Gidan Kawu Attahiru ta nufa, ganin motarsa a harabar gidan yasa ta jin dadi. daga ƙofar falo suka yi kacibis da Haj Hajara, kukan da take rusawa ya tashi hankalin Hajiyar, tana tambayar lafiya.
Nan ta hau rattafo mata Tahir yana ɗaukar kwanan su yana kai wa Ummulkhairi. Sauran maganganun da take ba sakaye cikin su, yasa Kawu Attahiru wanda ya taso dan jin ihun da ta ke rafkawa, bai kai ga karasowa ba ya tsaya turus.
Hajiyar ma nauyi zancan yai mata, ta dai yi ƙarfin halin bata hakuri, har ta juya ta koma inda ta fito. Falon ta shiga ta samu Kawun ya yi jugum ga tagumi ya rafka hannu bi biyu, yana kakkaɓin wannan mata da Tahir ya auro, anya akwai ƙamshin tarbiyya cikin lamarin ta.
Wayarsa ya janyo ya kira Tahir kan idan yana gida yana son ganin sa. Ya ce “Ya fita yanzu sai dai bai yi nisa ba” Juya kan motar ya yi zuwa amsa kiran uban goyon nasa. Nasiha sosai da wa’azi ya yi mishi, kan zama da mace fiye da ɗaya, da wajabcin adalci a tsakanin su.
Ba kaɗan suka ratsa Tahir ba ya yi mishi godiya ya fito ya ja motarsa, yana tafe yana tunanin abinda ya kawo wannan nasiha da baban ya yi mishi. Da rana ya kira ni ina zaune cikin takaicin zaman da ake a wannan gida,gaba ɗaya zaman gidan ya ishe ni. Cewa ya yi in shiga kitchen in yi girki daga Basma bata gama wartsakewa ba.
Da wuri na shiga kitchen din na soma aiki, ina gamawa ɗakina na koma ina shiryawa na bar Indo tana gyara kitchen din. Kwalliya nayi cikin atamfa ɗinkin doguwar riga mai aljihu, na kashe dauri na fito ina tashin ƙamshi. Halima da Latifa na zaune wuri ɗaya, ni ma wuri na samu na zauna dan doka ce jiran Ogan ya fito sai a ci abincin gaba ɗaya. Sai da aka kammala cin abincin ya aiki Latifa ta kira mishi Basma, fitowa tayi tana takawa a hankali, dama kuma ita ɗin me nutsuwa ce.
A fakaice na kalli matan biyu kallon da suka jefa mata suka dauke kansu, yasa na ƙara tsinkewa da al’amarin kishi. ta samu wuri ta zauna megidan ya ce mata ya ƙarfin jiki ta ce da sauki, ni ma na ce mata megidan ya yi gyaran murya, “Abin da yasa na ce ina son magana da ku Asabar me zuwa za a ɗaura auren ƴaƴan yayyena su biyu, mace da namiji. Ina so mu tafi da ke Halima da Ummulkhairi, na so muje da ke Latifa da ba ki taɓa zuwa ba, to ga ciwon Basma ba zai yuwu mu tafi mu bar ta ita daya ba, so sai wani lokacin kenan.
Hamdala na yi a zuciyata wani daɗi ya kume ni, jin zan tafi gida in ga family na. Latifa ya umurta ta miko mishi wasu ledoji da na lura da su tun fitowata. Ya umarci Halima ta zaɓi daya, ta miƙe ta dauka sai Basma, sannan ni Latifa da ta dauka ƙarshe kamar ta fashe. Ni dai nayi mishi godiya, su kam sai dai kowacce ta gyara zama.
“Wannan kayan na kwalliyar biki ne, akwai kuɗi a ciki sai ku yi amfani da su” Nan ma godiyar na kuma mishi. Basma ta mike da ledarta zuwa ɗaki, ni dai na ƙara zama dan idan na yi girki na kan zauna. Kitchen na shiga na ɗaukowa Ogan kunun aya, da na yi mishi tanadin shi. yana kurɓa a hankali Basma ta fito, gaba ɗaya muka bi ta da kallo, na lura ita dai tana son yin shigar da za ta bayyana jikinta, ko kyan surarta ke ruɗinta?
