Skip to content
Part 8 of 49 in the Series Wa Gari Ya Waya? by Maryam Ibrahim Litee

Key ɗinsa yasa a kunnensa yana dan sosawa, “Madam sarkin aiki” murmushi na yi, “Ni zan dan fita, zan dawo kafin isowar baƙin.” Daga haka ya juya na bi bayansa, ina mishi a dawo lafiya. Sai da ya shiga motarsa sai na juyo, ban lura da Latifa da kawarta da ke zaune akan fararen kujeru, a can kusa da wasu Flowers, sun zura mana ido tun fitowar mu, sai da na iso daf da su sannu na musu, sai dai ban san ko Latifa ta amsa ba, wadda suke tare dai ta amsa hada gaishe ni.

Miƙewa Fadila ta yi hada buɗe baki, Latifa ta kamo ta ta zaunar, “Ke meye?” Ajiyar zuciya ta fidda, “Wai Latifa me nake shirin gani ne?” Da sauri ta ce “Me kika gani?” “Wace ce wannan da ta wuce?” Matsiyacin tsaki ta ja, “Ita ce nake bi a gidan Tahir.” Ido waje Fadila ke dubanta, “Kina nufin kishiyarki ce?” tsaki ta kuma ja bata yi magana ba.

“To wallahi ita ce na gani jiya tare da Tahir ɗinki.” Wani kishi ne ya soki kirjin Latifa, har ta gwammace wata macen ce ta waje aka ga Tahir da ita. “Sai kin dage Latifa, yana da irin wannan a gida lafiyayyar mace maka malam, da ko wane namiji zai so ta kasance kusa da shi. In ma banda tarangahuma irin ta ɗa namiji, me kamar wannan har ya ƙara ganin wata macen ya ce zai dauko ya karo cikin gidansa. Ko da yake mijin naku gwarzo ne, mata hudu reras ka…” “Idan kin gama zagina Fadila, sai ki tashi ki tafi.”

Latifa ta katse ta cikin fushi, kama hannunta ta yi, “Yi hakuri ƙawata, amma dai gaskiya sai kin dage, tunda kin ce ita waccan ta Abujan bata da power a gidan. Ni wannan ina ce ita ce kika ce min yar ƙauye ce.” Baki ta taɓe “Yar ƙauye ce mana, an zo birni an sha jar miya sai a ka kile” Fadila za ta kara magana Latifa ta daga mata hannu “Na fa san ki Malama, kada ki ce min jarabar taki ta rasa inda za ta tashi sai kan kishiyata.” Baki ta lasa “To mu bar wannan maganar, akwai wani magani da na kawo miki, yana da matukar kyau, sai dai tsada, samun maganin ba ƙananan kuɗaɗe na karɓa a hannun alhazan birni ba.”

Sai sannan Latifa ta yi murmushi, “Yawwa yanzu na ji batu, muje ki bani.” Ciki suka shiga riƙe da hannun juna, sun ratsa falon da basu samu kowa ba zuwa dakin Latifa, ta bata maganin tare da bayanin yadda za ta yi amfani da shi. Ta nemi ta bata kudin maganin, transfer ta yi mata, ta taɓa kafadarta “Muje falon nan naku ƙawata, ban gajiya da ganin sa, kana cikin sa kamar kana ƙasar waje, ba fa ƙaramin dace kika yi da samun gayen nan ba, ga shi ya haɗu ga masu gidan rana ya tara.” Cije lebe ta yi “Ke dacen kawai kika hango, ba ki tuna bakar wuyar da na sha kafin in samu nasarar shigowa in amsa sunan matar sa” tafawa suka yi “Haka ne fa dan ni ba ma zan iya ba, ba dan namiji guda aka yi ni ba.”

Lumshe ido Latifa ta yi “Ba za ki gane ba ƙawata, gwarzon maza ne ogana, ban taba samun namijin da ya shiga raina irin sa ba, namiji ne da zai sa ki manta sunanki, ya iya tarairayar mace ya jiyar da ita daɗi” Fadila za ta yi magana txt ya shigo wayarta ta soma dubawa sai suka fito. Suna zaune ina ta hada hadar shirya abinci, duk na bi na tsargu saboda mayataccen kallon da kawar Latifa ke bi na da shi, dama tunda na gan ta hankalina bai kwanta da ita ba, bata yi kama da masu kamun kai ba. Ban da wani banzan ɗinki da ta sa har sarƙa na gani a kafarta, ga gashin doki da ta yarbatsa a kanta. Ina samu dai na kammala sai na wuce su zuwa ɗakina. Latifa ma miƙewa ta yi “Ke gidan fa yau manyan baki za mu yi, wani babban abokin Ogan ne da ke zaune a Abroad zai zo da matarsa, bari in shiga in shirya kar a raina ka cikin kishiyoyi.” Ita ma miƙewar tayi “Shi kenan nima bari in ƙarasa, akwai wanda muka yi alkawarin haduwa” Ta taka mata sai ta dawo ta wuce ɗakinta dan shiryawa, tare da ƙara jaddada kudirinta na kulla abota da matar abokin ogan nasu.

