Skip to content
Part 1 of 49 in the Series Wace Ce Ni? by Hafsat C. Sodangi

Godiya

(Godiya ta har kullum ga Ubangijinmu Allahu take, masanin abin da yake boye da wanda yake bayyane. Mai kowa, mai komai masanin yau da gobe, gwani mai hikima cikin dukkan aiyukan shi, wanda ya yi wa dan adam baiwar da ya bambanta shi da sauran dabbobi ta hanyar yin furuci ya kuma sanar da shi abin da bai sani ba. Tsira da amincin Allah ya tabbata ga Annabin karshe Manzon da ya kawowa duniya shiriya. Annabin Raharna Muhammad (S.A.W.) da Aiayycnsa da Sahabbansa da wadanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar karshe, wato ranar Alkiyama.)

Cikin kwalliya nake sosai, idan n ace kwalliya kuwa to ina nufin irin ta ‘yan matan zamani, gwanayen yin kwalliyar ta burgewa, masu kuma abin yin kwalliyar.

Tun ina yar karamata kwarai mutanen dasuka sanni suka san ni din gwanace kwarai wajentsara kwalliya ta yi kyau, to balle kuma yanzu dana zama cikakkiyar budurwa.

Taku daidai nake yi cikin nutsuwar da ke kara bayyanar da gwanintar iya tafiyata. Lokacin da na shigo cikin fence house’ din mu, wurin da Baba ya killace don kiwon dawakan shi.

Kayataccen wuri ne sosai da aka katange shi da farin katako. Harabar shi kuma aka mamaye shi da koriyar ciyawar lawn ta yi kore shar babu komai a wurin illa skable din daure dawakai, sai ko ginin katako da Baba ya yi ya kawata shi dakayan alatu, don hutawa a cikin shi.

Ina shiga wurin na hango Yaya Almu can nesa sanye cikin fararen kaya, yana rike da sprinkler a hannunshi, yana fesawa ‘yan shukokin da ke wurin ruwa, saboda kasancewar mu cikin lokacin rani.

Can wurin shi na nufa ina tafiyata a hankali don haka lokaci mai tsawo na dauka kafin in isa wurin shi, saboda kasancewarwurin mai girma ne sosai.

“Sannu da aiki.” Yaya Almu ya juya a hankali ya kalleni cikin nutsuwa kafin ya maida kanshi ga kallon agogon da ke daure a hannunshi. Ya sake dago ido ya dube ni.

“Ke kam kin yi sa’a komai na ki a makare kike yin shi dubi lokaci sai yanzu kika fito?”

Na dan ja baya kadan saboda irin kallon da yake yi mini. A hankali cikin sanyin murya na ce mishi.

“Yanzun ma fa fitowa kawai na yi, amma ko karyawa ban yi ba.”

Da sauri ya ce, “Eh ai yana da kyau. Haka din yana da kyau, sanyin jikin ki ya rinka ja miki dalilin rashin karyawa a gida, tun da ke ba ki san ki tashi da wuri ki yi abin da ya daçe ki yi ba, akan komai sai kin makara je ki sai kin dawo.”

Na yi maza na kauce daga wurin feshin da yake shirin jika ni, na ce mishi, “Ai zuwa na yi da in ce ko za ka sauke nine?”

Ya ci gaba da aikin shi yana tambayata, “Ina su Junaidu?”

Na ce, “Ai.babu. kowa a gidan duk sun tafi.”

 Bai bata lokaci ba ya kashe sprinkler din ya biyo bayana ya wuce ni ban iya yin komai akan lokaci ba, in mutum yana da abin yi ai ba zai yiwu ya iya hakurin jirana ba, in dai shi ma ba zama mai latti irina zai yi ba.

Kan in fito waje tuni ya tayar da motar da na wuce a gindin bishiyar da ke bakin get din shiga fence house din Toyota Camry 2008 model, fara sol hakan nan kayayyakin da ke cikinta.

Ina zama a cikin motar ya hau kan hanya har lokaci bai daina mitar da yake yi ba.

Jaddada mini muhimmancin yin abu akan iokaci yake yi.

“Kin san ma ma’anar iokaci kuwa?”

Ya dan waiwayo ya kalleni. Ban kalle shi ba, balle in tanka mishi.

“Yana da kyau a ce mutum yana kiyaye muhimmancin lokacin shi, ya rinka amfani da shi yadda ya dace ya rimka barin shi yana tafiya haka kawai ba, ba tare da ya yi wani abin da ya amfanu a cikin shi ba.

Ki yi kokari kina amfani da lokacin ki a yarda ya dace, sannan kar ki yarda ki saba da yin latti a kan komai ko kuma yawan saba alkawura.”

Na yi kokari na bude bakina na ce mishi, To Yaya afuwan na gode.”

Gaskiya ne Yaya Almu yana daya daga cikin mutanen da suke kiyaye lokutansu, suke amfani da su a yadda ya dace.

