Kafin tara rana na shiga kicin, sai da na tafasa ganda ta yi laushi, sannan na hada shi da naman na sake dafa su a tukunya guda daya.
Na kuma zuba musu maggi da gishiri na dauko asalin tukunyar da zan yi miyar a ciki wacce take katuwa sosai na dorata kan wani kunannen karfe din.
Na zuba wadatacciyan manja da isashsshiyar albasa, ban bari ta gama soyuwa ba na dauko tukunyar da naman nan da ganda suke ciki na juye duk da ruwan ciki, na kawo gyararren busashshen kifin na jufa, na kawo garin barkono da kayan kamshi gami da maggi da gishiri na zuba, na sa murfi na rufe na bar shi yana ta dahuwa.
Jimawa can na kawo ganyen water leaf da Baba Maigyada ta yanka mini, na bar shi ya yi kamar minti biyar sannan na juye ganyen Afang din na rufe.
Nan da nan kamshi ya gauraye ko’ina. Baba Mai gyada sai salati take yi tana cewa, Yanzu nan ke dama yarinyar nan ashe kin iya girki haka, amma kika rinka tabka irin wannan tsiya? Ai kuwa inda na sani da na gayawa su Lamido cewar dukan tsiya ya kamata su yi miki.”
Ni kam ban ce mata komai ba, kokari kawai nake yi in ga na gama tare kuma da addu’ar komai ya tafi daidai.
Tuwon shinkafa na yiwa mutanen gidan duka, su Baba Maigyada da su Baba Talatu suka tuka shi suka tayani, suka yi mini rabon.
Su yaya Almu kuwa na dafa doya na sa aka daka musu sakwara kafin karfe biyu har na baiwa kowa abincin shi na gama, na koma kusa da Umma na kwanta ina kallonta tana cin tuwon da na mata, tare da shan miyar da cokali, dadi ya kamata sai faman sanya mini albarka take yi.
Ina idar da sallah sai ga Baba Talatu ta shigo tana tambayata.
“Uwar dakina ko dabara za mu yi ne mu yi miki girkin daren?” Na ce mata, ‘A’a gani nan fitowa zan zo in dora.” Ta ce mini, “To.”
Ta tafi bayan ta ne na sha kunun zaki da Umma ta ba ni, na dan ji sanyi a raina.
Na je na samu har su Baba Maigyada sun shirya mini kurfo-kurfo din sun kunna gawayi don haka ina zuwa na dora sanyawar miya.
Baba Maigyada ta ce, “Ke yar nan yi musu dafaduka ki huta. “
Na ce mata, “Bari kawai Baba, Yaya Junaidu baya son cin shinkafa da daddare.”.
Ta ce, “Uhu! Haka ne. Tuwon alkama miyar kuka na yi, suma sun yi matukar jin dadi. Na gama salamar kowa na dawo daki na shiga cikin baf na kwanta cikin ruwan zafi tsawon lokaci ina tunanin wahalar da na yi a yau wajen aikin abincin gidan nan.
Wai a gobe ma haka ake so in sake yi.
Na dade a kwance ina tunanin kafin na yi wanka na fito na zo na yi sallah na gyara jikina na zo na zauna gaban Umma tana shafa mini gashin kaina, kafin ta taje mini shi ta tubke mini wuri daya.
“Yau kam kin wahala bari zan gayawa Babangida ya rage miki girkin nan.”
Na yi maza na ce mata, “Bar shi kawai Umma, ya ce mini nina fi kowa cancantar in ciyar da mutanen gidan nan, tun da baba ne ya tara su, to zan yi hakan komai wahalar shi.”
Umma ta zuba mini ido tana kallon cikin tunani, na san tausayina ne ya kama ta, don haka sai na ce mata, “Kar ki damu Umma nima na riga na gane ya zama dole in zama jaruma ba zai yiwu a ce ni da gidan ubana in zauna sai wasu ne za su rinka yin abincin gidan ba.”
Ta yi maza ta ce, “Haka ne, haka ne Adawiyyah, Allah dai ya yi miki albarka.”
Tun tara ba ta yi ba barci ya dauke ni a nan wurin saboda gajiya.
Washe gari kuwa Fried Rice na yi. Ga abubuwan da na yi amfani da su:
Shinkafa.
Tumatur
Nama
Maggi, gishiri
Kwai.
Albasa
Butter Curry
Tumaturin gwangwani.
Ga yadda na yi hadin, sai da shimkafar ta yi ta tafasa na tsawon minti goma sha biyar sannan na sa aka juyeta a kwanduna ta tsantsame aka ba za ta ta sha iska.
Na sa aka yi wa albasa yankan kwabo-kwabo aka yanyanka naman suka zamo yan madaidaita, sannan aka soya su cikin butter na sake. hada shinkafar nan tare da butter da yanlkakken kayan lambun nan su karas, kabeji, koren wake, curry da maggi na gauraya su gabadaya, sannan na nufe na sake maidawa kan wutar.