Ita ma Halima a nata fannin kudirinta kenan kulla alaƙa da matar abokin ogan dan haka shiri take ta yi ita ma.

Saɓanin Basma da ke kwance bisa kujera ta yi ɗaiɗai, bata ma da niyyar shiryawa, kallon Gwoggonta take wadda ke zaune tana cin abinci tana fadin “Kai wannan yarinya akwai baiwar iya girki, kana ci kunnenka na motsi, ga ta kuma yar albarka ita kadai za ta yi girki ta aiko min da shi har daki, girkinta ne kawai kuma za ka ci abinci me daɗi.”

Basma da ke kallon Gwoggon ta ta cikin fushi ta ce “Haba mana Gwoggo kishiyar tawa kike ma wannan yabon?” Kallonta tayi “To ai ni dai kin san in gaskiya ta zo bani boye ta, fadin ta nake.” Cikin kumbura baki ta soma kunkunai “Ni dai ba a kyauta min ba wallahi.” “In ma zagina kike kin dade sai na fadi gaskiya” Juya mata baya Basma ta yi dan ji take kamar ta tashi ta shaƙe ta.

Sallah na fara yi kafin na shiga wanka na fito na zauna gaban mirror, na yi shafe shafena, wata hoda da muka saya a Saudiyya ni da Aunty Laila na mitstsika nan take fuskata ta ƙara wani irin kyau da sheƙi, na zizara jam baki, na gyara girata. Wajen kayana na koma kayan da muka lafto a Saudiya na ke ta duba wadda zan sanya, idona ya tsaya kan wata abaya me masifar kyau, wadda kai da ka gan ta ba sai an gaya maka ita ɗin me tsada ba ce, na ciro ta na sanya, ɗan kunne me kamar awarwaro na sanya sai agogo na fata na daura a hannuna, na soma fesa turare, wayata ta yi kara alamar shigowar sako, na kai hannu na ɗauko ta ina dubawa, daga maigidan ne yana shaida min isowar baƙin, kan gadon na maida wayar, na janyo takalmi, me tsini ne da ya shiga da rigar, na yane kaina da gyalen abayar, sai na fito na rufo ƙofar.

Takun ƙwas ƙwas da takalmina ke yi yasa jama’ar da ke zaune falon kai dubansu inda nake, Halima kwalliyar shadda aka sha Latifa kuma less, baƙon da matarsa na zaune cikin two sitter sai namu Ogan da ke zaune a kujrerar da ke kusa da abokin nasa. Na ƙarasa ina musu sannu da zuwa, sai da muka gaisa da mijin kafin matar wadda ta ke me fara’a ce da matuƙar wayewa, ta dubi Tahir “Wannan ita ce amaryar taka? Mijinta ya duba “Ka ji matarka ko? ba ga ki ga su nan ba” Noƙe kafaɗa tayi “Na ƙi wayon, kai za ka faɗa min” Na miƙe tsam na wuce kitchen, cincin na zubo musu da coconut milk pudding na kawo, an dauki lokaci ana fira cikin raha, kafin na gayyace su cin abinci, sai mamakin Latifa nake yanda ta zake wurin yin saving din bakin kamar ita ta dafa.

Shiru kake ji sai ƙarar cokula ke tashi, kafin abokin me suna Muhammad ya dubi Tahir, “Gaskiya abokina ka samu duniya, bayan nasarar mallakar mata har huɗu, ga kuma daddaɗan abinci ana shirya maka.” plate ya yi saurin kanga masa “Ya kamata in maka waigi dan na lura santi ke ɗawainiya da kai.” Cokalin da ya debo dambu ya zuba bakinsa, ba zan musa maka ba wallahi, in ma ka ce santin nake, gimbiyata za ta zo koyon abin nan har ma da cincin ɗin da na ci.” Tahir ya ce “Dambun kake ce ma abin nan? Ya ɗan bude ido “Kai mutumina wannan daddaɗan abincin ne dambu?” Su Latifa da Halima na saci kallo, kowace yaƙe kawai take, matar tashi me suna Asiya ta yi murmushi “Wai ina ɗaya matar ba hudu bane?” Tsit aka dan yi kafin me gayya me aikin ya ce “Da yake bata jin daɗi, ba ta dade da fitowa daga Hospital ba” Addu’ar samun sauƙi suka yi mata, Ogan ya miƙe “Bari in dubo ta” A kwance take kan sopa, Gwoggonta na zaune kan carpet tana gyangyadi, jin motsin sa yasa ta bude ido sai ta miƙe ta shiga ciki bayan ya gaishe ta, duban Basma ya yi ta cikin farin glass dinsa, ganin ya ki magana yana kafe ta da mayun idanuwansa, yasa tsoron shi ya fara rufe ta.