Kullum ka shiga dakin shi matukar ya gama komai na wunin ranar yana shirin kwanciya, to za ka same shi ne yana rubuta abubuwan da zai yi a wuni mai biye daga karfe kaza zuwa kaza, zan yi abu kaza da kaza, ko kuma za ni wuri kaza da kaza.

Zai yi kuma wuya kwarai a ce bai yi hakan ba. Ma’abocin yawan istigifari da yawan salatin Annabin Rahama (S.A.W.). a kowanne lokaci ko da kuwa wani aiki yake yi in dai ba magana da wani yake yi ba. In ma maganar yake yi yana gama ta za ka ji ya koma kan abin da ya saba yi.

Wani irin mutum da hira ba ta dame shi ba, ya kan yi magana ne a lokacin da hakan ya zama mishi dole, don ko ni ce na saki baki ina ta surutu ya rinka kallon kenan.

Sau da yawa kuma idan na gaya mishi wata magana zuba mini ido yake yi cikin nazari sai in na ce mishi

Yaya Almu ba ka yarda da ni ba ne? Sai ya dan motsa kafada tare da tabe baki ya ce, ba zan iya fadin hakan ba, tun da ban saba kama ki da laifin yin karya ba, sai dai kina da alamomin hakan, don kuwa surutu ya yi miki yawa.

Shi mutum kuwa in ba ki sani ba an hore shi ne da fadin alkhairi ko kuma ya kama bakin shi ya yi shiru, amma ba ya yi ta sakin magana ratata-ratata ba.

Har muka iso hukumar zabe inda aka toro ni zaman sanin makamar aiki, saboda kasancewata daliba mai karatun diploma a Federal Poly garin mu. Yaya Almu bai daina yi mini nasiha akan mubimmancin lokaci ba, ta hanyar kawo mini ayoyi da hadisi da suka jaddada muhimmancin lokacin, ni kam kullum cikin mamakin Yaya Almu nake, musamman in ji shi yana karatun alkur’ani mai girma ko yana kawo hadisi da maganganun manyan malaman addini. Sai in ce oh oh! Ko yaushe ya samu damar yin karatun addini haka? Oho.

Tun da ni dai na san Yaya Almu ne bayan na yi wayo, shekarun kuruciyar shi gaba daya a London ya yi su. Can Baba ya kai shi karatu tun sa’ad da ya gama primary school dinshi, bai kuma dawo gida ba sai da ya kammala karatun shi.

Yaya Almu wana ne da muke uba daya.

Mutane da yawa suna yabon shi, saboda tsayuwar shi da kuma kulawar shi kan al’amari na.

Ni kuwa nake kallon abin da yake mini din a matsayin takura, ko kuma ma in ce yan ubanci irin na dan uba, don kuwa kafin dawowar shi gida cin karena nake yi babu babbaka, in ci duniya, kuma da tsinke.

Shi ne ya dawo ya takura mini ya hanani rawar gaban hantsi, ya tasani a gaba da yawan fada da yawan tsawa da yawan zare ido, da yawan fadin ke nutsu.

Ga barazanar duka a kowanne lokaci, saboda ni wai ya je ya sayi wata sharbebiyar dorina, irin ta Baba maigadin gidan mu da yake fito da ita kowanne lokaci ya sharbaneta da mai ya shanyata ta sha rana kafin ya dauketa ya je ya rataye ta a dakin shi wai don ranar da zai bugeni da ita, in ji jiki.

Yaya Almu ne ya dawo ya same ni ina tsakiyar zuba shagwabata ya katse mini hakan cikin kasa da makonni biyu kacal da dawowar shi.

Kasancewar shi mutum daya tal da Ummana ba ta daga ido ta kalli abin da ya yi mini, balle tambaye shi dalilin yin hakan ya bashi cikakkiyar dama ta shiga harkokin rayuwata ya takura su.

Kafin dawowar na shi ni din shagwababbiyar yarinya ce takin kárawa, gashi dai ni kadai ce yar da Ummana ta haife, ni kadai ce kuma ya maçe a wurin Baba.

Gani kuma da sunan mahaifiyar shi, kowa a gidan mu gudun bacin raina yake yi, don kuwa ya san bacin ran nawa yana nufin bacin ran Umma, don kuwa a fili take fada ba ta boye ba da batawa Adawiyya rai gara ita a zo inda take a bata mata.

Wannan dalili ya sa kowa yake kaffa-kaffa da ni, saboda an san abin da bacin ran Umma yake nufi a gidan nan.

Yau na zama zagin Baba, ba komai ba ne a wurina hakan nan in na ga dama ina iya warware yan yatsuna in wanke fuskar na gaba da ni da mari, yin hakan ba wani abu ba ne in an kai kara a wurin Umma hakuri take bayarwa ta ce kuruciya ce.

Wata rana ko da kudi aka ce ta yin hakan ba za ta yi ba, don ta yi hankali.

Hakan nan da wayona na san Umma tana goyani ta kuma ba ni abinci a baki.

