gida, washegarin da na haihu Hajiyar Tahir ta zo sai da muka kwana hudu ta koma ba yanda bamu yi da ita ba ta bari ayi suna ta ki fafur ta ce suna na yara ne suna nan zuwa ita barka ta zo. Yan Kankara sun zo da yawa dan ban da suna ga daurin auren Hadiza yan uwan sa maza duka suka zo dan daurin auren suka koma da yammacin ranar yarona ya ci sunan mahaifin Tahir Abdurrahman wanda Tahir din da kansa ya fara kiran sa da Sudes, Hadiza dai ta ce bata tarewa sai nayi arba’in Tahir kuma ya biye mata.
Washegari yan suna suka koma har da yan’uwana, Laila bata samu zuwa ba dan kwance take sharkaf cikin laulayi, sai bana Allah ya kawo rabo, yan Kankara kawai suka rage. Halima da ta gaji da zaman daki kannenta suka gunguro ta dan ta sha iska, Latifa da ke zaune ta dora kafa daya kan daya tayi musu yatsinannen kallon da ta saba, ran Halima ya baci ta ce da dai ba mu san asalin Ungulu ba sai ta ce daga masar take karyar banza karyar wofi ” wata irin shewa Latifa ta yi ta daga wayarta da ta fara kukan neman agaji “Kawata ina kika shiga ina ta neman ki? Ki ji abin arziki, in ba ki labari sweetie ya biya min aikin hajji ga gidan mu da na turo miki hotonsa an gama za mu koma daga na dawo aikin hajji kuma sweetie zai canza min rantsatstsar mota.” ta dan saurara kafin ta sa shewa “Ai mu duniya sabuwa mu wanke goma mu tsoma biyar.” ta gama dararrakunta Halima da ta hana a gungura ta sai lokacin ta ce su wuce Latifa ta buga cinya.
“Sai dai mutum ya gan mu da miji, kwaalelen kare da hantar kura. Ko da su ka fita ba su wani dade ba ta nemi su mayar da ita ciki dan wani bakin ciki da ke cin ranta, suna dawowa falon anan kannen suka tsaya dan hoton wasu masu garkuwa da mutane da aka kama ake nunawa a tv falon, daidai nan “Ummulkhairi ta fito daga dakinta sakale da babyn ta cikin wani madaukakin mamaki da ya kama Halima ta ga Latifa tayi saurin tashi ta nufe ta cikin wata fara’a da girmamawa irin wadda ta rika yi mata ta karbi yaron tana tambayar ta kwanan su Mimi, sai da suka gama gaisawa Ummulkhairi ta karbi danta, ta haura sama Latifa ta isa step din benen ta fakaici idon kowa da ke falon ban da Halima da ke ankare da ita ta fito da mugun abin ta barbada Indo da take goge goge Halima ta duba “Indo yi sauri ki duba min dankunne na a kafar bene” cikin azama Indo ta nufi kafar benen dan tana kusa da wurin Latifa da ta bar wurin tayi azamar komawa dan tare Indo sai dai ta makara har Indon ta kai wani tashin hankali ta ji ya ziyarce ta.
Halima kuma ta shiga fadin “Muguwa, Azzaluma, yanda kika cutar da ni ki saurari naki, ba dai kin sa min na taka ba? yan’uwan Tahir da suka fito dan kallon abinda ake nunawa na masu garkuwa suka tsaya sauraren Halima cikin su hada mahaifiyar Halimar wadda ta tako inda yar tata take ta ce tayi shiru amma sai ta juyo ta dubi uwar “Ya za a yi in yi shuru Innai? Alhali na san abin nan ba shi da makari kuma wallahi Latifa ce ta sa min na taka ” cikin fushi uwar ta tare ta “Ke dai sam ba Allah a tare da ke Halima Allah ya jarabce ki ki dora abin kan wani? “Wallahi da gaske nake Innai, tare da ita muka karbo ni zan sanya wa Ummulkhairi ita kuma za ta sanya wa Basma, shi ne ta sanya min dan tana barin dakina ta kira ni wai in fito in sanyawa Ummulkhairi ta fito, ina kuma fitowa kaina ya sara.”
Uwar ta kama haba ta na tafa hannu mutanen wajen suka barke da salati “Ai shi kenan Halima kin kai ga yanda kike so, to yau WA GARI YA WAYA? kullun ina gaya miki illar biye wa rudin duniya da kike yi, amma ba ki ji yau kowaccen su na zaune lafiya ke ce cikin masifa.”