“Meye hujjar ki na zama a daki? bayan na shaida muku za mu yi baki” Shiru tayi dan bata da wata hujja, har ya ƙare fadansa tana sauraran sa hakuri ne dai ba za ta iya bayarwa ba, ya juya ba tare da ya waiwayo ba ya ce “Ina jiranki, kuma kar ki sake ki ce za ki fito min a yadda kike” Kyabe baki tayi tana kallon rigar jikinta, tsaki tayi sai ta miƙe, wata doguwar rigar ta canza ta kama hanya ta fita cikin daure fuska, kamar yanda take kullun ba fara’a.

Da fara’a mata da mijin suka tare ta, sai dai sam ta ƙi sakin fuska, hannuwanta ta dogare a saman cushion, suna kuma gama gaisawa ta juya ta koma ɗakinta. Asiya ta dan ƙara matsawa kusa da mijinta “Allah honey abin nan fa yana ta ban mamaki, wai wannan handsome ɗin shi ne da wadannan manyan matan har huɗu kuma duk matansa ne” Murmushi ya yi “Kin raina mu kenan? shiru tayi dan ganin Halima na kallon su, tana gudun kar su ji, Latifa da Halima dai sai jan Asiya da fira suke, ni dai ina zaune ina sauraren su har sai in Asiyar ta jeho ni cikin zancan.

An kwala kiran sallar la’asar Tahir da Muhammad suka fita zuwa masallaci, ni ma na miƙe na dubi Asiya “Bari in shiga in yi sallah” Ita ma miƙewar ta yi “Muje ni ma in yi” Halima da Latifa da aka gyara zaman shan fira da bakuwa, suka raka mu da mugun kallo. Muna shiga ita na fara cewa ta shiga ta yi alwalar sai nima nayi, muna idarwa mun yi addu’a ta dube ni “Ina shigowa gidan nan na gan ki na ji kin min, sunanki Ummulkhairi ko? Na daga mata kai ina murmushi “Uwar alkhairi kenan ta fada ita ma tana murmushi “Kuma na gane wannan daddaɗan abincin da muka ci har sweetyna na santi ke kika yi shi.” nan ma murmushi na kuma yi mata, “To yaushe za a fara koya min?”

Na ce “Duk sa’adda kika shirya” Ta ce “To shi kenan, ki bani lambarki” na faɗa mata ta sa sai ta kira ta shigo, nima sai nayi saving. Muna ta fira ta faɗa min gidansu na nan a millennium City, sai da mijinta ya kammala ginin sa sannan suka dawo. Na ce “Allah sarki,” mu ma namu ginin anan unguwar yake yin sa” ta ce “E na ji suna maganar layi biyu ne a tsakani” mun yi fira sosai da ita dan bata da wuyar sabo, har sai da Tahir ya leƙo “Ina kuke ne?”

Na tsinkayi muryar sa, fitowa nayi ina faɗa mishi “Ga mu nan” sai da ya kalle ni sai ya ce “Ya za ki riƙe baƙuwar a daki? na ce “Mun yi sallah ne” ya ce “To ta fito za su tafi.” Na ce “To” na koma ciki na shaida mata, sai da ta gyara fuskarta ta fesa turare, na dauko wata humra nayi mata kyautarta ,sai muka fito. A fuskar matan za ka karanci canjin da suka samu, dan takaici ne ƙarara a fuskarsu, gaba ɗaya muka fito dan musu rakiya, sai da suka zauna cikin mota na bude bayan motar na ciro kwalin da nake sunne da shi cikin hijab na cake din da nayi musu na ajiye shi, suna godiya muna yi suka ja motar su suka tafi.