Ina cikin wannan sha’anin ne ya dawo ya same ni bai kuma yi kwana goma sha hudu a gidan ba sai da ya dauke ni daga gidan ya kai ni makarantar secondary yan mata ta kwana dama kuma ya zo ya same ni ne ina J.S.S 1, ya kuma yi hakan ne ba tare da ya shawarci kowa ba, bai kuma sanar da makarantar da ya kai nin ba, balle a samu damar kai mini ziyara.

Yana kai ni mamakarantar nan nan tsinci kaina cikin wata irin matsananciyar rayuwar da ban taba mafarkin ana yin irin ta ba.

Ni da na saba tashi daga barcina Baba Talatu, ko Umma wata cikin su ne za ta yi mini brush ta yi mini wanka, ta dauro mini alwala, sannan in fita in zo in yi sallah, a shafa mini mai a taya ni sanya uniform dina, a kawo mini abin karyawana in karya, direban da yake kai yaran gidanmu makaranta ya yi ta zirga-zirgar neman in fito in ban ga dama ba in ce ni ban gama ba.

Umma ta ce mishi kai je ka in ta gama za a kawo ta, wata rana a kai ni, wata rana kuwa in ce ba za ni ba, in hau gado in yi kwanciyata da uniform din a jikina ina kallon finafinan yara.

Shi ne wai Yaya Almu ya dauko ni ya zo ya jefar da ni a wannan fankaceciyar makarantar da kowa ta kan shi take yi.

Wuni nake yi ina kukan bakin ciki da rashin sanin abin yi, tun ina bai wa yara tausayi su taru suna ba ni hakuri sai suka koma cewa ai sai ki yi, ta yi har sarkin kuka ya zo ya same ki.

Da yake kinga wata wacce ba daga gida ta fito ta zo nan ba da za ki tasa mu a gaba da kuka kowanne lokaci in ba ki sani ba mu gaya miki muma duk iyaye ne da mu suna son mu kuma suka kawo mu, ba ke kadaice mai iyaye ba.

Da abu ya kai matuka ma suna ganin hawaye sun soma zubowa daga idanuna za su watse su ba ni wuri, suna fadin maiya in ba ki daina kukan nan ba sai mamanki da babanki sun mutu kya yi kukan mai dalili.

Wannan kalma ta su ita ce ta yi matukar razanani ta yi dalilin da na daina kuka, na koma zaman bakin ciki da damuwa da kunci da yunwa.

Ina cikin wannan halin ne har ranar ziyara ta zo Yaya Almu ya kawo mini ziyara yana sanye da fararen kaya kaftani da wandonsu, sun yi matukar karbar shi.

Rike hannuna ya yi ya jani ya kai ni cikin motar da ya zo a cikinta wacce take ta kanshi saboda ta dace da samun ma’abocin tsabta.

Tasa ni a gaba ya yi yana yi mini kalamai, saboda irin kukan da na rinka yi mishi.

“Hakuri kawai za ki yi, ya zame mini dole ne kawai in yi miki hakan, saboda ba zai yiwu in barki ki girma cikin yanayin da na same ki ba, in na yi miki hakan ban yi wa kainaa adalci ba, ke ma kuma ban yi miki ba.

Hakan nan ban yi wa Baba ba, ke din kina bukatar zama jaruma ne, saboda al’amuran da ke gabanki ki zama wacce wadansu za su dogara da ke, don tsayuwar su ba wacce ba za ta iya dogaro da kanta ba, komai sai an yi mata.

Ki zama wacce tasan darajar dan adam da girman shi, ba wacce take taka shi a duk lokacin da ta ga dama ba.

Wannan dalili ne kawai ya sa na rabaki da gida, don haka ki yi hakuri ki saki ranki, ki kwantar da hankalinki, ki koyi mu’amallah da mutanen da kika samu kan ki a cikin su, don ki ji dadin rayuwa tare da su.”

Har ya yi maganganun shi ya gama ban tanka mishi ba, ban kuma dainan kukan da nake yin ba.

“Ina kawayenki?”

Ya tambaye ni yana kallona cikin nutsuwa duk da bai furta ba, tsananin ramar da ya gani a tare da ni ya ba shi tsoro da tausayi.

“Ki yi kawaye ‘yan guda biyu ko uku za su taimake ki ki fita daga cikin damuwa mai yawa kin ji?”

Ban amsa mishi ba, ya ci gaba da magana.

“Ki maida hankalin ki akan karatunki, ki shiga duk harkokin da ake yi a makaranta za ki ji dadi yanzu mu je in kai miki kayayyakin amfanin da na zo miki da su.”

Ban tankaba, ban kuma musa mishi ba.

Shake bayan but din shi ya yi da kayayyakin amfani gaba daya aka jide su aka shirya mini su a lokata da lokar yarinyar nan da ke kusa da ni.

Asabe Aliyu, duk yaran da muke daki daya kuma sai da ya ba su sabulai da omo da kayan tea, sannan ya kama hanya ya tafi ya bar ni ina ta faman kukan takaici wanda in ban da tsananin tsoron shi da nake ji da rike shi na yi na ce mishi ya kai ni kawai wurin Ummana.

Wace Ce Ni? 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×