Halima ta fashe da kuka kamar yanda uwar ta ta ma ke kukan ta nuna Latifa “Wannan Azzalumar ta ja min” kukan kura Latifa tayi ta hankade Halima da ke kan wheel chair tana fadin ita za ta yi wa sharri Halima ta fasa kara ai kuwa kannen ta suka yi kan Latifa suka rufe ta da duka, duka kuwa ba na wasa ba duk tarin yan Kankara an rasa me matsawa ya kwace ta sai mahaifiyar su ke ta karajin su sake ta amma kamar ma tana kara zuga su, wata aka samu cikin yan Kankara ta kira Tahir a waya wanda ya yi sammakon barin gidan ta ce ya gaggauta dawowa gidansa za a yi kisan kai. An yi sa’a ya shawo kwanan layin zai dawo gidan shigowar sa yasa suka daga ta gaba daya sun gama yakushe ta sun yayyaga mata sutura ganin yanda Tahir ya tsaya cikin matukar bacin rai yasa Halima ci gaba da fadin Latifa Muguwa ce Azzaluma ita ta sa mata abu ta taka da sauran makirce makircen da suka yi tare ita ma Latifa jin za ta kwana ciki yasa ta soma ramawa tana fadin asirce asircen da Halima ta yi tayi kan zubewar cikunan Ummulkhairi har ma da Basma.
Nan fa suka yi ta tona ma juna asiri. Harde hannaye kawai Tahir ya yi yana jin sa kamar a sama wai shi Allah ya jarabta da wadannan iblisan matan? Wani gigitaccen mari da uwar Halima ta yarfa mata yasa ta yin shiru ita ma Latifa kuka ta shiga yi na tozarcin da yan’uwan Halima suka yi mata tsawa Tahir ya daka mata ya ce ta tashi ta fice mishi a gida ya sake ta ihu ta kwarma tana tuma tana faduwa yan’uwan Halima suka kamata zuwa dakinta, ita ma Latifa da lalube ta koma nata dakin dan an tattake mata glass dinta, wanda ta ce bata ga me fitar da ita ba. Yan Kankara sun shigo wurina suna maida yanda aka yi ina sauraron su, a bakin su na ji wai ita ma Basma da bata dawo ba ubanta ya kira Tahir a waya ya ce sabon gidansa kar yasa wa Basma irin kayan da zai sanya wa sauran matansa da ya ce saboda me ai shi duk daya suke a wurinsa sai ya ce ba daya suke ba Basma ta fi su domin ita din yar gata ce ya ce shi dai iri daya zai yi ya ce to ya bar na Basma zai yi mata order daga waje dan haka idan Tahir ya koma sabon gidansa ya kira shi sannan za ta dawo.
Shi ne matar Yaya Magaji ta ke ce min Ita waccan doguwar da ta ce an biya mata hajji da gaske take? Na ce Ban sani ba abinda dai na sani na ji wayar Tahir da wani abokinsa ya ce banda cuku cukun da yake na fitar da Halima waje ya so biyawa Latifa aikin hajji, amma yana ganin sai dai wata shekarar. Sun ci gaba da maida zancen sai dare Tahir ya shigo maigadi ya tambaya Latifa ta fita ya ce mishi A’a dakinta ya wuce kai tsaye ya same ta ya ce zaman me take yi mishi a gida? Ta ce ita dai ya yi mata hakuri ya maida ita ya ma za a yi ya sake ta ita kadai ya bar Halima?
Ya ce, “Ok dan na miki saki daya shi ne kike ganin kina da wurin zama to na cikashe miki saki biyun, kuma idan kika bari gari ya waye har na fito na same ki zan sa a fitar min da ke da kayanki.” Hannu ta dora a ka shi kuma ya sa kai sai ya bar dakin. Ta dade cikin tunani sanin waye Tahir kaifi daya ne yasa ta kiran Fadila kawarta a waya ta ce ta zo da sassafe ta fitar da ita da ta nemi jin yanda aka yi sai ta bata labarin komai. Da Tahir ya fito da safe ya ga ta tafi sai ya kira masu mota suka kwashe kayanta ya aika mata da su gidan su.
Wa gari ya waya 47