Wani abu naji yana taso min ganin Tahir yana bin ta da kallo, su ma sauran hakan ne dan har a fuskokinsu sun nuna. Wata yalolon riga ta saka da bata ɓoye komai na halittarta ba, a kasa kuma bata saka komai ba sai dan kamfai. Sama ta wuce muka raka ta da ido, dan kowa yasan ni nayi girki.
Ai nan fa ji nayi kamar ba zan iya daurewa ba, dan ƙirjina da ke sama da kasa. Latifa ta ja tsaki “Aikin banza dama ya maida ita wata macen kirki, za a yi mana salo”. Halima ma tsakin ta saki, miƙewa kawai nayi zuwa ɗakina,ina shiga na fara hawaye, wannan wane irin kalar wulaƙanci aka yi min?
Tahir na haurawa ya samu Basma tayi ɗaiɗai bisa gado, fuskar shi ɗaure ya ce “Wai meye wannan abu da kika yi? ke da ba ki da lafiya me ya kawo ki nan ɗin? Cikin ido ta dube shi, “Ai na warke kuma na ji zan iya karɓar girkina.” Wani kallo ya watsa mata, “Amma za ki iya girkin me ya hana ki fitowa ki yi, sai da wata tayi sai ki fado dakin, ba ki kyauta ba.”
Wani kuka ta fasa tana dafe kanta, ita Tahir zai wulaƙanta. Tunanin dokar likita kan ciwon ta yasa ya ce “Shikenan, ki yi shiru ki kwanta” Ya juya zai fita ta ce “Ina za ka kuma? Kamar ba zai mata magana ba, ba tare da ya juyo ba ya ce “Zan ma Ummulkhairi magana, dan kin san ba a kyauta mata ba.” Ɗauke kai tayi. Ya sauka ganin falon wayam ya ba shi mamaki, TV ya kashe ya wuce ɗakina. Kan gadona ya same ni zaune, na dogare gwiwoyina kamar me jin sanyi.
“Lafiya ummuna? ko jikin ne” ba shiri na dube shi dan jin ummun shi da ya kira ni dan rabon da in ji ya kira ni hakan, tun ina Lagos. Gira ya ɗaga min “Kin hada ni da kunun aya za ki zo nan ki takure” wani kallon ka raina min hankali na jefa mishi “Da yake wadda ka baro ita ma tana da abin, za ta baka ai” Idonsa ya gwalo “Wai da gaske Ummuna ce me sakin zance haka? ƙara daure fuska na yi, ganin ya kasa shawo kaina yasa ya ci serious. Gadon ya hau ya tallafo ni, ƙwace jikina na yi ina ture shi. “Ki bari kar in ji miki ciwo” daga haka ya kara jawo ni ya haɗa da jikinsa, shiru nayi yi ina zubar da hawaye. “Ki yi hakuri ban san za ta ce za tayi girkin ba na ce ki yi, ki yafe min ki yi haƙuri. Ganin yanda yake bani haƙuri na ce ya wuce. Ya ce “Kin yafe min? na daga kai, “To tashi ki yi shirin barci.”
Yana nan sai da ya ga nayi shirin kwanciya na kwanta, hada su min addu’a, sai ya min sai da safe ya ja min ƙofar. Yana fita na tashi zaune, humm namiji kenan ƙanen ajali. Na daɗe zaune kafin na ba kaina magana, na kwanta ina ta kiran sunayen Allah da neman dauki zuwa gare shi, Har na samu barci ya yi nasarar kwashe ni.