Bayan na rage mata karfi na soya kwan, sannan a zauna na yi mishi yanka na ban sha’awa.
Sannan na sauke shimkafar na shiga yin rabo su Baba Talatu, da Baba Maigyada sai murna suke yi, suna fadin wannan yarinya da iya shege kike yanzu a kwanakin bayan nan wa zai ce kin iya girki haka?
Da daddare kuma saboda Yaya Junaidu sai na sake yin tuwon semobita da miyar kubewa bushasshiya suma sun yi dadi ba kadan ba.
Tun daga rannan ban sake samun matsala da girkina ba, kullum zan yi abinci zan tabbatar na yi shi mai ban sha’awa a ido, mai dandano a baki.
Tuni na maida yin girki daga cikin abubuwan da suke san ya ni nishadi, sai na zamo ba ni da matsalar yawan abincin gidan mu, musamman da na gane yaran gidan ma zumudin zuwan girkin nawa suke yi, don kuwa yan matan gidan da ke biye da ni cika wurin girkin suke yi mu yi ta yi tare da su, suna tambayata anti Adawiyya daga ansa wannan sai wanne kuma? In ce musu sai kaza, shi kuma in an zuba shi minti kaza zai yi, kafin a sake zuba wancan.
A haka sai in yi girkin in gáma ban galabaitaba, suma su Baba Maigyada wurin girkin sai ya zamo musu wurin hira ko ban nemi taimakon su ba za su zo su zauna a yi ta hira ana raha suna taya mu dariya, suna fadin kai yaran nan sai a bar ku.
Suma masu gidan su Yaya Almu da su Yaya Basira dadi sosai muke yi da su, tun ma ba Yaya Junaidu ba, wanda ko yaushe zai shigo dakin Umma ya same ni yana zolayata.
“Ni Adawiyya ki daure ki karbi girkin gidan nan mana gaba daya.”
In yi murmushi in ce mishi, “To Yaya Junaidu in ka ce a yi hakan ai sai a yi.”
Ya zauna mu yi ta hirar mu sai ya ga na fara gyangyadi sannan yake tashi ya fita.
Tun da yan matan gidan suka kyalla ido suka ga gaba daya jama’ar gidan kara sona suke yi, saboda gwanintar iya girkina, sai aka shiga gasar girke-girke kowacce wai so take a ce ai ita ce gwana, amma ina?
Na riga na yi musu fintinkau.
Umma kuwa sai cewa take yi, ai shi girki da kike ganin shi har da baiwa a ciki, ni kam dariya na ke yi in na ji ta fadi haka a zuciyata kuma in ce girkin zamani dai har da koyo a ciki.
Tun da na riga na saba da girki ko ba ni ce da shi ba sai in ga ina sha’awar yin shi, don haka sai na shiga shiryawa Ummana abin karyawa da safe.
In ni ce da girkin kuwa sai Baba Talatu ta yi mana.
Rannan ina cikin kicin din Umma ina kokarin shirya mata abin karyawa yayin da ita kuma ta shiga wanka, sai ga Yaya Almu ya shigo cikin kicin din.
“Me kike yi ne Rabi na ke jin kamshi haka?” Na yi murmushi na ce mishi, ‘Abin karyawa nake yi wa Umma.”
Ya kara matsowa kusa yana kallon yadda nake gauraya tankadadden garin fulawa da citta a cikin narkakken butter, sugar, zuma, da lemon tsami da ke kan wuta. Ya kasa hakuri da abin da yake ganin ya gaji ya ce mini;
“Ni Rabi a ina kika koyi girkine haka?”
Na yi murmushi na ce, “Yaya Almu kenan ka mance credit biyun da kake cewa na ci a jarrabawa, akwai wata B3 da baka ambatonta wacce na samu a Home Management”.
Yaya Almu ya rike baki ya ce, “Haka kuwa aka yi, wato har da girki kika koya a zaman makarantar nan da kika yi?”
Na ce mishi, “Eh.”
Ya ce, “To ya tabbata dai na kin ne kawai ba ki tsaya kin yi ba, amma nawan duka sun samu.
Tun da ko ba komai gashi nan yanzu kowwa zumudin zuwan girkin ki yake yi, yara da manya.
To me ya fiye miki haka dadi?
Na ce mishi, “Babu.”
Ban san Umma tana jin mu ba, sai da na ji tana cewa, ‘Ai wannan ‘yan ubanci da ka yi wa Adawiyya ya yi matukar zama mata alheri tun da ya rufa mata asiri.”
Yaya Almu ya yi dariya ya zauna muka karya tare da shi.
Tun da su Yaya Almu suka gane ina yi wa Umma abin karyawa da safe sai suka maida sashinta wurin karyawar su kullum kuma da irin abin da nake shiryawa.
