Key ɗinsa yasa a kunnensa yana dan sosawa, "Madam sarkin aiki" murmushi na yi, "Ni zan dan fita, zan dawo kafin isowar baƙin." Daga haka ya juya na bi bayansa, ina mishi a dawo lafiya. Sai da ya shiga motarsa sai na juyo, ban lura da Latifa da kawarta da ke zaune akan fararen kujeru, a can kusa da wasu Flowers, sun zura mana ido tun fitowar mu, sai da na iso daf da su sannu na musu, sai dai ban san ko Latifa ta amsa ba, wadda suke tare dai ta amsa hada gaishe ni.
Miƙewa Fadila. . .