Tahir na komawa ɗakin ya yi shirin kwanciya, nesa da inda Basma take kwance ya hau ya kwanta, ya juya mata baya. Juyowa tayi ta dube shi, wasu hawaye ta ji sun taho mata, zaune ta tashi, jin saukar numfashinsa yasa ta gane ya samu barci. Sai kallonsa take ta raba dare a haka, sai gabanin asuba barci ya ɗauke ta.
Dan haka ko da ya yi ta tada ta tayi sallar asuba kin tashi tayi, ya yi shirinsa ya fita masallaci. Ko da ya dawo sai da ya yi mata jan ido sannan ta tashi, anan tayi sallar ta koma ta kwanta. Ya dade zaune yana azkar, kafin aka kira wayarsa kan harkokinsa ne, wanka ya yi ya shirya cikin wani yadi ɗinkin iya gwiwa da yayi matukar hawansa, sai ya manna Glass ɗinsa, yana feffesa turarukansa wayarsa tayi kara, aljihu ya jefa ta sai ya bar ɗakin.
Yana saukowa kallon ƙofofin matansa ya yi, Tsaki kawai ya ja sai ya bar wurin. Basma ta shari barcinta, yunwar cikinta ta tashe ta, bata ga alamar Tahir ba, ganin lokaci ya yi nisa yasa ta gane ya fita hamma tayi ta mike ta bar ɗakin. A ɗakinta ta samu Gwoggonta Hajjo ita ma tayi tsuru ita ma yunwar ta gallabe ta, bata iya gaishe ta ba sai ita ta tambaye ta jikinta, yamutsa fuska ta yi.
“Wannan yarinyar bata kawo abinci ba? Kallon mamaki ta bi ta da shi “Amma ke kam Basma sai a bar ki, ke wane irin tunani ne da ke? wa ke sauraren mu ya biyo mu da abinci dakin nan idan ba ita ba, amma kina dan jin ƙarfi da me za ki saka mata sai za ta karbi girki, ki ce ke za ki yi. Ai kin ja mana sai ki fita ki nemo mana abin da za mu ci.”
Ba yanda Basma za ta yi, fitowa ta yi ta ce Indo ta kawo mata ruwan zafi, dan ko kwai ba za ta iya hakurin a soya ba. Haka nan suka sha tea. Karfe biyu Tahir ya kira wayarta yana tambayar ta ta gama girki, ga shi nan zuwa, dan yunwa yake ji. Hankalinta ya tashi ta fita neman Indo, bata gan ta ba, kuma girman kanta ba zai bar ta tambayar wata ba. Yankewa tayi ta koma daki komai ta fanjama fanjam, ai yasan bata da lafiya zai ce sai ta ba shi abinci.
Yana isowa dakinsa ya shiga, ya sauya kayan jikin shi zuwa jallabiya,sai ya sauko ganin danning wayam saman shi ya koma, ya kira ta a waya, sai ga ta tana yauƙi ita ala dole yunwa take ji. Ya ce “Ina abincina? Dan kauda kai tayi, “Ban yi ba” Dalili? Ya tambaye ta, “Ka san dai bani da lafiya” Shat up my friend” ya da ka mata tsawa. “Kin san ba ki da lafiya, kika karɓi girkin? Wayarsa ya janyo Ummulkhairi ya kira, lokacin ina kallon wani shiri a tashar Afrika TV 3, sai da ya saurari gaisuwar da nake mishi, kafin ya ce “Zan samu abincin da zan ci a wurin ki.”
Dan jim nayi kafin na ce “E” “To ki ajiye min a dinning kafin in fito”. Ya kashe wayar. Shiru nayi “Me kenan hakan? na tambayi kaina, An kwace min girkin kuma yana batun in ba shi abinci. Kamar in kira Aunty Laila in ne mi shawarar ta,sai kuma dai na ga in adana sirrina kawai, miƙewa nayi na sauko.