Rannan da rana sai ga Yaya Junaidu ya dawo cikin sauri ina ganin shi na ce lafiya? Ya ce, ‘Lafiya Adawiyya na dawo ne zan yi shirin tafiya garin Edo gobe da safe.”
Na rike baki na ce, “Za ka dade ne?” Ya ce, ‘A’a sati guda zan dai yi missing din ki ne na wannan satin, kin san yadda nake son cin abincin ki kuwa?”
Ya zuba mini ido yana kallona, cikin nutsuwa na dan yi murmushi na ce mishi, “Na sani Yaya Junaidu to, bari in je in shirya maka abin da za ka rike ka rinka karyawa da shi.”
Ya yi maza ya.ce mini, “Ai kuwa da kin taimake ni, don ni lokacin karyawa da abincin dare sunan cikin lokutan da nake so a kula mini daa bin da zan ci sosai.”
Na ce mishi, “Haka ne.”
Na juya na tafi na je na soma yin shirye-shiryen yi mishi White Bread da Raisin Bread.
A white bread din ga abin da na yi amfani da su:
Sugar
Ruwan dumi
Yeast.
Margarine
Flour
Gishiri
Shi kuma Raisin Bread sai na yi amfani da wadannan kayayyakin:
Seedless raisin cup
Flour.
Sugar
Baking powder.
Kwai
Soda.
Madara
Gishiri.
Lemon Tsami
Oat.
Butter
Ina gama wadannan na sake yi mishi Meat Ball shi ma ga kayan hadin shi:
Nama Madara
Albasa. Flour
Garin bredi Kwai
Butter. Chese
Maggi. Mangyada
Gyada mai laushi da gishiri.
Ba zan iya kwatanta farin cikin Yaya Junaidu ba, a lokacin da na kai mishi kasa ce mini komai ya yi, ya zuba mini ido ya ce, ‘Adawiyya mijinkiza i more.”
Na yi maza na rage fara’ata na ce mishi, “Sai ka dawo.”
Na juya na koma sashin Ummana.
Ni kaina ban san mun shaku da Yaya Junaidu sosai ba, sai a wannan tafiyar tashi duk da gidan mu cike yake da jama’a ina kuma da al’amuran yi masu yawa kewar shi sosai na yi don kuwa mutam ne ma’abocin hakuri da juriya ga na kasa da shi, mu’amalla da shi kuwa mai dadi ne sosai, saboda komai na shi akwai ‘yanci mai yawa a cikin shi, saboda ya san yancin dan adam.
Yaya Junaidu yana cikin mutanen da na sha jin Ummna tana cewa ba za ta mance dawainiyar da suka yi mata da ni ba.
Ita da kanta tana mutunta shi, haka nan kasancewar shi dan’wan Baba ya sanya shi ya zamo mai karfi sosai a wurin Baban, kuma yardajjen shi, mafi yawancm al’amuran da yakan wakilta a yi mishi in dai akan dukiya ne to shi yake dorawa a kai.
Mu’amallar shi da Baba mai karfi ce kwarai, ban da zamowar shi shi ne mai zuwa ya dauko shi in zai zo gida, babu kan yarda wani ya tuka shi ne kawai in dai yana gari a lokacin da yaya Junaidu baya nan ko yana wurin aiki, shi din mutum ne mai cikar halitta yana matukar kama da Yaya Almu, ma’abocin yi ado ne, yana kuma kyau da adon.
Mutum ne shi da bai cika son hayaniya ba, sai dai yakan yi magana cikin nutsuwa, gashi da ilimi don ba na mantawa a ranar da baba ya dawo gida na kai mishi sakamakona na gama Secondary ya karba ya gani .ya yi ta yabon kokarina, wanda ba haka Yaya Almu ya so ba, da ya miko mini takardar cewa ya yi;
“Maza je ki ki Boye abincki kin yi kokari kar ki yarda ki bari Junaidu ya gane miki ita, don kar ya yi miki ba daidai ba, kin san shi a lokacin da va gama karatun shi na Secondary Excellent bakwai da Credit biyu ya fito da su.”
Ya juya wurin Junaidu cikin fara’a ya ce mishi, “Baka ga takardar ta ba ko?” Ya ce mishi,
“Na gani Baba sai dai ban lura da abin da yake cikinta ba.” Yana dariya ya ce, “Yauwa to ka kyauta da ka yi hakan, ka kuma yi dabara kwarai.”
Ni kaina na san Yaya Junaidu yana cikin yayyena da na ke so, nake girmamawa, nake kuma yawan mu’amalla da su zan iya cewa ma mu’amalla da shi kan yi mini dadi akan da Yaya Almu, saboda shi Yaya Almu akwai tsoro mai yawa a tsakanina da shi, sai kuwa Yaya Junaidu komai na shi mai sauki ne babu fada, babu zare ido balle ga yin barazana ko duka.