Sauri na yi na riga su wucewa zuwa ciki na shiga kitchen, tuwon semo miyar kuka da ta ji wadataccen nama da kayan ƙamshi nayi saboda Ogan, a sanin da nayi shi din me san tuwo ne, da muka kammala muka shirya komai da Indo ɗakina na wuce nayi sallah sai na sake kwalliya da wata riga doguwa kalarta danyen kore, me guntun hannu, ta kamani dam a jikina , sai na yane kaina da wani dan siririn gyale, ina zura takalmi sai na fito kitchen na shiga cake din da nayi na raba na ba Indo ta kai wa matan, na haura sama dan ajiye wa ogan na shi.

Na fito na zauna ba daɗewa ya shigo tare muka haura saman na hada mishi ruwan wanka, saukowa ta na samu matan dukan su sun fito, Latifa ce kawai ta ce min sai ga cake an kawo, sauran ba wadda ta tofa. Sai da ya fito aka ci abincin wanda kowa ya gane ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba, ranar an yi fira har goma da rabi. Mun yi shirin kwanciya har na soma barci na ji hannun mutum jikina, “Ya kamata in miki tausa, ta ban gajiyar aikin da kika sha a yau.” Ya tallafo ni jikinsa ina kokarin ƙwace jikina in kwanta na ce “Ni ban gaji ba, barci kawai nake ji.”

Al’amuran da yake min yasa dole na watstsake na biye masa, sai da komai ya lafa ina maƙale jikinsa na ce “Ya kamata a ce mun soma shiri na tsarabar da za a kai wa mutanen gida.” Dan tsaki ya ja. “Ni bana wata tsaraba.” Na ce “Shi kenan idan muka je, sai ka basu kuɗaɗe su sayi abinci, dan ka san ba lokaci me wahala a wurin mutanen mu na gida irin wannan lokacin na damina, abinci ya koma gona..”

Daga haka nayi shiru, shi ma shirun ya yi. Duban ta ya yi ganin har ta soma barci, miƙewa ya yi ya shiga bathroom wanka ya yi ya tsaftace kansa sai ya fito gindin window ya tsaya idanunsa na kallon harabar gidan, “Kwarai tun yana yaro ya san ba lokacin da ake shiga kaka ni ka yi irin lokacin damuna a karkara, amma me yasa tunaninsa bai taba ba shi ya maida hankali wurin taimakon ƴan’uwansa a irin wannan lokacin? Har sai da wannan yarinyar ta tunasar da shi. Ya dade tsaye cikin tunani kafin ya ja ƙafarsa zuwa gado ya kwanta.

Da safe bayan fitar maigidan makaranta, kwanciya kawai na yi sai da na sha barcina kafin na fito nayi musu abincin rana, na fita girki kenan, Latifa ta karba sai rawar ƙafa ake, ana kai da kawo, aka shirya abinci ga kwalliya an caba, an zauna zaman cin abinci dan rashin dabara ganin idan nayi tuwo ogan na ci sosai yasa ta ita ma yin tuwon, ni tun a ido da na kalla girkin bai bani sha’awa ba, na dai zuba, lomar farko da na kai na tsame hannuna dan wani amai da ya taso min. Ashe bani kaɗai ba ce ogan cewa ya yi,

“Latifa wannan wace irin miya ce? Mur ta sha kamar yanda shi ma ya sha, “Miyar har daban daban ce? Dan tsaki ya ja “Ai sai ki sha ki ji” Halima ma ta taɓe baki “Hala ba ki dandana ba? Shiru ta yi musu sai ta debo ta kai baki dan ta ji dalilin wannan tozarci da ake mata, rashin kan gadon miyar ta ta yasa ta ji kamar ta maido ta, amma tilas ta tauna ta hadiye. Sai tayi ta yan duniya “Meye to a cikin miyar?”

“Daga ba komai ai sai ki ci.” Tahir ya bata amsa yana tura kujera, sai ya bar wurin zuwa saman shi, matan ma da ɗai ɗai da ɗai ɗai suka zare aka bar ta da tulin abinci a gaba, kamar ta fasa kuka.

Basma na shiga ɗaki ta samu Gwoggonta ta tasa abincin ta yi jugum, ganin Basma yasa ta miƙe “Wallahi gobe gida za ni, ban zama gidanki yunwa ta kashe ni” Bata yi magana ba sai juyawa da tayi kitchen fresh yougourt ta ɗauko da glass cup, ta dire gaban gwoggon ta ta, gorar ta galla wa harara “Wai shi zan sha in kwanta? ina fama da ulser? Ni Lariya na kawo kaina” Da kukanta share share ta kira baban Basma, ta ce ya turo direba gobe ya tafi da ita yunwa za ta halaka ta. Ran mahaifin Basma ya yi matuƙar ɓaci ya katse kiran, ya shiga lalubar lambar Tahir.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wa Gari Ya Waya? 7Wa Gari Ya Waya? 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×