Abincin da na tanada in ci da dare na ɗumama mishi, na shirya a trey na ɗauka zuwa falo, na tarar Halima da Latifa sun fito, na wuce su zuwa dinning muryar Latifa na tsinkaya. “Wasu dai Allah ya yi musu neman cusa kai, ni dai ban ga rashin zuciyar da ta aike ni in yi girki a karɓe mijin, kuma in zauna ina musu abinci suna cinyewa. Ko da yake dan an maka abinda kake yi bai kamata ka ji haushi ba.”
Halima ta ce “Kamar ya?” To idan a girkin da ba naka ba, kana kebewa da miji,dan an maka haka ai ba ka ji haushi ba. Halima ta amshe cikin fushi, “Ai kuwa ba a haifi ƴar ba, ran girkina ta raɓi miji.” Wata shewa Latifa ta yi.
“Na nawa kuma? ai sai dai kar a kuma” Halima ta zaburo za ta yi magana suka ga ogan a kansu. Raɓa su ya yi kamar ma bai gan su ba, ya je ya zauna ya soma cin abincinsa, Juyawa nayi na koma ɗakina. Basma ta sauko, jin ƙamshin girkin cikinta ya soma ruri, yana tuna mata ba a ba shi hakkinsa ba. Kujera ta ja ta zauna suna fuskantar juna, yana cin abincin tana ta kallon sa, tunaninta zai ji tausayinta ya rage mata, sai ta ga ya tashi flate ɗin, Ya dauki tattacciyar abarba da na tsiyaya masa a Glass cup ya sha, ya goge bakinsa, sai ya fice falon.
Ganin ba sarki sai Allah Basma ɗakinta ta koma, kuɗi ta dauko ta fito zuwa harabar gidan, direba ta kira ta aike shi ya yo mata take away. ta juya Tahir da ke kallon abin da ke faruwa, ya kira direban, da saurin sa ya iso kiran uban gidan nasa, tambayar sa ya yi abin da Basma ta ce mishi, ya yi mishi bayani, “Ka mayar mata kudinta” ya fadi da dakewa, Ba yanda direba zai yi, dole ya kama hanya ya yi sa’a bata kai ga shigewa ba, ya ce “Mai gida ya ce a maido miki kuɗinki” bata damu ba, dan tunaninta zai bayar a sawo mata ne.
Ɗakinta ta koma tana zaman jiran tsammani, ga Gwoggonta me lalurar ulser, jin shirun ya yawaita yasa ta tashi ta fito, sama ta hau ganin ba Tahir sai ta koma harabar gidan. A kebabben wurin da yake motsa jiki ta same shi ya haɗa gumi kashirban, shagala tayi da kallon sa, dirarren namiji da ko wace mace za ta yi ma kanta sha’awar a ce nata ne kirjinsa ta zura wa ido, har jikinsa ya ba shi ana kallonsa, waiwayowa ya yi sai Basma ya gani tsaye. “Lafiya” ya ce yana dubanta. Ina abincin? ta tambaya kai tsaye, “Abinci kuma wane abinci? Bata fuska ta yi “Ba ka aiki direba ya sawo min abinci ba? Cigaba ya yi da abin da yake kamar ba shi da wata mas’ala, “Magana fa nake maka” ta fadi kamar za ta fasa kuka.
“Akwai abin da babu ne na nau’in abinci a gidan? ya tambayeta. Turus tayi, gane ba za tayi magana ba yasa ya ce “Ki shiga kitchen ki dafa, kuma dokar da nasa duk me girki ta ba jama’ar gidan abinci ki ka taka zamu gauraya. Ina daga miki kafa saboda lalurarki” Ya yi ƙwafa, ganin ya tunkarota yasa ta tunanin ko mangare ta zai yi, sauri tayi ta juya. Daga shi sai guntun wando ya shiga falon, Halima da Latifa da ke zaune har lokacin kowacce tana tunanin takurar da take ciki na zaman me gidan a gari ba halin fita sabgar gaban su.
Sun dube shi a tare shi kuma ya dubi ƙofar Ummulkhairi.